Showing 33001 words to 36000 words out of 60473 words

Chapter 12 - SALAME COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM SHARIFAT CE.doc

Safraz ba tamkar matar wani acikin manyan kasa hka take ado da gwalagwalai haka Karima ba abinda takeyi sai harkar ta ta madigo ta shiga cikin manyan kungiyoyin su yayin da take samun manyan kudade take kashe musu kmar ba gobe itama ta sai mota mama ma an siya mata wata aka dakko mata driver yake kaita duk inda take so, cikin kawayen ta kuwa sai daga kai ita uwar masu kudi.


Bikin Nafisa saura sati biyu kuma har yanzu bataje gidan ba suma basu zo inda take ba duk da cikin ranta tana kewar mahaifiyar ta da yan uwan ta amma ta zabi tayi aure ta bautawa Allah ya mutu cikin niimar sa a kullum cikin yi musu adduar shiriya take tana saka ran wata rana zasu gane gaskiya.



Mrs Sharif ce
' *SALAME*
57-58
OUM SHARIFAT CE>??

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE


Wani irin kuuuuu cikin momy ya bada wata irin kara wani tukukin bakin ciki ya rufe ta har wani duhu duhu take gani kmar an fuzgo magana ta fito cikin rawar murya ta ce " a zubar dashi likita fyaden da akayi mata ne anan ta samu cikin bama bukatar sa da sauri Daddy ya juyo ya kalle ta a fusace ya ce " Maryam kina da hankali kuwa kinsan dai wannan cikin halak ne ko akan me zaki kashe dan sunna ko kuma shi cikin yana da laifi ne ? Ko Safraz din zaa sake haifowa duka a tare yake jero mata wadannan tambayoyin idon sa ya kada yayi jazur sallama yayi da dr tare da yi masa godiya ya fice daga office din Yaya Musaddiq da ya rasa gane labarin cikin farin ciki ya saka shi ko bakin ciki ya tashi ya rufa wa Daddy baya inda aka kwantar da Salma suka nufa suka tarar da ita an ta dawo hayyacin ta tana kwance tana bacci bayan an daura mata drip.

Jiki a sanyaye khadija ta kama hannun momy suka bisu . Jugum jigum sukayi a dakin har akayi sallar azahar sannan Yaya Musaddiq ya samo musu abinda zasu ci. Da yamma aka sallame su suka dawo gida .

Gaba daya ranar ba wanda yake cikin walwala kowa da abinda yake sakawa bangaren momy bakin cikin haduwar jinin Salma da Safraz takeyi taso ace babu wani abu a tsananin su ta gama tsara yanda zata hada auren Salma da musaddiq ta tabbata zai kula mata da Salma bazai cutar mata da ita ba.

Wannan shine burin Musaddiq tin zuwan Salma gidan yaji ya kamu da son ta lokacin da yaji labarin ita ce aka aura Yaya Safraz yayi bakin ciki sosai a hankali ya janye soyayyar ta ya fara daukar ta a matsayin kanwa. Abinda yaya Safraz yayi ya dawo masa da soyayyar ta sabuwa har yana jin dama rabon sa ce shiyasa haka ya faru yayi alkawarin zagewa ya kyautata mata ya nuna mata ita din ba abar banza bace kamar yanda Safraz ya nuna mata yana so ya daga darajar ta ya nuna mata soyayya da gata ya shayar da ita zumar kauna amma jin labarin cikin yasa jinin jikinsa yake tsitstsinkewa ya rasa menene abinda zaiyi bazai goyi bayan a zubar mata da ciki ba da wanna tinanin bacci mara dadi ya dauke shi.

