Showing 54001 words to 57000 words out of 117506 words

Chapter 19 - IGIYAR RAYUWA Hausa Novels Complete Document.pdf

Unknown   

18 May 2025

8454

Anty rabi'ah zasu kai abinci" miemie tace "nima" little ma tace "me too, Anty Amrah
who's at hospital? Naji kince su sauban zasu je" nuri tace "just eat bana son surutu and sauban
ba uncle dinki bane kike kiranshi gatsau haka?" Pouting lips tayi tana cewa "but Anty nuri we
are mates, same class and everything be yi babba ba like yhu and uncle marwan" dariya su
Amrah sukayi miemie tace "se yayi girma kaman mu kenan zaki kirashi uncle" little tace "yes,
sauban, Anwar and sudais are not my uncles" tana 'bata fuska tace "no way".................

Amrah na dariya tace "yes way, sbd kannen paapi dinki ne kap d'insu yhu better start calling
them uncles na gayamiki" kara tura bakin tayi wai tayi fushi a haka har suka gama cin abinci
suna sauka daga dining din da niyyan tafiya momma na shigowa, da gudu little taje ta
rungumeta tana cewa "oyoyo granny" momma tace "oyoyo namesy how was ur
night?"....................

Tana kwa'ba fuska tace "hectic, I didn't see you and my paapi" momma tace "Eyyah sorry,
yanzu kuje ku ganshi I will be on my way too" little na tsalle ta fice, gaida momma duk sukayi
suna tambayar ya jikin nashi tace "yayi sauki Alhamdulillah, jinin ya sauka kila a sallameshi da
dare ko gobe muran ne de se a hankali ze sakeshi" ajiyar zuciya suka sauke, nuri tace "ba

abinda za'a iya yi akan kidneyn yanzu?" Momma tace "babu munyi magana da doctor Aslam da
safen nan yace ba wai ya kamu da wani ciwo bane yana barazana ne sbd baki da yayi" Amra
tace "Toh Allah bashi lafiya"................,,

Suka ce "Ameen" miemie tace "Toh da wa kika barshi?" Momma tace "wai Ai family sun cika
d'akin pim, kuje nima wanka kawai zanyi in tafi, nuri kije d'akinshi ki d'auka mishi kananan kaya
da sponge da soap ku tafin mishi dashi, basket nan fah?" Nuri tace "Ohk, lunch dinshi ne ciki"
momma tace "sannu khairi, har kin gama kenan?" Khairi ta gyad'a kai kanta kasa, momma tace
"to ki bi su kuje, nima yanzu zan biyo ku" tace "toh momma" dama da hijab dinta jikinta, so fita
kawai sukayi momma ta haura sama....................

Little ta shiga motan nuriyyah, yayinda Amrah da khairi suka shiga motan da Musharraf ya ba
miemie na zuwa makaranta, seda suka jira nuri taje part din musharraf ta dawo kan suka jera
suka fita a tare, bayan sun isa suka nufi d'akin little da nuri ne gaba se miemie tukun Amrah da
khairi a baya, da sallama nuri ta tura d'akin da gudu little tayi kan gadon ganin paapinta, d'aga
ta yayi zuwa kan gadon tana cewa "me ke damunka paapi kake kwance a
hospital?".....................

Yace "ba gaisuwa?" Tace "good morning paapi?" Yace "morning" yana d'ago kai se idonshi ya
fad'a cikin nata da ta shigo a karshe da sauri ta dukar da kai tana jin jikinta ya d'au rawa,
mutane ne a d'akin akallah sun kusa 30 yara da kanana kamshi ko ta Ina na turaruka daban
daban, gaban gadon ta nufa da basket din abincin rana a hannunta kafanta har rawa yake jin
yadda ido ke yawo a kanta...................

