Showing 60001 words to 63000 words out of 117506 words

Chapter 21 - IGIYAR RAYUWA Hausa Novels Complete Document.pdf

Unknown   

18 May 2025

8446


hud'uba nayi mishi da sunan baba na, don na gane baki da uban nan da yace min yana nufin
kar In saka mishi sunan babanshi, bayan na isa hamma Nasir da matarshi Anty Aisha suka zo
suka d'aukeni bamu ma shiga cikin gari ba muka wuce dukku, Anty Aisha rungume da
musharraf, ni kuma Ina rike da marwan lokacin yana da kwana hamsin a duniya.....................

Bayan mun isa naga suna ta fiddo kayayyaki daga motansu anan na gane  sun yi min duk wani
necessary sayyaya daga gombe, sossai su mamaji sukayi murnan ganin musharraf se
tabarakallah masha Allah suke cewa, a part din dadda (mahaifiyar mahmoud) na sauka, ranan
suna suka tambayeshi sunan yaro yace yana jin kunyan fad'a a tambayeni tsabar iya lauyanci,
ba kunya nace "Da sunan bappa ya mishi hud'uba" don bazan bari mamaji ya sa sunanshi ba In
je In shiga uku na ni kad'ai, sossai kuwa sukayi farin ciki da sunan, ranan suna mamaji ya bada
shanu aka yanka, bappa kuma ya yanka mishi raguna biyu basu ma bi ta kan mahmoud ba da
be zo ba be kuma kawo kudin rago ba sun ajiye hakan as kunya bayan kuma yi d'inne bazeyi
ba............

Bayan kwana arba'in sossai nayi kyau nayi bulbulbul har bana so ace yau zan koma Abuja duk
da sossai dadda ta fahimci be damu da ni da musharraf ba gashi tunda nazo bata ta'ba gani
nayi waya da shi ba, randa na cika kwana arba'in na tafi gombe sati biyu kwarara nayi, sati na
farko gidan yaya Nasir, kwana biyu gidan yaya Ahmad shima lokacin matarshi na da tsohon
cikin sufyan..............

Sauran kwanakin kuma gidan taheer nayi su kan na tarkata na koma dukku a lokacin dadda ta
kira mahmoud ta ci mishi mutumci daidai gwargwado don tunda na zo Gombe mahmoud be zo
ba har yau, dadda ta kuma jaddada mishi bazan koma ba har se ya zo In kuma yaga baze iya
ba Toh yayi ta zama shi kad'ai yana fakewa da aiki.............
Ba yadda ya iya haka yazo ya d'aukemu su yaya Nasir suka kaimu har airport ran nan a had'e
sbd fad'an da iyayenshi suka mishi a kaina, Ai ko isarmu bada jimawa ba ya min dukan da ba
gaira ba dalili ya kuma biya bukatarshi da ni a wulakance............

Renon musharraf na cigaba da yi har ya kai shiga makaranta na saka shi a makarantan da
nake koyarwa duk waennan shekaru mahaifinshi be kashe ko naira biyar akan komai nashi ba,
idan ya shigo site dinmu musharraf na nufanshi ze hankad'e shi wani lokacin har ciwo yakeji tun
yana zuwa wurinshi har ya daina, abu na farko da na lura musharraf na da shi kenan zuciya
yana d'an shekara uku idan har mahaifinshi ya bugeni haka ze zauna yayi ta kuka kaman ze
had'iyi rai inyi lallashin duniyan nan baze ta'ba shiru ba ban san ashe tsanan mahaifinshi na
ginuwa a zuciyarshi bane............

Rayuwa na gurguwa dayake albashina me tsoka ne hakan yasa ba abinda muka nema muka
rasa da d'ana improvement da na samu kuma shine cire damuwar mahmoud a zuciyana tun
wani mahaukacin hawan jinin da nayi kaman ba zan rayu ba, gashi ba wadda ya sani a
gida..........
Daga lokacin na cirewa zuciyata damuwanshi hakan yasa na d'anyi kyau dukda raman na nan
se kuma haskena ya dawo, In kuma kinga munzo nan gombe to babban abu za'ayi se muyi
shekara bamu je ba, a haka musharraf ya shekara bakwai In kin ganshi zaki rantse d'an
shekara sha uku ne sbd tsawo da Allah ya bashi zaki sha mamaki In na ce miki bayan
musharraf na d'auki ciki sau hud'u, biyu suka zube sbd duka sauran biyun kuma sbd rough sex
ko ince miki raping.............