Bayan sallar Isha'i momy ta shiga dakin Daddy jikin ta a sanyaye tayi sallama ciki ciki ya amsa ta saki dan guntun murmushi ta karasa inda yake a zauna ta kamo hannun sa cikin langwabar dakai tace "kayi ha?uri alhaji na banjin dadin hada jinin Salma da Safraz bane saboda ya nuna baya kaunar ta ya wulakanta ta ya zalince ta ya barta cikin halin mutuwa da rayuwa yanzu duk abinda yayi mata kana ganin ya cancanci ta raini gudan jinin sa ajikin ta har ta bari ya tsaga jikin ta ya fito dansa fa yanzu yakamata Salma tayi masa wannan gatan ka amince da haka bamu cutar da ita ba kuwa haba Alh idan muka bar Salma tayi wa Safraz wannan dawainiyar mun zalince ta ta karasa fada tana fashewa da kuka.

Dan guntun murmushi Daddy yayi ya kara matsawa kusa da momy yace " Maryam a hnkali ta dago kanta ta kalle shi sannan ta sauke idon ta kasa murya a dashe ta ce " na'am kinsan dalilin hada auren Salma da Safraz? Girgiza kai kawai ta kasa magana tausayin Salma ke nukurkusar ta da haushin abinda Safraz yayi ta tsinkayo muryar Daddy yana cewa " mudai iyayen su ne kuma mun hada auren su ba tare da sanin dalilin ba Ubangiji da ya bamu ikon hadawa shine yasan dalili shine yasan abnda zai faru yau da wanda zai faru gobe mai zai hana mu bar masa ikon sa.

Idan aka muka cire mata cikin kinsan munyi kisan kai kuma koda Ummusalma ta amince an cire cikin daga baya zatayi kuka damu saboda mun cutar da ita fiye da cutarwar da Safraz yayi mata kiyi hakuri maryama nasan kinajin abun a matsayi biyu na farko ke uwa ce kuma ke macece amma babu yanda zamuyi da abinda Allah ya tsara a karshen dukkan jarrabawar Ubangiji akwai nasara. Shikuma wancan yaron nasa an bincika min yana can Cairo kmar yanda Ibrahim yace bazan neme shi ba kuma bazan yi masa baki ba bazan fadi hukuncin sa ba har sai ya waiwaye mu ita kuma Ummusalma idan ma bakya so ta haihu da kanta idan cikin ya shiga watan haihuwa sai ku fadi duk kasar da kuke so kuje ayi mata cs.


Sai yanzu momy ta fahimci kuskuren da take shirin aikatawa cikin fushi murmushi ta sakar masa tace " nagode wa Allah da ya bani mijin mai tsoron sa da kuma hangen nesa ",kmar yara hada ya ja karan hancin ta yace " na godewa Allah da ya bani rigimammiyar matar da take shirin daukar jika amma har yanzu bata girma ba. Dariya gaba dayan su sukayi suka canza salon hirar .


Khadija kuwa bata farin ciki haka bata bakin ciki tana jira Salma tasan da maganar cikin idan tayi farin ciki zata taya ta idan tayi bakin ciki shima zata taya ta


Momy kasa fada mata maganar cikin tayi Saida aunty Aisha tazo gidan zuwa lokacin ta warware sosai duk da akwai yan laulaye laulaye a tare da ita amma tana samun kulawar Dr da kuma ta mutanen gidan ta kara kyau da hasken fuskar nan tayi kubul kubul da ita tayi dan kumatu . Sosai tayi farin cikin ganin Aunty Aisha bayab sun gaisa ne ta nemi ganin Salma a daki anan cikin nuna farin ciki take shaida mata tana ciki yanda Salma taga anty Aisha tana farin ciki yasa ta dauki abin da farin ciki itama ta manta yanda aka samu cikin ko kuma dai ince kuruciya na damun ta sai ta tna lokacin da taga Abu da cikin irin dadin da taji inama zata ga Abu ta fada mata itama tana da cikin saidai kuma mijin ya sake ta tasan menene aure kuma tasan menene saki ta kuduri niyyar zata haifi yarta kmar yanda ta fara jin shaawar ya mace kuma ba zata bashi ba shida baya son ta ma bare yaso yarta duk cikin ranta take wannan tinanin kanta a sunkuye ita a dole kunyar aunty Aisha take ji ( hmm jamaa nace yau ga Salma da kunya).



