Showing 45001 words to 48000 words out of 117506 words

Chapter 16 - IGIYAR RAYUWA Hausa Novels Complete Document.pdf

Unknown   

18 May 2025

8451

jin daad'i...........

Haka ta ci gaba da damun khairi da surutu har ta gama aikinta har zobon, a wani farin roba ta
sa ta sa a fridge, duk inda tayi little na bayanta, yarinyar ta shiga ranta sossai ta lura little dinma
na sonta...........

Bayan ta gama komai ta wanke duk abinda ta 'bata ta kuma goge kan kitchen island, gas

cooker da hot plate. little ta ja ta wai suje su zagaya gidan tunda bata san ko Ina a ciki ba, haka
ta bita suka dinga zagayawa har garden, sun jima sossai a chan kan suka wuce boysquaters
anan suka samu matar malam d'ahe inna laure  ita ke share share da goge goge a gidan da
sassafe take shiga tayi komai kan gari ya gama haske ta gama ta koma bata sake lekowa se
washegari...........

Gaisawa sukayi da khairi daga nan suka dawo cikin gida, a parlor suka samu momma tana
kallon khairi tace "wai sannu ummulkhairi naga har kin gama ayyukanki gabad'aya, harda zobo
kikayi na tabbatar wannan yarinyar ce ta saki yi dole"...........

Dariya kawai khairi tayi, momma tace "zaki iya tafiya, se ki d'ibar muku abincin a food flask, ya
sunan kannenkin?" Khairi tace "nabeel da nabeela" momma tace "twins ne" khairi tace "Eh"
momma tace "masha Allah ki duba store akwai gora se ki diba muku zobo zaki ga wani maroon
coolar me d'an miya a ciki da karamin basket se ki sa muku abincin a ciki"..........
Khairi tace "toh mun gode" ta mike taje ta sako musu, ta fito d'akin da aka bata ta shiga ta
d'auko jakanta ta fito d'ari biyu momma ta bata tayi kud'in napep godiya ta mata, tayiwa su
Amrah sallama har get little ta raka ta kan ta dawo...........

A natse take tafiya kaman me tausayin kasa kanta kasa kaman ance ta d'aga kai se idonta ya
fad'a cikin nashi ya sauya kaya daga manya zuwa kanana, milk jeans da maroon shirt me
guntun hannu kafanshi sanye da normal shoe na maza, zaune yake saman mota shi kad'ai
hannunshi rike da taba yana zuka............
"Subhanallah gentleman like him da shan taba? Be son lafiyan jikinshi ne?" A fili tayi maganan
tana ji mishi takaici da haushi ta tsani taban nan kai duk wani kayan maye ma, tsintar kanta tayi
da adu'ar Allah ya sa tabar kad'ai yake sha...........

Satar kallonshi tayi se taga shima ita yake kallo da sauri ta kawar da kai tana jin tafiyar na mata
wuya natsuwa na neman barinta tsabar karfin kwayar idonshi a kanta.........

Shi kuwa ko a jikinshi kallonta yake shi kad'ai ya san me yake karanta a jikinta, dukda ya ga ta
kasa tafiyar yadda ya kamata sabd kallon da yake mata hakan be hana shi ci gaba da kallonta
ba. Allah ya taimake ta se ga napep da sauri ta tsare ta shige tana sauke ajiyar zuciya, kau da
kanshi yayi ya ci gaba da shan tabanshi hankali kwance.............
Tafiyar mintuna a kalla 20 ya kawo ta gida, sauka tayi ta sallame shi ta shige gida, da gudu su
nabeel suka rungumeta suna mata oyoyo ajiye kayan hannunta tayi ta tarbe su da murna itama
tana tambayarsu ya school da lafiya suka amsa ta..........

Ta karasa tayiwa dada san da gida tana zama gefen taburman da take kai, nan ta fara ba Dada
labarin duk abinda ya faru a ranar duk labarin little ne da yadda yarinyar ta shiga ranta se
mutuncin mutanen gidan...........

