Showing 30001 words to 33000 words out of 60473 words

Chapter 11 - SALAME COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM SHARIFAT CE.doc

dora hannu aka tace na shiga uku Nafisa zata tona min asiri yarinyar nan bata kauna ta nayi asarar haihuwar Nafisa .

Toshe mata baki Hanan tayi ta ce "" aa mama karkice haka kar kiyi mata baki ki kyale ta nasan dai ba zaa cutar da Nafisa a gidan kawu ba saidai zasu dora ta akan bagidajen tsarin su har zuwa sanda zasu aura mata wannan matsiyacin Sulaiman din daga nan kuma kinga ai sai mu jira duniya ta dawo ta dawo da ita cikin mu ki kwantar da hankalin ki indai Nafisa ce zata dawo har inda kike wannan shawarar tasa mama jin sanyi a ranta suka cigaba da shagalin su daga nan suka wuce kitchen suka fara kokarin dora abinci.


Karbe hudu na yamma suna zauna gaba dayan su a cikin dakin Salma ta fara juya kanta cikin ihu da karaji ta fara fuzge fuzge tana cewa " kabari don Allah ka dena bani bace wlh bance Ina so ba mutuwa zanyi ka dena wayyyoooo Baffa mutuwa zanyi yaya na dena na dena mutuwa zanyi yaya
Da gudu Daddy yayi kiran Dr suka shigo tare likita yayi mata allura ta fara rage sautin muryar ta saidai bata daina juya kanta ba tana magana a hnkali wacce basa jin abinda take cewa momy da tinda ta farfado jikin ta yake a mace tana zaune akan kujerar dake kusa da gadon da Salma take kai banda hawaye babu abinda momy ke gogewa shi kansa Daddy yanayin da Ummusalma ya farka saida ya goge guntun hawaye cikin ransa yana tinanin irin hukuncin da zaiyiwa Safraz haka suka cigaba da kulawa da ita saidai bata magana sai kuka idan har zata ga namiji a kusa da ita zatayi ta maimaita abinda ta fada ranar da farfado

Wannan abun ba karamin daga hankalin kowa yakeyi ba saida Daddy yaso fitar da ita waje likita ya tsaida shi ya nemi ya bashi nan da sati biyu idan bata warke ba sai a fitar da ita

Kwanan Salma bakwai a asibiti ta fara samun sauki yanayin fitar fitsarin ma ya ragu sosai saidai har yanzu bata magana duk maganar da zaayi mata saidai aga hawaye ya fara bin fuskar ta koda sunyi kokarin rarrashin ta bata bari kowa yazo inda take sai Khadija itama ba magana takeyi mata ba saidai ta rike mata hannu tana kallon ta zuwa yanzu tanayin wanka ta gyara kanta da kanta saidai yanayin tafiyar ta ya canza bata yin tafiya kmar da dan dingisawa takeyi tana tafiya a hankali a nutse .
Khadija ce take bata magani ta sha ta zauna ta rike mata hannu tana karanta mata labaran ban dariya saidai bata yin dariyar kwata kwata ko murmushi batayi saidai ta kurawa khadija Ido tana kallon ta .

Hakan baisa Khadija ta daina ba don iya kallon ta da Salma takeyi Yana saka ta farin cikin kullum cikin yi mata adduar samun lafiya suke.


Kashegari Baffa ya iso asibitin bayan Daddy ya kirashi ya sanar dashi. Da sallama a bakin sa ya shigo dakin yana shiga momy ta tashi daga kujerar da take kai ta bashi ya zauna Khadija da musaddiq suka fara gaida shi yana amsawa fuskar sa dauke da faraa sannan suka kara gaisawa da Daddy da momy yayi musu ya mai jiki. Daya bayan daya suka fara ficewa suka barshi daga shi sai Salma a dakin, Kamo hannun ta yayi da hannun sa daya ta rike dayan kuma ya shafa kanta dashi yana kallon yanda ta sauya lokaci daya kamar ba ita ba wani irin abu yake ji a ransa yana matukar son ta duk cikin yayan sa.