Kuma har yau ban ta'ba fad'an halin da nake ciki ba, haka musharraf sbd Allah yayishi ba me
son magana ba kuma sam baya shiga harkar da bata shafe shi ba yasa be fad'awa su dadda ba
ko a hira kuwa, a tsakanin ne aiki ya dawo da mahmoud gombe wani abinsu na siyasa da ban
sani ba kuma 4years ze yi achan hakan yasa muka tarkato muka dawo sam ban so dawowarmu
ba sbd tonuwar asiri ne a garemu, gashi ajiye aikana nayi, abinda yafi damuna kenan Ina zan
samu kudin da zanyi enrolling musharraf makaranta? Kuma Ina zan samu kud'in da zan ci
damu?.................

Bayan munyi settling a gidanshi dake gefen government house, naje gidan yaya Nasir da siyasa
nace mishi Ina so in fara business kaman ya san kud'i nake nema a lokacin ya min transfern
200k sossai na mishi godiya haka mukayi da yaya Ahmad ma, shima 100k ya bani tare da
sanya albarka business na fara na manyan leshuka da atamphopi, veils, shoes se perfumes irin
na harkan manya de.................

Matan su yaya ahmad ne suka dinga had'ani da manya sossai harka ya bud'e har na samu
shigarda musharraf makaranta a lokacin yana primary four, na kuma yi mana sayayyar kayan
abinci, a kwana a tashi har mukayi shekara a Gombe business kawai na sa a gaba se kula da
tilon d'ana, wata ranan alhamis muna zaune a parlor ni da musharraf Ina koya mishi assignment
muka ji an turo kofa a tare muka d'aga kai ganin babanshi ne yasa suka ci gaba da abinda
sukeyi.................

Toh kullum ya dawo se ta mishi sannu da zuwa amma be ta'ba amsawa ba tun tanayi ta zo ta
gaji ta daina, dayake gidan sun nan se an shiga main parlor ake shiga part part na gidan wadda
guda biyu ne se boysquaters, Ashe yaji haushin banzan da mukayi dashi a tsawace yace "Kai
wawa marar anfani, baka ganni bane da baza ka min sannu da dawowa ba In ita uwarka taki
min din ni ba ubanta bane, kai baza ka min ba Ina ubanka?" Shiru musharraf yayi.................

Yana matsowa yace "Kai don uwarka wannan ba magana nake maka ba?" Musharraf yace
"bade uwata ba" cikin gunguni wani wawan mari ya sauke mishi da sauri ya nufi wurin tv ya
fisgo wayar Av ya dawo Ina ta zungurin musharraf ya gudu amma wawan zuciyarshi ya hanashi
tashi yana zuwa ya rufeshi da duka tunda musharraf ya nad'e kafafuwanshi ya d'aura kanshi a
kai be kara motsi ba kaman itace ake duka..................

Abinka da uwa se na kasa jurewa na san tunda musharraf yayi haka baze ta'ba gudu ba kuma
baze yi ihu ba, hakan yasa na rike Av Ina cewa "kayi hakuri yaya mahmoud" mari ya saukemin
tare da komawa kaina ya fara duka yana yi yana masifa "duk ke ce me hure mishi kunne gaki
uwar banza me koya mishi tarbiyar banza aka gaya muku da maganarku da rashinshi wani abu
ze karamin ne, en iska kashin tsiya".................

