Showing 111001 words to 114000 words out of 117506 words
Chapter 38 - IGIYAR RAYUWA Hausa Novels Complete Document.pdf
Unknown
18 May 2025
8453
ma baya son ji bare a kai ga
sawa a bakinshi da sunan sha Amma har yanzu d'an bakin da yayi mixing da asalin red lips
d'inshi na nan, murjewa da kyau kam ya ninka na da sbd kulawar da yake samu daga
qalbeenshi hakan ke sa su fad'a akan 'yan matan dake binshi.
Little na nan tana karatunta yayinda Abba ya sa su nabeel makarantansu class d'insu d'aya
inda suka kasance kaman wasu triplet gasu ba laifi Allah ya basu ilimi, Abul de har yanzu ba
abinda yakeyi daga bacci se kallo a sabuwar system d'inshi da Abba ya aiko mishi don har
yanzu basu dawo ba, kuma yaki fad'a musu ko aikin idon dada anyi nasara ko ba'a yi ba.
Tafe take cikin sauri sbd makara da tayi ta san zuwa yanzu babynta ya dawo be cika rigata
dawowa ba itama ta fi so ta ringa rigashin sbd shirya wasu abubuwan kan ya dawo amma yau
gashi exams ya d'an Chaza mata kai bata fito da wuri ba har lokaci ya wuce sossai ga go slow
da ta gamu da shi a hanya.
A hanzarce tayi horn gateman ya bud'e mata da mamaki take kallon tsakar gidan ganin ba
motanshi a parking space time ta kalla tuni ya kamata ace ya tashi daga office da mamaki ta
sauka ta rufe motanta ta shige cikin gidan a parlor ta samu little da gudu tazo tayi mata oyoyo
rungume ta tayi tana cewa "sannu pretty yau ba karatun yamma ke kad'ai a gidan" murmushi
little tayi tace "kin kira malam d'in kinji ya jikinshi mommy?" Khairi tace "wallahi ban samu
kiranshi ba kinga bari nayi wanka na ci abinci se na kirashi" little tace "Ohk mommy se kin fito
zan baki labarin abunda duk ya faru a school" khairi na murmushi ta haura sama har tayi wanka
ta shirya cikin riga armless wadda ko cibinta be kai ba yellow da jeans blue ta sauko musharraf
be dawo ba.
Abun ya matukar d'aure mata Kai ta kira kusan sau biyar kan ta gama Shiri wayanshi switch off,
zama tayi tana jin hiran little ba tare da tana fahimta ba ko abinci bata yi niyyan ci ba, haka suka
zauna har magrib kowa ya mike sukaje sukayi sallah a d'aki ta zauna tayi karatunta har lokacin
isha tayi adu'o'inta tare da kiran layin shi ya shiga ba'a d'aga ba, sallah tayi ta idar tare da
saukowa ta leka d'akin little taga tana sallah ta dawo parlor ta zauna kenan taji an turo kofa.
Da sauri ta mike ganin shine tace "sannu da dawowa" tare da karasawa tayi hugging d'inshi
shima rungumeta yayi se yaga tayi saurin janyewa yace "sorry baki ganni ba, ba kuma ki jini ba
wallahi munje wani office dinner ne da ma'aikatanmu a gidan wani friend dinmu and my phone
was slipped from my hand ya dena yi kwata kwata, se Ina dawowan nan na biya na sayi wata".
Ba tare da ta yarda ba tace "Ohk" tare da kar'ban brief case d'inshi ta haura sama ta barshi da
'yarshi tana welcoming d'inshi, da ido ya bi bayanta se yaga kamar bata yarda da abinda yace
ba haka ya haura de bayan ya had'a little da chocolates da ya saya mata a hanya, a bakin toilet
ya ganta tana share hannunta da karamin towel ba tare da ta kalleshi ba tace "ruwa na toilet" a
d'an dame yace "wai qalbee me ya faru ne? Look am sorry for not informing yhu shima kuma
with reason am sorry plz".
