Showing 3001 words to 6000 words out of 117506 words

Chapter 2 - IGIYAR RAYUWA Hausa Novels Complete Document.pdf

Unknown   

18 May 2025

8443

ta kara murd'awa tana danne
hakwaranta da gudu Abul da Abba sukayi kan khairi suna kokarin cire hannun khairi amma ko
motsa hannun sun kasa hauwa ma ta karaso da d'ingishi tana ture khairi wani wawan mari me
kurmantarwa khairi ta sakewa hauwa da hannun hagunta inda ta ci gaba da murd'a hannun
uwar da na damanta, zuwa lokacin duk makwabta na kusa sun shigo mazan suka taru suna
kokarin cire hannun Maman hauwa a cikin na khairi amma abun ya ci tura da sauri Abba ya nufi
kitchen ya d'auki cup tare da kanfatan ruwa a randar kasarsu wasu adu'o'i yayi da sauri da sauri
ya tofa tare da zuwa ya watsawa khairi a fuska wani irin ihu ta sake tare da sulalewa kasa ta
sume nan kukan Maman hauwa ya cika gidan ita da 'yarta tana ta fad'in "ta karyani shikenan ta
nakastani kaman uwarta" nace(Lallai matan nan wato bakin nan be mutu ba) wasu daga cikin
waenda suka shigo ne suka fice da ita, yayinda gidan ya saura daga su Abba se sulaimi da
iyayenta, wasu adu'o'in Abba ya karatofawa a same ruwa tare da watsawa khairi a hankali ta
motsa tana dafe kanta da take jin kaman ze rabe sheshekar kukan mahaifiyanta da kannenta
yasa ta fashe da kuka itama dukda bata san me y faru ba amma tasan abun beyi kyauba,
sulaimi ce ta kamata zuwa kan taburma inda Abul ya kama hannun Dada ya zaunar da ita yana
share mata hawaye Abba kuma na lallashin su nabeel, seda iyayen sulaimi suka ga gidan ya
d'an natsu tukun suka saka 'yarsu a gaba suka fice suna adu'ar Allah ya kiyaye gaba, sossai
khairi tayi kuka inda take ta maganganu tana neman yafiyar iyayenta musamman dada da ta sa
kuka anan ne take fad'an "wlh Abba ban mata komai ba haka ban saka idi shed'an bugunta ba
Wlh banda masaniyar hakan ze faru da data bangajeni ban tanka mata ba da shiru nayi
kaichona...." Abba ne ya katse ta "kul uwar alkhairi yi shiru abinki ba laifinki tun kafin a haifeku
take nuna mana wannan hali, ta musgunawa mahaifiyarku ba kad'an ba" Abul yace "Abbanmu
me kuka mata?" Shiru Abba yayi kaman baze yi magana ba kuma se yace "talatu tazo ta same
mu a unguwan nan da farko a mutunce muka kar'beta duk da bamu san inda ta fito ba hakan be
hana mu bata kulawa ba ganin babban ciki a jikinta kuma tana halin neman taimako ni nayiwa
Bala dillali magana ya bata gidan da taken nan haya da yake da d'an kud'inta ta zo shawarana
ta tambaya na sana'an da zatayi inda na bata shawaran yin abincin sayarwa a bakin kasuwa

wadda har yanzu shine sana'anta bayan kwana biyu da ta d'an natsu se ta tareni da wani
magana wai In ta haihu na yarda na aureta tunda matata makauniya ce, sam na nuna mata
bana sonta ta nemi wani namijin tun Ina mata yadda zata fahimta taki har taja na fara
wulakantata ana haka ta haifi 'yarta mace har nan ta zo ta roki mamanku wai inje In ma 'yarta
hud'uba da sunan da yamin mamanku bata damu ba kasancewar bata san abunda ya faru
tsakanina da ita ba, ta tursasani naje nama hauwa hud'uba da suna hauwa, bayan haihuwan
hauwa ta ci gaba da bina ni kuma naci gaba da wulakantata har ya kai na kai karanta fadan
sarki inda ya ce ta fita harkana don ta matsamin har kasuwa take bina daga lokacinfa ta d'auki
tsana ta daura mana da mahaifiyarku ko motsin kirki bamu da daman yi shine har ya gangaro
kanku, kun ji fah"..........