Suna nan zaune suna labri har aka kira magrib suka mike sukayi sallah, yadda al'adarsu take
karatu ne bayan magrib hakan kuwa sukayi seda akayi isha suka ci abinci, khairi tayi wanke
wanke don akwai kwanukan abincin rana da su nabeel suka ci............

Ta shirya kwanukan momma a basket din ta Adana basuyi wani hira ba suka kwanta don kowa
ya gaji..........

Kwance yake kan gadon momma yana aikin  danna waya, turo kofan akayi d'ago kai yayi se
yaga momma ce tace "wai ni ka zo ka min bake bake a gado bayan ka san lokacin bacci na yayi
a kanka kake so in kwanta?"..........

Murmushi ya sake yana cewa "momma zan tafi jibi flight na 10 zan bi, if possible a rubuta duk
abinda babu gobe se nuriyyah suje su sayo, zan basu kudin shopping dinsu a goben ma"
momma tace "Ohk toh se da safe wannan kam, and Musharraf In kaje ka daure ka dinga cin
abinci plz In ka dawo bana jin daadin ganin yadda kake raman nan, ko de har yanzu kana sa
damuwa a ranka
ne?"............

Murmushin yake yayi yace "ko d'aya momma" jin yadda ya amsa mata a takaice yasa ta san be
son maganan shiru tayi ta kudurta a ranta a gobe ita da khairi zasu mishi danbun nama, donuts
da duk wani abinda ta san baze 'baci nan kusa ba ya tafi dashi kila ya taimaka mishi..........

Mikewa yayi yace "seda safe mother" tace "good night and kar a manta da alwala da kuma
adu'ar kwanciya yana murmushi ya fita a zuciyarshi yace se kace little?............

A parlor ya samu su nuriyyah nan ya fad'a musu gobe zasu je shopping ko wacce ta rubuta
abinda take so ze duba a goben, godiya suka mishi ya fice ba tare da ya amsa musu ba...........












#vote
#share
#comment

'Yar mutan Adamawa



🎗🎗🎗🎗🎗







                 IGIYAR RAYUWA😭







                                              🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

             'Yar mutan Adamawa

*wipe away the tears of the orphans in order to attain the pleasure of the most merciful and a
house in paradise*

Page➡�4�⃣4�⃣▶�4�⃣5�⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Washegari

Karfe bakwai da rabi dai dai yayiwa khairi a GRA, duk gidan ba wadda ya tashi bacci
kasancewar weekend ne, d'akin da aka sauketa ciki ta shiga ta ajiye bag dinta, tare da komawa

kitchen ta fara dube dube duk tunaninta ya tafi kan ko me zasu ci da safen? Tana d'aura
hannunta kan kitchen island se taji paper an d'aura karamin robbern tumeric a kai d'auka tayi ta
bud'e se taga an sa "kiyi pepper soup na kifi, za'aci da bread se kiyi tea but na soya beans"
gyad'a kai tayi kaman a wurin aka bata umarni tare da fara aikin.................
Cikin lokaci kankani ta gama tare da shiryawa a dining ta koma kitchen ta wanke duk abinda ta
'bata, tana share kitchen din taji zuciyarta ya buga gabanta ya fara fad'uwa da sauri ta juya se
kuwa idonta ya fad'a cikin nashi da sauri tayi kasa da kai tare da cewa "Ina kwana?" Kaman
baze amsa ba se kuma yace "Lafiya" tare da ci gaba da tsayuwarshi.............
Juyawa tayi ta ci gaba da goge kan gas se kuma taga kaman hakan be kyautu ba se ta juyo
tace cikin tsiririyar muryarta "ranka ya dade akwai abinda kake bukata ne?" Juya idonshi yayi
tare da ta'be baki yace "just coffee" Kai ta gyad'a ya juya ya fita, coffeen ta had'a mishi tare da
sa cup din kan karamin tray fari ta fita dashi a kan one seater ta Ganshi zaune se lokacin ta
samu zarafin kallonshi da kyau sbd kanshi dake kan waya...............