Ya d'aga ze kai kenan yaji an rike Avn yana juyowa yaji saukan mari yaya Nasir ne da matarshi
se d'ansu mari ya kife Mahmoud dashi hagu da dama yace "mahmoud irin tarbiyar da aka bamu
kenan? Ko bare ce zaka sa ta gaba kana wannan dukan a gaban d'anta balle er uwarka? Me ta
maka haka? Yarinya me hankali da natsuwa" mikewa musharraf yayi da gudu ya fad'a jikin
uncle dinshi, kirjinshi se tashi yake yana sauka shi ba kuka ba shi ba shiru ba yace.................

"Uncle ka gayamishi ya fita harkar uwata da ni tunda baya karinmu da komai, uncle kullum
mutumin Chan se ya duki momma bayan bata mishi komai, momma na ke saya mana kayan
abinci, momma ne ke biyamin kud'in makaranta duk abinda nake so ita ke saya min ta kuma
saya ma kanta to me yasa ze zo yayi ta dukanta?" Da matukar mamaki yaya nasir ke kallona ya
kuma kalli mahmoud..................

Dukawa yayi yana kallon jikin musharraf da yayi rud'u rud'u da duka yace "son kayi kuka, kaji In
kayi zuciyarka ze yi sanyi irin haka na sawa mutum ciwon zuciya, kaji yi kuka" kuka ya fashe
dashi sossai yayi kuka, seda hawaye ya cika idon yaya nasir da matarshi, samun wuri yayi ya
zauna muma muka zazzauna a hankali yace "Fatima gayamin rayuwarki na aure daga farko har
yau" Shiru nayi, be ce komai ba ya fiddo waya yayi kira "duk inda kake ka zo gidan mahmoud

yanzu yanzu it's urgent plz" Shiru muka zauna se kallon mu yakeyi ya kalleni ya kuma kalli
mahmoud...................

Ba'afi fives minutes ba akayi sallama Ahmad ne ya shigo zama yayi yana cewa "lafiya?"
Hamma Nasir yace "ba lafiya ba" ya kalleni "ke fatima, kalleni Ina wasa dake??" Girgiza kai nayi
yace "bani labarin rayuwan aurenki daga farko har yanzu" a hankali na fara bashi labari jin ba
wasa a lamarinshi kallona suka dingayi kaman tv har na gama a tare suka maida idonsu kan
mahmoud...............

Baki ya bud'e da niyyar maganan a tare suka sauke mishi mari d'aya haggu d'aya dama, Yaya
Ahmad yana hawaye yace "irin tarbiyar da dadda da diddi suka mana kenan? Mahmoud me
yasa zaka ci amanar aure ka san kuwa illar dukan mata matan ma matarka?" Yaya nasir kam
kasa magana yayi, da kyar yayi mishi nasiha me ratsa jiki, Ahmad kam fad'a sossai yayi mishi
kuma da zaran ya bud'e baki da niyar magana se ya d'auke shi da Mari a karshe yace mamaji
ze fad'awa......................

A hankali nace "kuyi hakuri hamma Dan Allah karka fad'a musu baza su ji daad'i ba kuma ka
san mamaji nada hawan jini plz kar wani abu ya sameshi" yace "naji Amma In yana so muyi
Shiru se ya sayo kayan abinci ya cika store sannan ko marinki yayi ki fad'a min wallahi zaka sha
mamaki na banza marar tunani" juyawa yayi ya fara tafiya har ya kai bakin kofa yace "sannan
ka cire musharraf a makarantar da ta sa shi da kud'inta ka maida shi wadda yafi tsada a gombe,
zan zo gobe da rana inga bakayi abinda nace ba zaka sha mamaki na mahmoud" ya juya yayi
tafiyarshi..................

Fad'a sossai da nasiha yaya nasir ya kara mishi don ya san yafi jin tsoro da kuma maganan
Ahmad ya san dole yayi abinda yace, kaman kuwa nasihar ta shigeshi a washegarin yayi duk
abinda yaya Ahmad yace kuma da gaske yazo ya gani sossai ya ja mishi layi ya mishi tijarar da
ya bani tsoro don beda fad'a sam, Ashe jiyan ma don ganin yaya nasir ne....................
Ai kuwa sossai maganan yaya Ahmad ya shigeshi, ya ajiye mana kayan abinci sossai ya kuma
sauyawa musharraf makaranta, kuma be sake min ko kallon banza ba, ba lefi kuma In yazo
karban hakkinshi ba ya mata ta karfi, a haka na samu cikin nuriyyah, ranan na tashi da laulayi
sossai Ina kwance zazza'bi ne ke damuna, dama tunda ya sayo kayan abinci dashi nake girki
kuma yana ci.................