#vote
#comment
#share


'Yar mutan Adamawa



��潤����潤����潤����潤����潤��






IGIYAR RAYUWA��踫葉




��潤����潤����潤����潤����潤��

Written & story by: fateemah Muhammad Gurin

'Yar mutan Adamawa

Page��∴��5儭������塚��6儭����
��潤����潤����潤����潤����潤����潤����潤��

Tsaye yake gaban balcony d'inshi idonshi na kan rana da yake shirin fad'uwa a lokaci d'aya
hannunshi rike da karan sigari (taba) yana busawa kare mishi kallo na tsaya yi kai gaskiya
gayen had'add'e ne sossai akallah zeyi 34 sanye yake da dark blue jeans da wani yellow riga
me kaman sweater da gashi gashi a jikinshi long sleeve me had'e da hula igiyan hulan sun
sauko gefe da gefe har kan faffad'an kirjinshi, kyakyawar kafanshi fari tas me d'aukan hankali
sanye da yellow normal flat shoe na maza na companin Gucci, a natse na kai idona kan
fuskanshi Ina kare mishi kallo, yana da round face me d'an fad'i tare da kananan ido da ya
had'u da tsiriryar hancinshi zuwa kan lips dinshi masu fad'i kad'an red ko kuma ince maroon
kasancewar shi me shan taba lips dinshi yayi baki kad'an se ya had'u da red lips dinshi ya bada
wani color me d'aukan hankali, abinda yafi d'auke hankalin mata kai harda wasu mazan a
fuskanshi shine kwantaccen bakin sajenshi da ya mugun kawata fuskanshi gashin kanshi
kaman wadda akayi coiling tsaban yauki da murdewa wadda ya zo har kan goshinshi kai masha
Allah, duk da idonshi fad'uwar rana yake kallo amma tunaninshi ba nan yake ba yayi zurfi cikin
tunanin bakar rayuwanshi na baya me cike da duhu da tsananin kalubale tabbas his father is
the villain of his story a take madaidaitan idanunshi da ake referring as kanana sbd kankancesu
da yake yi suka koma red a fili ya furta "A bad egg" meaning worthless person, kara zukan
taban da ya rike da hannun hagu yayi cikin kwarewa har seda karan ya kare jefarwa yayi a kasa
yana shirin kunna wani kenan wayanshi dake cikin pocket dinshi ya fara ringing, kaman baze
fiddo ba yana yatsuna fuska ya fiddo yana kallon fuskan screen din wayan nashi da ya kasance
Samsung galaxy latest one d'in, 'My little' ya gani karamin murmushi da bai gama maye
fuskanshi ba yayi tare da d'auka ya kara a kunnenshi cikin murya irinta yara yaji tana cewa
"Afternoon paaapi" yace "Afternoon sweetheart how are yhu?" Daga d'ayan bangaren tace "I'm
Fyn paapi, paapi I mistakenly broke my laptop" yace "Ohk baby uncle murtala will fix it for yhu,
where is my momma?" He guess tana juya manyan idonta masu kama da balls da ta d'auko
daga mahaifiyarta, sunan kawai da ya kira na 'mahaifiyarta' da yayi guessing a zuciyarshi yasa
yaji ranshi yayi matukar 'baci d'an fara'an da yake kan fuskanshi duk ya 'bace a sama sama yaji
tana cewa "she's at her sitting room lemme take the phone to her" a kasalance yace "no baby I
will call her later, bye take care" ya kashe wayan yana sauke nannauyar ajiyar zuciya juyawa
yayi zuwa cikin bedroom dinshi anan ya cire kaya daga shi se boxers, cikin tafiya ta cikakkun
maza da suka sha gwagwarmayan rayuwa ya nufi bayi tare da tara ruwa a jacuzzi ya shige ciki
tare da lumshe ido yana tuna bakin azabar da ya sha a rayuwanshi......

