Showing 51001 words to 54000 words out of 117506 words

Chapter 18 - IGIYAR RAYUWA Hausa Novels Complete Document.pdf

Unknown   

18 May 2025

8450

a
rai amma abun na shirin fin karfina"...................

Momma tace "zaki iya ummulkhairi, dukda ban san wacece ke ba, na tabbatar bakiyi sanadiyar
mahaifinki ba sbd yanayinki da tarbiyarki be nuna hakan ba, In ba zaki damu ba Ina so ki bani
labarin rayuwanki, Ina son zama miki gini wadda zaki dafa ki tsaya har ki kai ga cimma nasara a
rayuwanki" khairi tace "toh momma zan fad'a miki wacece ni, amma yanzu azahar yayi bari In
munyi sallah" Da toh momma ta amsa kan ta mike ta haura, miemie ta zo ganganta ta dafa
kafad'arta tare da bubbugawa kan ta wuce itama, Amrah ce ta taimaka mata ta mike sukayi
d'akin khairin....................

Anan sukayi sallah tare, bayan sun idar sukayi adu'o'i suka shaafa Amrah tace "bari In debo
miki abinci kici kan momma ta sauko" abincin taje ta d'ibo mata, bata wani ci mai yawa ba ta
ture, da Amrah suka fito yayi daidai da saukowar momma, miemie, da nuriyyah, zama sukayi,
momma a two seater, Miemie a kasa kan rug, don bata cika son zaman saman ba haka Allah
yayi ta, se nuri da ta zauna a one seater..................

Amrah bata zauna ba tace "bari In d'aura mana abincin dare" sam bata son sake jin labarin
khairi don kuka sossai yake saka ta, don a sadda taji na farko ta jima batayi bacci ba tayi kuka
har idonta ya rine seda momma ta tambayeta me ya sameta amma ta boye da abu ne yafad'a
ciki, "jollof rice kiyi da nama, se pepper soup din cow-tail" Cewar momma, kitchen din ta
shige......................

Gyara zama khairi tayi akan rug din parlorn ta fara da "kamar yadda kuka sani sunana
ummulkhairi sunan mahaifina Umar sanda sannan mahaifiyata sunanta safiyya Ali gamji........."
sallamar musharraf ce ta katse ta, a hankali ta d'aga kai ta kalleshi shima cikin sa'a kanta
idonshi ya fara fad'awa, sanye yake da kananan kaya da alamu be samu yaje sallar juma' a ba
sbd ita, tun kafin sallamanshi kamshinshi ya sanar da ita kusantowarshi haka sauyawar bugun
zuciyarta, sanye yake da black jeans da red polo shirt me guntun hannu, ba tare da ya tanka
kowa ba ya samu doguwar kujera ya kwanta tare da lumshe ido.................

Ba yadda khairi ta iya haka ta ci gaba da bada labarinta daki daki, tun daga kan labarin iyayenta
har nasu, har zuwansu gombe da abinda ya faru dasu 'batar d'an uwanta, neman aikinta zuwa
ga fyaden da ya so afkawa cikin rayuwanta su musharraf suka ceceta kawo yau..................

Kuka nuri da miemie ke yi bilhakki yayinda silent tears ke bin fuskan momma, musharraf kam be
bud'e idonshi ba ma balle In san wani hali yake ciki, khairi ma kukan take momma ce tayi karfin
halin share hawayenta tace "kuyi shiru dan Allah kuna kara mata ciwon abinda ke ranta" se
shiru su nuri sukayi amma hawaye yaki dena fita sossai tausayinsu khairi ya kamasu, momma
ce ta dinga lalla'ba khairi da kalamai masu daadi har ta samu tayi shiru.................

Duk abunda sukeyin  nan idon momma na kan musharraf tana son sanin halin da ya shiga jin
labarin khairi amma yaki bata daman sanin hakan, don ko motsi be yi ba balle ya nuna alamun

yaji komai, tun kan ta gama jin labarin khairi take kitsima abu a ranta kuma tana fatan
tabbatuwarshi sede bata San ko khairi zata amince ba.....................

