Showing 36001 words to 39000 words out of 117506 words

Chapter 13 - IGIYAR RAYUWA Hausa Novels Complete Document.pdf

Unknown   

18 May 2025

8452

amma seda taji cikinta ya d'uri ruwa, horn ya buga ba 'bata lokaci wani ya fito
ganin motar yasa ya koma da sauri aka wangale gate din suka kutsa kai har gaban entrance na
parlorn gidan musharraf ya Parker haidar ya juya ya kalli khairi yace "muje ko" fita tayi shima ya
fita da sauri suka haura steps na kofan parlorn shi haidar ya d'auka musharraf dinma ze shigo
se gani yayi ya ja motar a guje ya fice daga gidan...................

Girgiza kai kawai yayi yana shiga parlorn da sallama khairi na biye dashi har yanzu kuma tana
share hawaye, hajjiya rukayyah ce zaune kan kujerun parlorn a had'e take cikin leshi me tsada
da ya amsa sunanshi dukda mijinta baya gari kwalliyan nan de baya barin jikinta murmushi ta
sakarwa haidar da ke tsaye.................
Tana nuna mishi set din kujerun ledan dake gefenta ganin jikinshi a jike baza ta yadda ya zauna
mata a royal cushion ba, murmushi shima yayi yana zama dama ya sani, a kasan tiles khairi ta
zauna tana takure jikinta idon Maami a kanta har tayi sallama da mijinta tukun ta kalli haidar ta
kuma kalli khairi ya gane me take nufi hakan ya sa ya bata labarin abinda ya faru................
Ta tausayawa khairi sossai dayake Allah yayi ta mai tausayi da jin kan talakawa tace "en mata
ya sunanki?" A hankali khairi tace "ummulkhairi" jijjiga kai Maami tayi ta kuma cewa
"ummulkhairi me ya fito dake da dare kuma cikin ruwan nan har mummunan abu ya so samunki
ba don Allah ya turo su haidar ba" a natse ta fad'a mata abinda ya fiddo ta.................

Cikin tausayawa Maami ke kallon khairi kan tace "kar ki damu bari In had'a ki da autata kiyi
wanka ki chanza kaya ki ci abinci gobe se akai ki gida" tun kan Maami ta karasa khairi ke
girgixa kai tace "mahaifiyata makauniyace kannena kuma basu wuce shekara biyar ba na san
suna chan hankali tashe bazan iya kwana ba kiyi hakuri hajiya".................
Cikin tausayawa Maami tace "toh za'a maida ki gida amma se kinyi wanka, zaki kuma tafi muku
da abinci gobe In shaa Allahu zan tura drivern da ze kaiki yau ya d'aukeki zuwa gidan wata
aminiyata dake neman er aiki" cikin tsantsan farin ciki da ya gaza 'boyuwa khairi tayi ta godiya,
Hafsat maami ta kira ta had'ata da khairi, hafsa ma tana da kirki kaman en gidansu Cewar khairi
dake wanka kenan bayan hafsa ta nuna mata yadda zata yi anfani da duk toiletries
d'in....................

Tana fitowa hafsa ta bata doguwar riga da gyalenshi ta saka tayi kyau sossai kuwa komawa
parlorn sukayi ta samu Maami ta sa an shirya mata abinci cikin basket bata ga haidar ba don ya
jima da shigewa part dinshi dake gidan duk da yana da gidanshi amma zamansu gidan
iyayenshi yafi yawa sbd yanayin aikinshi kuma be son dinga barin matarshi gida ita kad'ai da
yara...................

Driver Maami ta kira lokacin karfe tara na dare kuma ruwan ya tsaya, ya d'auki basket din khairi
ta bi bayanshi kan ta fita Maami ta kirata ta dawo kud'i ta d'auko da d'an yawa ta bata Tace "inji
haidar, ga wannan" ta bata wani leda da bata san me a ciki ba godiya sossai tayi kan ta fice
ranta kal................