Tin daga ranar da taji zancen cikin laulayi ya kara ta'azzara kullum da zazzabi take kwana bata iya cin komai sai snacks da panta, savon fridge Daddy ya siyo ya kara a cikin lakin su inda daya aka cika mata shi da snacks daya da panta kulawa kuwa ta ninku shi kansa Daddy idan ya yafi kasuwa taana kiran Salma sau hudu sau biyar haka zai yi ta tambayar ta ko taba bukatar wani abu. Yaya Musaddiq ma baa barshi a baya ba kullm cikin tambayar ta abnda take shaawa yake Koda bata fada ba duk abinda ya gani a hanya zai siyo wani taci wani race bata so haka bazai hana shi gobe ma ya sake siyowa ba.



An yi bikin Nafisa da Sulaiman cikin rufin asiri kawu Kabir da ragowar yan uwan mahaifin ta ne suka hadu sukayi mata komai daidai karfin su. ma sha Allah kasancewar gidan karami daidai zaman mace daya sai gashi an cika mata gidan da kaya komai yayi ita kanta Nafisa tayi mamakin ganin kayan da su kawu sukayi mata wannan va karamin Kara mata ganin girman su da mutuncin su yayi ba.

Gidan su mama babu wanda yazo duk da Hanan taso taje bikin tayi wa yar uwar ta bajin ta saidai mama fir ta ki amince wa daga baya ma tace duk wanda ya nemi Nafisa bata yafe masa ba haka Hanan ta hakura, ita kuwa Karima bata kasar ma tana can tare da wasu matan turawa guda biyu da suka aure ta suke jika ta da dolers zuwa yanzu tafi Hanan komai har gidan da suke ciki ma ta zanca musu wani babban mai sama da kasa part uku ne a ciki daya anan take saukar kawayen ta a cewa ta amma a zahiri babu kawaye face abokan sheke ayarta ita kanta Hanan ta fara tsorata da kudin da Karima ke turowa har ta bude katon shopping moll ita kuwa mama babu ruwan ta bata taba zama tayi tinani akan inda yayan ta ke samun kudi ba musamman Karima da yanzu ta gama yiwa talauci kaura.


Sannu a hankali cikin ya fara girma laulayi yana yin sauki har ya cika wata biyar bata zuwa makaranta malami daya Daddy ya dauka daga makarantar yake zuwa gida yanayi mata lesson ranar jarabawa kawai suke jira.


Momy ta nemi mijin Abu kuma yazo har gida inda ta shaida masa ko ita din wacece lokacin da yaga Salma cikin yanayin kamala saida ya tafi tinanin lokacin daya fara cewa yana son Abu Salame ta tasa shi gaba taba tabe dankon ta tana sakar masa dutse tin yana jurewa har ya gudu da kafar sa tin daga lokacin yake dawainiya da soyayyar Abu saboda tsoron Salame gashi ita Abu bata da raayin kanta sai abinda Salame tace har zuwa lokacin da ta bar garin sosai yayi dariya tina baya itama dariyar tayi don tabbas ta tina abinda yake wa dariya.


