Showing 21001 words to 24000 words out of 60473 words

Chapter 8 - SALAME COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM SHARIFAT CE.doc

zuwa Daddy dake zaune akan stool yana operating system yaji duk abinda Khadija tace sakamakon momy a handsfree ta sakawa wayar yayi murmushi ya ce " to ai sai ku fara shiri ai dole ta damu tayi kawaici ma duk da nasan dannewa kawai takeyi amma tana kewar gida sakkowa momy tayi daga kan bed din tace " wlh kuwa Alh yarinyar tana bani tausayi kodon halin Safraz ma taso gida shiyasa na fita daga sabgar dan naki nake kiranta inji ta bangaren ta kuma na saka Khadija tana dubamin yanayin ta kuma Alhamdululillah ina ganin kmar ya gyara tabe baki momy ta ce " ni yaushe rabon da na yiwa Safraz maganar Ummusalma ai ya zama makaryaci ? Nima dai naga yanzu kmar ba wata matsala bari inje mu fara shiri ta karasa fada taja fita daga dakin shi kuma daddy ya cigaba da abinda yakeyi.


Dakin Khadija momy ta shiga inda ta iske Ummusalma tayi sharkaf da hawaye gani takeyi kamar ba zaa tafi ba da sauri momy ta karasa gare ta ta jawo ta jikin tana bubbuga bayan ta ta ce " sorry my doughter ai gani ta hawo yanzu zamu tafi bari mu shirya kafin nan an gama break muna karyawa zamu wuce kuma acan zamu barku keda Khadija sai kunyi kwana bakwai sannan driver zaije ya dakko ku.Wani irin tsalle Salma tayi tayi tana murna wahayen ta suka hade da dariya sai ta dawo sal Salamen ta mai abin haushi da abin dariya ba karamin farin ciki momy tayi da ganin dariyar dake fuskar Salma ba ta tabbata farin cikin daga cikin zuciyar ta yake. Idanuwan ta Hafsu suke nuna mata a fuskar Salma nan da nan zuciyar ta tayi rauni wata kwalla taji tana shirin zubo mata tayi saurin mayar da ita cikin ranta kuwa cewa take "ya Allah ka bani ikon zamewa Ummusalma Salma Uwa ta gari mai samar mata da farin ciki ya Allah kar ka bari tayi kewar mahaifiya matukar tana tare damu.


Itama Khadija ba karamin dadi taji ba jin zaa barsu a can tanason kauye sosai dk da ba zuwa sukeyi ba saidai tana tina lokacin da ake zuwa da ita tana karama.


Khadija ce ta fara shiryawa ta raka Salma driver ya maida su gidan Safraz ta taya ta debo kayan da zatayi amfani dasu suka yiwa Mama Talatu sallama ya maida su gidan Momy inda suka tarar da ita ta shirya tana daining tana jiran su.


A gurguje sukayi break din gaba daya murnar tafiya tasa basa jin yunwa ganin haka yasa momy tasa mai aikin su ta zuba musu a warmer suka saka a mota inda sukayiwa Daddy sallama driver ya jasu zuwa Rugar Jallu.



Mrs Sharif ce
' *SALAME*
43-44

OUM SHARIFAT CE>??
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI


(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE

Sharara gudu kawai driver yakeyi a titi tin suna hira har sukayo shiru bacci ya daukar Salma sannan Khadija momy kadai suka bari shiru tana ta lazimi.Basu farka ba sai bayan azahar aka tsaya daidai wani gidan mai suka fita suka huta shi kuma driver ya nufi masallacin da ya hanga a wajan. Saida suka huta suka wa ke bakin su suka dawo cikin motar suka bude abincin da suka taho dashi suka fara ci banda momy da ruwa kawai tasha ta kwantar da kanta a jikin sit din ba dadewa driver ya dawo suka cigaba da tafiya.