**
Safa da marwa kawai take tana tunanin hukuncin da zata d'auka akan malam umar sanda da
familynshi idonta ta maida kan hannunta da yau kwana biyu kenan da aka gyara gurdewan wrist
din amma maimakon ya sa'be se kara kumbura yake yi, kaman yadda suka sa ta wahala se ta
d'an d'ana musu bakar azaba rayuwa tabbas akanta zasu san kaidin mace da ake cewa ko

shed'an tsoronshi yake murmushin mugunta tayi da ta tuna abunda ya rabo ta da garinsu wani
d'an banzan munafurci ta had'a har yakai aka yi rashe rashen rai Allah ya taimake ta tana da
ciki da an Kone ta manyan sukace a barta albarkacin cikin jikinta taje amma kar ta sake
shigowa cikin garin ko da bakin wasa shinefa ta shigo cikin garin jalingo, wani murmushin tayi
tace a fili "zaka San ka sa mahaukaciyar 'yarka gurd'ani, bazan bari na warke ba a yau zan
aikata abunda na kudurta akanka, se kayi zaman gidan kaso na shekaru kan ka fito kuma
iyalanka sun tagayyara" wayanta ta fidda ta kira wasu 'yan iskan 'yan tasha tace su sameta da
dare akwai haaja..

Tsaye take a jikin ginin kitchen d'insu ta jingina kanta da jikin gini gabad'aya jikinta a sanyaye da
fad'uwar gaba da take fama dashi tunda garin Allah ya waye, Abba dake zaune kan taburma
kusa da Dada ne ya kalleta, da yake yau ya dawo da wuri tun 4 ya shigo gidan suna ta shan
hira abinsu Abul na zaune gefensu kan turmi yayinda nabeel da nabeela ke wasa a tsakar gidan
duk rabin wasan fad'a ne, Abba na shirin magana kenan nabeel ya kwasa da gudu zuwa kanta
yana Jan hannunta yace "Adda khairi Ina ni kika ce In na iya karatu zaki ba biyar In saya
sweet?" Nabeela ma tazo da gudu ta taho ta rike d'ayan hannun tana cewa "A'a Adda khairi Ina
ni kikace zaki bawa? Ai kince nafishi iya karatu koh" da Lafiya klau ne zatayi murmushi tace 'eh
duk wadda ya iya karatu shi zan siyama sweet banda me kan kifi' Ai kuwa se su hau musu da
bitar karatunsu duk da take musu, Amma yau se ta daga musu tsawa "dallah ku kyaleni haba!!!"
A tsorace suka matsa suna kallonta Abul yace "er uwa??" Da tsantsan mamaki a muryanshi
don ko mutanenta suna kusa ne tana fama da ciwon kai da bugun zuciya lalla'basu takeyi su
kyaleta ba tsawa haka ba yayinda mutanentan karan kansu suke tsananin son kannen nasu,
kuka ta fashe dashi harda shesheka se duk sukayi shiru suka zuba mata ido Abba da kanshi ya
tashi yaje ya kamo hannunta ya karaso da ita kan taburman seda ta zauna tukun ya zauna yana
zama ta fad'a jikinshi ta kuma fashewa da wani kukan da yafi na da, Dada tace "Eyyah bongel
am me ke damunki ne haka? Tunda garin Allah ya waye na lura bakya cikin natsuwa da farin
ciki sam me aka miki?" Cikin kuka tace "Dada nima ba za'bina bane d'aga muku hankali Wlh
ban san me ke damuna ba ga gabana dake ta fad'uwa" Abba yace "In shaa Allahu alkhairi ne ki
dinga maimaita la ilaha illalahu wahdahu la sharika lahu lahulmulku wa lahul hamdu yuhyi wa
yumitu wa huwa ala kulli shai'in qadeer, zaki ji sauki In shaa Allah" Kai ta ringa gyad'awa tana ci
gaba da shesheka Abul yayi shiru ya zuba mata ido, suna zaune shiru shiru duk jikinsu a mace
har aka kira magrib suka mike kowa yayi alwala ya gabatar da sallah sukayi duk activities d'insu
da suka saba bayan sunci abinci Abba ya mike yace "bari inje In zo" duk suka had'a baki wurin
cewa "A dawo lafiya Abbanmu" yana fita Maman hauwa dake tsaye ta daka tsalle har da fame
ciwonta amma bata damu ba dama da suka fito sallahn magrib ta aiki wani yaro ya kai mishi
papper da ya kunshi rubutun sarki na son ganinshi bayan isha don shine limamin babban
massallacin sarki dake cikin unguwan sarki unguwansu kenan na nan cikin jalingo, tana ta Allah
Allah kar ya lura ba stamp na sarki Ai kuwa be luran ba ya fito don zuwa, ta had'a baki da wani
dogari da yake cikin masu gadin gate akan idan yazo yace sarki ya ce ya zauna ya jirashi zuwa
In ta kirashi se ya kuma cewa, sarki ya ce yayi hakuri ze sake nemanshi. Maman hauwa na
shiga gida ta samu kujera ta zauna tana kallon samarin nan su biyu tace "kuje kuyi aikinku, ki
tabbatar yayi kaman fyad'e aka mata" Kai suka gyad'a suka shige d'akinta suka hau kan 'yarta
na cikinta tsabar bakar zuciya da hassada ne ko me zan kira wannan tana ji tana gani wasu

