Showing 105001 words to 108000 words out of 117506 words
Chapter 36 - IGIYAR RAYUWA Hausa Novels Complete Document.pdf
Unknown
18 May 2025
8449
fito suka wuce gida.
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—
         IGIYAR RAYUWAí ½í¸
Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—
í ½í²«ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
         'Yar mutan Adamawa
Page➡�9�⃣4�⃣▶�9�⃣5�⃣
í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—
Har suka shigo gida uffan be ce mata ba kuma be sake fuska ba hakan yasa suna shiga d'aki
tayi narai narai da fuska tare da kwanciya a gadon bayanshi ta zagaye cikinshi da hannunta duk
biyu cikin taushin murya tace "am so sorry dear, plz Kayi hakuri bazan kara ba" lumshe ido yayi
yana tunanin anya son yarinyar nan baze yi ajalinshi ba? Juyota yayi ya rike tafin hannunta
yace "ni zan rokeki qalbee baki san yadda hawayenki suke da tsada da daraja ba? Zubar dasu
kaman wani babban asara ne a gareni plz ki dauri ki dena irin wannan kukan it really hurt here
wallahi" ya karasa yana nuna setin zuciyarshi.
Dukar da kai tayi tabbas maganganunshi sun shigeta kuma da yardar Allah bazata sake kuka a
gabanshi ba tunda yana damunshi, tsintar muryarshi tayi yana cewa "baza kiyiwa assiddiq d'inki
wannan alfarmar ba?" Dayake haka In ta bushi iska take kiranshi kuma sunan na mishi daad'i
sossai kasancewar ba wadda ke kiranshi ko da Abubakar d'inshi ne bayan 'yan office d'insu.
Zagaye hannunta tayi ta wuyarshi ta kara tsai tayi brushing lips d'insu kan tace "In shaa Allahu
bazan kara kuka haka ba baby" murmushi yayi yana cewa "Ohk baby amma fah kin tada wani
fitinar" kashe mishi ido tayi tana jefanshi da wani irin murmushi da shi kad'ai ya san ma'anarshi
bata hankara ba se ji kawai tayi ya rabata da kasa zuwa gado, a hankali na fita na ja musu kofa.
Washegari kuwa suka koma gidan Alhj Abdulrashid inda anan ya roki sanin su wanene su, ba
tare da wani damuwa ba Abul ya zayyane mishi labarinsu wadda seda sukayi hawaye
musamman Afreen da Nasreen da suka kasance masu raunin zuciya, irin kallon da musharraf
ke wullo mata ne ya hanata kuka a wannan karon da ta tuna labarinta for the first time in history,
bayan Abul ya gama ta basu labarin bayan barin Abul gidan har kawo yau, jinjina kai Abul
yakeyi cike da farin ciki wai yau 'yar uwarshi ce tayi aure a garin Abuja tana jin daad'inta cike da
soyayyar mijinta gashi tayi wani irin mugun kyau ta kara haske.
Nan musharraf ya roki alfarmar Abul yayi zamanshi dasu Abba In sun tashi komawa Gombe se
su tafi gabad'aya suyiwa dada surprise, tambaya Abul yayi "yaushe ne tafiyankun hamma?"
Musharraf yace "nan da three months" dukda Abul be so ba sbd kewan dadanshi da kannenshi
da yakeji amma ba yadda ya iya musamman da yaji Abba na cewa "hakan shine daidai sbd ko
ni zan samu nayi scheduling duk wani aiki nawa" haka suka tsayar kan kowannensu ya wuce
abinda ze yi Afreen da Nasreen duk Nile university suke karatu amma different courses.
