Showing 9001 words to 12000 words out of 60473 words

Chapter 4 - SALAME COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM SHARIFAT CE.doc

, ganin tnanin bazai fishshe ta ba yasa ta daukar waya ta kira kanwar ta Aisha ta sanar da ita komai.


Itama dai irin tinanin momy ne a ranta saidai itama tasan halin Alh Abdullah, ajiyar zuciya ta sauke tace"" Kinga Yaya karki damu kanki bawa baya wuce ?addarar sannan hukuncin da ya yanke din ma yayi daidai dole Safraz zai san nauyi da hakkin wata a kansa kuma kinga tinda yace babu saki haka zai koyawa kansa son ta, itadai yariyar kawai za kija ki nuna mata mahimmancin sa a wurin ta, kuma nasan ba wani abu da zai shiga tsakanin su har zuwa lokacin da zata kai inda kike so takai duk da dai yaran yanzu baa shaidar su kuma ai ta fara alada ko ? Eh ta fara wai wacccan shekarar momy tace jikin ta a sabule, " to kawai ki gyara yariya babu abinda zai faru sai alkairi in sha Allah.

Sun dade suna tattaunawa har dai momy ta gamsu da maganar Aunty Aisha sannan sukayi sallama.


Mrs Sharif ce
Share fisabilillah=?O?
*SALAME*
23_24

OUM SHARIFAT CE

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION

SORRY NOT EDITED


(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE
Ikon Allah ne kawai yakai Safraz gida ya shige part din sa ya fara rage kayan jikin sa ya fada toilet ya sakar wa kansa shower yana furzar da iska mai zafi daga bakin ya yana shafa sumar kansa zuwa kyakykyawan sajen sa zuciyar sa babu komai sai tsanar mata da yake ganin dukkan su halin su daya.


Irin yanayin daya samu Hanan har tausayin ta ya samu wuri a zuciyar sa ya taimake ta tare da iyayen ta har soyayyar ta mai karfi ta shiga zuciyar sa ya aure ta ya zame mata gata ta ko ina ya tsaya mata tayi kararu har zuwa inda take so duk da rashin haihuwar ta baisa ya juya mata baya ba ya dauki hakan a matsayin iko ne ma Allah amma daga karshe taci amanr sa ta karyata kanta akan soyayyar da take nuna masa wasu hawaye masu dumi ne suka shiga wanke masa fuska gaba daya zuciyar ta raunana duk a sanadin mace kamar ba shine major Safraz ba wanda mutanen dake kewaye da shi ke tsoron fishin sa amma a haka Daddy yake so ya sake komawa cikin rayuwar mace shi kadai yake ta sakawa da warwarewa har ya gaji ya fito ya shirya cikon kakin sa ma sojoji ya saka takalmin sa ba karamin kyau kayan sukayi masa kwarjini da haibar sa suka fito saidai fuskar nan babu annuri kallo daya zakayi masa kasan ransa a bace yake .


Cikin takun sa mai cike da Izza ya fito ya kamshin mayataccen turaren sa dake kidima yammata da sauri Joseph ya janyo mota ya bude masa ya shiga Ibrahim ya zauna a baya suka fice daga gidan.



Gyara sosai momy ta fara yiwa Salame ciki da waje cikin kwana uku farar fatar ta ta kara haske ta fara sheki gashin kanta da ake shafa masa hadin karkashi da kwai ya kara kyau da santsi sai daukar ido yakeyi.

Khadija tayi magiya har da kuka akan Daddy ya amince su koma gidan Yaya Safraz tare amma yaki amincewa , ba karamin damuwa Salma ta shiga ba Jin za a raba ta da Khadija dakyar Momy ta kwantar mata da hankali akan cewa zasu dinga haduwa kullum a school duk da haka ba don taso rabuwar ba.