Basu suka isa rugar jallu ba sai da aka fara kiran sallar la'asar glass din motar Salma ta bude ta zuro fuskar ta lokacin da suka fara tafiya ta gefen gonaki wata irin iska ta fara shaka mai dadi da kukan tsintsaye yayin da korayen ganyayyaki suke motsawa abin gwanin shaawa ba iya Salma ba itama Khadija haka tayi tana jin wani sanyi a ranta yanayin garin shiru babu hayaniya ga tsaftatacciyar iska dake dukan hancin ta ta lumshe ido tana sakin kayataccen murmushi.


Daidai kofar gidan Baffa driver yayi parking da mamaki Salma ke kallon gidan da batasan ko na waye ba a hankali ta ziro kafafun ta ta fito yara ne burjik a wajan motar wasu na kallo wasu kuwa sai shafawa sukeyi ,da kallo Salma ke bin garin nasu babu abinda ya sauya saima cigaba da garin ya samu tin daga gonakin su yanda taga ko ina shukoki sunyi luf abin yake burgeta gidan da momy ta nufa itama nan ga shiga tare da Khadija da sallama a bakin ta ta shiga gidan saidai bata karasa sallamar ba ta daka tsalle tana ihu tayi kan inna wacce itama sai ware Ido takeyi taga ta inda Salamen tata zata bullo a tare suka rungume juna suna murna sai yanzu Inna ta kula da Khadija dake tsaye tana murmushi. Yafuto ta Inna tayi ta hade su duka ta rungume duk da ciwon kafar da takeyi hakan bai hana ta take kafar ta ba saboda tsananin murma saida Momy tayi magana sannan suka saki Inna suka karaso aka gaggaisa.


Suna cikin gaggaisawar ne ta jiyo sallama da muryar da ba zata taba mantawa da ita a rayuwar ta ba da sauri ta juyo da gudu Abu tayo kan Salame suka rungume juna wani irin kuka Abu ta saki kamar dan da ya dade baiga uwar sa ba itama Salamen kuka takeyi sosai ko ba a fada ba da momy da Khadija sun fahimci ita ce Abu saida sukayi mai isar su sannan momy ta rarrashe su suka zauna suna ta kallon juna .


Zabbin da Baffa ya sa aka yanka aka yi musu farfesu aka gabatar musu tare da dambu wanda yaji wadataccen zogale da albasa da gyara ga ruwan mai sanyi cikin wani tsaftatacccen kwanan sha na sulba fari sol dashi sai kamshin kasa yakeyi sakamakon daga randa aka debo shi .


Ita dai Abu kallon Salame kawai takeyi yanda ta sauyi tayi kyau ta kara haske ita kuma Salame tana kallon yanda Abu ta rame tayi baki kmar ba abun ta ba har wani tafasa zuciyar ta takeyi burin ta kawai su kebe taji wanda ya dame ta.


Anan Inna ke bawa Salame labarin auren Abu tin bayan tafiyar ta da wata uku jikin Salame ne yayi sanyi tsam ta tsame hannun ta daga cikin abincin ta kama hannun Abu sukayi waji ganin sun fita yasa Khadija tsame nata hannun ta bisu da sauri ta cimmu su inda Abu ke gaba suna binta a baya har zuwa wani gida dake can gefen gari.


Da sallama suka shiga gidan inda suka iske wata tsohuwa tana ta zagaye tana kwafa sunayin sallama tayo kan Abu cike da masifa tace"" wato ga uwarki Salame tazo ko shine kika bar kayan wankin Binta kikayi waje shegiya yar iska mara mutunci to wllh ko zaki kwana kina wankin nan sai kingama shi tsaf zakiyi bacci.