A hankali tace "ummulkhairi zaki iya auren d'ana musharraf???" Ba khairi da musharraf ba har
miemie da nuri seda maganar ta dake su, da sauri ya mike ya zauna yana warowa momma
idanunshin nan, harara ta sakar mishi tana kau da kai tace "ba zan tilasta ki ba, sbd banda
wannan hurumin amma Ina mai tabbatar miki ba yabon kai ba d'ana ze iya zama miji na gari a
gareki sbd kyawawar halayyanshi, duk da rayuwa ya chanza min shi, amma har yanzu shi dinne
de daga ciki, I want my old son back, Ina kwad'ayin miki samun miji kaman shi, a lokaci d'aya
Ina mishi kwad'ayin samun mace irinki me kyau, baiwa, ilimin addini da tarbiya...................

Zaki iya zuwa kiyi tunani kuma kiyi shawara, be wise and chose what will be best for yhu and ur
family daughter, all the best dear" musharraf ze yi magana kenan suka ji hayaniya daga waje
gashi an fara yayyafi duk da musharraf be son shiga ruwa haka ya mike ya fito su momma suka
biyo bayanshi, daga kan varendern parlorn ya tsaya yana kallon mai gadi na kokuwa da wani da
be sani ba ko don be lura da kyau bane oho................

D'aga hannu yayi ya yafito me gadin hakan yasa ya sake mutumin suka nufo wurinsu tare, yana
matsowa kamanninshi na fitowa, wani irin tsawa da ya tsorata dukkansu musharraf yayi inda
yace "me ya kawo ka!!!! Me ya kawoka inda muke??? Ka manta mu marasa anfani ne? Ka
manta mu kashin tsiya ne? Ka manta ni marar tarbiya ne? Ka manta uwarmu ballagaza
ce?"....................

Kuka mutumin da khairi bata san wanene ba ya fashe dashi yana durkusawa kasa ga ruwan se
kara karfi yake, cikin sanyin murya yace "na tuba Abubakar ku yafemin, fatima ki taimakamin
don Allah na kwanta da yardar 'ya'yana da kuma adu'arsu a kaina, wallahi na chanza ba
senator Mahmoud Adam da kuka sani ba ne a da, I'm so sorry for all my mistakes, plz find place
in your heart to forgive me ko ba don ni mijinki ba ko ba don ni cousin dinki ba, ko don ni
musulmi d'an uwanku".....................

Momma da ta fara hawaye musharraf ya kalla tare da lumshe ido a hankali ya bud'e har sun
sauya kala a zafafe yace "baza mu yafe ba, ka fice ka bar min gida wallahi na tsaneka, tsana
mafi muni a duniya da Allah ya bamu daman kisa ko da na mutum d'aya ne da kai zan fara
kashewa a rayuwata, tirrrr tirrr Ina ma ana chanza uba? Nayi Allah wade da ranar zuwanka
du............" tasssssss tasssss momma ta d'auke musharraf da mari hagu da dama a zafafe tace
"baka da hankali Abubakar mahaifin da ya tsuguna ya haifeka kake gayawa irin wannan
magana? Irin tarbiyan da nayi maka kenan Musharraf??" Baya baya ya fara har ya sauka daga
kan varender din ruwa ya soma dukan shi sossai don ruwan ya fara karfi.....................

Da tsantsar mamaki yake kallon momma ya manta when last ta d'aga hannu a kanshi a
rayuwanshi gabad'aya amma yau yau sbd wannan mutumin mommanshi me ji dashi ta iya
d'aga hannu ta mareshi har sau biyu, hawaye ne ya fara zuba a idonshi wadda In ba ka kula
sossai ba baza ka gani ba sbd ruwan dake zuba a kanshi....................

