Showing 27001 words to 30000 words out of 60473 words

Chapter 10 - SALAME COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM SHARIFAT CE.doc

ya fara kiran Daddy three Miss call bai dauka ba sai sharara gudu yakeyi hankalin sa yana kan Salma da hanyar ga kuma wayar daddy da ya kasa samu.

Sai a karo na hudu Daddy ya dauka da sallama "Alh Musa ne driver hajiga Ummusalma yanzu haka muna hanyar asibitin Dr mahfooz bata da lafiya a kidime Daddy yace "Ummusalma me ya same ta ina Safraz din yake" cikin shashshekar kuka Musa driver ya ce " bansani ba Alh amma dai bata numfashi yallabai kuma ya fita dazun nan

Hayaniyar Daddy ce ta tashi momy a hanzar ce ta mike tana cewa " alhaji lafiya naji kana kiran sunan Ummusalma wani abu ne ya same ta? Dakko hijabin ki tana asibiti kawai ya ce yana saka jallabiyya zucuyar sa cike da sake sake kala kala da gudu momy ta shige dakin ta dakko hijab zuwa lokacin an fara kiran sallah wanda yayi daidai da tashin Khadija da sauri daddy ya sauka kasa ya fara kwalawa mai gadi kira jikin Khadija ya bata ba lafiya ba hijabi kawai ta dauka ta dora akan rigar baccin ta ta fito parlo daidai nan itama momy ta fito da sauri ba tare da ta kula da Khadija ba ganin halin da momy ta fito ya tabbatar mata akwai mtsala da sauri ta rufa mata baya tana fita ta iske momy na kokarin shiga mota da gudu ta karasa itama ta shige Daddy da kansa yayi driving da gudu ya fice daga gidan zuciyoyin su cunkushe da tambayoyin da babu wanda zai basu amsar su sai Salma da Safraz cikin kankanin lokaci suka karaso asibitin ko gama parking baiyi ba ya balle murfin motar ya fito suma suka fito sukayi ciki.


Drivern yana zuwa ya shiga danna horn da karfi cike da tashin hankali babu jimawa aka bude get din ya shiga jin yanda ake horn ya tabbatar wa da nurses din dake cikin asibitin akwai patient da sauri sauri suka fito da keke tare dasu aka fito da Salma suka dora ta akan keken suka yi ciki da ita mama Talatu ta rufa musu baya daidai wani babban daki suka tsayar da mama Talatu suka shige da Salma ko minti biyu baayi ba wata nurse ta fito tace ta biyo ta a kofar wani office suka tsaya nurse din tayi Knocking daga ciki aka ce "yes" suka shiga a tare cike da damuwa nurse din tace " sir wannan matar ce tazo da patient kuma matsalar rape ce koma ince ta wuce rape a kalla kuma ina tinanin maza sun kai biyar suka afka mata .

Da sauri dr ya mike ya dubi matar yace ke wacece dinta " ni Mai aikin ta ce matar major Safraz ce dan gidan Alh Abdullah kwangila tinda ta ambaci major Safraz bai bari ta karasa ba ya fice da gudu daga office din yayi dakin da aka kaita da nan da nan aka shirya ta aka shiga da ita dakin theater mama Talatu sai zagaye takeyi tana tafa hannu idanun ga sunyi jazur .

Daidai nan dr ya fto da gudu gudu har tana tuntube tayo kansa tana cewa "likita ina hajiyar mai ya same ta bai iya amsa mata ba illa cewa da yayi "Alh ya sani? E ya sani muna hanya driver ya kirashi okay kawai yace ya cigaba da zirga zirga hannayen sa goye a bayan sa daidai nan kuma Daddy momy da Khadija suka shigo suna waigen ta inda zasu hango mama Talatu.