Bayan wata uku
Khairi ta samu nasarar kare exams d'in first semester cikin nasara don Allah yayita me
kwakwalwa hakan yasa exams d'in be yi mata wahala ba, ta 'bangare d'aya kuma soyayyarsu
da musharraf se kara gaba yake yi basu ta'ba ji sun gunduri juna ba, dukda zaman yau da
kullum ana samun sa'bani amma daga d'aya ya hau d'aya ze sauka se wadda ya hau d'in ya
sauko da kanshi tukun su fahimci juna, haka zumuncinsu da su Abba ya kara tsanani In ka
gansu kaman wasu family yawanci 'yan matan suna gidan khairi hakan yasa Abul ma nan yake
tarewa In Abba ya samu sarari da kanshi yake zuwa ya tattara su amma baze hana a
washegari khairi ta gansu ba, little ma ta kare term d'inta itama ta saba sossai dasu Anty
Nasreen d'inta, dukda khairi ta lura da take taken Afreen na son musharraf hakan be sa ta
chanza mata ko a fuska ba don ta yarda da kanta ta tabbatar ita kad'ai ce a birnin zuciyar
mijinta dukda shi musharraf d'in ba kowa ke ganin fuska a wurinshi ba halin shin nan na nan
yadda yake treating su Amrah haka yake yiwa su Nasreen.
A washegari zasu bar Abuja to gombe Abba yayi musu komai na flight da zasu bi dukkansu har
'ya'yanshi don yana so da kanshi ya damka Abul a hannun mahaifiyarshi gashi kuma yana son
yaron har ranshi, zaune suke akan gado shi yana daga bakin gadon kafafunshi na zube a kasa
system ne akan desk dake gabanshi yana dannawa gefen system d'in hot coffee ne yana
sipping daga shi se wani gutun three quarter milk in kuka ga yadda ya kara wani irin haske da
murjewa se kunyi mamaki.
Khairi na kwance daga bayanshi daga ita se a wani 'bingilelen riga nylon pink me hannun vest
gashinta a sake bata saka mishi ribbon ba ko de tace ta saka musharraf ya cire fuskanta d'auke
da kwalliya sossai wadda har seda nayi mamaki (a su khairi an wayeí ½í¸œ) kunnenta sanye da
fashion pink video call takeyi da Amrah da miemie se surutu suke zubawa ba ma su san
musharraf na gefenta ba se tsokananta suke.
Amrah tace "irin wannan kyaun haka khairi ko hammanmu ya miki ajiya ne" hararar ta tayi tace
"wallahi ki kiyayi bakinki na gaya miki ba wani ajiya" suka saka dariya Miemie tace "seriously
Khairi kinga wani irin fresh da kikayi sa'banin Adda nuri da ciki ke wahalar da ita ba kaman
farkon aurenta ba itama baki ga yadda ta zama ba amma yanzu se kashi bata iya cin komai"
Khairi ta waro ido tare da yin fuskan tausayi tace.
"Dama haka cikin yake? Da gaske mutum baya iya cin komai?" Amrah na dariya tace
"matsoraciya khairi ke damuwanki kar babynmu ya hanaki d'urin da kika saba ko" harara ta
wurga mata "ban son tsiya dama chan ci ne dani?" Miemie tayi saurin cewa "a'a kede yanzu me
albishir d'in?" Ta san karamin aikin khairin ne ta kashe wayanta kan ta fad'a musu albishir da ta
kirasu dominshi, murmushi ta saki tace "muna hanya gobe idan Allah ya kaimu" wani irin ihu
suka saka cikin jin daad'i maida idonsu da zasuyi kan wayan suka had'a da musharraf Ai da
gudu suka watse suka bar fuskan wayan na kallon gini, murmushi ya saki yayinda khairi ke
dariya harda rike ciki.
Kallonta yake tayi yana mamakin mutanen da suke cewa In ka auri mutum sonshi raguwa
yakeyi a zuciyarka, shi kam be gani ba sema sonta da kaman kara mishi a keyi a kullu yaumin
sossai ya shagala da kallonta har be san sadda ta gama dariyar ba se iska me kamshin
strawberry da ta hura mishi a fuskanshi hakan ya sashi lumshe idon ya kuma ware a kanta a
hankali yace "Ina sonki ummu Abdurrahman".