Da sauri nuriyyah ta zo gaban momma tace "momma me yasa zaki d'aga mishi hannu bayan ya
fad'i gaskiyar abinda ke ranshi? Ba hamma musharraf kad'ai ba ko ni bazan iya yafewa wannan
mutumin ba ko kin manta halin da ya jefaki a ciki? In kin manta naki na san baza ki ta'ba manta
nawa ba, In kuma shima kin manta na tabbatar ko za'ayi duniya sau nawa ne baza ki ta'ba
manta na hamma musharraf ba, yanzu akan wanchan azzalumin kika mari hamma?"
..................


Juyawa tayi kan baban nasu tace "A rayuwana ban ta'ba ganin mutum me son kanshi irinka ba,
duk abinda ka mana be ishe ka ba se ka dawo ka raba  kan mu? Hakan da kakeyin kana
tunanin ze sa mu soka? To Albishirinka hakan sede ya kara mana tsananka, tsana kuma wadda
tafi ta yanzu" momma tace "nuriyyah plz" nuriyyah da yanzu take kuka on top of her voice tace
cikin tsawa "then he should leave and never come again".....................

Kallonshi tayi tace "leaveeeee!!!!!" Cikin muryan kuka kuma a tsawace, mikewa yayi yana kuka
ya fice, musharraf dake tsaye kaman gunki ne ya fara layi basu ankara ba se fad'uwarashi suka
ji, da gudu sukayi kanshi momma dake kuka sossai ne ta fara jijjigashi tana kiran "musharraf
musharraf Dan Allah ka tashi, no plz kar ka min haka wallahi ba da niyya na mareka ba,
musharraf! Musharraf!! Musharraf!!!"....................

Mai gadi ne yaje da gudu ya kira drivern momma da na musharraf din suka zo suka sashi a
mota, Amrah da zuwan baban nasu ta fito itace taje da gudu ta d'auko musu hijabai, momma ta
kalli khairi tace "plz khairi ki kula da zarah dake site din musharraf" bata jira amsanta ba ta bisu,
da gudu suka fice zuwa asibiti, FMC suka je take family doctor d'insu ya kira wasu doctors din
suka rufu kan musharraf da numfashi ke shirin barin kirjinshi.................









*ga na gobe😊 don gobe baza ku jini ba*

#vote
#share
#comment








'Yar mutan Adamawa



🎗🎗🎗🎗🎗







                IGIYAR RAYUWA😭







                                             🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

                   'Yar mutan Adamawa

Page➡�5�⃣2�⃣▶�5�⃣3�⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Musharraf ba shi ya farka ba se bayan magrib, a hankali ya bud'e ido yana kallon momma dake
zaune kan sallaya tana karatun Qur'an a wayanta, mayar da idon yayi ya lumshe yana tunanin
marin da momma ta mishi sbd mutumin Chan, duk tunaninshi yayi ya rasa me yasa momma ta
mareshi don ya gayamishi abinda y dace dashi da rayuwanshi....................
A hankali ya mike ya zauna tare da gyara pillown da yake kai zuwa bayanshi ya jingina yana
taune lips sbd kanshi da ke Sara mishi da jirin da yake ji, motsin shi ne ya sanar da momma
farkawanshi tsayar da karatun tayi tana kallon gadon, ganin da gaske ya farka ne yasa ta
mikewa tana cewa "sannu musharraf"....................
Kai ya gyad'a ba tare da ya kalleta ba, a hankali tace "wai kai se yaushe zaka girma ne ka san
abinda yake daidai da wadda ba daidai ba?" Tura lips dinshi yayi ba tare da yace komai ba,
seda ta kuma cewa "ba da kai nake ba musharraf?" Yace "Toh ni momma me kuma nayi bayan
ba nine da lefi ba kika mare ni gaban kannena da masu aiki" murmushi momma tayi tana girgiza
kai tace "Toh yanzu fushi kake da ni kenan?" Kara tura bakin yayi ita kuma ta saki murmushi
tana cewa "Toh kayi hakuri, na san ba lefinka da be maka abinda ya maka ba da baka
fad'amishi ko wacce kalma ta fito daga bakin ka ba"........................