Kusan kowa kallonta yake a d'akin ganin bakuwar fuska har kasa ta duka,
Ta gaida wasu manya da ta gani su uku zazzaune akan plastic chair, da fara'a suka amsa mata,
bayan ta ajiye basket din ta d'an saci kallonshi da sauri ta kawar da kai ganin shima kallonta
yake, cikin kasa da murya tace "Ina kwana? Ya jiki?" A hankali shima cikin dashewar murya
yace "Alhamdulillah"......................
Kan darduma ta karasa da ta ga mata hud'u zaune suna hira, a kasa ta duka ta gaishesu suma
suka amsa mata ba laifi, baza ido tayi a d'akin tana duba inda zata tsaya don tuni su Amrah ko
wacce ta samu abokiyar hira bayan sun gaggaisa da uncles d'insu da Anties d'insu, wasu
matasa biyu kyawawa idonta ya fad'a kai suma ita suke kallo gaishesu tayi, d'ayan ya amsa da
d'an murmushi d'ayan kuma ba walwala ya amsa yana mai da kai kan wayanshi........................

Kusa da Amrah taje ta tsaya tana lura da yadda d'ayan saurayin ke kare mata kallo up and
down, ganin kallon yayi yawa kuma en matan gefen Amrah na ta yatsina fuska yasa khairi ta
nufi kofa, yana magana da little amma yana lura da irin kallon da sufyan ke bin khairi dashi,
ganin ta fice daga d'akin yasa ya sauke ajiyar zuciya, yana mai me da hankali kan little, Amrah
kuma ganin khairi ta fita se taji ba daad'i hakan yasa ta bi bayanta.................

#vote
#share
#comment









'Yar mutan Adamawa


��潤����潤����潤����潤����潤��







�� �� �� �� �� �� ���� IGIYAR RAYUWA��踫葉








�� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� �� ���� ��潤����潤����潤����潤����潤��

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo


�� �� �� �� �� �� �� ���� 'Yar mutan Adamawa

*wannan page d'in naki ne Sadiya (Maman khalil) ina jin daad'in comments dinki sossai, irin
sossai d'innan plz keep it up dear, Allah ya bar kauna*

Page��∴��5儭����4儭������塚��5儭����5儭����
��潤����潤����潤����潤����潤����潤����潤����潤��

Dube dube Amrah ta fara bayan fitanta Chan ta hange ta zaune kan wani dakali daga bayan
d'akin ta zabga tagumi, karasawa tayi ta zare tagumin hakan yasa khairi d'agowa tana
kallonta..........

Murmushi sukayiwa juna kan khairi ta d'an matsa Amrah ta zauna, bayan ta zauna tace "family
sun cika d'akin" khairi tace "Ai kam duk ban san su ba gwara su Anty salima" Amrah tace "eh su
da iyayensu ne, bari nayi miki bayani dalla dalla kan ki shigo daga ciki" hararanta khairi tayi tace
"Toh wa ya gaya miki zan amince balle har in shigo daga cikin?" Amrah na dariya tace "har se
an fad'a!! Lallai ni kam har na hango wani boyayyen sirri" waro ido khairi tayi tace "wani sirri?"
Amrah ta fashe da dariya tana cewa "na san baza ki ki bane kawai amma ba wani sirri" a tsarge
khairi ke kallon Amrah kar de har ta har'bo jirginta............

Ganin tana shirin tona asirin kanta yasa tayi saurin cewa "uhm Ina jinki suwaye da waye a
d'akin?" Amrah tace "Duk waennan family da kika gani Alhaji Mahmoud dukku shine tushensu
da shi da matarshi hajja marwa wadda yanzu duk sun rigamu gidan gaskiya, Allah ya bashi
'ya'ya guda biyu rak a duniya kuma duk maza da kakanmu ta wurin uwa da kakanmu ta wurin
uba, Alhaji Adam wadda shine mahaifin Abbanmu se Alhaji Abubakar wadda shi ya haifi su
momma.......................

Alhaji Abubakar da Alhaji Adam sun taso kaman en biyu sabida ba wani tazara bane tsakaninsu
sannan komansu d'aya, da yake mahaifinsu sana'ar saida dabbobi yake hakan yasa suma suka
tsunduma sana'ar mahaifin nasu inda sukayi shura a ciki har ya kai ga sunyi suna a dukku da
ma gombe gabad'aya, a yawace yawancen da sukeyi na safarar dabbobi ne suka had'u da
Aslamiyya da kanwarta shuwa a garin chad suma ya da kanwa ne iyayensu sun mutu
sakamakon harin da aka kaiwa kauyensu...................