Juya ido tayi alamun tunani kan tace "waye ummu abdurrahman kuma?" Yace "ke mana duk
kika haifi d'a namiji Abdurrahman Sudays zanyi naming d'inshi don Ina son sunan" shagwa'be
fuska tayi tace "zan iya kuwa baby? Baka ji su Amrah na cewa Adda nuri na wahala ba?" Yace
"I didn't believe them me yasa muna waya da nuriyyah bata ta'ba sanar da ni ba? And more
over Ai kowa da yadda pregnancy dinshi ke zuwa so plz ki manta da maganansu" shafa cikinta
yayi yace yana karya wuya "ni kam Ina mamaki duk irin jarumta na dinnan ace har yanzu banyi
ajiya anan ba?".
Baki ta turo tare da ture hannunshi wayanta ta d'auko ta kira momma ta sanar dasu zuwansu,
haka ma dada nan kam ya kar'ba suka gaisa da dadan da kuma twins, nan fah ta shiga group
din family d'insu ta sanar da shigowarta gombe a goben don saura kwana uku a fara events d'in
bikin su marwa duk ankon da za'ayi sun turo mata sample ta nema a nan abujan telan su
Afreen ya kashesu da styles d'inshi masu tsananin kyau aka goge mata sune ma kasan akwatin
tafiyansu.
Bayan ta gama wayoyinta ne ta dubi musharraf dake kwance rigingine ya zuba mata idanu tace
"baby lafiya kuwa irin wannan kallon?" Yace "wallahi kyau kika min bana ta'ba gajiya da kallonki
hasken idaniyata Ina sonki har ban san adadi ba, a tsakankanin da kika shigo rayuwata ban
ta'ba zaton zan fad'a irin wannan komar son ba ko da ance zan fad'a to tabbas me rabani da
wadda ya fad'a d'in se Allah.
Amma gashi yau Abubakar Assidiq (musharraf) ya zurma ciki yayi Nisan da baya jin kiran,
idonshi yayi rufewar da inba tauraruwarshi ummulkhair ba baya ganin ko wacce mace a
matsayin mace se ma maza 'yan uwanshi da ya maishe su" fuskanta ta matso setin nashi tana
d'an hawa jikinshi tace "ummulkhair ma na tsananin son mijinta, hasken rayuwanta, me cetonta
har yau Ina jinjina tsayuwa da kayi ka ceceni a lokacin da wasu suka so keta min haddi na
tabbatar da kai ka so hakan ne sbd kaine me driving a lokacin kuma kai ka fara fitowa kan
haidar, sannan ba'a mamaki da ikon Allah baby, Allah shi ke sawa bawanshi son wadda ya so a
lokacin da ya so, zaka sha mamaki In na ce maka tun daga randa na fara d'aura idona a kanka
a arabian estate na fad'a tarkon sonka me tsanani da azaba so me hana bacci..." katseta yayi ta
hanyar maidata kasanshi yayi mata runpa da broad bare chest d'inshi.
Yana kallon tsakiyar idonta yace "ya isa haka qalbee In ba so kike zuciyata ta fashe da
kalamanki ba, dukda kin riga fara sona amma kuma na fi sonki yanzu akan son da kike min,
kece numfashi na, In har bakya tare dani to tabbas na dena numfashi kece hasken idaniya na a
duk sadda kika barni to bana iya gani sbd kin tafi da hasken dake haska min hanya ta cikin
idanu na, kece fitilar zuciyata a duk sadda kika dusashe toh fah zuciyata bazata kara wani
anfani ba sbd ba jigonta kinyi kane kane a cikinta, bana iya kwararren minti guda ba tare da
kwalkwalwana, zuciyana da kuma numfashina sun ambaci sunanki ba, wallahi ban san iya son
da nake miki ba, Ina miki....." bakinta ta rufe da nashi duk tsikar jikinta na tashi kalamanshi na
narkar mata da zuciya.
