Showing 39001 words to 42000 words out of 60473 words

Chapter 14 - SALAME COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM SHARIFAT CE.doc

" haba Salma kina jina fa " yanda yayi maganar cikin shagwaba yasa wacce aka kira da Salma kallon sa ta saki murmushin daya kara daskarar dani dashi lokaci daya muka fara tinani mabanbanta , idan banyi kuskuren gani ba Salamen Inna da Abu nake gani a jikin wannan balarabiyar haka na dinga murza ido na ina sake dubawa still dai ita ce daga karshe na koma gefe ina jinjina iko da buwayar Ubangiji, shi kuwa tsananin kyawun da murmushin ta keda shi ne yasa shi shiga shok duk da ba yau ya fara gani ba saidai na yau yazo masa daban , shekara daya kenan da fara zuwan ta makarantar tana level 100 yayin da shi kuma yake shekarar karshe tin ranar daya fara dora idanun sa akanta zuciyar sa ta buga da karfi, bai taba ji ko ganin macen data tafi da zuciya da ruhin sa kamar ta ba yasha ganin murmushin ta saidai baya kaiwa zuciya irin murmushin nan ne da zamu iya kiran sa da ya?e wanda bahaushe ke cewa yafi kuka ciwo saidai yau tayi murmushin da yake jin har cikin ranta tayi shi , cak ya tsaya ya fara tina ranar da ya yiwa abokin sa maganar ta " kaga jay ka cire yarinyar nan a ranka kana gani ai tinda kai ba makaho bane dik rawar kai irin ta yan 100 level bata kawance da kowa bare aboki bare kuma wata soyayya yan class dinsu ma sunce girman kai gare ta mace daya take kulawa itama yarinyar ce ta makale mata so ba yanda zaayi yarinyar nan ta so ka , sannan ko da ta so ka kasan su Daddy ba zasu taba yadda ka auri musulma ba, tin wuri gara ma ka cire son ta. Dage kafadar sa yayi alamar bai damu ba yabar abokin nasa a wurin, tin daga lokacin yake bibiyar Salma yana shiga rayuwar ta saidai taki bashi dama koda ta abota ce tana tashi daga wuri idan ya zauna tana hade rai idan ta ganshi, shi kuma baya jin zai iya hakura da soyayyar ta wannan dalilin yasa ya dawo tin digreen sa na biyu don ya cigaba da farautar soyayyar ta, Koda ya dawo din ma bata canza ba saidai yau ta zama rana mai dumbin tarihi a rayuwar sa duk da bai san dalilin murmushin ta ba. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya dawo daga dogon tinanin daya tafi a fara dube dube "ta tafi " ya fada yana sakin murmushi tare da sumbatar sarkar cross din dake wuyan sa ya wuce department din su.



Da sallama ta shiga class din nasu inda direct ta wuce wurin zaman ta murmushi ta sakarwa faiza wacce tin shigowar Salma take washe baki "barka da zuwa yau kin kusa makara faiza tace tana gyara zaman " murmushi Salma tayi ta ce " yauwa sannu kema , suna cikin hakan lecturern ya shigo suka fara karatu, sosai take maida hankalin ta wurin daukar duk abinda ake koya musu faiza ma tana son karatu shiyasa Salma ke sakewa da ita.

Awa biyu karatun ya dauke su sannan suka fito a gajiye suka wuce wurin da suke tattaunawa akan abinda suka koya , ajere suke yafiya suna yar hira wanda gana daya hirar akan case din raping da raping da malamin su ya basu labari akan wata yarinya yar shekara biyar wacce hakan yayi sanadiyyar rasa rayuwar ta, wani yawu mai daci Salma ta hadiya idanun ta suka firfito sukayi ja Safraz kadai ke zuwa mata arai da yanda yaci zarafin ta ya wulakanta ta sai a yanzu take jin zafin kalaman sa da take jin su kmar zubar ruwan dalma a zuciyar ta, batason sake ganin sa a rayuwar ta saidai tana fatan samun damar da zama wulakanta rayuwar sa ta tabbatar masa da cewa ita mace ko a bola aka dakko ta sunan ta baya canzawa daga mace sannan ta tabbatar masa da cewa duk kankantar allura karfe ce kuma idan baayi hankali da ita zata raunata mutum , saidai kuma bata fatan haduwar tasu koda a lahira. Ganin zata bata ranta akan wanda ya manta da shafin rayuwar ta yasa ta fara kiran sunan Allah har ta fara jin sanyi a ranta .

