Showing 45001 words to 48000 words out of 60473 words

Chapter 16 - SALAME COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM SHARIFAT CE.doc

fado mana gida,tana karasa fada ta haye sama ba tare da ta juyo ba.gaba daya aka rasa wanda zaice Masa komai kowa jikin sa yayi sanyi ji yayi gaba daya ya muzanta a gaban yaran da yayi rainon sa da hannun sa juyawa zaiyi da nufin komawa idanun sa suka sauka akan Salma dake takure a jikin khadija, da sauri kirjin sa ta buga wata zufa ta karyo masa lokaci guda idanuwan sa suka fara sauya kala, dama momy tasan Salma? Kodai kawar khadija ce? Duk a zuciyar sa yake wannan tambayar da babu wanda zai bashi amsar ta kuma har lokacin idon sa kirr akan Salma.

Kokarin yi masa magana Yaya Musaddiq yakeyi yabi inda yake kallo yaga gaba daya attention dinsa na kan Salma wani bakin kishi ne ya dira a zuciyar sa nan take zuciyar sa ta shiga tariyo masa irin wukancin da yayiwa Salma a baya wani uban tsaki yaja wanda ya maido da hankalin su gaba daya kansa a fusace ya matso kusa da Salma yaja hannun ta ta gefen sa ya raba ya fice tare da ita, ba karamin gigicewa Safraz yayi ba ya bisu da ido yana kokarin bin bayan su bai san yazo karshe parlon ba saida ya buga goshin sa a jikin kofa sannan yayi baya ya bugu da karfen step din dake cikin parlourn saura kiris ya fadi yasa hannun sa a kasa ya mike tsaye zuciyar sa tana tukukin bakin ciki har wani daci yake ji a bakin sa runtse idon sa yayi ya ga hannun Musaddiq a jikin Salma da sauri ya bude ya fice a zafafe, yana fita ya hango su kan fararen kujerun kamar ma sun manta dashi yayin da Salma take ta dariya tana nuna Yaya Musaddiq shi kuma ya kura mata Ido kana iya hango zallar kaunar ta a cikin idon Yaya Musaddiq.

Da sauri yayi wajan yna huci ko mai ya Tina kuma sai ya dawo baya ya nufi wurin motar sa yaja ta da karfi ya fice daga gidan.

Tin yana hanya yake kiran layin Ibrahim har yaje gida bai dauka ba, Sarai Ibrahim ya gane Safraz ya dawo yana sani yaki daukar wayar, Saida yaga kiran yaki karewa ya dauka zai fara masifa yaji muryar Safraz din kamar shide bakin sa sai rawa yakeyi ya kasa magana. Hankalin sa me ya tashi ya fara tambayar lafiyar Safraz din amma tsananin bacin ran da yake ciki ya hana shi magana sai wata zazzafar iska da yake fesarwa daga bakin sa.

Fahimtar akwai matsala duk da Ibrahim ya jima yana hangowa Safraz babbar matsalar da taurin kansa zai iya jawo masa cikin kasa da minti talatin ya isa gidan Safraz din , part dinsa ya wuce kai tsaye inda ya tarar dashi a tsakiyar parlor yana ta zagaye hannun goye a bayan sa lokaci lokaci yake kaiwa iska naushi yana huci, inuwar mutum ya gani a tsaye da sauri yayo kansa yana magana cikin karaji yace " Ibrahim ka sanni? Ka gane ni? Dafa kafadun sa Ibrahim yayi yace " easy mana guy wannan wacce irin tambaya ce? ko a filin adi na ganka zan kasa gane ke ne? Ko don kaga ka kara kwanji ya fada da sigar wasa.