Malamin dake zuwa yi mata lesson aka canza zuwa mace wacce zata dinga zuwa gidan Safraz tana yi mata,


Kayan daki masu kyau da tsada Daddy ya hadawa Salma tin daga kanta furniture cottons da carpet da kayan kitchen ganin kayan ba karamin faranta ran Salma yayi ba har ya mantar da ita damuwar da take ciki ta fara dokin komawar ta gidan.




Ranar da akayi nadin sarautar Baffa ranar aka daura auren sa da wata bazawara Yar limamin garin wacce mijin ta ya rasu, gyara sosai yayi wa gidan sa da gidan Inna sannan yafara kawo tsare tsare cikin mulkin sa ya cire wa manoma harajin da tsohon mai gari ya dora musu saidai ya dabbaka zaka ga masu arzikin garin kmar yanda addini ya tanadar takanas ya tafi wurin hakimi suka kai ziyara har masarauta yayin da ya gabatar da abubuwan da kauyen su yake bukata bayan sarki ya karfi korafin su sannan suka dawo, sun dawo ba dadewa aka fara gabatar da aikin da babu wanda yasan za ayi.

An jawo musu kwalta har bakin garin su tare da wuta sannan aka inganta musu ruwan shan su cikin kankanin lokaci rugar jallo ta fito bakin titi sula samu cigaba sosai duk wani tallafi da ake samu akan noma Baffa baya kasa a guiwa wurin nemowa al'ummar sa tare da samo musu hanyoyin fitar da kayan da suke nomawa Baffa adali ne baya samun nutsuwa a duk lokacin da yaga wani cikin damuwa yakanyi iya kokarin sa wurin magance damuwar matukar batafi karfin sa ba .

Ya zauna da wadanda ke yiwa mutane sace sace wanda an sansu tsoron iyayen su yasa akeyin shiru ya saba babban hukunci ga duk wanda aka kama da kayan wani , wannan abubuwan suka jawowa Baffa karin kima da mutunci da kuma soyayya daga mutanen garin yara da manya.




Ranar Alhamis aka je aka yiwa Salma jere a gidan Safraz domin Saida Momy tasa aka fitar da duk wani Abu da Hanan tayi amfani dashi aka saka mata komai sabo, falo ne da bedroom guda uku a cikin part din nata sai daining area kitchen da store a ciki sai kofar da zata sada ka da bangaren masu aikin gidan ta cikin parlor.

Gaba daya dakunan Saida Daddy ya cika mata su da Kaya Wanda dukan su zabin Khadija ne dakin farko aka zuba mata furniture's pink and white daki ma biyu ash colour yayin da daki na uku aka saka marnon and golden colour, kujerun palourn maroon ne masu adon gold haka labulaye da carpet komai na cikin part din ya tsaru tsaf daga gefe aka cika mata shore glass da turaruka irin nata matan barebari.


Kashe gari jumaa aka dakko make-up artist tazo ta baje basirar ta akan farar bafulatana Ummusalma Hashim fadin kyau da hasken dake fita a fuskar Salma bata baki ne ita kanta Khadija Saida tayi mamakin ganin tsananin kyawun da tayi anty Aisha kanwar momy ta nada mata lafaya kalar sararin samaniya ta saka takami half shoe kalar lafayar ta rike mata hannu momy na biye dasu suka nufi parlon Daddy.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I8MjhVQl9zZ1QeXYX871gv




*SALAME*

25-26

OUM SHARIFAT CE

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION
(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE

Da Sallama suka shiga parlourn suka iske Safraz a zaune akan carpet kansa a sunkuye, murmushi ne kawance a fuskar Daddy yace "" karaso kusa dani ya ta kanta a kasa ta karaso wajan kafafun Daddy ta zauna itama akan carpet jiki a sanyaye tace Daddy ina wuni lafiya kalau Ummusalma Daddy yace tana kara fadada murmushin sa.