Ba karamin dadi yaji ba da abinda momy ta zo masa dashi babu ja ya amince saidai dawowar Abu cikin birni yake da yakinin ba zaiyiwu ba innar da ba zata amince ba. Ganin yanda momy ta dage akan ya gwada yasa shi amsawa ya shirya ya nufi rigar jallo,, bayan ya huta ya sanar da Inna Asabe abinda ya kawo shi yayi matukar mamaki da ta nuna farin cikin ta akai hadda cewa dama bai kamata kana wanu wurin matar ka tana nan ba duba da cikin dake jikin ta sai kune gidan su kuyi sallama ku kama hanya Allah ya tsare baki sake yake kallon innar sa wacce taci alwashin idan har tana da rai Abu za ta koma birni ba suje su dinga cin dadi amanta da ita a kauye. Haka kuwa akayi kashe gari sukaje gidan su Abu albarka sosai iyayen ta suka dinga saka musu tare da nasiha kafin su tafi mahaifiyar Abu ta hadawa Abu kayan amfanin gida da Fura mai yawa wacce zata kaiwa Salma sannan ta saka ta a daki tayi mata fada sosai ,har gidan Baffa sukaje sallama ranar da zasu tafi haka suka dakko hanya Inna tana daga musu hannu tana murna zata rabu da masifa tasan dai yanzu babu abinda wadancan mugayen sojojin zasu hango" can gasu gada " ta fada a fili tana shigewa gida.

Mrs Sharif ce
'
Ina barar adduar ku plx=?O?
*SALAME*
59-60
OUM SHARIFAT CE>??
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI


(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE

Sai bayan magrib Abu da Sulaiman suka karaso Salma batasan da zuwan su ba wani irin farin ciki ta tsinci kanta a ciki mara misaltuwa lokacin da taji labarin Abu ta dawo kusa da ita, godiya sosai ta dinga yiwa momy ta rasa inda zata saka ta.saida momy tayi musu magana sannan tabar Abu ta zauna khadija ta matsa kusa da ita ta fara matsa mata kafar ta wacce ta kumbura suntum saboda zaman mota don ma Sulaiman yayi ta matsa mta a motar kasancewar cikin ta ya shiga watan haihuwa.

Saida Daddy ya dawo ya nemi ganin Sulaiman a part dinsa bayan sun gaisa yake tambayar sa raayin sa akan karatun boko nasa dana matar sa.Rasa inda zai saka ransa saboda tsananin farin ciki yayi a zahiri Sulaiman yanason karatun boko yana son waye wa babban burin sa bai wuce ya ganshi yana turanci ba haka Abu yana so yaga ta waye yana so matar tayi gogayya da mata masu aji wadanda sukeji da alimin addini dana boko.

Babu bata lokaci ya amince tare zubawa Daddy godiya kmar zai ari baki. Dan murmushi Daddy yayi ya dakatar dashi ya ce " haba Sulaiman kaima fa dana ne menene abin godiya haka abinda yakamata uba yayi shi nakeyi . Idan Allah ya kaimu gobe Musaddiq zai raka ka makaranta ta marasa wadanda basu fara karatu da kuruciya ba zai yi maka komai daga nan zai raka ka company na na shinkafa zaka dinga lura da leburori ne ka kula sosai yanda zasu dora shnkafa akan lokaci a fita da Kaya akan lokaci. Daga nan zai raka ka gidan da na baka kyauta ce ba aro na baka ba nakane halak malak. duk yanda Daddy ya hana Sulaiman godiya sai da ya gigice da godiya hadda hawaye , Saida ya nuna masa bacin ransa sannan ya bari ya fito.

Anan gidan ya kwana wurin Musaddiq kashe gari da safe kmar yanda Daddy yace haka akayi Yaya Musaddiq ya dauke shi ya kaishi makaranta akayi masa register daga nan suka wuce company ya nuna masa bangaren da zai dinga aiki. Musabiha sukayi da masu daukar kayan suka gaggaisa tare da adduar Allah ya dafa musu a cikin aikin su sannan yayi musu sallama bayan ya sanar dasu gobe zau fara zuwa aiki.

Gidan da Daddy ya bash suka wuce tin daga waje yake mamakin gidan da aka ce an bashi halak malak ba aro ba ji yake kmar mafarki ne nan gaba zai farka , Yaya Musaddiq yayi masa jagora zuwa cikin gidan, two bed room ne da parlor, bin ko Ina yake da kallo gidajen su na ruwa kadai ya taba kwana lokacin da ya fara dako a kasuwar kwari kuwa daddre cikin gari suke shiga su kwana a soron wani babba gida bayan sun bada ajiyar kudin da suka samo sai kuma gidan daddy daya kwana daya yake jinsa kmar a cikin aljanna ya kwana.