Jan Ibrahim yayi har kan sopa ya dube shi yace " ka kalle ni sosai menene ya canza a jiki na da momy ta kasa gane ni? Musaddiq bai kulani ba khadija ma haka , Ibrahim yarinyar da nake matukar so wacce kalaman ta suka kara tausada zuciya ta wacce nake bacci da hoton ta a kirjin na wacce nake Jin sonta yana karuwa kowane bugu na zuciya ta ita ce a tsaye a gaba na a gidan momy da Ido na naga Musaddiq ya rike hannun ta Ibrahim soyayya na gani a idanuwan su Ibrahim wlh idan na rasata mutuwa zanyi.


Wata irin dariya Ibrahim ya sheke da ita har yana tafa hannu yace " tabbatas ba haushe yayi gaskiya da yace duk girman gona akwai kunyar karshe kuma duk nisan jifa kasa zai fado sannan yace duk dan da ya hana uwar sa bacci wlh shima bazaiyi ba,
To bari kaji ko mutuwa kayi ka dawo koda kowa zai kasa gane ka banda momy na tabbata koda bugub numfashin ka momy zata gane ka, abinda baka sani ba shine momy ta yafe ka tin sanda ka nuna bata Isa tayi iko da rayuwar ka ba tin sanda ka wulakanta mata ya tin lokacin ka dasa bakin ciki a zuciyar momy wanda har yanzu bai wanke ba.

Salma kuma wacce kake maganar kana so itace wacce Musaddiq zai aura nan da sati hudu rana daya zaayi auren da namu nida khadija, kuma ma banda abinka wannan yarinyar ai ka wuce ajin ta ba mate dinka bace kaine fa brigadier general Safraz mai zakayi da wannan kucakar bagidajiya, wata irin tsawa Safraz ya daka wa Ibrahim cikin zafin rai yace kar ka sake Ibrahim kar ka sake kaskantar min da burin zuciya ta wlh idan kana fadar mummunar kalma akan ta zuciya ta zata iya fashe wa.

Murmushin takaici Ibrahim yayi yace "to naji saidai kmar yanda na fada maka kai kafi karfin Salma domin Salma da kake mgana akanta ba wata bace daban Salame ce dai tsohuwar matar ka villager wacce har abada ba zaka taba so ba don haka kabar mgnar ta don duk duniya a yanzu babu wanda ta tsana kmar kai ita a yanzu tafi karfin ka ta wuce ajinka zuciyar ka kuma idan kaga dama ka fito da ita ka tattauna ta ka hadiye ka mutu kowa ya huta ni bari inje in sanar da Daddy a fara shirya likkafani.

Gaba yayi zai fita daga parlon da karfi Safraz ya janyo shi ya turashi kan kujera yana muzurai ya daga hannu zai naushe shi cikin zafin nama Ibrahim ya kauce ya mike a zafafe ya shake Safraz ya kaishi jikin bango da bacin ran da Safraz bai taba gani a tare da shi ba ya ce " sau nawa nace ka tausaya mata? Sau nawa nace ka daga darajar ta? Sau nawa nace ka maida ita irin matar da kake so? Kuma sau nawa kace min baka son ta? Sau nawa kace min har abada ba zaka taba kaunar ta ba kafi karfin auren bagidajiya mai warin kashin dabbobi? Sau nawa kace min da kiwo ta dace bada auren ka ba?

Ka wulakanta ta ka ci mutuncin ta ka zalince ta ka zage karfin ka kayi mata fyaden da likitoci ma rahoton mutum biyar suka fitar duk a burin ka na ganin bayan rayuwar ta sai yanzu da yayi abinda ka kasa ta zama mutum abar so sannan zaka lallabo ko kunya baka ji ba, to ka sani wlh Salma tafi karfin auren Wanda ya bijire wa iyayen sa , sakin sa yayi Yana furzar da iska daga bakin sa yace " sannan inaso nayi maka albishir a kokarin ka na kashe Salma ka bar mata kwayoyin ka a mahaifar ta kuma cikin ikon Allah ta haifi yara guda biyu shekara hudu kenan sun girma saidai yanda momy ta cire ka daga cikin yaran ta haka ta cire ka daga matsayin mahaifin sultan da Sultana . Musaddiq shine uban su kuma shine wanda suka sani matsayin mahaifi a makaranta ma da sunan sa suke bearing.