Murmushi kawai ta mishi ya shige bayin ba tare da ya yarda ta aminta dashi ba, yana shiga ta
ga wayanshi da ya ajiye a kan dressing mirror yayi haske, haka kawai ta ji tana son gani ta mike
taje ta danna fuskan "I'm very sure zuwa yanzu ka isa gida, can I call yhu plz baby? am missing
you" jiri ne taji yana neman kada ita ta sauri ta dafa jikin mirror ta zauna tana jin wani tension na
building cikin kanta da kirjinta tashin hankali kenan shi yasa ya jima? Dalilin kenan da ta ji yana
kamshin turaren da ba nashi ba?.
Kuka ta saka sossai, wani irin bala'e'en kishi ne ke cinta bata ta'ba zaton tana da kishi haka ba
se yau tashin hankali mijinta ya fara dare a waje sbd wata? Ta kai five minutes tana kuka kan
taji motsin fitowanshi da sauri ta mike ta kwanta akan gado tare da juya ma kofan toilet baya
tana ci gaba da hawaye, kallon bayanta yayi na mintuna kan ya sauke ajiyar zuciya ba haka ta
saba mishi ba ya kamata tazo ta tare shi ta shafa mishi mai ta taimaka mishi ya sa kaya amma
tana kwance.
Shafa mai yayi ya sa kayan baccinshi cotton trouser da riganshi me igiyar d'aurewa kawai daga
tsakiya gabad'aya gaban kirjinshi a bud'e yake kara feshe turare yayi.
gadon ya hau tare da juyota a take hankalinshi yayi matukar tashi ganin hawaye na gangara a
idonta a rud'e yace "qalbee me ya faru? Me yasa ki kuka?" Se kuwa ta fashe mishi da kuka me
sauti rungume ta yayi a kirjinshi yana shafa mata baya har tayi ta koshi idonshi a runtse Allah
kad'ai ya san me yake ji, ganin kukan yaki lafawa ne yasa shi d'agota tare da had'e bakinsu
special lallashi ya dinga mata har seda ya ga kukan ya d'auke chak dukda kokarin tura shi da
take yaki sakinta sam.
Yana saketa ta mike da sauri tayi bayi ta dinga tofar da nyau ranshi ya fara 'baci da wannan
sabon d'abi'a nata shine ze yi kissing d'inta ta tofar da nyau? Kwanciya yayi ya rufe ido da nufin
fita harkanta tunda haka ta za'ba, yana ji ta dawo ta kwanta a chan karshen gadon haka suka
kwanta ta jima sossai tana juye juye shima yana kwance Shiru be tanka mata ba dukda ba
bacci ya yi ba, yana ji ta mike da fita da alamu duba little taje yi, Ai ko hakan ne seda ta
tattabatar ta kwanta kan ta hauro ta chanza zuwa kayan bacci ta koma ta kwanta Shiru.
Har misalin shabiyu da rabi ba wadda ya iya bacci a cikinsu don basu saba irin wannan fad'an
ba tunda suka shirya basu ta'ba 'batawa sun kwana ba'a jikin juna ba, ganin kaman yayi bacci
yasa ta mike ta zauna ta had'a kai da gwiwa tana me ci gaba da kukanta sossai yayi kokarin
share ta amma sam ya kasa hakan yasa shima mikewa yayi ya zauna cikin taushin murya yace
"ummulkhair" d'ago kai tayi dukda baya kallon fuskanta sbd kashe wuta da tayi tun kan ta
kwanta amma ya tabbatar kuka take yi.
"Gayamin plz me na miki da zafi haka? Ko kina tunanin zan fara miki karya ne a zamantakewar
mu abunda ban ta'ba miki ba?" Shiru tayi tana shesheka kaman baza tayi magana ba kuma se
tace "yhu never lied to me but I didn't believe what you said earlier, kana smelling different
perfume ba naka ba, naji hakan ne a sanda nayi hugging d'inki shigowarka and".