Sanye yake da jallabiya coffee color me guntun hannu da ya matukar amsar fatan jikinshi, duk
da be yi wanka ba amma kamshin shi duk ya cika parlorn, ganin ze d'ago yasa tayi saurin
karasowa ta janyo center table ta ajiye mishi, ko kallonta be yi ba har ta juya ta fice, komawa
tayi bakin aikinta Bayan ta gama goge gogen ta fice varender ta fara wanke mop din da tayi
anfani dashi bata hankara ba taji an rungume ta, juyowa tayi ta d'aga ta sama "morning cutie"
khairi na murmushi tace "morning pretty, ya kk?" Little tace "lafiya klau cutie Ina friends d'ina?"
Khairi tace "sun je islamiyya, ke bakya zuwa ne?" Little tace "a gida malam ke zuwa ya mana da
Anty miemie da Anty Amrah, ko wani weekend da yamma" kai khairi ta gyad'a tace "wa ya miki
wanka?"...............

Little tace "momma tare muka sauko ma she's at the sitting room" khairi ta ajiyeta a kasa tare
da kama hannunta suka fito, cikin ladabi ta gaida momma nan ta shaida mata ayyukan dake
gabansu yau, da kai kawai khairi ta amsa, se misalin karfe goma su Amrah suka fita da,
gabad'ayansu har little, da su salima.............
Ba sune suka dawo ba se azahar sayyaya kam sossai sukayi, a lokacin khairi ta jima da gama
abincin rana har tayi donuts, naman ta ma yana wuta, da gudu little tayi kitchen da leda a
hannunta "oyoyo cutie" khairi na murmushi tace "oyoyo kun dawo?" Little tace "yes cutie gashi
na sayo miki tsarabar chocolate" khairi tace "aiko na gode" bata fiddo daga leda ba kawai
lekawa tayi murmushi shimfid'e a fuskanta, bata kai ga magana ba taji momma na
kiranta.................

Fitowa sukayi inda momma ta bata umarnin tattare kayayyakin kitchen ta kaisu wurin zamansu
d'iban sayayyan ta fara da kad'an kad'an har ta gama, yau kam bata gama aikinta da wuri ba
sam sbd ayyukan da suka mata yawa se bayan magrib ta gama goge kitchen a gurguje ta koma
d'akin da yanzu ya zama nata duk da ba kwana takeyi a cikinshi ba, ta d'auko bag dinta ta
fito...............

Momma dake zaune parlor ita da su Amrah da little tace "sannu khairi yau kam Kin sha aiki,
gashi har dare ya miki bari inyi magana da driver se ya mayar dake gida sbd baza ki samu
napep da daren nan a unguwan nan ba" kan khairi kasa tace "Toh na gode momma" little tace
"Ayyah momma tunda da driver za'a kuma daga chan nan ze dawo In bisu mu dawo da driver?"
Amrah tayi saurin cewa "Eh Allah nima zanje" momma tace "Toh shikenan kuje se kun
dawo"................

Da gudu Amrah taje ta d'auko gyalenta ta gangaro don ita kam Allah ya d'aura mata son khairi
ba kad'an ba, Jan hannunta tayi little ta d'auki basket din abincinsu suka fito suka wuce, har
kofan gida khairi tayi mishi kwatance yana parking suka fito Amrah tacewa drivern "Dan Allah
bari mu gaishe su mu zo baba Adamu" yana murmushi yace "toh 'yata" sossai yake jin daad'in
aiki da su momma sbd mutuncinsu sam basa rena na kasa dasu, dukda a karkashinsu yake
kuma motarsu amma se sun had'a shi da Allah akan aikinshi.............

Khairi na sallama nabeel da nabeela suka taso da gudu suna mata oyoyo itama rungume su
tayi na mintuna kan ta sake su tana cewa "ga friend na maku" wara ido sukayi suna kallon Little
dake makale da hannun khairi, nabeel ne ya fara cewa "hi" se nabeela ta fad'a murmushi little
tayi tace "hello twins kuma kuna da kyau kaman cutie amma baku kaita ba, sunana Zarah and
yhu?" Nabeel yace "am nabeel" nabeela tace "nabeela"...........