Yar karamar dariya yayi yace " ohh sorry na manta ashe fa ba albishir zan maka ba jaje zan maka ka hada jini da yar kauye kayi ha?uri yin Allah ne bana mutum ba yana fada ya fice yana Yar dariya.

*SALAME*

71

OUM SHARIFAT CE>??

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI


(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE


Sosai yake kukan da yake fitowa daga karkashin zuciyar sa nadama marar amfani ce tazo masa a lokacin da bata da amfani, dade a wurin zuciyar sa na tukukin bakin ciki ganin babu abinda kukan zai amfanar dashi yasa shi tashi ya haye sama, toilet ya fada yayi alwala ya fito ya shimfifa pray mat ya tada sallah saida yayi sallah rakaa takwas sannan ya dauki carbi ya fara istigfari, hankali yake jin nutsuwa tana saukar masa saidai fargabar dake cin zuciyar sa, saida yayi sallar Isha'i sannan yayi wanka ya shirya cikin wani farin yadi kansa ba huka bakin gashin sa a kwance sai kyalli yakeyi saidai kana ganin sa kasan yana cikin damuwa, karsashin sa ya ragu yanayin sa yayi sanyi babu walwala a tare dashi ya dauki motar sa shi kadai ya fice ya nufi gidan nasu.

A kofar gidan yayi parking ya fito ya shiga ciki tambayar maigadi Daddy yayi yace yana ciki, shiru yayi yana tinanin wani abu a ransa kafin ya kalli maigadin yace " baba zaka iya taimako na ? Da gudu kuwa yallabai cewar maigadi don bazai taba manta a yanayin da Safraz ya tsince shi bab da irin taimakon da yayi masa a rayuwa, so nake ka sanar da Daddy yana da bako ka ce masa baka san bakon ba. Har zaiyi magana sai kuma ya kada kansa ya shige ciki , a kofar parlon ya tsaya yayi sallama daga can khadija ta amsa yace " a fadawa alh yana da bako ' da to khadija ta amsa ta wuce parlon Daddy ta sanar masa sannan ta dawo ya bude kofar parlon tace " wai kayi masa iso ya same shi a parlon baki, to shikenan hajiya Dije dariya tayi ta shige ciki shi kuma ya nufi wurin Safraz ya sanar dashi abinda Daddy yace , godiya yayi masa ya ciro kudin da baisan ko nawa bane ya bashi ya wuce ciki.

Kai tsaye ya wuce parlon baki akan carpet ya zauna ba jimawa Daddy ya shigo da sallama daga kansa yayi zai amsa suka hada ido da Daddy da yanzu momy ta gama bashi labarin zuwan sa, hade ransa yayi zai juya Safraz yayi sauri rarrfawa ya rike kafar sa yace " kayi min rai Daddy nasan ni mai laifi ne a gare ki don girman Allah don soyayyar da kukewa fiyayyen halittar manzon Allah saw kuyi min kowanne irin hukunci amma kada ku yafe ni kar ku janye ni daga jikin ku don Allah ku barni da iya hukuncin kuntata kaina da nayi na tsawon shekaru ba tare da ku ba don Allah Daddy ku canza min kowanne hukunci ne zan dauka amma banda wannan Daddy.