#vote
#share
#comment





'Yar mutan Adamawa

��潤����潤����潤����潤����潤��








IGIYAR RAYUWA��踫葉







��潤����潤����潤����潤����潤����潤��

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad: Gureenjo

'Yar mutan Adamawa

Page��∴��3儭����6儭������塚��3儭����7儭����
��潤����潤����潤����潤����潤����潤����潤����潤��

Har kofan gida drivern ya kaita tayi mishi godiya sossai kan ta fice, da sallama ta shiga gidan
hakan yasa Dada da ta zuba tagumi sauke nannauyar ajiyar zuciya tana zaune ne kan turmi
dukda sanyin da garin ya d'auka ta tabbatar damuwar da mahaifiyarta ta shiga baze fad'u ba a
hankali ta kira sunanta "ummulkhairi".......................
A raunane ta amsa sbd tuno abinda ya so faruwa da ita awanni kad'an da suka wuce tabbas da
ya farun da bata san wani hali zasu shiga ba ita da waennan en uwa nata, hawayen fuskanta ta
share tare da gyaran murya jin dadan ta fara magana cikin sanyi "khairi me ya ajiyeki a waje
haka kin san ba magriba kukeyi a waje ba yanzu fah goma saura".................
Bata jira Cewar khairin ba ta kara da "lafiyanki ko? Ba wani abinda ya sameki? Wallahi tun
fitanki gabana ke ta aikin fad'uwa" murmushi khairi tayi hawaye na kuma zuba mata ta karasa
gaban dadan tana Jan er kujerar tsugunonsu ta zauna kan tace "lafiyata kalau dada kin ga ma
albishirinki?" Dada tace "goro" khairi tace "Dada na samu aiki, matar ce ma ta riqeni ganin

hadari se da ruwa ya tsaya tukun ta had'ani da drivern ta ya dawo dani gobe ma in shaa Allahu
shi ze zo ya d'auke ni"...............

Ta karasa with so much excitement in her voice, ta boyewa mahaifiyarta ibtila'in da yaso afka
mata, farin ciki sossai ya bayyana a fuskan dada a fili tace "Alhamdulillah, Alhamdulillah ya
Allah ka ci gaba da rufamana asiri duniya da lahira ba don halinmu ba" cikin murmushi khairi
tace "Ameen mamanmu, Ina su nabeel ne ban ji su ba" Dada tace "suna ciki sallah sukeyi tun
d'azu suke jiran dawowarki da kyar na sasu yin magrib kin sansu da kafiya Toh isha dinma se
yanzu suke mika ta".......................

Khairi ta gyd'a Kai ta kuma cewa "Allah ya sa ba abinda kuka ci don hajiya ta had'oni da abinci
don naki ci a chan gidantan harda abu a leda ta ban kinga ko bud'ewa banyi ba" cikin jin daadi
ba wai don abincin ba se don jin daadin khairi ta samu uwar d'aki me mutunci don a wannan
zamani me mutuncin ne kawai ze iya maka haka, dada tace "aaa harda d'awainiya Toh Allah ya
saka, ai ko an gode dama ba wani abinda muka d'aura".............

Khairi tana cikin bud'e coolers din su nabeel suka fito da gudu suna cewa "oyoyo Adda" fasa
bud'e flask din khairi tayi tare da taran kannenta cikin murmushi tace "oyoyo chutu'ben dada"
(chutu'be means en biyu da fulatanci) rungumesu tayi tana jin kewar kannenta bayan ta sakesu
tace "Dada ya kamata mu koma ciki wajen nan akwai sauro ga sanyi".............
Komawa ciki sukayi Allah ya sa akwai wutan nepa tarwal a gidan bayan d'auke ruwa suka dawo
dashi, plates khairi ta d'auko musu da serving spoon ta zo ta bud'e coolern fried rice ne
had'add'e da pepper chicken se cowslow a gefe da yaji kwai, a lokacin In kaga fuskan waennan
familyn zaka tabbatar suna cikin farin ciki saka musu tayi yadda ze ishe su sukayi bismillah suka
fara ci a natse.................