Salame ce ta yunkura zatayi magana Khadija ta ruketa gam ta jata suka fice suna fita Salame ta kalli Khadija da idon ta da suka fara tara hawaye zatayi magana Khadija ta katse ta da cewa karkiyi komai yanzu inada plan ta hanyar da zamu magance abun har abada amma yanzu idan kikayi wani abu zaki jawo mata wata masifar bayan mun tafi, girgiza kai Salame ta shigayi tana kokarin kwace hannun ta ta koma cikin gidan amma Khadija taki sakin dakyar ta fahimtar da ita tare da yi mata alkawarin gobe da safe zasu dawo suyi maganin abun gaba daya badon Salma taso ba sa don ta gamsu da kalaman Khadija ta yadda suka koma gida.


Suna shiga ta fara tambayar inn abinda ya ke faruwa da Abu

Gyara zama Inna tayi fuskar ta tayi kalar tausayi ta ce ai Salame tinda akayi auren Abu yariyar nan take cikin wani hali kinga mijin ta Samaila yana ji da ita sosai to ita kuma uwar sa ta tsane ta duk aikin dake gidan itace takeyi har wankin ta yanzu haka ya tafi cirani can binni wajan ku shine kanwar sa Binta ta kaso auren ta ta dawo gidan har wankin ta da kayan kashin danta duk Abu keyi to Baffan ki ya kirasu yayi mata fada sosai ta nuna ta daina tayi nafama sai jiya nake ji wai yanzu har dukan ta takeyi kuma yanzu haka yaron ciki ne da ita wasu hawaye ne suka fara gangarowa daga idon Salma tare da murmushin farin cikin yaron cikin da akace Abu nada shi sosai take tausayawa Abu tana matukar son ta yar uwa take daukar ta ba kawa ba.


Haka ta wuni jikin ta babu kwari daddare ma ba wani baccin kirki tayi ba idanun ta a kumbure ta tashi tayi sallar asba sannan bacci ya dauke ta sai wajan karfe tara ta shirya tayi wanka dakyar ta tsaya tasha koko da daddadan kosan da amaryar Baffa tayi musu itada Khadija suka nufi gidan Abu.


Khadija tana sanye da riga da wando ta dora bakar jacket akai tayi rolling bakin mayafi fuskar ta dauke da katon bakin glass irin wanda ake cewa no respect ita kanta Salma da taga Khadija saifa tayi dariya , irin kayan itama ta saka wanda sun taho dasu ne saboda yanayin damuna .


Da karfi sukayi sallama suna shiga cikin gidan Abu ce kadai a tsakar gidan tana kwara amai gefen ta ga tulin uban wanke wanke nan yayin da wannan tsohuwar keta masifa ta cika musu kunne da kakatu kuma ko zata mutu sai tayi wanke wanken nan zuciyar Salame tayi dan rauni tana kallon Abu zatayi kuka Khadija ta girgiza mata kai.


Turamen dake kafe a tsakar gidan sukayiwa kansu mazauni suna jijjiga kafa a gadarance Khadija ta kalli Abu da tayi wajan wanke wanken zata fara ta ce " ke zo nan babu musu ta zo gaban su ta tsuguna .


A hasale uwar mijin Abu tayo kansu tana cewa " kiji ni da yar iskar yariya wacece ke da har zan saka suruka ta aiki ki hanata sake tamke fuska Khadija tayi kana tayi dan danne danne a wayr ta ta mika mata hoton ta ne da kayan sojoji wanda yaya Ibrahim abokin yaya Safraz ya dauke ta hannun ta rike da bindiga bayan ta saka uniform din yaya Safraz din da ya bata ta kai masa part dinsa .

Baya tsohuwar tayi tana zaro ido take cikin ta ya fara kuka fitsari da gudawa suka kawo mata ziyara lokaci take ta kokarin rike su kafin ta tsuguna akan guiwar ta Binta dake tsaye a wajan itama taga abinda ke cikin wayar tini ta fara hawaye a iya sanin su da soja shine yana kashe duk wanda yaga dama koda baayi masa komai ba kuma babu abinda zaayi.