A wurin saida sauran dabbobinsu don tseratar da rayuwansu suka gamu inda Adam ya nemi su
zo su koma tare don sossai ya tausaya musu jin labarinsu, tare suka dawo Nigeria inda hajja
marwa ta tarbe su hannu biyu take basu kulawa sossai jin labarinsu haka Alhj Mahmoud ma

duk wani kulawan da uba ze bawa d'anshi yana basu daidai gwargwado a lokacin Aslamiyya na
da shekaru sha bakwai yayinda shuwa ke da shekaru sha biyu a duniya......................

Inda Adam ke da 26, Abubakar kuma 24 wasa wasa soyayya me tsanani ya shiga tsakanin
Adam da Aslamiyya sossai Alhj mahmoud yaji daadin haka ba'a 'bata dogon lokaci ba akayi
musu aure, anan cikin dukku suka gina gidan irin na zamani babban gida ne me part uku, Adam
a d'aya Abubakar a d'aya In yayi aure se na tsakiyar na iyayensu, da kyar suka shawo kan Alhj
mahmoud ya yarda suka koma gidan gabad'aya...................

Alhj mahmoud yaga ranar haihuwa sossai don a lokacin ba abinda yakeyi na aiki haka hajja
marwa en aiki baja Baja, a hk suka ci gaba da rayuwa cikin tsantsar kwanciyan hankali don
basu da wani damuwa, har Allah ya azurta Adam da samun d'a na farko, Alhaji Nasir shine
wadda kika gani daga daman ya musharraf sanye da fararen kayan nan In kin lura duk ya fi su
tsufa, bayan shekara biyu da haihuwarshi suka sake samun wani d'a namijin shine Alhj Ahmad
shima yana nan ciki da sky blue shadda...............

Bayan haihuwan Ahmad ne hankalinsu Alhj mahmoud ya fara tashi akan rashin auren Abubakar
yayi mishi magana ba sau d'aya ba ba sau biyu ba, amma amsan d'aya ne a kara mishi lokaci,
ba irin lokacin da bai d'ibar mai ba amma ba mata, da ya gaji kawai se ya had'a aurenshi da
marwa a lokacin ta gama secondary anan cikin dukku.....................
Zama suke kaman ba auren had'i ba don iya gwargwado suna kula da junansu, Allah be basu
rabo ba seda suka shekara biyar da aure a lokacin, yayyunsu sun sake samun karuwa inda
suka haifi mahaifinmu Senator mahmoud Adam, sossai farin ciki ya cika wannan familyn don
sun damu sossai da rashin haihuwan nasu akan lokaci.....................
Sossai cikin yaga gata ba na wasa ba, har ya kai lokacin haihuwa inda suka samu 'ya mace taci
suna 'fatima' momman mu, bayan haihuwanta da shekara biyu suka haifi uncle taheer shima
yana cikin room din sanye da black gezner, bayan shekara biyu suka kuma haifan Anty Rabiah,
ita ma tana d'akin, tun daga kan babanmu su Alhj Adam basu kara samun wani haihuwan
ba....................

Nasir, Ahmad, da mahmoud a ABU zaria sukayi karatu inda Nasir ya karanta business yayinda
Ahmad ya karanci Education se mahmoud da ya karanta political science, sossai suka dawo da
nasara mai yawa, a wurin bautan kasa suka had'u da matarshi Aisha a jihar bauchi inda suka
kulla soyayyarsu mai tsabta, haka Ahmad ma ya samu matarshi zulaiha a nan cikin dukku
dayake shi anan yayi service suna gamawa service aka sha buki na ji da fad'a inda duk suka
samu gida a cikin Gombe.................

Haka Allah ya basu Aiki cikin sauki basu wani sha wahala ba, sbd kyaun results d'insu, a nan
Gombe state university uncle Ahmad ya samu karantarwa yayinda Uncle Nasir ya samu aiki a
wani textile company, Bayan aurensu ne suka tashi da mummunar rashi na Alhaj Mahmoud
Dukku, sossai suka jimanta rasuwar don tabbas sunyi rashi babba, bayan rasuwanshi da

wattani biyu hajja marwa matarshi ta bishi tashin hankalin da suka shiga ba'a magana amma se
suka fawallawa Allah......................