Amsa yayi ya fara aika mata da wasu irin darrusa da ita kad'ai ce me iya fahimta har tayi hadda
ta kuma rubuta gwajin aji da jarabawa a kanshi ba tare da ta kuskure ko abu guda ba, ita
kad'aice me fitowa da flying colors a wannan class na malamintan, zamewa nayi waje kan
waennan malama da d'aliban su rutsani, sossai suka nunawa juna irin son da sukeyiwa juna
bayan sunyi wanka ta saka mishi akwati biyu a gaba tana mika mishi kaya yana shiryawa nata
ya fi girma komai ta d'auko ta miko.
Dariya da mamaki suka kamashi yana dariya yace "qalbee Ina zaki da waennan kayan? Ba de
planning barina kikeyi ba don wannan yafi karfin sati biyu sede shekara biyu" turo baki gaba tayi
tace "baby me abun dariya anan? Duk fah zanyi anfani dasu" yana ci gaba da murmushi ya
girgixa kai ashe da gaske ne da aka ce duk inda mace take bata rabo da tarukucen kaya yanzu
dan Allah ina zata kai duk waennan kayan, be kara cewa komai ba se dariyan da yakeyi jefi jefi
yana kallon akwatintan, Ai kuwa ta turo bakin nan kaman ze ta'ba gini hakan kuwa kara bashi
dariya yake.
"Kina da kyau" ya fad'a In a whisper kallonshi tayi ya d'aga mata gira tare da kashe ido,
murgud'a mishi bakin tayi tare da ficewa daga d'akin yana murmushi ya ja musu zips d'in
akwatunan tare da d'agawa ya jingina da jikin wardrobe jallabiya ya sanyo sbd su nasreen da
suke nan ya sauko kasa d'akin da suke sauka ya kalla dayake dad da Abban gombe sun
turomata da kayayyakin d'akin, kokonto yake na inda ta shiga daga karshe d'akin little ya bud'e
se kuwa suka had'a ido tana tsaye tana shirya mata kayanta cikin akwati yayinda little ke zaune
bakin gado tana zuba mata surutu.
Ciki ya karasa ya biyewa little sukayi ta surutu har sukayi nasarar sata dariya harda rike ciki
cikin farin ciki da kaunar juna suka fito khairi na cewa "yau na bar baba A'i da aiki" me aikin da
hajiya ruqayyah ta turo musu mijinta ya rasu kuma bata ta'ba haihuwa ba gashi ta manyanta
don zatayi sa'a da momma hakan yasa suke girmamata kaman ba me aiki ba, bayan su
musharraf sun zauna ta kawo musu natural lemo da take harhad'awa ta sa a fridge a gabansu
ta ajiye da cup ta wuce kitchen don duba baaba A'i.
A daren su nasreen suka tafi don samun su had'a kayan da zasu tafi dashi washegari karfe
goma cip suka had'u a airport ba wani 'bata lokaci suka sauka a gombe motoci biyu suka zo
taryansu daga gidan momma Inda ba 'bata lokaci suka isa har parlor momma tayi musu iso
Bayan gaisuwa da sannu da hanya ta gabatar musu da abinci dayake 'yan boko ne ba wani
fulako suka zauna suka kwashi gara.
Momma kam farin ciki kaman ya kasheta don ganin yadda tilon d'anta ya koma gashi kulawar
da khairi ke bashi a gida haka take bashi a gaban kowaye don shi ya koyarmata da hakan
Bayan sun gama ci suka koma parlor inda khairi tace "momma banga su Amrah ba" bata rufe
baki ba suka shigo parlorn ihu suka saka tare da nufarta suka rungume suna jin daad'in ganinta
tsaki musharraf yaja yana girgiza kai bayan gama oyoyo d'insu musharraf ya dubi momma.