.
Karaf idon sa ya sauka kan dr mahfooz dake ta zurga zurga da karfi ya kwala masa kira jin kiran ya sa shi saurin juyowa da sauri ya karaso wurin Daddy kafin Daddy yace komai dr mahfooz ya ce " Alh da gaske wannan yarinyar surukar ka ce " daga masa kai Daddy yace" e suruka ta ce kuma Yar dan uwa na sauke ajiyar zuciya yayi ya kalli khadija ya ce" zauna nan ki jira mu.

Ja hannun daddy yayi ya nufi office dinsa dashi suna shiga ya nuna musu kujera suka zauna idon su yana kansa shima ya zagaya tasa kujerar ya zauna yana zare glass din dake idon ta dora shi akan table din dake gaban sa ya fuskance su ya ce"


Alh fyade akayi mata wanda zan iya cewa ba wai fyade ne wanda muka saba gani ba wannan duk wanda yayi wannan aikin yayi shi ne don punishing din yarinyar bawai don jin dadin kansa ba saboda yayi mata fata fata yanzu haka na baro ta da yan uwanta mata zasuyi mata dinki bayan munyi kokarin saita numfashin ta .

Daskarewa sukayi a wajan momy kuwa tini hawaye suka fara sintiri akan fuskar ta duk yanda Dr mahfooz yayi don ganin hankalin momy ya kwanta amma ta kasa nutsuwa kuka kawai takeyi tana kiran sunan yarta Salma shi kansa Daddy kukan zuci yakeyi wani irin kuna zuciyar keyi.

Dakyar ya lallashi momy sukayi Sallah ta dade tana kuka cikin sallar tana yiwa Salma addua


Lokaci an fito da Salma aka kaita wani dakin bayan an saka mata drip koda su Momy suka shiga dakin Saida hawayen ta ya dawo Khadija ma da batasan abinda ke faruwa ba ganin halin da Salma take ciki ba karamin daga mara hankali yayi ba hakuri nurses din suka dinga basu daga nan dukq fice suka bar su a dakin bayan sun bada umarnin kar ayi hayaniya.



Mrs Sharif ce
'
Kuyi hakuri da wannan dakyar nayi shi wlh saboda farin cikin ku kawai

*SALAME*
51-52

OUM SHARIFAT CE>??
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE

Jugum jugum suka zauna kowa da abinda yake sakawa a ransa har aunty Aisha ta shigo da sallama jikin ta a sanyaye suka gaida ta karasa wurin gadon da Salma ke kai tana kwance sambal babu alamar numfashi a tare da ita ta jikin naurar dake gefen gadon kawai ake ganin habrwar ranta .

Jiki ba kwari aunty Aisha ta zauna akan kujerar dake kusa da momy ta ce " Yaya me ya same ta ne? Saida Momy ta goge wani guntun hawaye kafin tace " danki nayi wa fada akan ta shine ya yi mata fata fata saida akayi mata dinkuna kuma mai gadin gidan yace tin kafin afara kiran sallar asba ya fita hadda troly sannan likita yace " yanayin abun ba wai anyi shine domin raayin kai ba, alamar an shige ta ta ko ina ne kmar zaayi punishing din ta kinga kenan yana sani ya aikata kila ma kashe ta yayi niyya Allah bai bashi iko ba.yanzu haka sunyi mata gwaje gwaje sunce a jira su zasu fadi result.


B iya aunty Aisha ba hadda Khadija saida ta girgiza sarai ta gane abinda yayan nata yayi wasu zafafan wahaye ne suka fara sauka daga idon ta ta dago kanta a hankali ta kalli gadon da Salma ke kai zuciyar ta kuna lokaci daya ta rame tayi haske duk wannan sanadain dan uwanta ji take ita kanta ba zata yafe masa ba Aunty Aisha kuwa tsananin takaici ne ya sa fa daukar waya ranta a bace ta fara kiran layin sa saidai amsa daya ce wayar a kashe sai fa canza akalar kiran kan Ibrahim saida ta kusa yankewa sannan ya sauka da sallama a dakile ta amsa tace " inason ganin ku kaida abokin ka a asibitin Dr mahfooz aunty ai major baya nan ya tafi Cairo ko kin manta da tafiyar what!! Aunty Aisha tace tana mikewa tsaye cikin karaji tace to kazo kai Ina neman ka yanayin yanda take maganar ya tabbatar masa ba lafiya da sauri ya fara hada kayan sa ya shiga motar sa ya nufi asibitin .