Dawowa Daddy yayi saidai fuskar sa babu alamar annuri yace" Safraz kai da muka haifa ka nuna zaka iya rayuwar ka ba tare da mu ba sai mune zamu kasa rayuwa babu kai? To Ina so ka sani ni kayi min laifi laifin kuwa daya ba wai kin bin umarni na dakayi ne babban laifi a guri na ba saidai hucewa da kayi akan yarinyar da yadda muka baka umarni haka itama muka bata babban abin takaici na shine yanda Hashim ya iya bawa Salma tarbiyyar da ni da bani na haife ta ba ta sadaukar min da rayuwar ta tabi raayi na amma ni na gaza ta bangaren tarbiyya shiyasa ka kasa bin umarni na. Saidai ina hango laifi na awani bangaren domin tinda aka sanar dakai matsayin Salma a wurin ka ka fara nuna min ni banida mutuncin yin iko dakai amma ni dinnan har wani tinkaho nake ina dukan kirji Ina cewa na aurar wa Salma dana Safraz bansan cewa niba kowa bane a gare ka ka tashi ka fitar min daga gida wlh Safraz ba zan taba zama da dan da nine zan bishi ba.

Nayi dawainiya dakai tin kana ciki har kazo duniya na baka abinci na nema maka lafiya na baka ilimi nayi kokarin baka tarbiyya.

Mahaifiyar ka ta saudaukar da rayuwar ta don kai kazo duniya tasha wahala a cikin ka ta kasa haihuwar ka har saida aka yanka ta aka ciro ka, a lokacin banida kudin da zan dauki mai rainon ka inakan nema dai itace tayi maka komai kayo mata fitsari ta wanke kayi mata kashi ta wanke ko kallon banza batayi maka kayi amai kayi tmbudi duk ta wanke ta kalle ka tayi farin ciki taki ci ta baka amma saboda ta nemi wata alfarma a cikin rayuwar ka ka kasa yi mata, na tabbata inda Musaddiq ne iya alkairin da ahalin Salma sukayi wa mahaifiyar sa ya isa yasa rayuwar sa ta inganta duk da bazai iya biyan abinda sukayi ba amma zai kwatanta akan yarsu . don haka bama bukatar ka kaje kayi rayuwar ka muma kabar mu muyi tamu da yaran da suka dauke mu da kima da mutunci.


Kuka sosai Safraz keyi harda majina ya sunkuyar dakansa kasa yace " naji kunya Daddy nayi nadamar rayuwa ta nayi nadamar kasancewa ta a haka ban kasance da na gari a gare ku ba don Allah ku yafe min , khadija da tindazu ta shigo kawowa bako ruwa ta tarar da Yaya Safraz ganin halin da yake ciki yasa gaba daya jikin ta yayi sanyi haka ta fita daga parlon jikin ta ba kwari, momy ta lura da ita ta tambayi lafiya khadija ta kasa cewa komai saida momy ta maimaita sannan khadija tace " Yaya Safraz ne a wurin Daddy, da gudu momy tayi kitchen kafin khadija ta ankara ta fito da nufin part din baki, daidai lokacin da Safraz ke rokon Daddy ya yafe masa ya nema masa tafiyar momy gaba daya basu ji shigowar ta ba sai saukar muciya sukaji a kafadar Safraz kafin ya kara wani yunkuri ta kara buga masa ita a gadon bayan sa.

Biyu biyu ya fara gani cikin dakiya yace " ki kashe ni idan har zakiji saukin bakin cikin dana sakawa zuciyar ki momy na tuba don Allah ki yafe min kar ki bari a kaini kabari ba da bacin ranki momy inason Salma wlh ina kaunar momy kafin ya karasa momy ta sake kai masa a bayan sa duk da yunkurin kwacewa da Daddy keyi amma momy ta ki bashi dama wani karfi takeji a jikin ta a idon ta take hango Safraz ya zage karfin sa yana yiwa Salman ta fyade, Safraz bai sake cewa komai ba a zube a wurin babu alamar rai a tare dashi.



Karima saidai muce arziki yaci uban nada ta shiga cikin manyan mata masu lesbian na maxico tana babbar kungiyar madigo wadanda suke safarar mata zuwa kasashen larabawa bayan safarar mata Karima har cocaine suke fita da ita ya canza tayi kiba space din dake tsakanin kofofin hancin ta an saka mata wata sarka haka lips dinta na kasa an saka wani abu kmar barima ta gold daga kafadar ta ziwa gefen wuyan ta zanen wani katon maciji ne akayi shi ja dokin wuyan ta kuwa katon tatto ne aka zana shi irin shegun arna ba zaka tana gano hasken musulunci a tattare da Karima duk da dama tajima da ajiye sallar.

