Showing 15001 words to 18000 words out of 60473 words

Chapter 6 - SALAME COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM SHARIFAT CE.doc

iyayen mu maza da mata daga cikin iyayen mu maza da yawa akwai wadanda basa farin ciki da haihuwar mu mukan samu damarmaki da yawa da kuma buri ka Ubangiji ya halicce mu da fikira da basira muna saka abubuwa da dama a ranmu da tinanin zamu zama wasu abu a rayuwa wato dai mafarkan mu, muna girma burikan mu suna kara yawa da hasashen samun nasara saidai lokaci daya ake katse mana wannan burin ba kowa ke katse mana ba sai iyayen mu maza a tinanin su ita ya mace bata da yancin cika burin ta batada damar zama wata abu a rayuwar ta zasu dauke mu su aurar damu ga maza daga nan wani namijin ya sake karba zai dora shima, da farko zasu fara numa marmarin su akan mu amma daga lokacin da suka gama karar da alatun jikin mu ko kuma sukaji sun saba da dandanon mu sai su juya mana baya su fara hango wasu irin mu idan sun auro suma haka zasuyi dasu ana zaku gane cewa maza sun dauke mu tamkar ababen jin dadin su a lokacin da suke bukata kuma sun dauke mu tamkar rigar jikin su yau su saka wannan idan sun gaji koda batayi datti ba zasu cire su saka wata, a hankali zasu saka mu fara amsa sunan Zawara daga sunan mace wato tinda an dandani zumar mu darajar sunan mace ma ba zaa kiramu dashi ba saidai zawarawa, still dai zamu dawo gidan iyayen mu daga nan iyayen mu maza zasu fara cewa mun zubar musu da mutunci ba zasu dubi halin da muka tsinci kanmu a ciki kawai burin su mu matsa daga gare su, lokuta da dama nakan yiwa kaina wata tambaya wai shin idan har iyayen mu suna gudun haihuwar mace su wacce suke aure fadowa daga sama tayi ba haifar ta akayi shi meyasa nata mahaifin ya haife ta ya bata kulawa da tarbiyyar da ka gani kaji kana so? Meyasa burin namiji shine a haifa masa yara maza ? Meyasa basa tausayin mace? Duba ba wahalar laulayi da nakuda ya kamata acw koda takami mace ta haifo a ganshi da mutunci, to ma wai in fitsari banza ne kaza ma tayi mana , ta karasa fada cikin bacin rai gaba daya gurin ya rikice da maganganun dake nuni da goyon bayan ta wasu daga cikin su kuma wadanda suke da irin matsalar da ta fada aka sosa musu inda yake musu kyaikayi.

Gyaran murya tayi a speaker gurin yayi shiru ta sauke ajiyar zuciya tace " to wannan kungiya tazo da salon ramuwar gayya ina alhazawan birnin nan da suke daukar mace kamar takalmi? To su zamu fara farauta daga gefe muna da uban mu maganin kukan zawara wato malam Balan kusa ya hada mana wani turare wanda duk wanda ya shake shi zaiyi ta bin ki kumar rakumi da akala to mu kuma sai mu hada da kissa da kwantar da kai da shagwaba da salo salo irin namu na mata mu kara damke zuciyar su idan sukayi nisa sai mu raba su da matan su da yayan sannan mu tatse su daga baya mu hada musu tarkon da zasu fada mu fece mu barsu da kallon kansu a matsayin masu laifi gaba daya suka saka shewa kowacce ranta fess aka cigaba da tattaunawa sannan ta raba musu turaren a cikin karamar kwalba basu tashi daga taron ba saida aka kira sallar magrib.



Gaba daya maganganun Aunty mery ke yi mata yawo a zuciya tin bayan tafiyar ta, jikin ta a sanyaye tayi sallar magrib tana nan tana sake sake gefen ta mama talatu wacce momy ta daukar mata domin aikin gida da kuma debe mata kewa tana ta bata labari saidai kawai ta daga kai ba tare da ta fahimci komai ba har aka kira sallar isha'i sukayi sallah ta taimaka wa mama wurin dakko abinci suka zauna suna dan hira jefi jefi suna cin abincin suna gamawa ta kashe kanukan takai kitchen ta wuce dakin ta ta watsa ruwa tare da yin brush ta dawo tsakiyar palon ta fara tafiya a hankali idan takai bakin kofa sai ta dawo baya ta girgiza kai ta kuma sake wa , ta gwada tafiya tafi kala goma kafin ta gaji ta fada kan bed tayi addua bacci mai dadi ya dauke ta.

Bata farka ba sai bayan an idar da sallar asba da sauri ta shige toilet tayi alwala ta fito tayi nafila tayi sallar asba ta dakko qur'ani ta fara karantawa cikin wata nutsatstsiyar muryar da ita kanta batasan tana da ita ba a wurin kararun Alqur'an kawai take amfani da ita.