Da momy da Khadija ma mikewa sukayi suna kallon Aunty Khadija da jiran karin bayani wahaye ne suka shiga wanke mata fuska ta ce "tabbatar yana sane ya aikata ya gama tsara komai ashe yau ne tafiyar da yake cewa zaiyi karo karatu a Cairo ya tafi ta fada tana tsugunawa akan guiwoyin ta kmar wacce aka sakawa shock haka momy taji ta daskare a wurin ko motsi ta kasa zuciyar ta wani irin bugu takeyi shikenn na shiga uku danki ya wulakanta ni Aisha ya cutar da jinin Hafsu ya cutar dani Aisha ..

Daddy ne ya shigo dakin a gigice fuskar na nuna zallar tashin hankalin da yake ciki ya zauna kan kujerar dake dakin ya ta fara goge zufar dake keto masa jikin momy ya gama mutuwa ta karasa wurin sa ta tsuguna gaban sa tace kayi wa Allah ka sanar dani abinda Dr yace maka zuciya ta zata dauka ko menene ka fadamin doguwar ajiyar zuciya ya sauke yace " ya zama dole na fada miki koda baki tambaya ba zaku zauna anan wurin Salma na sati biyu saboda dalilin abinda Safraz yayi mata ta kamu da karamin ciwon yoyon fitsari sautin faduwar momy kawai sukaji da gudu aunty Aisha da Khadija sukayi kanta suna jijjigata. Da sauri Daddy ya fita yayi kiran nurses suka shigo suka saka momy a keke suka tura ta zuwa wani daki suka saka mata drip suka yi mata allurar bacci.

Daddy ya dubi Khadija yace " kije driver ya kaiki can gidan yayan ku ki debowa yar uwar ki kayan da zaa dinga canza mata daga kai kawai takeyi ta fito idanuwan ta sun kasa daina zubar da hawaye wajan motar kawai ta nufa ta tsaya ta kifa kanta tana kuka.
Driver ne ya karaso wurin yace " hajiya wani wurin zamuje gidan yaya tace " tana shashshekar kuka.


" kiyi hakuri hajiya komai yayi zafi maganin sa Allah kuma Ubangiji (SWA) Yana cewa "inna ma'al'usrin yusrah" kowanne tsanani yana tare da sauki. A wani wurin kuma yace wa 'iza asabathum musibatan kalu innalillahi wa'inna ilaihiraji'un " nasan kin sani damuwa da tashin hankali ne yasa kika manta abinda ya kamata ace kinyi kiyi hakuri ki dawo da nutsuwar ki ki ambaci Allah kmar yanda yace "fazkuruni azkurkum washkuruli wala takfurun" .

Sauke ajiyar zuciya ta dingayi akai akai tana gyada kanta tace " nagode baba, gyada mata kai kawai yayi yana murmushi ya bude mata kofar ta shiga ta cigaba da karanta innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin .

Haka ta dinga maimaitawa har suwa iso gidan a kofar gidan tace ya tsaya ta shiga ta fito babu musu yayi parking ta fito ta shige cikin gidan direct part din Salma ta nufa ta wuce bedroom dinta nan ta iske bedsheet din dake kan gadon kaca kaca da busashshen jini girgiza kai kawai takeyi hawaye na sintiri akan fuskar ta tana ambaton Allah.

Troly daya ta dauka ya bude wardrobe dinta ta shiga debo mata duk abinda zata bukata saida ta cika ta taf sannan ta rufe ta jawo tayi hanyar fita har zata wuce ta hango wata farar takadda akan drower ta dawo ta saka hannu ta dauka bata tsaya budewa ba ta rike ta a hannun ta ta fito ta shiga motar suka juya asibitin.