Abbanmu kuma ya tsunduma siyasa kuma be da niyyar aure sossai ya kashe kud'in mamaji
(Alhj Adam) akan siyasan har ya samu nasarar samun kujeran chairman a haka ya dinga taka
matsayi har ya zama ministern man petur na kasa a lokacin ran mamaji ya kai makura wurin
'baci da rashin aurenshi hakan yasa sukayi shawara da bappa (Abubakar) akan su aura mishi
fatima wato momma................

A lokacin ta kusa kammala karatunta na NCE anan gombe tana zama gidan Uncle Nasir sam
bata ce komai ba sbd ta kasance mai biyayya da ladabi ga hakuri da Allah ya zuba mata, a fili
mahmoud ya dinga nuna kiyayyar shi ga auren har barazana ya dinga yiwa momma daga baya
da yaga an fi karfinshi sai kawai yayi shiru amma da mummunar kuduri a ranshi game da
momma duk da ba kyau ta rasa ba ba komai ba don duk cikinmu tafi kowa d'ibo kamannin
shuwa arab dukda suma sauran suna da kyau kuma farare amma se Abbanmu ya fita chocolate
color, Kinga Adda nuriyyah colornshi ta d'auko................."

Bazan iya baki labarin zaman auren da momma tayi ba wannan kam se ita ko yaya musharraf
haka kuma bazan iya gayamiki takamamman laifin Abba ba..... sbd....." kuka ne ya sarke ta ta
kasa karasa maganan, side hug khairi tayi mata tana bubbuga dantsen hannunta, seda tayi
kuka akallah na two mins kan tayi shiru tana share hawayen fuskanta tare da karamin
murmushi tace ....................

"Yaran Uncle Nasir da Anty Aisha hud'u hamma marwan wadda shine ze auri Adda nuri, se
Maryam wacce kin Santa, se salim da muke sa'anni se autansu sudais sa'an Little, duk tazara
mai yawa ne tsakaninsu don Anty Aisha In ta haihu se tayi planning na akallah shekaru hud'u
kan ta cire. Se Uncle Ahmad babban d'anshi ya sufyan, salima itama kin santa se Rufaida,
zainab waenda kusan kanmu d'aya autansu shine Ibrahim wadda yanzu yake 12years
old................

Se Kanin momma Uncle taheer da matarshi hajiya Asiya 'ya'yansu hud'u Zainab wacce kin san
ta se Farida da fatima da suke en biyu kuma sa'anninmu se auta Anwar sa'an little. Se er
autansu momma Anty Rabi'ah mijinta uncle Isma'il 'ya'yansu biyu Afreen da itama sa'ar mu ce
se sauban sa'an little" Ajiyar zuciya ta sauke tare da karawa da "Toh kinji familyn Marigayi Alhj
Mahmoud dukku"..............

Murmushi khairi tayi tace "masha Allah what a huge family!! Allah ya kara had'e kanku" Amrah
zata amsa kenan taji miemie tace "eyeeeh ku kuma nan kuka zo kuka 'boye kuna ta gulma
momma na Chan ta damu ya Musharraf na ta cigiyarku" waro ido sukayi a tare suka ce "ya
musharraf???" Dariya miemie ta fashe dashi harda kama ciki tace "irin wannan tsurewar? Ko de
baku da gaskiya ne" harara Amrah ta banka mata tana mikewa...................

Khairi ma mikewa tayi zuciyarta na luguden bugawa a tare suka nufi d'akin, Ashe bayan fitansu

daga d'akin ba jimawa sufyan ya fita hakan ya sa zuciyar musharraf ta kasa sukuni da ya rasa
dalili, har yaje yayi wanka ya sauyo kaya daga bayi ya fito yaga basu dawo ba, ranshi yaji yayi
wani mugun 'baci ya dinga buga tsaki wadda se da kowa ya tambayeshi ko lafiya yace 'kanshi
ke sarawa ga muran da yaki barinshi na toshe mishi kirji' duk sannu sukayi mai.................
Da kai kawai ya amsa har momma ta dawo be bar kananan tsaki ba, idonshi kuwa na kan kofa
kur kaman me jiran wani abu mai matukar muhimmanci, ganin basu da niyar shigowa yasa
yana kallon momma yace "Ina Amrah ne? I want to ask her something" Anty zulai tace "Ai sun
d'an jima da fita da yarinyar nan da su farida suka ce mai aikinku ce ya ma sunanta?" Momma
tace "au wai ummulkhairi?" Hannu Anty zulai ta juya alamun bata sani ba................