Ta dan jima tana karatu kafin ta ajiye ta daga hannu kamar yanda ta saba tana kwararowa umman ta adduar samun rahamar Ubangiji sannan aka yiwa Baffa da Inna da momy,Daddy Yaya Musaddiq Aunty Khadija sannan ta shafa ta tashi ta shige toilet a gurguje tayi wanka ta fito daure da towel ta zauna a kujera mudubi ta fara murza mayuka masu dadin kamshi a jikin ta,

White powder tare da white lips kawai ta shafa ta saka uniform tare da takalmi ta dauki school bag dinta ta fito parlo, ba karamin kyau kayan sukayi mata ba farar riga ce da siket ne mai yar tsaga a baya dack blue sai dan karamin farin hijab, agogon hannun ta ta duba 7:10 da sauri ta karasa daining tana gaida mata a gaggauce tasha tea da waina ta fice tana yi mata sallama, driver da Daddy ya daukar mata yayi ready dama ita kadai yake jira tana fitowa ya bude mata mota, gidan baya ya bude mata ta girgiza masa kai tana murmushi ta bude kusa da driver ta shiga shima murmushin yayi ya zagaya shiga mazaunin driver ya zauna yana shirin tafiya ya tsinkayo siririyar muryar ta wacce aka fara training din gyarawa tana gaida shi cike da jin dadi ya amsa yana mamakin tarbiyyar yarinyar.


Mrs Sharif ce

*SALAME*
35+36

Oum Sharifat ce

=???JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI=???
(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE

Da murmushi a fuskar sa ya fita daga gidan ya hau titi ya nufi makarantar, cikin zuciyar Salma kuwa zakuwa tayi tana dokin zuwa domin ta hadu da Aunty Khadija kwanan su uku basa tare amma tana ji kamar tayi shekara uku bata ganta ba .


Sake sake take ta yi a ranta irin abinda zatayi mata idan suka hadu tana jin haushin yanda ta barta har kwana uku batazo gidan ba , kamar tana kallon ta ta turo baki a zuciyar ta tace ko kewa ta ma batayi ba.

Daidai nan driver yayi parking tare da bude mata murfin motar a hanzar ce ta fto ta kalle shi ta sakar masa murmushi ta ce sai anjima shima murmushin ya sakar mata ya ce '" to Allah ya bada ilimi mai amfani da amin ta amsa tana shigewa cikin makarantar .


Karfe 10:00 daidai aka fito break Khadija ce zaune a inda suka saba zama tare da Salma tana ta waiwayen ta inda taza hango ta taji an dafa ta ta baya a hankali ta juye don ganin waye turus tayi tana kallon Salma wacce take tsake ta harde hannuwan ta a kirjin ta tana kallon Khadija fuskar ta a hade bakin nan an turo shi gaba kiris take jira ta fashe, kallon sama da kasa Khadija tayi mata ta kara tabbatar wa kanta Salma ce ta zanca a zaton ta zata fado mata akai ne kmar yanda ta saba cikin zuciyar ta ta ce" haka aure ke zanca mutane ? " Ita kuwa Salma ganin Khadija taki kulata sai faman kallon ta takeyi yasa tayi saurin juyawa zata koma da sauri Khadija ta ruko hannun ta ya jiyo da ita zuka zauna ta ce "" kiyi hakuri my lovely sister ina ra mamakin yanda kika canza ne kinyi kyau kmar bake ba kuma naga kina wani yanga kin zama yar gayu aikuwa kmar an sosa wa Salma inda yake mata kaikayi ta yi wani farr da ido ta ce "" tin yaushe na zama yar gayu yar boko ke nifa yanzu ba villager bace" dariya sosa Khadija tayi tana jin dadin kasancewar ta da Salma ta ce ai dama ke ba villager bace duk wanda yace miki villager ma to shine villager din ba ke ba " abun yayi wa Salma dadi nan ta shiga bata labarin Aunty mery ana yanga ana yauki ita Yar gayu yar boko basu yi break din bama aka koma aji suka tashi kowacce tayi bangaren su sakamakon Khadija tana bangaren secondary ne tana jas3 ita kuma Salma tana primary 4 amma Daddy yace ana zatayi jarrabawa da yake dama makarantar daga primary 5 ake gama primary.

Da aka tashi ma tare suka fito suna hirar su abin shaawa har suka iso bakin gate drivern Salma ya dauke ta suka nufi gidan Safraz yayin da itama Khadija drivern gidan daddy ya dauke ta suka tafi suna dagawa juna hannu.