Ajiyar zuciya ta sauke kan ta ci gaba "Ina kwa'bar ka ne don bana son Allah ya kama ka da laifi,
sbd uba de uba ne ko min lalacewarshi adu'a ne kawai tsakaninku ba wai zagi ba, yanzu In ni
ce nayi maka haka haka zaka dinga zagi na?" Had'e rai yace "subhanallah ki dena kwatanta
kanki dashi plz momma, baza ki ta'ba ko da kwatanta abinda ya aikata ba" girgiza kai tayi tace
"In yana cikin kaddara na dole hakan ya kasance ko da kuwa bana so, shi yasa nake so ka
yarda kaddaranshi kenan, ku yafemishi tabbas ya tuba, don naga hakan" Shiru yayi be ce
komai ba....................

Kanshi ta ta'ba jin jikinshi har yanzu da zafi yasa ta mikewa tace "bari na kira doctor zazza'bin
nan be sauka ba" hannunta ya rike yace "a'a momma zanyi sallah tukuna ko la'asar banyi ba"
duk maganganun da yake yin nan muryanshi ba wani fita yakeyi ba sbd mura da ciwon kai,
bowl ta samo mishi a toilet da ruwan gora ta rike mishi yayi alwala don ba ze iya mikewa ba sbd
jiri haka yake mishi In har jininshi ya hau...............

A zaunen yayi sallah yana idarwa ta sa mishi pepper soup da Amrah tayi, da kanta ta dinga
bashi har ya ce ya koshi, magunguna ta 'balla mishi wadda bata jima da sayowa ba, yana 'bata
fuska yana komai haka ta sashi sha dole, yana gama sha doctor na shigowa da fara'a ya mishi
sannu da jiki amsawa musharraf yayi yana d'an murmushi....................
Dube dubenshi yayi kan yace "masha Allah, Dan Allah ka kwantar da hankalinka samun jinin da
ya hauran nan ya sauka" murmushi kawai musharraf yayi ba tare da ya ce komai ba, fita doctor
Aslam yayi don ba yau ya san halin musharraf ba, momma tace "ga jallabiya nan ko zaka
chanza" kar'ba yayi ta fice daga d'akin bayan wasu mintuna ta dawo da waya sakale a kunnenta
tana kallonshi ya chanza zuwa jallabiyan brown color sossai ya mishi kyau kaman ba shine

mara lafiya ba........................

"Eh yaya, amma da sauki sossai a'a hawan jinin ne de, toh mun gode se da safe" tana kashe
wayan ta kara danna wani layin bayan an d'auka suka gaisa tace "Rabi'ah ya kk ya su afreen?"
Be ji me aka ce daga d'ayan bangaren ba se momma da tace "Toh gashinan de musharraf ne
Wlh ba lafiya muna asibiti" Shiru tayi kan tace "Eh amma da sauki sossai, Ohk toh se
kinzo"...............

Bayan ta kashe ta kuma yin wani kiran "hello taheer ya kk?, ya su takwara na? Eh dazu da
mukayi waya da yaya Ahmad ya fad'amin.......... Ohk toh dama musharraf ne ba lafiya yana nan
FMC......... wlh hawan jinin de........ Ohk toh se ka zo se da safe"..............

Zatayi wani kiran taji an rike hannunta d'ago kai tayi tana kallon musharraf tace "lafiya de ko?"
'Bata fuska yayi yace "momma dan Allah de wayan ya isa, na san yanzu gobe d'akin nan ze
koma kaman kasuwa wlh kuma kin san bana son hayaniya" waro ido tayi tana cewa "don baka
son hayaniya se bazan fad'awa dangi ba? Yanzu dakata bari inyi waya da hajiya ruqayyah se
muyi wata magana tunda na ga kaji sauki"....................

Yana saurarenta har ta gama waya da hajiya ruqayyan ita ma rashin lafiyanshi ta fad'awa kan ta
kalleshi tace "An kawo tambayan Saliman Yaya Ahmad" karamin murmushi yayi a zuciyarshi
yace ta gaji da jiran gawon shanu kenan, a fili kuma se yace "Allah sanya alheri" momma tace
"Ameen amma yaushe rabonka da gidan yayyun mahaifinka da kannena?" Yana 'bata fuska
yace "momma In na zo ba lokaci kema kin sani, last zuwana ma seda na shiga time din aikina
da kika sani zuwa dukku wurin grannys" momma tace "wannan ba hujja bace dukkansu cikin
gombe suke ba wani gari ba balle kace akwai tafiya me yawa tsakani wallahi ka gyara halinka
musharraf"...................