Wayan Amrah momma ta kira se sukaga side bag d'inta ma a d'akin ta bari, sallaman da su
Uncle nasir ke yi musu ne yasa hankalin momma ya bar kan su khairi da d'add'aya suka dinga
ficewa se da d'akin ya saura su yasu tukun momma tace "ni kam Ina yaran nan suka shiga ne?"
Musharraf da tunda su uncle nasir suka fara tafiya ya sulale ya kwanta tare da lumshe ido yana
ta yaki da zuciyarshi da ya rasa gane abinda yake ji se kokarin controlling kanshi yakeyi amma
abun na neman fin karfinshi, jin momma tayi maganan dubosu yasa ya sauke boyayyiyar ajiyar
zuciya..................

Be bud'e idon ba seda yaji sallaman miemie kofan ya kurawa ido, sam momma bata lura ba sbd
ita kad'ai ce a d'akin da little dake bacci, Nuri kuma suna waje da marwan, Amrah ce ta shigo
daga bayan miemie se Khairi daga karshe, had'a ido sukayi a tare gabansu ya fad'i da sauri ta
kau da kai zuwa wurin momma dake cewa "Ina kuka shige ne haka?" Amrah ce tace "muna
daga baya muna hira ne momma"................

Momma tace "Ohk" khairi tace "sannu da dawowa" momma na murmushi tace "yauwa khairi"
Amrah na kallon musharraf tace "hamma musharraf gani" Shiru ya mata yana kallon momma
yace "Am starving"�� momma na shirin mikewa khairi ta mike ba wai don kanzagi ko wani abu ba
kawai gani tayi be kamata sunanan momma ta dinga wani aikin na daban ba musamman ma ita
da ta kasance er aiki......................

Kusan basket shidda ne na abinci a d'akin hakan yasa ta bud'e duk coolers dake ciki, bayan ta
gama ta d'ago ta kalleshi shima ita yake kallo kasa tayi da manyan idanunta tana mamakin yau
wani irin kallo yake mata ne oho, cikin tsiririyar muryarta tace "wanne zan zuba maka?" Shiru
yayi seda ta d'ago kai tukun ya kalli abincinta ya kuma kallonta.....................
Cikin kankanin lokaci ta fahimci abinda yake nufi danbum shinkafar ta zuba mishi da sous din
hantan ta d'aura akan karamin tray, a bowl ta zuba mishi fruit salad marar sanyi sbd murar da
yakeyi, mikewa yayi ya zauna a hankali yana tankwashe kafa, a gabanshi ta ajiye mishi garin
ajiyewa ne hannunta ya karkace saura kad'an trayn ya fad'i a tare suka kai hannu amma nata
ya riga sauka hakan yasa hannunshi ya sauka akan nata......................

A tare suka d'ago kai suna kallon juna basu san wani irin abu bane ya rike musu idanun cikin na

juna, sossai take kallon kwayar idonshi cikin 'batar basira wani maiko da bata san na me ba
dake kwance a kwayar idanunshi, take kallo ta jima tana contemplating haka idonshi yake ko
kuwa, se yau ta tabbatar da ashe haka idanunshi suke kaman an zuba ruwan
zaiba.....................
Shima kallon manyan eye ball d'inta dake sakashi cikin wani yanayi da be san na mene ne ba
yake yana jin wani tension na building inside him, rufe kofar da akayi ne ya dawo dasu daga
thoughts d'in da suka fad'a, da sauri ta kawar da kanta a kunyace tana zame hannunta, satar
kallon su Amrah tayi se taga duk sallah suke da alamu momma ce ta shiga toilet................
Wani munafukin murmushi ya sake he looks so charming with it sbd be bari murmushin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login