So ya fito se be samu breakfast d'inshi ba, a zafafe ya shigo d'akina ina kwance cikin bargo ya
janye bargon tare da cewa "ke!! Me kike nufi? In sayo kayan abinci kuma baza ki girkamin In ci
ba? Ai ko baki isa ba karkiga kaman don na sararamiki kwana biyu ki zata tsoron su hamma
nake wallahi yanzu se in tattakaki" a hankali nace "kayi hakuri bana jin daad'i ne" ban rufe baki
ba ya janyoni kasa "ba ruwana da rashin jin daad'inki ki wuce ki samamin abinda zanci" kasa
mikewa nayi yace "taurin kai ko? Ohk" belt na jikinshi ya zare ya fara dukana.................

Kaman daga sama mukaji musharraf yace "baba me tayi maka kake dukanta? wallahi ka kara

dukanta se na rama mata da tsantar mamaki babanshi ke kallonshi jin furucin da ya fito daga
bakinshi kan ya d'auke shi da mari, ganin ko gizau be yi ba sema kafa mishi ido da yayi yana
kallonshi juyawa yayi ya fice a fusace kama ni yayi na mike ya taimaka min zuwa kan gado zan
mishi magana akan abinda yayi yanzu se kawai ya juya da sauri ya fice.......................







*thanks for your prayers ya samu sauki sossai Alhamdulillah*











#vote
#share
#comment









'Yar mutan Adamawa


🎗🎗🎗🎗🎗

IGIYAR RAYUWA😭






🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad gurin

Wattpad:- Gureenjo

'Yar mutan Adamawa

*This page is dedicated to yhu mama on this your special day, Ina rokon Allah ya karo miki
shekaru masu albarka, ya biya miki dukkanin bukatunki na duniya da lahira, Allah ka bata
tsawon kwanan da zamu faranta mata kamar yadda ta faranta mana kuma take kai. Yhu the
best woman I've ever met and strong lady I've ever known. I love yhu so very much mama*

Page➡�5�⃣9�⃣▶�6�⃣0�⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Musharraf ne ya kula da ni a ranan, dukkanmu da ni dashi tea muka yini sha sbd be iya girki ba
ni kuma bazan iya ba, da dare mahmoud ya dawo ganin ba abinci a dining yasa ya nufi d'akina
da belt a hannu Ina kwance cikin burgo ya yaye blanket d'in ya fara dukana, bai hankara ba
kawai yaji saukan kwalba a keyanshi a matukar razane ya juya da tsantsar mamaki yana kallon
d'anshi d'an shekara tara wai yana dukanshi..........................

Kwalban pepsin dake hannunshi ya bi da ido, belt mahmoud ya zuba mishi shi kuma ya d'aga
kwalban da niyyar sake kwad'a mishi a firgice nace "innalillahi wainna ilaihi rajiun Abubakar!! Me
zan gani haka? Me kakeyi" na karasa maganar cikin d'aukewar hankali ban kara sanin inda
kaina yake ba se na ganni asibiti su hamma Ahmad suna tsatsaye kaina sannu suka dinga
min...............