Fita Aunty Aisha tayi ta bar Salma da Daddy da kuma Safraz wanda tinda suka shigo yaji zuciyar sa tana kara zafi tsananin kin ta da yakeyi. Gyaran muryar da Daddy yayi shine ya katse masa tinanin da yakeyi na yanda za zauna da ita.

Nasiha sosai Daddyn yayi musu karfin nasihar gare shi ne saidai yayi abin ta sigar hannunka mai sanda ita kuwa Salma kasancewar ta karamar yarinya bai wani dauki lokaci yana mata nasihaba domin koda yayi mata ba komai zata gane ba.

Saida yayi musu addua sosai sannan ya kira aunty Aisha ta fita da Salma daga ita sai Khadija suka raka Salma gidan yayan ta kuma mijin ta major Safraz Abdallah.

Saida suka shiga da ita dakin ta suka zaunar da ita bakin gado aunty Aisha ta yaye mata lullubin da tayi mata sannan ta dube ta da kyau tace ""Ummusalma Kinga nan shine gidan mijin ki kuma gidan yayan ki nasan dai yanzu me ba Salame bace ba ko? Gyada kai Salma tayi cike da kwari guiwa
""Good" Aunty Aisha tace sannan ta dora da cewa so nake ki daina yin abun da zaa ce miki Salame ki zama yar gayu yar boko kinji ko? Sannan duk abinda yayan ki yace kiyi karkiyi masa rashin kunya kinji idan kikayi masa Allah yana kallon ki kiyi duk abinda ya saka ki kinji yata da "to kawai Salma ke amsawa tana washe baki jin ance mata yar gayu, basu wani dade ba suka tafi sai a sannan me jikin Salma ya fara rawa hawaye suka fara wanke mata fuska ta rike Khadija gam tana kuka itama Khadijan kuka ne ya subuce mata ta saba da Salma duk da shirmen ta amma tana son zama da ita tana saka ta farin ciki.

Girgiza kai Aunty Aisha tayi tana basu hakuri kafin taka hannun Khadija suke fice .



Kara fashewa da kuka Salma tayi tana Jin dama bata amince ta biyo su ba daida tayi mai isar ta sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya anan bacci ya kwashe ta.



Safraz bai shigo gidan ba sai 12 am hakan ma Ibrahim ne ya dame shi da tsokana ransa ya fara baci ya a fusace ya dauki mota ya nufo gida ba tare da ya jira gurd dinsa ba, yana cikin tuki yaji alamar shigowar message a wayar sa, kmar zai share sai kuma ya duba sunan momy ya gani ya saka shi saurin bude message din yana fatan ko menene ya kasance lafiya.


"Inason ganin ka gobe kafin ka tafi office idan da lokaci idan kuma ba lokaci idan ka dawo Ina neman ka ". Shine abinda sakon ya kunsa jijjiga kansa yayi ya ajiye wayar yana fatan kiran ba akan waccan bagidajiyar yarinyar bane.

Yana isowa ya fara Danna Horn sojan dake bakin get ya bude yana kamewa ko ta kansa Safraz bai bi ba yayi parking ya shige ciki, Direct part dinsa ya nufa ransa a jagule ya cire kayan dake jikin sa ya daura towel ya fada toilet, ya jima a ciki yana wanka tare da sake sake a ransa kafin yayi alwala ya fito daure da wani towel din a kugunsa da kuma karami yana goge sumar kansa dashi, saida ya gama goge jikin sa sannan ya karasa jikin mirror yaja kujera ya zauna ya fara goga mayuka masu taushi da dadin kamshi ya tashi ya karasa wajan wardrobe ya Ciro wasu nighty masu laushi milk color ya feshe jikin sa da turaruka ya dauki praymat ya tada sallah ( Oh kaida kake da amarya kayi sallah kai kadai)

Saida yayi rakaa hudu sannan yayi addoin sa kmar yanda ya saba ya tashi ya kara gudun ac ya haye bed ya kwanta tare da adduar bacci.