suka hau kan 'yarta duk don bakantawa wasu bayin Allahn da ko mummunan zato basa
d'aurawa a kanta, dama chan 'yarta bata da budurci sbd business takeyi da ita sossai amma
yau ta ce wa samarin nan su mata kaca kaca se tayi kaman fyad'e aka mata...

Malam Umar sanda ganin ya dad'e sarki be aiko ayi kiranshi ba yasa ya mike ya sake samun
wannan dogarin ya tambayeshi hakuri dogarin ya bashi akan sarki abubuwa sun had'u mishi ze
neme shi, godiya mal umar yayi tare da ficewa shapp ya manta hanky d'inshi da ya shimfid'a ya
zauna akan dakalin kofan sarkin yayi gaba abunshi, nan dogarin da suka had'a baki ya kirata ya
fad'a mata Ai kuwa tayi murna tace ya kawo mata dama ta samu takalminshi sawu d'aya zata
had'a.. yana shiga gida ya samu har yara sunyi bacci seda suka ga shiganshi tukun
ummulkhairi ta d'auki nabeela yayinda Abulkhairi ya d'auki nabeel sukayiwa juna se da safe
suka shige d'akunansu don dare yayi.....

Washegari - wadda sukayiwa lakabi da bakar rana.

Bayan sun dawo sallahn asuba Abba ya shiga wanka yayinda Abul ya d'auki tsintsiya ya fara
share musu tsakar gidan inda Khairi na kitchen tana shirin abun breakfast d'insu, bayan Abba
ya fito ya shige d'aki don shiryawa zuwa kasuwa wani irin banko kofa akayi da yasa khairi fitowa
da gudu Abul ma da yanzu shiganshi bayi don yin wanka ya fito da sauri Abba ma da sauri yasa
riga ya fito dogarawa ne da polisawa a tare inda suna ganin Abba suka kamashi police d'aya ya
rige kugunshi d'aya kuma ya kama hannunshi ya sa mishi handcuff cikin rawan murya khairi
tace "bayin Allah lafiya me yayi muku?" Ta karasa tana kallon Abba da yayi mutuwan tsaye
hawaye na zuba a idonta kaman panpo wani daga cikin dogarayen ne yace "kana nan kaman
mutumin Allah limamin massallaci dakai da aikata aika aika irin haka, munafukin Allah ai Allah
ba Azzalumin bawanshi bane kaima Kana da 'ya buduruwa" Abul yace "me yayi na wannan cin
fuska haka?" Abba dake ta kallon Dada da tafito tana dogara sanda har bugewa take tsaban
rud'ewa, a matukar firgice ya juyo jin wani dogari yace "fyad'e yayiwa 'yar mutane" a tare
sukace "me??????"��踫董