Har suka gama ci ba wadda yayi magana a cikinsu daad'in abincin kam ya wuce misali, bayan
sun koshi suka ajiye saura a kitchen kan nabeela ta dawo ma khairi ta bud'e ledan aiko
designers abaya ne masu kyau guda biyu se turaruka arabian perfumes guda biyu, se kud'in da
haidar ya basu 10 thousand...................
cikin jin dad'in karamcin maami da haidar khairin ta d'aurawa Dada kayan akan kafa tatta'bawa
dada tayi tana sharara musu adu'a kan ta mayarwa khairi kayan khairi tace "Dada baza ki dau
d'aya ba?" Dada tace "a'a ernan rabani ni kam Ina ni Ina kayanku na zamani balle ni da ya
kamata in d'au nauyinku bayan kushewar mahaifinku se kece ke d'awainiya dani ni Ina nan bani
da anfanin komai"..................

Ta karasa da sanyin murya da alamun abun na damunta, da sauri khairi tace "haba dada me
yasa zaki ce haka ke kika fi komai anfani a garemu a yanzu haka dan Allah ki daina daurawa
kanki damuwa dama tun asali d'a ne ya kamata ya ji kan iyayenshi bayan ya mallaki hankalin
kanshi bare ke da lafiya bata isheki ba" murmushi kawai dada tayi tace "hmmm khairi kenan
d'awainiyar ya mace bai barin kan iyayenta har se sun damka ta a hannun mijinta, don ba

yadda zanyi ne kawai, ki d'au rigunanki turaren ma ki d'au d'aya kya bar mana d'ayan mu dinga
fesawa da kannenki...................

Sannan kud'in ki cire mana na kayan abinci se ki duba makaranta anan kusa na gomnati ki sa
kannenki, daga baya ke kuma maga yadda Allah ze yi" khairi tace "Hakan yayi Allah ya shige
mana gaba" ta mike ta cire na jikinta wadda hafsat ta bata ta had'a da sauran ta adana kan ta
fita tayo alwala tazo tayi isha dama tayi magrib gidansu haidar kan suka kwanta sbd sanyin da
gari ya d'auka, tsintar kanta tayi da tunanin wadda aka kira da musharraf ajiyar zuciya ta sauke
tana lumshe ido view din kyawawan lumsassun idanunshi da yake hararanta da shi ya dawo
mata tsab kaman wadda ta d'au videon ta ajiye tana kallo a haka har bacci ya d'auke
ta..................


*******

Da kyar musharraf ya kai kanshi gida jikinshi na tsananin rawa hakwaranshi na had'ewa duk da
zafin da motan ke fitarwa hakan be hana shi jin sanyi ba, horn ya danna malam d'ahe ya zo da
gudu ya bud'e mishi kan motan na galau galau haka ya shiga da ita be iya shiga parking lot ba
ya Parker ta tsakiyar gida, zama yayi a motan yana kallon ruwan dake zuba har isowarshi
gidan..............

Shahada kawai yayi ya bud'e motar ya fita sede ya kasa sauri hakan yasa ruwan ya ci gaba da
dukanshi har ya isa d'akinshi zubewa yayi kan gado yana Jan bargo duk da jikinshi dake a
jike................

Zaune suke a parlor suna jiran shigowarshi tunda ya danna horn zahra ke tsalle kwana biyu
kennan bata sa mahaifinta a ido ba tayi ta kiran wayanshi yaki shiga, ita, momma, Amrah, nuri,
miemie, salima se Maryam ne kawai zaune a parlorn yayi nasaran koran Afreen, da Zainab inji
ta fad'ar momma...............
Ganin har mintuna 10 sun shige da shigowarshi ne yasa momma mikewa taje ta bud'e kofar
parlorn tana duba waje, don In har Musharraf ya shigo gari be ta'ba biyawa wani waje be fara
zuwa wajenta ba, sede In ba lafiya ba, yadda taga parking na motar kad'ai ya sanar da ita ba
lafiya ba, da sauri ta fita tana kira nuri tare suka fita zuwa part dinshi ko wuta be kunna ba seda
suka shiga ne suka kunna................