A kasalance na amsa Ina dudduba inda zanga musharraf baya d'akin, yaya Ahmad yace "sannu
fatima, dukanki ya sakeyi ne? Musharraf ya kira mu da gaggawa wai yazo ya ajiyeku a asibiti

yayi tafiyarshi" girgiza kai nayi nace "a'a hamma be dakeni ba ban da lafiya ne, Ina musharraf
d'in?" Yaya Nasir yace "yana waje yaki ce mana komai" ajiyar zuciya ta sauke tana runtse ido,
doctor Aslam ne ya shigo yana kallon su hamma Nasir yace "congrats tana d'auke da cikin wata
biyu" cikin jin daad'i sukayiwa Allah godiya...................
Nan suka tambayeshi yaushe ne sallama, yace za'a iya sallamanta zuwa gobe da safe, godiya
suka mishi ya fice a take suka kira su dadda suka fad'a musu suma sunyi farin ciki sossai da
sukaji da laulayi kuwa suka ce zasu bani dattijuwar me aikinsu ta kwana mini biyu, Ai ko
washegari aka sallameni na samu ma mai aikin ta iso na bata d'aki cikin part d'ina tunda aka
kaini asibiti musharraf be yarda mun had'a ido ba har aka sallamoni..............

Bayan mun dawo ne na samu ganinshi sossai na mishi fad'a da nasiha yace baze sake ba, a
haka a haka na yi renon cikin nuriyyah har na haifeta tun daga sanda musharraf ya d'aga ma
mahaifinshi hannun kaina be sake dukana a gabanshi ba sede yayi min hukunci a lokacin
kwanciyar aure, abinda ya matukar bani mamaki kuwa shine ganin sa'banin yadda na gani a
lokacin haihuwan musharraf.......................

Allah ya d'auramishi son nuriyyah tun daga randa ya d'aura ido a kanta hakan yasa ta samu
gatan suna sossai daga wurinshi har su yaya nasir suka zata ya sauya haline amma hausawa
suka ce hali zanen dutse yana nan da kayanshi, seda nuriyyah ta shekara biyu tukun muka
koma Abuja inda ya ci gaba da shaye shayenshi wadda da bayayi a gombe, ko da yanayin
kuwa be ta'ba shigowa gida a buge ba....................

Sam jituwa be ta'ba shiga tsakaninsu da musharraf ba nayi iya yina da kokarina don ganin
musharraf be tsani mahaifinshi ba amma ban ci nasara ba ganin abun na shirin kwa'bewa yasa
na yi enrolling musharraf a boarding school don tun kafin mu dawo mahaifinshi ya dena biya
mishi kud'in makaranta wai ba yadda za'ayi yana wahala da yaro bayan ci da sha ya kuma biya
mishi kud'in makaranta amma yazo yana mishi rashin kunya ba....................

Sam musharraf be so ba da kyar na samu na shawo kanshi ya yarda don shi gani yake In baya
nan babanshi ze samu damar ci gaba da dukana yadda yake so, shekaran nuriyyah hud'u na
haifi miemie wacce asalin sunanta Aslamiyya muke ce mata miemie, seda mukayi rikici sossai
kan ya yarda da sunan don seda na had'a shi da yaya Ahmad abunda ya mugun bashi mamaki
kenan don be zata zan iya ba, shekarar miemie be cika biyu ba na samu cikin
Amrah..................

A lokacin musharraf ya gama secondary school yayi jamb ya kuwa ci, sossai aikina ya
taimakeni don tun dawowarmu Abuja na koma, da kud'ad'ena da nake tarawa na samu yi mishi
chukuchukun samun University of Abuja, yanzu muna cin albarkacin son da yake yiwa nuriyyah
yana saya mana kayan abinci, ya saya a makaranta me tsadar gaske, duk da rayuwan aurenmu
be koma kaman na mutane ba amma ya bar dukana sbd nuriyyah tace bata so..................

Shekarar musharraf 24 ya gama jami'a har service inda ya karanci accounting a lokacin na

samu kawata hajjiya ruqayyah wacce tun zuwanmu Abuja muke mutunci sossai amma
kawancen be yi karfi ba sbd ban bada fuska ba, sede 'ya'yanmu musharraf da haidar da suke
abokai, itace ta kar'bi takardun musharraf ita da mijinta suka mishi hanyar samun aiki a
CBN...................
Shekarar nuriyyah 15, yayinda miemie take 11 se Amrah 9, a lokacin kuma musharraf ya fara
matsanancin ciwon ciki kullum muna hanyar asibiti Zaki sha mamaki kuwa In na ce miki har
lokacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login