A hankali ta bude idon ta ta sauke su akan sa cikin wata siririyar murya irin ta marasa lafiya tace" Baffa na murmushi ya sakar mata yace "Inna ta sannu ya jikin naki? batayi magana ba sai fashewa da tayi da kuka tace cikin muryar kuka " Baffa ka tafi dani karka barni anan mutuwa zanyi" saida ya hadiyi yawu mai daci sannan ya kakalo murmushin yake yace "Inna ta?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? kiyi hakuri ki sani tin muna cikin iyayen mu aka rubuta ?addarar mu iya kawanakin da zamuyi a duniya ranar da zamu koma ga Allah da duk abinda zai same mu mai dadi ko mara dadi kuma wanda yayi Imani da wannan shine cikakken mai imani ki kwantar da hankalin ki kinji akwai mutane da yawa wadanda suke cikin halin jarrabawa da yafi naki kiyi hakuri kuma godewa Allah a duk halin da kika tsinci kanki.
Nasiha sosai ya cigaba da yi mata yana tina mata wasu abubuwa da suka wuce har saida ta saki jikin ta tana murmushi sannan ya fito .

Yana fitowa su momy suka dawo yanda suka same ta ba karamin dadi abin yayi musu ba har yar hira akayi da ita tana murmushi, momy ce ta bata abinci a baki ta gyarara mata jikin ta sannan ta dago mata bayan gadon ta dan kishin gida .

Kallon Khadija tayi tana turo baki tace baki karasa karanta min labarin jiya ba " hararar wasa Khadija tayi mata tace " bazan karanta ba da kina jina kike share ni. Kallon momy tayi kmar zatayi kuka tace" momy kin ganta ko "kwantar da hankalin ki Autar momy ai dole ta karanta ko zata kwana anan gwalo tayi wa Khadijan tana dariya itama Khadija dariyar tayi zata cigaba da karanta wa Yaya Musaddiq ya taso ya karbi littafin da take karantawa yace " oya tashi zan fara kula da kanwata tabe baki khadija tayi ta mika masa ta tashi ta koma kukerar daya taso tana latsa wayar ta.

Sai da ya matso da kujerar da daf da gadon cikin wata nutsatstsiyar murya ya fara karanto mata labarin.

Daddy ne yaja hannun Baffa suka zagaya lambun dake cikin asibitin suka zauna akan wasu fararen kujerun dake wajan shiru yayi ya rasa abinda zai ce Baffa kallon sa kawai yakeyi yana murmushi ganin shirun bazai masa ya bude baki dakyar tare da kamo hannun Baffa ya rike hawayen da yake boye wa suka fara sauka yace" na rasa da irin idon da zan kalle ka na rasa bakin da zanyi magana dakai ,bai karasa fada ba Baffa ya daga masa hannu yace " dakata Abdallah bana son kace min komai , ka bani mamaki da kake tinanin Ummusalma yata ce ba taka ba ka bani mamaki da kake neman kalmar da zakayi min maganar abinda ya faru da Salma nifa nazo duba yarka ne da bata da lafiya shine zaka tare ni da wasu maganganu banaso kasani tin ranar da kuka taho sa Ummusalma na barmaka ita bawai don auren ta da Safraz kadai ba na baka ita ne gaba daya a waje na bata wuce yata ta wajan dan uwana Abdallah ba.

Sakin baki Daddy yayi yana kallon ikon Allah ashe har yanzu akwai irin wadannan mutanen a duniya abinda Safraz yayi baisa yayi tinanin rabasu da Salma ba wanda gaba dayan su shine abinda suke tsoro lallai Safraz yayi asarar hada jini da mutanen kirki.