"In zaki lura da wanchan zaki ga irin kaman da sukeyi da qalbee ko momma?" Ta kalli Abul tace
"kwarai kuwa" yace "toh shine twin brother d'inta" nan ya basu labarin yadda ya tsinci kanshi a
hannun muggan mutane da yadda ya tsira momma salati ta dingayi tana mamakin halin
mutanen duniya maganan musharraf ne ya katse mata mamakinta "yanzu na tara familyn Alhj
Abba Umar suna jirana da surprise da nace zan musu"Â mikewa momma tayi tace "Toh ku tashi
mu tafi" mikewa sukayi suka fito, ababban parlorn inna suka tarda mutanen gidan gabad'aya
zaune, sallaman Abul ne yasa dada mikewa da karfi.
*Aslm kwana biyu kun jini shiru banji daad'i bane na lalla'ba na yi muku ba don na warke ba se
don kar nayi ta ajiyeku jira zanyi briefing in shaa Allah 2-3 pages left*
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—
        IGIYAR RAYUWAí ½í¸
Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—
í ½í²«ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
         'Yar mutan Adamawa
Page➡�9�⃣6�⃣▶�9�⃣7�⃣
í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—í ¼í¾—
Da sassarfa ya karasa ya fad'a jikinta yana jin kewan mahaifiyarshi na dawo mishi sabo
hawayen tausayin kansu ya ci gaba da sulala daga idanunshi, mutuwar tsaye dada tayi na
mintuna abunda bata ta'ba mafarki ba, bata ta'ba sa rai ba, ko a kiyasce bata ta'ba kiyasta
ganinshi yanzu ba sede ba'a mamaki da ikon Allah, Allah aka ce yafi gaban komai yau gashi
bata mutu ba Allah ya had'a ta da d'anta da ta fidda ran ganinshi kuka ta fashe dashi tana tuna
rayuwansu na baya.
Khairi da tayi narai narai da ido alamun itama kukan zatayi suka had'a idanu da musharraf
harara ya sakar mata hakan yasa ta mayar da hawayen nata don dole inna ce ta katse shirun
parlorn da cewa "Kai Habu menene wai ka wani tara mutane ba tare da wani jawabi ba
kwatsam wani katon saurayi yazo ya fad'a jikin safiya yana ta kuka kaman wadda akayiwa
mutuwa" murmushi musharraf yayi yace "Abulkhair kukan ya isa haka plz saketa ka samu wuri
ka zauna, inna yanzu zamu miki bayani" sake dada yayi ta zauna shima ya zauna a gefenta
tare da riko hannunta se a lokacin yaji kunyan abunda yayin ya kamashi ganin mutane dayawa
a parlorn don duk familyn an had'u sbd bukin da suke dashi.
Cikin natsuwa Alhj Abdulrashid yayi musu bayanin kanshi da yadda ya samu Abul inda yana
ajiye aya Abul ya d'auka ya musu bayanin bayan fitanshi gida da abunda ya faru dashi inna
kuwa ta dinga zagin waenchan mutane yayinda Abba ya sha Adu'a dada ma sossai ta mishi
godiya murmushi kawai yayi nan 'yan matan sukayi waje haka hajjiya ruqayya, dada da momma
sukayi d'akin dadan inna ma ta tafi d'akinta yayinda haidar da su Jamal suka ja musharraf zuwa
part d'in samarin gidan.
Drinks aka kawo wa iyaye mazan inda shafin hira ya bud'e anan Alhj Abdulrashid ya amayar da
abunda ke ranshi don d'an boko ne tsantsa be iya rufa rufa ba, sunyi murna sossai inda suka ce
zasu tuntu'bi dada, a bangaren musharraf kuwa suna de zaune da su jamal se hiransu sukeyi
amma shi kam be sa musu baki ba sam sede abun dariya yayi murmushi, haka 'yan matan da
suka kasance su goma sha d'aya chas a zaune a parlorn mommy suna shan hira amare da
Adda fadeelah suna site d'in umma little ita kad'ai zaune a parlor tana kallo sbd su nabeel suna
makaranta