Leka dakunan yayi kowanne an saka bed da wardrobe da mirror sai parlon da aka kawata shi da manyan kujeru ka pridge a gefe ga kuma uwa uba daining da tinda yazo duniya bai taba hawa ba ko ganin sa bai taba yi a zahiri ba sai dai a film idan ya turo a wayar sa ya kalla yau shine a gidan da yake jin wai mallakin sa ne, shi kansa toilet din gidan wani daban yake ganin sa .
Baiyi duhun kaiba ya dinga tambayar Yaya Musaddiq abinda bai san yanda ake amfani dashi ba, Yaya Musaddiq bashi da girman kai yana da wasa da son mutane sosai ya dinga nuna masa abubuwa suna dariya. Anan suka bata lokaci suna ta hira nan da sabo ya shiga tsakanin su domin Sulaiman bashi da kauyanci mutum ne mai ilimin addini da iya furta magana ta hankali.



Sai da Yaya Musaddiq yazo tafiya ya bashi mukullin machine din da Daddy ya ce ya bashi sannan ya kaishi inda machine din yake ya dauka, shima gudumuwar waya babba ya bashi ya bude masa abubuwa masu amfani domin kara samun experience akan rayuwa haka suka rabu bakin Sulaiman yaki rufuwa.



Abu wacce momy ta saka dokar ta baci akan sunan ta inda ta koma Zainab tinda sukazo take jiran ganin mijin Salma duk a tinanin ta yaya Musaddiq ne Saida taji an kira shi da musaddiq sannan ta gane ba shi bane don ba zata manta sunan mijin Salma ba Safraz .

Kashe gari da sassafe khadija ta shirya ta nufi school suka samu kebewa su biyu cikin dakin, Zainab ce ta zunguri Salma ta ce " wai ina mijin naki ne? Kura mata Ido Salma tayi bata ko kiftawa wasu abubuwa suna dawowa kanta kmar a film nan da nan kwakwalwar ta ta fara fassara mata wasu abubuwa da suka faru a baya wadanda bata dauke su komai ba. Zuwa yanzu ta gano tsananin kiyayyar da Safraz ya nuna mata wacce take gani a da can matsalar sa ce tinda itama ba son shi takeyi ba wasu hawaye masu dumi suka zubo akan fuskar ta wadanda suka tashi hankalin Zainab dakyar take motsawa ta masto kusa da ita ta kama hannun ta gam ta rike ta zuba idon ta cikin na salma tace" menene ya faru bayan rabuwar mu.

Lumshe idon ta tayi hawayen suka karasa gangarowa ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar da Zainab, Hade kansu sukayi wuri guda suka fashe da kuka suna rike da hannun juna ,saida sukayi mai isar su babu mai lallashin su haka suka hakura suka yi dariya a tare da kafin Zainab tace"" a lokutan baya idan aka ce wai zamu shiga yanayin da muka tsinci kanmu a ciki ba ba muba duk wanda yasan Salame da Abu bazai yadda ba amma kinga yanda buwayi gagara misali yayi damu badon baya son mu ba sai don jarraba imanin mu a yanzu nagane cewa ba rayuwa mukayi a baya ba yanzu ne zamu fuskanci rayuwa sai ta kara kama hannun Salma tace " kmar a ruga zamuyi dariya tare zamuyi kuka tare zamu yaki rashin adalcin da akeyiwa mata da iya karfin da Ubangiji ya bamu Ina ji a jiki na kaddarorin mu suna da alaka da nasararorin mu na gaba. Daga karshe Ina rokon ki karkiyi fushi da abinda zaki haifa ki kula dashi ko ita ki zama uwa hamshakiya jajirtacciya ki nunawa duniya cewa yar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login