Se ta mike ta je gaban mirror ta d'uko sabuwar wayan nan ko samun ya duba da kyau be yi ba,
ta kunna hasken har yanzu sakon na nan ta kawo mishi ta kunna mishi fuskan wayan kar'ba
yayi ya karanta da sauri ya mike tsugunne akan gadon tare da sa hannu ya kunna hasken
d'akin yadda ze kalleta da kyau yace "I swear to God ban san wacece wannan ba, kin san ba
yadda zanyi in miki rantsuwa akan karya ko to wallahi ban santa ba sannan kuma turaren da
kika jin nan.
Nuruddeen ne ya saya yace inji kamshin naki shine ya fesa min a kirji ban bari ya karasa ba na
ture hannunshi wallahi ba abinda kike zato bane haba ummulkhair kin 'bata min rai banyi zina
Ina saurayi ba banyi bayan abunda surrayyah ta min ba, banyi bayan fitowana prison ba se
yanzu da nake tare da masoyiyata, abin alfahari na, uwar 'ya'ya na?" Shiru tayi kanta kasa yace
"In baki yarda ba lemme call him tunda ba mata yake dashi ba" wayan ya bud'e ya fara
dannawa da sauri ta rike hannunshi In low tune tace "am sorry".
Rungume ta yayi suka sauke ajiyar zuciya a tare cikin kunnenta yace "kar ki kara plz bana so,
bana son zargi ya dinga shiga tsakanin mu sbd yana 'bata aure, kin kuwa san yadda na tsani
zina to tun daga randa na kalli mahaifina akan......" da sauri ta had'e bakinsu bata so sam taji
zancen sbd duk waenda sukayin suna tare da mahallicinsu bata so sam ya dinga aibanta
mahaifinshi bata yarda In har a gabanta ne.
Seda suka farantawa juna sukayi wanka kan suka dawo suka kwanta a manne da juna kaman
zasu had'iye juna, washegari da safe aka sanar da su haihuwan nurriyyah inda ta samu d'a
namiji aiko khairi tace zasu zo tunda ranar Monday zata gama last papper d'inta na first
semester level 200, sati uku ne hutun Bayan sun gama wayan ne taga kiran dada.
'Dagawa tayi suka gaisa take tambayarta Abba tace ya fita da turanci da mamaki khairi tace
"dada kaman turanci naji kinyi?" Dada tayi saurin cewa "nop hausa ne, na san Monday zaki
gama paper in ba matsala ki roki mijinki zamu tafi taraba Abbanku ya matsa akan na komawa
mahaifina watakil yanzu gaskiya tayi halinta" Khairi tace "Toh zan gwada tambayarshi Allah ya
sa ya amince, da su nasreen?" Tace "a'a kin san tsarin makarantanku ba d'aya ba zamu dawo
Wednesday mubi jirgin Adamawa se mu karasa jalingo a mota".
Khairi tace "sede tafiyanmu inaga zeyi daban daban sbd nuriyyah ta haihu yau da safe zamu
tafi gomben watakil Tuesday" dada tace "masha Allah, Allah ya raya ya d'ayyaba, me ta samu?"
Khairi tace "namiji" dada tace "d'ayyib zan kira hajiya fatima In mata barka, zan kira me jegon
ma, muma wucewa be kama mu ba zamu shigo gomben kafin suna in shaa Allahu se mu wuce
gabad'aya tare" sallama sukayi.
Musharraf dake tsaye a gefenta yana had'a tea duk wayan da sukayin a kunnenshi sbd a
speaker wayan yake yace "gaskiya ya kamata ku waiwayi gida haka shekaru dayawa se muje
tare zan d'auki leave na two weeks kinga hutun su little ma three weeks ne tafiyan yazo a
daidai" Kai ta gyad'a duk fargabanta maganan mahaifin dada ne na ze tsine mata duk randa ya
kuma ganinta kofan gidanshi da kuma tuna irin rantsuwar da mahaifinta yayi kan fitowarsu Allah
sarki Allah ya ji kanka Abba, ko ya rayuwan su hauwa? Ta'be baki tayi suka ci gaba da abunda
sukeyi.