Hanan.

Da kuka ta shiga gidan su yayin da ta samu mahaifiyar ta da kannen ta a tsakar gida suna ganin ta suka yo kanta hankali a tashe suna tambayar lafiya, bata kulasu ba ta cigaba da kukan ta saida tayi mai isar ta sannan ta ce "" mama da sauri dattijuwar da aka kira da mama tace naam Hanan badai sakinki yyi ba ko? Ya sake Ni mama ta fada tana sake rushe wa da kuka gaba dayan su suka hau salati domin sun san Safraz shine gatan su shine cin su shan su harda suturar su.

Me kika yi masa? Mama ta fada cikin firgici da tashin hankali , Saida taja majina kafin tace dama wani ne yake kirana Ina ce masa ya bari ni matar aure ce yaki denawa kawai dazu sai ya kirani shine Safraz ya dauka kawai daga jin muryar namiji sai ya hau duka na ba bincike kawai sai saki kuma fa mama can inda yake aiki matan banza shima yake muamala dasu nasha kamashi da abubuwa irin haka sai ya bani hakuri banason tonawa mijina asiri sai nayi shiru shine shi yau ya wulakantani ta karasa fada tana rushewa da kuka tare da satar kallon maman don ganin yanda ta dauki maganar.

Aiko ba mama ba har kannen ta sun dauki zancen don gaba daya suka hadu suka fara kwashe mishi albarka babu mai tinanin a kirashi aji daga bakin sa.


Oum Sharifat ce

*SALAME*
28-29


Oum Sharifat ce


=??=???
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION=???*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hDDDDD
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*?&??J.A.W=???=،?


(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE
Nafisa kanwar Hanan wacce ke zaune can gefe tana danna wayar ta wacce tinda aka fara mata maganar bata saka baki ba ta dago kanta cike da nutsuwa da kamun kai tace " mama nifa ina tinanin kamata yayi a kira Yaya Safraz ko iyayen sa ko kuma a fadawa kawu tinda shine ya daura auren a neme shi aji daga inda matsalar take may be kishi ne kawai ya sa ya yanke wannan hukuncin idan da rabon komawa sai kiga ta koma gidan mijin ta yafi mata rufin asiri.

Kamar zata dake ta mama tayi kanta tana masifa tare da cewa bazan neme shi dinba kuma shi kawun naku idan ya daura mata aure haihuwar ta yayi da zata zauna katon gardi ya dinga sauke fushin sa a kanta wato ya kashe ta kenan bakida asara shegiya mai bakin hali irin na uban ta kedai wlh inda a asibiti na haife ki sai ince canza min ke akayi shashashar yarinya kawai mara kishin yar uwar ta, itama Hanan sai faman aikawa Nafisa harara take wacce take shirin tona mata asiri cikin zuciyar ta kuwa tsine wa Nafisa takeyi wacce suke wa kallaon munafuka.


Kinga aunty Hanan bari in kai miki jakar ki daki ai ba jaka aka kai masa ba kuma yanda kike din nan ai kina gama Idda ake ce mata ko menene ma dai oho zadai kiga alhazawan birni suna layi cewar Karima yayar Nafisa wacce kallo daya zakayi mata kaga rashin kamun kai a tare da ita.

Cike da jin dadi Hanan ta mike tana bin bayan Karima suka shige dakin da karimar ta nufa ita kuwa Nafisa gaba daya bata yadda da zancen Hanan ba sarai tasan Safraz mutum ne mai kyamar matan banza kuma ta tabbata akwai wani abu ba abinda iya Hanan din ta fada ba cikin ranta take yiwa yan uwan nata tare da mahaifiyar su wacce ke daure musu kugu suna abinda suka ga dama shiriya.