Suna shiga d'akin tun daga bakin kofa suke iya ganin yadda jikinshi ke rawan sanyi da kuma
atishawar da yake ta jerawa da sauri momma ta karasa tana yaye blanket din jikinshi a d'an
rud'e tace "Musharraf me ya shigar da kai ruwa bayan ka san yanayinka? Ina shi haidar d'in
yake har ka shiga ruwa ba tare da saninshi ba? Musharraf ka fa san yadda ruwa ke wahal da
kai?"..................

Shiru yayi nuri ce tace "momma ki sa shi ya cire jikakkun kayan nan sanyi na kara shiganshi da

su bari inje In dubo me zan iya bashi da first aid" da yake nuri likita ce, da sauri ta fice momma
ta taimaka mishi ya mike da kanta ta ciremai rigan taje drower dinshi ta d'auko mishi sweater
riga me had'e da wando na cotton me taushi blue tazo ta mikamai tana cewa "lalla'ba ka tashi
ka je ka watsa ruwan zafi zaka rage jin sanyin".............
Da kyar ya mike ya nufi toilet momma ta bishi da towel da kayan, ruwan zafi ta had'a mai tare
da ajiye mai kayan da towel din kan mirror stand dake bayin ta fice a d'akinshi ta zauna zaman
jiran shi be fito ba har nuri ta shigo hannunta d'auke da tire da d'an madaidaicin flask da cup a
kai se wasu magunguna a gefe, ajiyewa tayi akan bedside tana cewa "momma ga wannan se ki
bashi in ya fito, bari inje inji da namesyn kin nan kin san yanayinsu d'aya da babanta amma se
rikici takeyi wai se ta zo ta ga paapinta"...................

Murmushi momma tayi tana cewa "'yar kwal uba da kin barta ta biyoki In yaso su had'u su
kwanta tare" nuri na murmushi ta fice, fitan nuri ba da jimawa ba wayan momma ya d'auki kara
haidar ne ke kiranta dama yanzu take tunanin kiranshi taji ya akayi musharraf ya shiga ruwa
haka, d'auka tayi suka gaisa ta tambayeshi gajiyar hanya inda yace "gajiya yabi jiki momma,
dama musharraf nayi ta kira inji ko ya isa gida lafiya amma baya d'agawa"..................

Momma tace "Ina ko ze d'aga bayan yana fama da ciwon shin nan de, me ya shigar dashi ruwa
hk haidar?" Nan haidar ya bata labari ya kara da "gani nan zuwa In ya so se in kwana dashi"
momma tace "Allah sarki Allah ya ci gaba da kare mna 'ya'yanmu mata da irin waenchan maza
Allah kuma ya saka muku taimakon da kuka mata, sannan ba se ka zo ba kai da kayi tafiya ka
dawo matarka na bukatar kulawarka kayi zamanka zan kula da shi"...................

Sallama sukayi bayan haidar ya mishi adu'ar samun lafiya, suna cikin waya da haidar ya fito
sanye da kayan sanyin da suka mishi kyau sossai, gado ya hau ya zauna yana kame jikinshi
atishawa kam yayi su ba adadi ga muryanshi ya dishe makokoronshi se zafi yake mishi yana jin
kaman an shake shi, kaman ze yi kuka yake kallon momma yana jiran tayi mai fad'a se ji yayi
tana cewa "sannu ga coffee nuri ta kawo maka ka samu ka sha se ka had'iyi
magani"...................