#vote
#share
#comment




'Yar mutan Adamawa

��潤����潤����潤����潤����潤��







IGIYAR RAYUWA��踫葉





��潤����潤����潤����潤����潤��

Story & Written by: fateemah Muhammad Gurin

'Yar mutan Adamawa

Page��∴��7儭������塚��8儭����
��潤����潤����潤����潤����潤����潤����潤��

A kullum mahaifiya itace jigo a kan ko wani hali d'a ze shiga tana tsayama d'a akan ko wani
kaddara ze fuskanceshi tabbas ya yarda da kalman nan na 'behind every successful man their
must be a woman' in ba don mahaifiyarshi ba be ta'ba tunani ko zato ze zo inda yake yanzu ba,
ta tsaya tsayin daka akanshi da rayuwanshi, ya ginu ne bisa kalaman nan guda uku "hakuri,
kaddara, jarabawa" ya ga jarabawa iya jarabawa amma da ya kasance me hakuri da yarda da
kaddara se hakan ya zame mishi nasara a rayuwa..

Maganan momma ne ya dake shi da kalaman da ba sabo bane a gareshi ya saba jinsu kullum
In har yana tare da ita ko ze yi waya da ita "babu hutu da kwanciyar hankali ga bawa a wannan
rayuwa ta duniya sai yayi imani da kaddarar Allah, wato ya sakankance cewa duk abinda Allah
ya qaddara mai aukuwa ne kuma abinda be so faruwansa ba to haqiqa ba zai faru ba, Allah ya
rantse cewa hakuri Alheri ne ga masu yinsa a inda yake cewa 'kuma Lallai idan kukayi hakuri
toh babu shakkah shine mafi alheri ga masu hakuri' Musharraf ka sani masu haquri ne kawai
ake cikawa ladar su ba da lissafi ba, toh kai me yasa bazakayi haquri ka rungumi kaddaranka
da jarabawar da Allah ya saukar maka a rayuwa ba? Shekaru Akallah 4 ba wasa bane sam kaki
bari komai ya wuce a rayuwanka? Ya ci ace yanzu ka manta da duk wani rayuwan mu na baya,
ka samu mace ta gari ka aura itace zata zama fitila me haske rayuwanka da ta jima cikin duhu,
Ina maka adu'a a kullum randa na gaji kuwa sede kaji an d'aura maka aure na gaji da wannan

halin naka" karyewa muryanta yayi alamun kuka na shirin kubce mata, idonshi dake runtse ya
bud'e sunyi ja kaman an zuba mishi yaji yana jin tsananin ciwo da zafi a zuciyarshi cikin sanyin
murya yace "kiyi hakuri momma" karamin murmushi tayi daga 'bangarenta tace "nayi
Musharraf" ajiyar zuciya ya sauke shi de bayan mahaifiyarshi da 'yan uwanshi da suke ciki
d'aya�� se 'yarshi ba macen ko namijin da ze kara yarda dashi a duniyannan kuma har yanzu
ta'bon zuciyarshi d'anye ne sam be shirya wani aure yanzu ba ko nan gaba sbd ya gama
sarewa da al'amarin mata, "Allah ya maka albarka ya za'ba maka mata ta gari" a sanyaye yace
"Ameen Ina su Miemie?" Tace "sun shiga school Amrah nada lectures so ta raka ta" "uhm"
kawai yace sun d'an ta'ba hira tukun sukayi sallama yana jinshi wasai..........


***

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun" Da Abul ke ta nanatawa ne ya dawo da ummulkhairi daga suman
tsayen da tayi, idonta ta kai inda dogarayen suke tare da polisawan da suka sama Abbanta
ankwa, wayam taga wurin ba kowa alamun sun tafi dashi tana daskare a wurin wani irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login