Mayan kudade take samu ta daina shigowa Nigeria saidai tayiwa mama aiken makudan kudade ita kuwa mama bata damu da rashin ganin Karima ba itadai Babban farin cikin ta shine ta samu duniya fiye da yanda take zato a baya, tayi kyau abinta tayi bulbul kmar bata haifu su Hanan ba, yaro ta samu yayan sa biyu ya saki matar sa ya auri mama take jika shi da kudi shi kuma take jika ta da love, idan yana gida yana makale da masoyiyar sa idan kuma ya fita yana makale da Hanan a hotel suna sheke ayar su.

Mrs Sharif ce
' *SALAME*

72


OUM SHARIFAT CE>??



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE
Da gudu khadija tayi kansa ta fara jijjiga shi tana kwala kara tana kiran sunan sa. Musaddiq da Salma dake harabar gidan suna shan kaunar su suka jiyo ihun khadija a tare suka tashi da sauri sukayo cikin gidan inda suka jiyo ihun suka nuna ganin khadija tana jijjiga mutum yasa Musaddiq leka fuskar sa Safraz ya gani kafin yayi magana yaji muryar khadija cikin kuka ta ce " ka taimaka mu kaishi asibiti momy ta kashe, sai a sannan Musaddiq ya fahimci Momy ce tayi wani abun ba tare da ya wani damu ba ya dakko mota maigadi ya kama aka saka shi a mota yaja hankali kwance ya nufi asibitin Dr mahfooz dashi yana zuwa ya kirashi a waya ya sanar dashi zuwan su, nurses ne suka fito suka dorashi akan gadon marasa lafiya suka shiga dashi ciki shi kuma Musaddiq ya juya kan motar sa ya koma gida.
Bai shiga gidan ya sanar dasu dawowar sa ba ya shige part dinsa ya kira wayar Salma suka cigaba da soyayyar su ba tare da damuwa da halin da yabar Safraz din ba, Daddy kuma jiran Musaddiq yakeyi yaji abinda ya faru khadija ma haka saidai ganin Salma yana waya yasa hankalin ta kwanta tasan tinda Musaddiq ya dawo to ba wani abu bane, sakin jikin ta tayi itama ta cigaba da sabgogin ta. Shima Daddy sharewa yayi yayi baccin sa momy kuwa wani sanyi taji a ranta koba komai ya fara Jin kwatankwacin abinda yar ta taji.


Gwaje gwaje sosai akayi wa Safraz bayan sunfit Dr ya fara neman Musaddiq saidai ko motar sa bai gani ba ya fara kiran wayar sa , busy yaji ya kira wayar Daddy baa dauka ba Musaddiq kuwa yana ganin Kiran bazai koma asibitin bane yasan dai matsalar bata wuce suma yayi ba shi kuma idan zai suma sau dari bazai iya zuwa ya zauna tare da shi ba, idan yagaji ya nemi sallama ya koma inda ya fito Daddy kuwa wayar sa a silent take baisan ma ana kira ba.


Ba karamin tashin hankali Dr mahfooz ya tsinci kansa a ciki ba ganin ya kasa samun layin kowa na Safraz. Ba yanda zaiyi haka ya kaishi wani daki dake vip section yayi masa allurai ya daura masa drip da kansa ya zauna dashi har asuba sannan wani nurse ya karbe shi ya tafi gida sai karde takwas ya dawo inda ya tambayi nurses ko wani yazo suka ce babu wanda yazo.

Bakaramin mamaki yayi ba kuma abin ya daure masa kai Safraz dai wanda kowa dake cikin familyn sa da mutanen dake kewaye dashi suka son sa tare da ji dashi Safraz dai madubin ahalin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login