Sunday suka had'e kayansu tsab trolley uku kowa da nashi Monday tayi last paper d'inta
tuesday suka kama hanyar gombe a mota sukayi tafiyan wannan karon duk khairi ta galabaita
ko don bata saba tafiya me nisa irin haka a mota bane se Allah, sun samu tarba sossai daga
wurin momma gidan a cike da 'yan barka da shike tun kan nuriyyahn ta haihu ta dawo gidan da
zama sbd matsalolin da cikin yayi ta bata.
Khairi kam kaman ta had'iye yaron, suna zaune da musharraf suna ta kallon yaron gwanin
sha'awa da sauri taga ya mike ya fita chan kuma ya dawo ranshi ba daad'i kwata kwata don
fuskan nan a had'e yana zama Anty rabi da Hajiya zulai tare da Afreen da kuma sufyan suka
shigo, uncle Ahmad da uncle nasir biye da su, duk zama sukayi khairi ta zame kasa ta gaida su
Haka musharraf amma shi Uncle's din shi kad'ai ya gaisar ya koma yayi zamanshi tare da
gaidasu Anty rabi a haka, ta'be baki tayi ba tare da ta amsa ba ta mike ta zo ta kar'bi yaron, tare
da satan kallon su Uncle Ahmad dake gaisawa da su momma tace tana kallon hajiya zulai
"kinga gara na kar'beshi kar ta hallakashi sbd bakin ciki abinka da juya" hajiya zulai tace "Ai ko
de kinga irin abinda ake gayawa su Alhj suka ki ji gashi ko wacce da akayi aurensu tare na
shirin juyewa yau ko gobe amma banda ita da ko alamun abun arzikin babu ace mutum be
sonka tsakani da Allah dukiyarka yake bukata aki yarda, banza juya" tassssss suka ji saukar
mari, a razane kowa ya waigo zuwa inda suke. To fah
Alhamdulillah thanks for the prayer í ½í¹�
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—
       IGIYAR RAYUWAí ½í¸
Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—
í ½í²«ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
    'Yar mutan Adamawa
Las Las
Pageâž¡ï¸�1ï¸�⃣0ï¸�⃣0ï¸�⃣▶ï¸�í ½í´ší ½í´ší ½í´š
í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—
Gabad'aya parlorn mikewa sukayi ganin yadda yake 'bari kamar mazari dama ranshi a 'bace
yake ga maganganun hajiya zulai da Anty Rabi'ah yau ba don matar uncle Ahmad bace, ba don
yana ganin girman uncle Ahmad fiye da sauran uncles dinshi ba, ba don ba tarbiyar momma ba
kenan da ba abinda ze hanashi yiwa matar dukan mutuwa, shiyasa ya sauke hannunshin akan
d'anta da dama shine silar 'bacin ranshi tun farko, uncle nasir ne yace "musharraf wai lafiyanka
kuwa?" Momma tace "me ya maka haka?" Hararan da sufyan ke mishi ne yake kara tunzura shi
hakan yasa shi had'ashi da gini ya shakeshi da sauri khairi ta dafa hannunshi ganin yadda
hajiya zulai ke ihun ze kashe mata d'a.
Momma ta karaso ta d'aga hannu da niyyar sauke mishi mari da hanzari khairi ta shiga marin ya
sauka a fuskanta har seda ta zube a kasa tsabar karfin marin, ido ta runtse yanzu da haka
marin ze sauka a fuskanshi inaa ta san komai musharraf yayi akwai dalili tana kyautata zaton
ba Haka kawai ze hau dukan shi ba, da azama musharraf ya sake Sufyan yana d'agota kallon
cikin idanunshi da yayi ja tayi ta runtse ido se hawaye da kirjinshi ya had'ata yana kallon
momma da ta tsaya kaman mutum mutumi haka su uncle nasir ma karfin halin khairi suke
jinjinawa.