Suna shiga ya daukar maga trolyn suka shiga ciki ya ajiye tare da yiwa Alh yamai jiki ya fito komawa gefe Khadija tayi ta bude takaddar ga fara karantawa a cikin zuciyar ta " nasan lokacin da zaku riski takaddar nan nayi nisa daku ku yafe min iyaye na nasan kuskure amma ba a son raina bane zuciya ta ce bata bukatar kowacce ya mace ta kusance ta daga karshe ni Safraz Abdullahi na saki matata Ummusalma Hashim saki daya idan ta samu miji tayi aure don Allah ku yafe min .


Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un ta fara fada a fili wanda ya jawo hnkalin Aunty Aisha tayi kanta tana cewa Khadija lafiya ba magana sai kuka tana girgiza mata kai ta mika mata takaddar dake hannun ta baga karasa karantawa ba ta yadda takaddar tace Subhanallah innalillahi wa'inna ilaihiraji'un Daddy ya matso kusa dasu yace lafiya kuwa ganin takadda a kasa ya sunkuya ya dauka ya karanta murmushi kawai yayi ya saka ta acikin aljihun sa ya nemi wuri ya zauna ya sunkuyar da kansa cikin kunar zuciya yace " Mai zan fadawa Jauro ? Mai zan fadawa Inna Salamatu da ta bani amanar jikar ta mai zan fadawa duniya idan taji cewa na kasa bawa dana tarbiyyar da zai bi umarni na.


"Aa Daddy ba laifin ka bane kayi kokari wurin bamu ilimi da tarbiyya duk wanda ya zargeka akan abinda yaya aikata hakika baiyi adalci ba kuma duk mai hankali bazai zarge ka ba musaddiq ne yake fada wanda bai san abinda ya faru ba sai yanzu wurin sa Khadija tayi da gudu ta ce Yaya Musaddiq kaga halin da yaya ya saka Salma daga mata kai kawai yayi yana hawaye ita ma kukan takeyi ya rungume ta tsam a kirjin sa yana bata hakuri.

Nasan zakuji ba dadi yanayin typing din kuyi hakuri wlh azmi ke bani wuya ga yariya ta ba lafiya ku dinga hakuri da Wanda kuka samu ina alfahari daku masoya

*SALAME*
53-54
OUM SHARIFAT CE>??

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI


(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE

Karima dake zaune akan cinyar wata hamshakiyar mata tana sipping wani abu a kofi kiran Hanan ya shigo da sauri ta sauka daga kafar matar ta ce " zan tafi hajiya ta bata fuska matar tayi ta ce " haba my dear na zata fa kwana zaki min amma shine kike cewa zaki tafi"kiyi hakuri sweetie nayi miki alkawarin idan na dawo zan yi miki sati guda washe baki matar tayi fuskar ta fall farin ciki ya ce idan kuwa haka ne zanyi mana booking flight ki fadi duk kasar da kike so zamuje mu mu huta wata irin shekawa karima ta fada kan matar ta rungume ta tare da kissing labban ta tace dako na shayar dake zuwa mai dan karen zaki idan na ganni a Londo.
" Kisa a ranki kawai kinje cewa matar tana wata irin dariya irin ta rikakkun yan bariki. Da haka sukayi sallama ta hada kayan ta har zata wuce matar ta kamo hannun ta ta damka mata bandir din yan dubu guda biyar tace ga wannan ki gyara min kanki kafin ranar tafiya zamu yi magana ta waya inaso nima gobe zan wuce Abuja cike da farin ciki tabar hotel din ta kama hanyar gidan.

Tana kofar gidan ta tarar da motar da aka bawa Hanan wani zaro ido tayi cikin ranta tana yaba kyawun motar a fili tace wani bakon arzikin mukayi.