Tsiyaya mishi tayi a cup ta mika mishi kar'ba yayi yana sipping a hankali jikin rau kaman wuta, a
zuciyarshi kuwa ba masifan da be yi ba duk ya d'aura laifin kan khairi da ya lakabawa suna da
'kantin ball' ��橙提 Wai idonta kaman kantin ball (inji musharraf fah ba ni ba tohm��踫��) so sunan da
yake kiranta kenan a fili kuma yayi tsaki yafi dubu..............
Bayan ya gama shan coffee d'in ya sha maganin tare da sulalewa ya kwanta momma taje
wardrobe dinshi ta samo socks ta zo ta saka mishi tare da ja mishi blanket ta rufe shi, kanshi ta
dawo tana ta'ba temperature d'in jikinshi a hankali tace "sannu babana Allah ya biyaku taimakon
da kukayi, Ina wayanka?" Yace cikin dashewar murya "yana mota" tace "bari inje In d'auko
maka zuwa anjima In na tafi kaji jikin ya matsa maka se ka kirani koh?" Shiru yayi ita kuma ta
juya ta fice...................

Washegari��潤����潤��

Yadda khairi ta saba tashi a kwanakinnan haka ta tashi tayi komai yadda ta saba tayiwa su
nabeel wanka suka shirya cikin uniform d'insu na islamiyya ta rakasu har islamiyyan tana
dawowa ne ta tsaya gidan Maman hamdeeya suka gaisa tayi mata albishir samun aikinta ta
tayata murna sossai............
Bayan khairi ta koma gida ta fara zaman jiran driver jefi jefi suna hira da Dada ta matsu sossai
ta ganta gidan tana son zuwa wani government day secondary school da ta gani daga Chan
farkon unguwan ta duba me da me zasu bukata na admission din su nabeel amma tana tsoron
kar ta tafi driver ya zo...............
Se around 11 sukaji an kwad'a sallama khimar khairi ta d'auka ta sanya tana shewa dada "se na
dawo" Dada tace "Allah ya tsare ya bada sa'a" fita khairi tayi ta shiga motar tana gaida drivern
din cikin fara'a ya amsa ta kan ya tada motar suka bar unguwan...............

Masha Allah take ta furtawa ganin unguwan da suka shigo gidajen cikinshi masu tsananin kyau
da d'auke hankali unguwan shiru sossai, a tsanake drivern ke tafiya har ya iso gidan ya danna
horn malam d'ahe ya wangale gate d'in suka shige kan su shiga ma drivern ya tsaya suka gaisa
yace mishi kar ya rufe ajiyeta kawai ze yi ya tafi...........
Ai ko yana ajiyeta ya juya d'ago kan da zatayi idonta ya fad'a cikin nashi a tare zuciyarsu ya
buga da tsananin karfi da har seda ta hard'e da kayan jikinta ta kusa fad'uwa kan ta d'ago kuma
bata ganshi ba, kofar da ta tabbatar shine na asalin cikin gidan ta nufa, a hankali ta fara
knocking, ta kusa five minutes a tsaye tukun taji an bud'e.................









#vote
#share
#comment

'Yar mutan Adamawa


��潤����潤����潤����潤����潤��







�� �� �� �� �� �� �� IGIYAR RAYUWA��踫葉






�� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� ���� ��潤����潤����潤����潤����潤����潤��


Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

�� �� �� �� �� �� 'Yar mutan Adamawa

*~~dedicated to MU KARU DA JUNA group, a gaskiya Ina jin daad'in comments d'inku, bani da
abinda zan biyaku dashi tabbas ba don ku ba da na jima da dena rubutu, but yhu always
support me kune karfin gwiwana thank yhu so very much for the care and support Allah ya bar
kauna~~~*
Page��∴��3儭����8儭������塚��3儭����9儭����
��潤����潤����潤����潤����潤����潤����潤����潤��

Wata kyakyawar yarinya da baza ta wuce sa'ansu nabeel bace ta gani tsaye cikin shigan
kananan kaya Jeans da pink tshirt, kanta kitson kalba masu kyau an sa mata beats, murmushi
ta sakarwa khairin hakan ya sa khairin ma sakar mata murmushi............

"Hey cutie I'm fatima Abubakar Mahmoud but yhu can call me zahra or little, yhu are beautiful"
murmushi kawai khairi tayi mata kan tayi magana taji ance "little wanene a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login