Karfafa masa guiwa Baffa ya dinga yi har akayi sallar la'asar daddy yaso Baffa ya kwana amma yace zai dawo driver Daddy yasa yakai Baffa ya kwana acan gobe sai ya juye tinda zasu kai dare a hanya har bakin mota ya raka shi sukayi sallama ya dawo ciki.


Yana shiga yaga momy tana kaiwa da komowa a kofar dakin da sauri tayo gurin Daddy tana cewa " Alh ya ake ciki yana fada mata abinda Baffa yace saida ta kalli gabas tayi sujjada domin tinda suka kebe ganan ta ke faduwa tana matukar tsoron rasa Ummusalma


Alhamdululillah yau satin Salma uku a asibiti kuma yau aka sallame ta ta warke sumul ta kara haske har yae kiba tayi tayi kyau kamar ba jinya tayi ba, sosai yaya Musaddiq yake kulawa da ita har hutun ya karba a wurin aiki ya dawo kula da ita .

Daddy ne dauki momy da Khadija a motar sa d yaya Musaddiq ya dauki Salma suka wuce gida .

Suna zuwa gida ta tarar da abin makakin da bata san dashi ba yaya Musaddiq ne ya shirya mata walima a harabar gidan inda ya dakko masu decoration suka gyara wurin sosai aka kawata wurin da wasu kalolin futulu wanda suke kawowa suna dauke wa suna rubuta"welcome back Salma" har makeup artist ya dakko tayi mata kwalliya ya shirya cikin wata pick din gown wacce ta amshi jikin ta komai na ta ya fara fitowa alamar yammatan ci ta faru zuwar maga brest dinta ya fara cika haka jikin ta ya fara fitar da shape tayi matukar kyau kmar yar tsana.


suit ya saka kalar kayan ta yayi kyau sosai kmar ango karfe hudu na yamma suka fito wajan da ya cika da yan uwa da abokan arziki ya dakko wayar sa ya mika mata ya rike hannun ta suka yanka cake ya saka mata a baki itama ta bashi ta bawa Khadija aka saka tafi ana mata barka da dawowa.


To muma dai munce Welcome back Salamen Inna kanwar musaddiq da Safraz.

Mrs Sharif ce
'
*SALAME*

55-56

Oum Sharifat ce>??

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE



Anci ansha ayi farin ciki sosai itama ta sake kmar ba ita ba sai da aka fara kiran sallar magrib sannan suka tashi, daga dakin su ta wuce ta cire rigar ya wuce toilet tayi wanka tare da alwala jallabiyya ya saka da hijab tayi sallah ta zauna a wurin tana azkar khadija ta shigo itama wankan tayi da alwala tayi sallar suka dan taba hira har sukayo sallar Isha'i sannan suka sakko kasa inda suka tarar da momy ita kadai "sannu da hutawa momy suka fada a tare ajiye wayar dake hannun ta tayi cikin jin dadin yanda Salma tayi tace" yawwa yammatan momy kun sakko to kuzo mu jira su daddy muyi lunch kusa da ita suka zauna suka saka ta a tsaki yayin da Salma ya kwantar da kanta a kafadar momy itama momy zagaye Salman tayi ta tana shafa bayan ta a hankali tana kara mata sannu.
Suna nan zaune Daddy ya sakko suka gaisa ya kara yiwa Salma ya jiki a kunya ce take amsawa. Yaya Musaddiq ne ya sakko ya gaida momy da Daddy Salma da khadija suka gaida shi a tare suka yiwa juna ya gajiya suna dariya. Gaba daya daining area suka nufa khadija tayi serving nasu . Shiru wurin da dauka bakajin sautin komai sai karar cokula .

Salma kuwa juya cokalin kawai takeyi a cikin mata plate din amma hnkalin ta sam baya kan abincin Daddy ne ya fara lura da hakan ta kasan table din ya taba kafar momy tana dago kai ta kalleshi da ido yayi mata nuni da Salma. Ajiye nata colalin tayi itama ta kalle ta da yanayin damuwa tace " Auta lafiya ko? Girgiza kanta tayi tana kokarin fara cin abincin tace bakomai momy numfashi momy ta saukar tace ki daure kici abincin kinji? Daga kanta kawai tayi ya fara cin abincin wanda take jinsa kmar magani.