Kiran sallahr farko ne ya tada Safraz daga nannauyan baccin daya dauke shi a hankali ya zuro kafafuwan sa ya sakko ya shige toilet ya watsa ruwa tare da alwala ya fito ya saka jallabiyya coppy ya fita masallaci saida yayi azkar a can karfe shida ya shigo cikin gidan yayi part dinsa ya kashe light din dakin ya koma bacci.

Salma bata tashi ba sai karshe shida tana hamma ta cire kayan ta kamar yanda Khadija ta saba mata ta fada toilet saida tayi wanka da brush sannan ta fito daure da towel ta bude daya daya cikin trolys din da aka kawo mata ta saka wata doguwar riga tare da hijab tayi sallah sannan ta dauki Alqur'an ta fara karatu cikin suratu Nurr da zazzakar muryar ta mai fitar ta daddadan amo tana fitar da makarij tare da bawa kowanne harafi hakkin sa, ta dauki lokaci tana kafin ta rufe Qur'an tayi addua ta maida shi inda ta dauka ta koma kan bed ta kwanta tana ta juyi ganin baccin bazai zo ba yasa ta fitowa ta sakko downstairs tana karewa parlon kallo.


Cikin uniform dinsa ya fito ya biyo ta main parlon inda ya hango ta tana ta shafa kujerun parlon sa sukayi matukar burgeta tana ta washe fararen hakoran ta.


Kallon banza tare da tsana ya watsawa bayan ta Villager ya fada tare da jan dogon tsaki a fili , a dan tsorace ta juwo har zata dauke kanta sai ta tuno nasihar Daddy ta rusuna kanta a kasa tace "Yaya Ina kwana" kallon sama da kasa yayi mata ya watsar kafin yace "ke dalla dakata banason munafinci yaushe kika iya gaisuwa ko har ruwan Rugar ya sakin ki ya fada yana toshe hancin sa a wulakance yace kina ji na ko? Kar ki sake bari mu hadu bana son ki na tsane ki banason ganin wannan fuskar taki idan kika sake kika kara nuna min wannan ugly face din taki saina lalata ta kazamar banza ya karasa fada tare da kai mata wani rankwashi a kanta wanda saboda tsananin azabar sa saida ta sunkuya ta rike kanta take wasu zafafan wahaye suka wanke mata fuska.


Wani killer smile ya saki yana jin zuciyar sa wasai ya fice Joseph ya bude masa mota ya shiga Ibrahim ma ya shiga suka saka shi tsakiyar convoy suka fice


Gidan Momy kawai yace ba tare da ya kalli Joseph din ba kasancewar koda yaushe kunnuwan su a gare shi suke saboda sun san yanayin maganar sa da ba kowa ne zai ji abinda yace ba sannan kuma ba zai maimaita ba, "okay Boss Joseph ya fada yana daukar hanyar main house din nasu.


Horn sukayi maigadin yazo ya bude yana washe baki yana cewa " Soja marmari daga nesa" ga mamaki na sai ganin Safraz nayi ya fito ya nufi dattijon tare da rusunawa ya gaida shi cike da faraar data kawata fuskar sa, suna gama gaisawa ya sake tamke fuskar kmar bashi ba ya shige cikin gidan.


A parlon kasa ya tarar da momy tana zaune kan sopa hannun ta rike da canbaha tana ja, da sallama ya shigo parlon tare zare takalman kafafun sa ya karaso kusa da kafar momy ya zauna a kan carpet dabiar sa ce baya iya zama a sama matukar iyaye???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n nasa suna sama.


Kafar momy ya fara matsawa yana murmushi yace "" Ina kwanam sweetheart" sunan da yake kiran momy kenan da murmushin itama a fuskar ta ta amsa tana tambayar sa Salma saida ransa ya dan sosu amma bai bari ta gane ba ya amsa da tana lafiya.


Momy ce ta gyara zama ta fuskanci Safraz da alamar magana a bakin ta ganin haka yasa shima sata nutsuwar sa ya tankwashe kafa yana sauraren ta.


"Safraz yau zan fada maka abinda ban taba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login