Tura kanta cikin gidan tayi babu ko sallama ta same su zaune kowa da tulin kaya a gaban sa, turus tayi tana jiran karin bayani gudar da mama tayi ne ya kara tabbatar mata akwai wani abu kafin ta kai ga tambaya mama ta fara bata labari zabura tayi ta fara daga rigar jikin ta ta fara rawa tana wakar rawar baza riga itama mama biye mata tayisuka cigaba da rawar ganin hankalin su ya tafi wajan rawar Hanan kuma ta shiga dakin mama yasa Nafisa yin sadaf Sadaf ta bayan su ta fice da kullin kayan ta.

Saida suka gama tikar rawar sannan Karim ta kwaso yan kayan ta kadan suka zuba a mota sannan suka shiga neman Nafisa.

Ko kina sun duba a gidan babu Nafisa sun kira wayar ta bata dauka har mama zata fara fada Karima ta ce kinsan fa Nafisa akwai gidadawan kawaye may be ta tafi sallama dasu kawai ta tura mata address din gidan sai ta biyo mu shawarar Karima suka dauka aka turawa Nafisa address din gidan sanna suka shiga motar suka wuce.
Sunan zuwa bakin get din gidan mama da Nafisa suka fara waro ido suna santin gidan suna shigar mamaki ya kara rufe su.kujerun dake cikin parlon mama ta fara latsawa tana kallon katuwar flazma dake parlon ga sanyin ac dake kadawa har lumshe ido mama takeyi.

Nafisa tinda ta fice daga gidan ta fita bakin titi ta hau napep ta wuce gidan Kawu Kabiru.lokacin da yaje bayanan sai matar sa da yayan ta da faraa suka karbe ta Aisha wacce ba zata wuce saar Nafisa ba ta karbi kayan ta takai dakin ta sannan ta kaiwa Nafisa ruwa tayi wanka ta zubo musu abinci suka fara ci farin cikin ganin Nafisa Aisha takeyi itama Nafisan tana farin cikin haduwa da Aisha da zata zauna tare da ita haka maman su ma bata da matsala.
Duk kiran da su Karima suke mata tana gani ba zata iya zama a gidan da aka same shi ta mummunar hanya ba iya abinda taci ma tana rokon Allah ya yafe mata suna cin abincin sakon address din ya shigo wayar ta murmushin takaici tayi tayi musu reply" kuyi hakuri bazan iya zama a gidan da aka saida daraja da mutunci na ya mace ba zan zauna a gidan kawu Kabiru har zuwa ranar da za a daura aure na da Sulaiman. Tura musu tayi sannan ta kashe wayar ta ta sai bayan sallar Isha'i kawu ya dawo inda ya iske Nafisa a gidan ba karamin dadin hakan yaji ba bayan sun gaisa Nafisa ta sanar dashi duk abinda ya faru tindaga farkon shigar Hanan wannan kungiyar ta zawarawa har zuwa motar da ta samu da kuma gidan da suka koma yau hadda Karima data taba ganin vedion tsiraici na mata a wayar ta da alama turo mata sukayi itama kuma tana turawa wasu wannan abun shine abinda yafi dagawa kawu hankali zuciyar sa ta fara tuhumar sa da rashin kulawa da yayan dan uwan sa sai dai kuma ba daga su bane mahaifiyar su ce ta hana su shiga sabgar yaran ta akan su har kotu takai su sharri kala kala tayi musu akan yayan nata daga karshe alkali ya bata yayan ta ita kanta Mama taji bakin cikin halin da mama ta jefa yayan ta adduar shiriya suka yi musu sannan kawu ya kara yiwa Nafisa da AISHA nasiha yayi musu addua suka tashi suka nufi dakin su.


Hanan suna cikin dube duben gidan sakon Nafisa ya shigo wayar Karima wani uban ashar Karima ta dura kafin ta karanta musu sakon dabas mama ta zauna akan carpet ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login