A zahiri bata jin wani ciwo a jikin ta saidai tanaji a ranta batasan menene abinda ya faru da ita ba zata ita tuna lokacin da yaya Safraz yake zaginta yana yi mata wani abu wanda ta kasa fassara shi da kowane irin abu daga nan kuma ta ganta a asibiti kuma taji ance bazata iya rife fitsari ba har aka saka mata robar da fitsarin ke taruwa daga karshe ta warke bata san menene silar ciwon ba kmar yanda bata ga Yaya Safraz yazo duba ta ba.

Jiki ba kwari taci kadan tace ta koshi duk yanda sukazo janta da hira kin sake wa tayi takoma dakin su tana tashi khadija ta bita don batason ta bata space din da zataji tinani.


Haka dai suka cigaba da rayuwa bata nuna kowacce irin damuwa saidai tana tinani akan abubuwan da suka faru da ita har tayi wata guda zuwa lokacin ta dawo Salamen ta mai faraa da son wasa duk da tana kebe kanta a wasu wuraren tayi kukan da ita kanta bata san dalilin sa ba.

Tinda ta tashi daga bacci take dafe kanta khadija ya lura da hakann ta matso kusa da ita tace " Autar momy yane? Yamutsa fuska tayi ta ce " zazzabi nake dan yi da daddre sai ciwon kai ayya sannu Ina da magani bari muyi break sai na baki kuma wlh idan baki sha ba sai na fadawa yaya Musaddiq yayi miki allura waro ido tayi ya shagwabe fuska tace " to wai nace bazan sha bane? Dariya khadija tayi tana gwada maganar tata tace " ai nasan hali ne gaba daya dariya sukayi .

Gyara zama khadija tayi ta ce " yawwa wai Salma yaushe zaki koma school ? Rau rau tayi da ido kamar zatayi kuka ta ce " ni bazan koma kowacce irin makaranta ba na dena zuwa bana shaawar komai ." Ina burin ki na zama barrister"? Na hakura na fasa ta fada hawayen da suka taru a idon ta suna sakko wa .

Sauke ajiyar zuciya khadija tayi tace " kenan kin fasa kwatowa matan da aka yiwa fyade hakkin su? E kawai tace tana shirin fita daga dakin Khadija ta ruko hannun ta idon ta cak ta tsaya tana juyowa suka hada ido da khadija wacce itama hawayen takeyi ta ce "Salma kinsan menene fyade? Jikin tane yayi sanyi ta girgiza tace bansan shi ba amma dai nasan mata akeyi wa kuma maza ne sukeyi kuma ana mutuwa zauna khadija tace tana gyara zaman ga itama tace "abinda yaya yayi miki shine fyade baya tayi da sauri kuka ya kwace mata ta shiga girgiza kai ta kasa cewa komai sai kukan da takeyi kmar wacce aka aikowa da sakon mutuwa.

Salma ke ba zamu iya kiran abinda ya same ki da fyade kai tsaye ba saboda ta hanyar aure abin ya faru nasan kinsan menene aure tinda yanzu ke ba yariya bace ko a islamiyya ma kinji bayanai akan aure ya hanyar da aka bi ne ba zaki gane komai ba kuma yayi amfani da suffar masu fyade.
Salma wasu matan samarin su keyi musu wasu ma basu san juna ba wasu fa a hanyar zuwa school ko dawowa zaa sace su ayi musu fyade ko kinsan akwai wadanda sukeyiwa mace daya fyade su uku ko sama da hakan ?kinsan ana yiwa kananan yara harda jarirai? Kinga wannan ciwon da ga same ki yana iya samun kaso tamanin cikin dari na wadanda ake yiwa fyade wasu fa yadda su zaayi har sai ciwo yaci karfin su wasu ba zasu warke ba shikenn an lalata musu rayuwa an barsu da ciwo a haka akwai wasu lauyoyi da aka bawa kudi domin su kare wanda yayi fyaden .