Zamewa yayi ya kwanta yana dafe kai, tace "Toh ba wannan ba ma, musharraf Da gaske nake
har zuciyata Ina maka kwad'ayin auren khairi, In har kana son farin ciki na da kwanciyar
hankalina toh ka aureta" Shiru yayi na mintuna tukun ya sauke ajiyar zuciya kan yace "In haka
kike so momma so let it be, Allah ya sanya alheri" murmushi tayi tana jin son d'an nata har cikin
ranta duk abinda tace take so ko da baya so haka ze yi shi..................

Maganan da take son mishi na gaba shine na shan taba amma tafi son se an sallameshi sun
koma gida tukuna, abinci ta di'ba taci suna hira jefi jefi har ta gama, bargo ta d'auko ta lullu'ba
mishi, ta kuma shimfid'a wani akan sallaya ta jefa pillow ta kwanta tana rufuwa da hijab dinta,
cikin tausayawa yake kallonta Eyyah uwa de ko ya take bata gajiya da d'awainiyar yaronta tun
daga yarantan shi har girmanshi yanzu dubi a kasa zata kwanta da girmantan nan bayan shi
yana kwance akan gado...........................

Washegari

Kamar yadda khairi ta saba da wuri ta tafi wurin aikinta, duk basu tashi ba, ta fere dankali ta

soya da kwai, ta dafa black tea da yaji kayan kamshi, ta san dole akai na asibiti hakan yasa
bata jira tashin su nuri ba ta shirya a basket ta fito ta ba driver ya tafi dashi, sauran ta shirya a
dining, ta gyara kitchen din, bata jira komai ba ta d'aura abincin rana, dambun shinkafa tayi da
sous na hanta, se tayi pepper soup na kayan ciki da fruit salad.......................
Lokacin da ta gama 11 yayi, tana fitowa parlor su nuriyya na saukowa duk a shirye suka sauko
har little sun shirya ta cikin duguwar rigan atampha orange da black se white hijab da white
shoe tayi kyau sossai, da murmushi ta musu barka da safiya suna nufan dining suna kuma
gaisawa, Amrah na tambayar khairi ya su nabeel da dada, tana amsawa da suna
lafiya..................

Little da ke rike da hannunta ne tace "cutie I want to see them plz come with them 2morrow"
nuri tace "gaskiya nima Ina son ganin twins din nan da su miemie suka dameni da kyaunsu"
khairi tace "Adda Ai suna zuwa islamiyya ne shiyasa ban ta'ba zuwa dasu ba" little tace "plz plz
plz cutie su hakura da na gobe kawai su zo mu yini plzzzzzzz" Amrah tace "yes plz Tbest"
miemie tace "please" nuriyyah ma tace "plz Adda khairi" a tare suka sa dariya har khairin tana
girgiza kai tace "Toh shikenan zan zo dasu In Allah ya kaimu" "yeeeaahaahhahhhhhh💃💃"
little ta dinga rawa da tsalle...................

Khairi ta ja kujera ta d'auke ta ta d'aura ta akai tana cewa "oya ci abinci tukun ki tsayawa
mutane da rawan" wani dariyan sukayi tana kallonsu tace "Toh yanzu Anties breakfast zaku ci
ko lunch?" Miemie tace "khaih kar de har kin gama lunch?" Khairi ta gyad'a kai tana murmushi
nuri tace "weldon khairi na asibiti fah?" Khairi tace "tun 8 na bada driver ya kai musu" nuri tace
"masha Allah sannu da kokari" murmushi kawai khairi tayi......................

Amrah tace "nide chips zanci se in mun dawo hospital se inci lunch ko kuma inyi achan don na
san su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login