Amrah ce da ta gaji da tsayuwa tace "hi twins I'm Anty Amrah Adda khairi's best friend" waro ido
sukayi har khairi kan suka fashe da dariya yayinda khairi ke murmushi, shagwa'be fuska Amrah
tayi tace "au ni ba kawar ki bace?" Khairi tace "babba ma kuwa" nabeel yace "but Adda sulaimi
min andi"(Adda sulaimi muka sani)"............
Har khairi zatace bata jin fulatanci se ta tuna jiya taji little nayi, Amrah tace "ha toi Adda sulaimi
mai woni?"(a Ina Adda sulaimin take?) nabeela tace "ha jalingo"(a jalingo) Amrah tace "Toh
kunga wadda yake nan dashi akeyi nice a nan sulaimi a jalingo" zasu sake d'auko wani
maganan khairi tace "kinga Adda Amrah muje ki gaida dada dare nayi kar momma tayi fad'an
kun zauna"............

Karasawa wurin Dada sukayi a cikin d'aki da tun d'azu take jinsu kasa Amrah ta duka tace "'yan
nyalli jam na dada?"(mun yini lafiya dada?) dada tace "jam noi shomri noi saare"(lafiya ya gajiya
ya aiki?) Amrah tace "jam wala ko d'ume"(lafiya kalau ba komai)...............

Tana mamakin me yasa ta amsa mata bata kallonta se wani direction d'in bata gama tunanin ba
idonta ya fad'a kan sandar dada da take anfani dashi wani tausayinsu ne ya rufeta don ta
tabbatar Dada bata gani gashi bata ga alamun akwai wani namiji a gidan ba don d'akin dai
kwaya d'aya dashi ake anfani d'akin zaure a rufe............
Duk tana Chan duniyar tunani little suka gaisa da dada, har seda khairi tace "Adda Amrah
lafiya?" Firgigit tayi tana cewa "lafiya Adda khairi, dada ba kinga khairi ba na hana ta ce min

Anty ta dawo Adda bayan kuma ta girme ni" ta karasa da tura baki kaman tana gaban
momma.............

Dariya sauran yaran sukayi har khairi dada kuma tana murmushi tace "Toh khairi kinji bata son
Adda ko Anty ki ce mata Amrahn ta" Amrah tayi saurin cewa "yauwa dadanmu" tana yiwa khairi
gwalo dariya suka sake yi...........

Khairi ta mike tace "bari In kawo muku ruwa" Amrah tayi saurin cewa "Ke yi zaman ki, tafiya
zamuyi mun bar baba Adamu a waje yana jiranmu oya little lets go"..........

Sallama sukayiwa Dada tana ci musu albarka, har mota nabeel da nabeela da kuma khairi suka
raka su, suna d'aga musu hannu har suka tafi...........

Da hira suka shigo parlorn se kuma sukayi shiru ganin musharraf zaune kusa da momma yana
shan coffee, little ce ta karasa tana hawa jikinshi tace "I miss yhu paapi" yana gyaramata zama
yace "ba wani ba kin samu wata Chan kin manta da ni ba" little ta shagwa'be fuska tace "waye
kuma wata Chan paapi" har ze kira sunan khairi se kuma ya Basar yace "you better start saying
sorry"............