Kinsan wani abu? Khadija ta fada tana shashshekar kuka girgiza kai Salma tayi wacce hawayen tausayin kanta da wadanda suka tsinci kansu a wannan halin take zubar mata kmar an bude famfo .
Khadija tace " idan wadannan lauyoyin sukayi nasara haka zaa tambayi wanda yayi fyaden shin ya yafe sharrin da akayi masa wani zai yafe wani kuma zai ce yana neman hakkin sa bisa sharrin da akayi masa haka mace tana tsaye tana fuskantar wanda ya wulakanta mata rayuwa yana neman hakkinsa akan ta wata a saka mata tara wata ma dauri .

Yanzu ba zaki tsayawa wadanda matan ba? Ba zaki karbi kaddara ki cece su ba? Ba zaki bada gudumuwa wajan dakile masu aikatawa ba? Inaji a jiki na wannan ?addarar ta fado kanki ne don kinsan zafin abun kisan zafin da wacce aka yiwa take ji ki kwatar mata hakkin ta, don Allah kiyi tinani ki zamewa matan da ake cuta garkuwa. Hannun ta cikin ma khadija take jijjiga kai tana hawaye da majina can kasan makosho take cewa " zanyi zanyi zanyi sai kuma ta fara tari sosai har tana shidewa, da gudu Khadija ta sauka tana kwala kiran momy momy dake zaune tana jira fitowar su suyi break ta mike da sauri cikin kidima tace " lafiya menene" Salma kawai take cewa tana nuna dakin su.


Da gudu momy har tana bige khadija ta haye saman yanda taga Salma kmar bata numfashi ya sa da karfi ta cewa khadija kirawo Musaddiq.


Da gudu khadija ta fita daga part din tayi nasa tin kafin ta karasa take kwala masa kira yana shirin fitowa yaji wo muryar khadija da sauri ya fito suka ci karo a kofar part din kafin yayi magana tace " Salma anan ya barta da gudu yayi part din nasu kafin ya hau sama ya ga momy ta dakko ta a baya da sauri ya fice ya jawo mota momy ta karaso ta saka ta bai jira khadija ba yaja motar da gudu ya fice sai sannan Daddy ya sakko shima a gigice ya dauki tasa motar khadija ta hau suka rufa musu baya.


Asibitin Dr mahfooz suka koma tin kafin suje Daddy ya kirashi ya sanar dashi zuwan su, suna zuwa aka karbe su aka shiga da ita aka fara kokarin ceto numfashin ta.


Momy Daddy Yaya Musaddiq khadija gaba daya sun rude kallo daya zakayi musu kaga tsantsar tashin hankali a tare da su .

Sun kai kusan minti talatin kafin Dr mahfooz yayi kiran su gaba daya suka fada office din suna zare ido . Saida ya basu wuri suka zauna sanna ya kalle su da murmushi yace " ku kwantar da hankalin ku wannan karon ba abin tashin hankali bane saidai muyi farin ciki domin gwajin da mukayi mata mum gano tana dauke da ciki na sati bakwai.



Rayuwa tayi dadi Mama Hanan da Karima sun kara canzawa s sun dauki mai aiki wacce take yi musu komai hadda gyaran dakunan su da girka musu abinci a rana sai tayi abinci kusan kala goma da zaran ta gama wani abun zaa ce tayi wani kwata kwata basa barin ta ta huta sai dare .
Hanan ta samu sabanin costumers masu kudi wadanda suke sakar mata bakin aljihu yanda take shigar ta da kwalliyar ta ba zaka ce itace tsohuwar matar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login