Karfe 4 na yamma Hanan ta shirya cikin doguwar rigar atamfa wacce aka yiwa dinkin straight gown ya kama jikin ta sosai tayi daurin dan kwalin ta ya zauna sosai wuyan ta sanye da sarka yar siriya kalar silver haka ma yarin ta da agogon hannun ta flat shoe ta saka da yar karamar jaka sai baza kamshi takeyi tayi mama sallama ta fice ita kuwa mama sai washe baki takeyi tana bin Hanan din da addua, tana fita ta shiga motar Hasina suka wuce wani babban Restaurant dake gaban unguwar su.


Yanayin girma da tsarin wajen da kuma manyan motocin dake fake a wurin kadai ya isa ya sanar da kai cewa wuri ne na wadanda suka isa.

A gefe Hasina tayi parking motar ta wacce zuwa wurin yasa taji ta girmi hawa irin wannan motar ranta a jagule tana karewa motocin wurin kallon suka shi suka ja kujeru suka zauna kalle suka farayi ta wutsiyar ido suna kallon yanda mutanen gurin ke cin abnda sukayi order kmar basa so maganar da sukaji a bayan su ne ya saka su juyawa a tare"" me kuke bukata ? Matar dake tsaye sanye uniform din maaikatan wurin ta tambaya da sauri Hannah ta ce "ruwa da lemo kawai ya isa " okay mah ta ce tana juyawa, su kuma suka cigaba da abinda sukeyi.


Idon Hanan ne ya sauka kan wani dan dattijo wanda zai iya kaiwa shekara 50 saidai haduwar sa da jin dadin sa suka boye shekarun nasa zatayi zaton dan shekara 40 ne yana sanye da farin wani lallausan yadi dinkin yar ciki da babbar riga kansa dauke da bakar tangaran takalmin kafarsa half shoe ne baki sai kyalli yakeyi idon sa dauke da farin glass hannun sa rike da jarida yana karantawa lokaci lokaci yake sauke jaridar ya dan kurbi lemon dake gaban sa .


Zungurar Hasina tayi ta nuna mata shi da ido itama ta nuna mata wani dake bayan su wanda ke sanye da bakar suit a tare suka saki murmushi suka fito da kwalbar turaren da uwar zawarawa ta basu suka goga shi a hannun su sannan suka tashi kowacce tayi tata hanyar.


Tana zuwa wurin da mutumin yake ta goga turaren da kirjin ta da wuyan ta a wayen ce ba tare da kowa ya kura ba sannan ta karasa ta ce "" Assalamualaikum" a hankali ya sauke jaridar ya dago kansa ya sauke kananun idanuwan sa akanta wani yarr yaji tin daga yatsar kafar sa har tsakiyar kwakwalwar sa ga wani daddan kamshi da ke tashj daga jikin ta samun kansa yayi da sakar mata murmushi ya ce " Amin wslm warahmtllh Bismillah ya fada yana nuna mata kujerar dake gaban sa a yangan ce ta dan dosana mazaunan ta ta ce ""suna na Hanan sakon zaka bani " da mamakin yake kallon ta yana maimaita sako kuwa yammata " dan fari tayi da ido ta ce " eh mana ba kaine mijin Zubaida ba ? Ai tace min zamu hadu a wannan eatry din zaka bani sakon, Yar dariya yayi domin ya fahimci makuwa tayi ya gyara zaman sa tare da dora kafa daya kan daya ya ce"" ba nine mijin Zubaida ba saidai Ina neman alfarma na zamo mijin Hanan" dan yamutsa fuskar tayi cike da shagwaba ta ce " don Allah ka dena yimin wasa sauri fa nake yi.

Duk wata gaba ta jikin sa saida ta amsa yaji ya kara narkewa a cikin kaunar ta ya sauke kafar sa ya dan rankwafo wurin fuskar ta yana sakar mata murmushi ya ce "" dagaske nake ba nine wanda kike nema ba amma ina godiya ga Zubaida data turo ki neman mijin ta ke kuma kikayi batan hanya.



Sunana Alh Jibril ana kirana da mai dolar kallo daya nayi miki naji kaunar ki ta samu isashshen wuri a zuciya ta ki amince da soyayya ta ni kuma nayi miki alkawarin zan maida ke sarauniyar mata duk da dama sarauniyar ce amma zan bada gudumuwa dari bisa dari domin dorewar zaman ki akan kujerar ki.


Mrs Sharif ce

*SALAME*
37-38
OUM SHARIFAT CE>??
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE

Boyayyiyar a jiyar zuciya ta sauke cikin ranta wani farin ciki ne mara misaltuwa ya lullube ta a fili kuma cewa tayi " tinda muka rabu da miji na bnsake tinanin wata soyayya ba dama kuma shima ba son shi nakeyi ba yan uwan mahaifina ne bayan rasuwar mahaifin nawa suka aura min shi saboda yana basu kudi daga karshe kuma ya dinga yi min gori zagi da duka har yayi min sakin wulakanci shiyasa nake tsoron masu kudi saboda gudin fadawa rayuwar da nayi a baya ta karasa maganar tana shashshekar kukan karya


Kalar tausayi Alh Jibril yayi yace" dama haka rayuwa take marayu da dama ana sadaukar da farin cikin su day rayuwar su ma domin cikar burin wasu , Ina so ki kwantar da hankalin ki zan zame miki tamkar ruwan wanke datti zan goge miki duk wani tabo da aka dasa a cikin rayuwar ki.