Tace "sorry paapi" yace "Ohk then" hiransu momma ne ya d'auke mishi hankali duk da sam be
yi kaman yana jinsu ba inda Miemie ke cewa "Ina kuka je ba ni?" Amrah  tace "Ina zaki sani kin
shiga d'akin Adda nuri maula" hararanta mimie tayi tana nuna musharraf da baki wato ba don
shi ba da ta gane.............
Momma tace "kun dawo?" Amrah tace "Eh momma baki ga gidansu ba abin tausayi amma they
live happily na lura ba wani namiji babba a gidan ga mamansu makauniya siblings dinta kuma
sa'annin little ne" momma tace "Ayyah" Miemie tace "Allah sarki next time in za'a kaita nima
zani" Amrah tace "Ohk" mikewa musharraf yayi yana cewa "good night momma" momma tace
"Allah tashemu Lafiya da zarahn zaku kwana?" Yace "Yeah amma Amrah kiyi mata wanka ki sa
mata nightwear se ki kawota".........

Tsalle little ta dinga yi don tana mugun son kwana da shi shikuma ba ko yaushe yake yadda ta
kwanan ba, fita yayi yana amsa seda safen miemie...........

Yana kwance yayi zurfi cikin tunani wadda ban san na me ba se ga little ta shigo ta kwanto
jikinshi tana bashi labarinsu cutie be hana ta ba sam sema hankalinshi da ya bayar kanta dukda
ba amsa ta yakeyi ba, a haka ta gaji tayi bacci............

Washegari

Bayan sun gama breakfast yam and sous se tea da khairi tayi musu da misalin karfe 9:30 ya
fiddo akwatinshi aka sa a mota, sanye yake da well ironed three pieces suit navy blue da ya
matukar amsarshi, yayi kyau sossai har ya gaji yana shigowa parlorn kamshinshi ya bule ko

Ina.........

D'akin momma yaje tayi mishi adu'a suka fito tare da su Amrah little se shagwa'be fuska takeyi
alamun kuka don wannan karon ya d'an jima, sun fita daga parlorn har sunje wurin mota yace
"opps Ina zuwa" ya juya ya koma parlorn direct kitchen ya shiga tana tsaye tana chopping carrot
kawai taga mutum a kanta, sake gaisheshi tayi duk da ta gaidashi da Safe amsawa yayi, yana
nufan fridge ruwa ya d'auka dukda ya san akwai ruwa a fridge din parlor amma haka kawai ya
tsinci kanshi a kitchen, bayan ya d'auko ruwan ya 'balle murfin ya kafa a baki dukda sanyinshi
be cire ba seda yayi rabi kan ya juya ya fice...........

Yana fita ya samu haidar ya zo gaisawa sukayi kan ya shiga mota shima rakiyar mota uku suka
mishi har airport, seda sukaga departing d'insu kan suka dawo............

One month later

Zuwa yanzu khairi ta saba sossai da gidan aikinta da ma mutanen gidan gabd'aya sossai suke
kawance da Amrah har ta san labarinsu bayan alkawarin baza ta gayawa kowa ba, khairi na iya
kokarinta ganin bata wuce matsayinta ba, sun saba sossai da little In baka sani ba se ka d'auka
mamanta ce..............
Tunda musharraf ya bar Gombe almost month kenan be sake zuwa ba sede suyi waya da 'yan
gidan yana Chan yana rayuwan da ya saba na kad'aici se shan taba iyakarshi da mutanen
office d'insu gaisuwa se kuma In aiki me muhimmaci ya had'aku daga mazan har matan, har
gwara mazan ma da mata kam, me makon abun ya ragu amma se karuwa yake..........
Rayuwa tayiwa su khairi daadi don zuwa yanzu ba abinda suka nema suka rasa albashinta na
farko da ta d'auka last week ta saya musu duk abinda zasu bukata har kayan sawa ta kara
musu kad'an, sauran kud'in da ba wani yawa ta cire kud'in napep dukda momma na yawan bata
kud'in napep amma ba kullum ba gwara ta dinga rikewa In an batan ma se ta ajiye na wurinta
sauran kud'in sukayi savings...........

Matsalan da ta fara fuskanta na d'aya a gombe wadda ya girgiza ta shine cewa da mijin Maman
hamdeeya yayi yana sonta, a wata ranan laraba ta fita don zuwa gidansu musharraf ya tare ta a
daidai kofan gidan shi, inda ya furta mata shi de

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login