Khadija ce ta fara magana " sunana Khadija Abdullahi ni jamiar soja ce nazo nan gidan wajan kawar kanwata Salma na tarar da abinda ya sabawa doka anan gidan sakamakon bautar da matar danki da kikeyi nayi magana da abokan aiki na yanzu haka ma suna kan hanya don tafiya dake da yarki


A take zawon da tsohuwar take rikewa ya saki kansa ta fadi a wajan tana kuka tare da rike kafar Khadija Binta kuwa suman tsaye tayi basu tsinke da lamarin ba saida Khadija ya kira waya sukaji muryar namiji ya fara magana" ranki ya dade gamunan zamu taho mun tsaya ne mu karo motar sojoji biyu kuma Kinga dama hukuncin daurin shekara goma zaayi mata kuma kince yarinya tana da ciki kuma tana dukan ta shikuma dama kinsan hukuncin dukan mai ciki yanke hannuwan mai dukan ne to shine zamu taho ta likitocin da zasu yanke mata hannun Kinga an huta muna zuwa da ita nan sai a daure ta kawai idan ma anga jikin yarinyar da alamun dukan to kila kawai harbe ga zaayi don barin irin wadannan mutanen a gari bazarazana ce ga al'umma.


Mrs Sharif ce
'
*SALAME*
45-46
OUM SHARIFAT CE>??
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE

Wani uban ihu da ta kurma tana neman agaji saida ya bawa Khadija tsoro a zaton ta aljanu tsohuwar zata tada gashi tana mugun tsoron aljanu dakyar ta aro jarumta ta dake ta kashe wayar, ihun da babar Samaila tayi ne ta janyo hankalin makota suna fara leke ta katanga ganin fuskokin da basu sani ba cikin shigar da ba irin tasu ba yasa suka fara shigowa gidan domin ganewa idon su abinda ke faruwa.

Da sauri ta mike tsaye tana share hawayen da suka ki tsayawa ta nuna wata tsohuwa ta ce " kece kika cuce ni laraba ke ba kawar arziki bace kece kika dinga zugani akan Abu tin kafin auren kece nan kika bani shawarar bata ayyuka a gidan nan kika ce in maida ita baiwa Allah ya isa tsakani na dake laraba gashi kin jefa ni a masifa yanzu harbe mu zaayi nida Binta bayan an yanke min hannu ta karasa tana rushewa da kuka tare da fadin kaico na ni Asabe kaice kanmu.


Wuki wuki wacce aka kira da laraba tayi tana zaro ido Khadija ta kalle ta fuska a tamke ta ce zauna nan ta nuna mata inda Asabe da Binta suke jiki na rawa ta karaso ta zauna tana share zufar dake keto mata da gefen zanin jikar ta data yafo ta fito .

Dan danne danne Khadija tayi a wayar ta tayi dialing wata number ta saka hands free " ranki ya dade gamu nan yanzu mun gama hada komai okay to dama akwai wata mata wacce ita ce ta zuga ita babar Samaila to gata dai na kama ta to sai ku karo Bullet kawai a harbe ta.


""Hannu Laraba ta dora aka ta zubduma ihu wayyo Allah ni laraba ba shiga uku na lalace baki na ya zame min masifa dama liman tace harshe yafi tako bi innalillahi salamun kaulan wama ramaita innu mun sulaiman Allahumma inni a uzubika lahaula subhanakallahumma Allahumma ajirni .

Kiyi mana rai soja mun tuba wlh ba zamu sake wa kowa koda kallon banza ba sai kuma suka rarrafa wurin Abu suka rike rigar ta suna kuka hawaye da majina suna fadin Abu ta yafe musu.

Ya isa haka kun cika min kunne cewar Khadija tana gyara zaman glass din fuskar ta ta ce " lokaci yana kurewa ku dauki buta kuyi alwala kuyi nafila ku fara tuba domin yau taku ta kare .