Kasa da kanta tayi tana wasa da zoben hannun ta alamar kunya ta ce " to shikenan na amince" ajiyar zuciya ya sauke yace Alhamdululillah yanzu abinda zaayi ki tashi na kaiki gida kar mama tayi fada ko?, kamar wata doluwa ta daga kai tana mikewa tayi gaba ya bita a baya Saida tazo saitin inda Hasina tayi taga wayam babu ita babu mutumin data hango ta saki wani shuumin murmushi cikin zuciyar ta ta ce " shegiya Hasina tayi cikin da shi.

Suna fita ta tsaya a baya yayi gaba gurin wata katuwar bakar mota wacce ke kyalli kallo daya zakayi mata kasan ba ta kananan mutane bace ya tsaya tare da dannan remote fitulun motar suka kawo sannan ya bude murfin mai zaman banza ya kalle ta ita shidin take kallo suka hada ido ta sakar masa murmushi, da ido yayi mata inkiya ta karaso cike da kwarkwasa da jan hankali ta shiga motar shima ya zagaya bangaren driver ya shiga yayi wa motar key suka fice daga wajan gaba daya.

Tinda suka fara tafiya yake satar kallon ta yana jan ta da hira tare da yaba kyawun ta ita kuwa saidai tayi murmushi ta ce "" nagode alajina " ba karamin dadi hakan yake masa ba yanayin kunyar ta tana kara burgeshi soyayya da kaunar ta suna sake gina babbar fada a zuciyar sa, abinda bai sani ba kuwa wannan duk cikin plan din ta ne.

Sunyi tafiya mai dan nisa kadan yayi parking daidai wani tangamemen shopping mall ya bude musu kofar a tare suka fito ta jingina da jikin motar ya zagayo kusa da ita tare da rankwafowa wurin fuskar ta kamshin sa ya daki hancin ta saida ta sauke ajiyar zuciya kafin ya jiyo sautin tattausar muryar sa mai cike da nutsuwa ya ce " muje ko gimbiya, lumshe ido tayi tayi masa murmushi suka jera zuwa cikin wajan.

Kyau haduwa da tsarin wajen ba karamin gigita Hanan yayi ba a kauyan ce take kallon wurin badon bata saba zuwa shopping mall ba saidon bata taba tinanin zata taba shiga irin wannan wuraren da take ganin su a hotuna ko a finafina ketare a badini ji take kamar tayi tsalle a zahiri kuma ta kame kanta binsa kawai takeyi saida sukaje tsakiyar wurin sannan ya tsaya ya juyo yace to "Madam ki dauki duk abinda kike so "
Turo baki tayi cikin shagwaba ta ce to ai ni bansan abinda zan dauka ba, yar karamar dariya yayi yace " to ni bari in dauka miki .

Nan ya shiga zagaye wajan yana daukar abubuwa kala kala yana zubawa a cikin basket tana nan tsaye tana jaddada irin aikin da turaren yakeyi dakuma mamakin dama akwai irin wadannan mutanen a garin nan amma ta zauna zata kashe kanta a gidan Safraz gashi da shegen kishi ga bakar zuciya kmar kuturu, tana cikin tinanin taji numfashin mutum a kusa da ita sarai tasan shine domin taga tahowar sa amma sai ta tsorafa har tana dafe kirji dariya sosai yayi ya ce "to matsiyaciya nine "shagwabe fuska tayi kmar zatayi kuka tana kallon sa ,hade hannayen sa biyu yayi tare da sunkuyar da kansa alamar bada hakuri saida tayi farrr da idon ta sannan tayi dariya suka fice.

Mamaki ne ya kmata ganin kayan da ake ta lodawa a cikin boot din motar ta bude baki zatayi masa magana ya saka dan yatsan sa akan labban sa yace "" Shhhh kar kice komai kedai shiga mota in kaiki gida babu musu ta shige yaja motar suka kama hanyar gidan su .


A motar ma jefi jefi suke jira duk da yawancin hirar shine yakeyin ta har suka karaso kofar gidan yayi parking ya bude motar suka fito sannan ya bude boot din ya fito mata da kayan ya dinga ajiyewa a gaban ta kafin yace gashi nan a rabawa yan gidan ya saka hannu da aljihun wandon sa ya dakko rafar yan dubu guda biyu ya bata ya ce wannan kuma ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login