A hankali ya fara magana cikin rawar murya ya bada labarin abunda aka turamishi ran aurenshi
wadda yayi sanadiyar kwanciyanshi asibiti ya kara da irin zaman da yayi da khairi kan ya zo ya
gane karya ne da alqawarin da ya mata ya d'aura da "na shafe wata shidda chur Ina neman me
wannan numbern, har experts a harkan tracking fiye da mutum hud'u na biya amma ba'ayi
nasara ba se yau a d'azu d'aya ya kira ni ya bani full details na wadda ya had'a hoton kuma
sunje sun sameshi da police inda ya amsa fault d'inshi ya kuma bada details na waenda suka
sa shi, and that turns out that sufyan ne ya biyashi don aikata hakan and wanchan munafukan
ya nuna Afreen ita ta zo har cikin gidan nan ta d'ad'auki qalbee hotuna daban daban" yana
shafa bayan khairi yace "am sorry qalbee na kasa cika alkawarinki sbd munanan kalaman da
iyayensu suke jefanki dashi" kallon su Hajiya zulai yayi yace "and yhu this is my first and last
warning Wallahi wallahi mata ta kara zagarmin mata se nayi mata abunda bata ta'ba tsamanni
ba, ku kuka hallici juyan? Ko ku kuka h......" "musharraf" momma ta kira shi In a whisper.
Shiru yayi tare da jan hannun matarshi suka fice daga parlorn, basu karasa fita ba suka ji
saukar mari har kusan kala hud'u, uncle nasir ne yake saukewa sufyan duk sanyinshi seda
ranshi ya 'baci yau haka ya rufe Afreen da duka wasu irin yara ne su, seda uncle Ahmad ya
gama dawowa daga suman tsayen da yayi kan ya kalli Hajiya zulai yace "ki tafi gidanku se na
neme ki" waro ido sufyan yayi tare da zubewa a wurin yace "kayi hakuri dad wallahi bazan kara
ba, karka hukunta mom akan abinda ba ita ta aikata ba na tuba" hararanshi uncle Ahmad yayi
kan ya juya ya fice momma de bata ce komai ba amma kallo d'aya ka mata zaka san ranta a
'bace yake haka su Amrah da mai jego ma se harara suke sakewa su afreen din, wato uncle
Ahmad ya san hukunta mahaifiyar sufyan ne kad'ai ze sa shi ladabta yayi nadamar gaskiya
sanin yadda yake kaunar mahaifiyar tashi, ita kuwa cikin kuka da ihu ta fice daga gidan, hajiya
rabi'ah ta rufa mata baya Afreen kuwa Uncle nasir yace da ita ze tafi zata ci me unguwan
garinsu a gidanshi cikin sacewar gwiwa sufyan ya mike ya fice, nan momma ta kira bappa ta
fad'a mishi duk abunda ya faru ta kuma tabbatar mata da hakan, inda bappa yayi alkawarin sa
taheer yaje har gidanta ya ci mata mutunci kuma shima ze kirata haka diddinsu ma, hakuri ya
dinga bata har taji kunya.
Bayan ta kashe suka zauna tattaunawan da su Amrah, a bakin gado ya ajiyeta shima ya zauna
hannunshi na kan yatsun momma da suka fito a kumatunta cikin kasa da murya da tsantar
damuwa yace "am so sorry qalbee, me yasa kika shiga? Dan Allah karki sake da na gani da
ban bari ba am sorry" murmushi khairi tayi tana kifa kanta akan kirjinshi tace "mind not hayatee,
bazan iya ganin wani abu ya ta'ba min lafiyanka ba da rai na da lafiyata In bari" zagaye
hannunshi yayi zuwa cikinta yace "Ina sonki" murmushi me sauti tayi tace "same here hayatee".
Anan suka shantake, kwana uku da zuwansu su dada suka sauko Gombe ana washegari suna
kenan, tun washegarin barinsu Abujan suka diro, musharraf da khairi ne suka je taransu mota
biyu sukayi amma gidan inna zasu sauka shi kuma Abba a