Wadanda suka zo kallon ma ihu sukeyi nan da nan maganar harbe Laraba Asabe da Binta ta fara yawo a gari su kuka gaba dayan banda warin kashi babu abinda sukeyi da rarrafe suka lara tahowa suka rike Khadija suna tuba ganin yanda tsofaffin da sunyi jika da ita suka jiga ta yasa ra sassauta murya ta ce " zan kira su yanzu amma kune kuka san irin alkawarin da zakuyi masa idan ya amince shikenn amma fa ku sani koda ya amince sai ya saka muku yan leken asiri da garin nan idan yaji labari mara dadi to saidai a tashe ku daga bacci da karar bindugu.


Jijjiga kai suka dinga yi kmar kadangaru fadin a taimaka a kirashi, saida ta faki idon su tayi dan guntun murmushi sannan ta kirashi ta kasa handsfree ta fada masa duk abinda yace ""suma suka dora da fadin yallabai soja mun tuba munbi Allah mun bika ba zamu sake koda makamancin wannan ba daga cikin wayar aka daka musu tsawa wacce tayi daidai da karar sakin wani zawon daga Binta da ta fice daga hayyacin fa gaba daya.

"Ban yadda daku ba ku mugaye ne ba zaku canza ba sai mun karbarwa Abu hakkin ta na zalincin da kukayi mata cigaba da rantse rantse sukayi har saida yayi gyaran murya tare da cewa ya isa naji kun tuba zamu kyale ku amma akwai sharadi " mun amince wlh yallabai mun yadda ko menene.

Sai Abu ta yafe muku sannan zakuji namu sharudan da sauri suka dubi abu zasu fara magana tace " na yafe muku Inna

" daga yau duk wacce ta sake yiwa Abu kallo wanda bai mata dadi ba zamu saka camerori a gidan ku kunsan camera ko? Wacce ake daukar hoto to akwai wacce ake sakawa a gidaje don ganin meke faruwa a gidan daga nan zamu dinga ganin duk abinda kuke mata ta cikin computer kungane ? A tare suka daga kai da fadin "e mungane irin ta tsohon dan mai gari dama yace har kayan cikin mutum ana gani da ita . " to yayi kyau daga yanzu Abu ta daina aiki sannan a kula da ita da cikin ta duk abinda kukeyi ma zamu gani yana karasa fada ya kashe wayar sa ajiyar zuciya suka dinga saukewa suna murmushi tare da hawaye da majina .


Binta kuwa duk da warin kashin da takeyi hakan bai hana ta daukar yaron ta ta saba shi a baya ta dubi Asabe ta ce " nidai na tafi zan koma gidan mijina dama kece kika ce in dawo gida rabon ki jefa ni cikin masifa ashe Abu da nake wulakantawa ita ce zata ceceni tana kuka tana yiwa Abu godiya ta fice daga gidan itama Laraba ficewar tayi suna hararar juna ita da Asabe suma su Khadija suka ja Abu suka fice tare suna dariya.

A ranar momy ta koma bayan ta karbi number Samaila da nufin kiran sa idan ta koma, tana so Abu ta dawo kusa da su idan ya amince.



Hanan duniya sabuwa soyayya sosai suke sha da Alh Jibril shi ko ya bude bakin aljihu yana ta kashe musu kudi ita da ahalin ta Nafisa ce kawai bata damu da abinsa ba saidai yanzu shine ya dauki nauyin gidan gaba daya shiyasa dole take cin abincin sa amma bayan nan duk wani abu dazai fto daga hannun sa baga karba a cewar ta tana kyamar hanyar da akabi aka samar da abin .

Dangin mahaifin su taje ta gabatar musu da wanda take so domin burin ta bai wuce tayi aure tayi nisa fa duk wani abu daya shafe su ba .

Sunyi farin ciki da hakan sunan matukar son yayan dan uwan nasu saidai mahaifiyar su ce bata son alakar su da yayan ta domin har gaban alkali sukaje akan suna shigar mata sabagar yaya babu irin sharrin da batayi musu ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login