Zaman su kenan suka fara duba littafin su suna karaw juna bayani.

" Barkan ku dai sukaji muryar da duk cikin su babu wacce zata ce bata santa ba ,Faiza ce ta daga kanta tace" yawwa Salma kuma cigaba da duba littafin ta tayi batare da ta dago ba hakan ba karamin karyawa jay karfin guiwar sa yayi ba , cikin saa aka kira wayar Faiza tayi saurin mikewa tana murmushi tace " Ina zuwa ".


Da sauri Jay ya zauna wanda ya tilastawa Salma dago kanta ta kalle shi ta fara hada kayan ta zata tashi. Mikew yayi ya dawo gaban ta ya tsaya yace " Salma don Allah ki tsaya jin kalmar Allah a bakin sa yasa Salma kallon sa wanda ya rasa mamaki takeyi ko menene oho dai murmushi yayi ya ce " kiyi hakuri idan nayi kuskuren Kiran sunan Ubangijin musulunci ina rokon ki don girman sa ki saurare ni, nasan kinsan komai game dani har bibiyar da nake miki kinsam menene sila kuma kinsan saboda ke na dawo school dinnan ko har yanzu baki gamsu da soyayya ta bane. Tsuguna wa yayi akan guiwar sa hawaye masu dumi wanda suke fitowa daga karkashin zuciya suna yawo akan kumatun sa ya ce " Salma idan duniya makaranta ce to ni a ajin zuciyar ki nake so na zauna , so nake na zama dalibin ki, inaso na karasa rayuwa ta a koyon darasin soyayyar ki,inaso na karanci duk abinda zai saka fuskar ki murmushi, na kasa tantance a tsakanin mutuwa da kuma rayuwa babu ke wanne yafi radadi, domin nasan mutuwa mutuwa ce, haka ma rayuwa babu ke mutuwar a gare ni, soyayyar ki a zuciya ta bata da masarrafi bare na iya sarrafa ta, tafiya kawai nake a soyayyar ki ba tare da sanin inda na dosa ba, fata na dai daga karshe zuciyar ki ta zamo gurin sauka ta ,Ina son ki, Ina son ki .



Safraz zaune yake a daya daga cikin kujerun parlon yana duba abubuwa a Facebook , zanen fuskar mace yaci karo dashi wanda zaka zana shi tana kuka har zai wuce sai kuma ya tsaya tanai karani rubutun dake kasan hoton .


"Yake yar uwa budurwa bazawara matar aure, ko kinsan kina da hannu cikin fyaden da ake yiwa kananan yara da wasu daga cikin yammata ?
Ko kinsan kina da rawar takawa wurin dakile fyale a nahiyar ki?
Ko kinsan zaki iya zama silar farin cikin kananan yara da yammatan da ake ketawa haddi?.

Profile ya duba inda yaga hoton wasu yara mace da namiji fuskar su tayi kaca kaca da cake ba zaka iya gane ainihin fuskar su ba alamar hoton birthday ne, sunan da aka bude account din dashi ya koma dunawa , Bare Salma ya gani.

Tsintar kansa yayi da shiga comment section inda yaga mutane sama da dari biyu sunyi comment da tambayoyi kala kala, so yake ya fita amma ya kasa zuciyar sa tinzira shi takeyi tanason sanin dalilin wannan post, " ? " Kawai ya ita sakawa ya fita ya sauka daga Facebook din gaba daya.


Mrs Sharif ce
' *SALAME*

65-66
OUM SHARIFAT CE>??

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI


(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE

Ka tashi jay banaso mutane suna wucewa suna ganin ka anan zaka tara mana mutane." Ban damu koda duniya zata taru anan ba nidai kawai abinda na sani shine nagaji da boye soyayyar ki duk da kin sani kina nuna baki fahimta ba bazan bar nan ba har sai kinyi alkawarin zaki dinga kulani, gefe da gefen ta ta kalla ta ga mutane sun fara taruwa wasu na dariya wasu suna nun su dawo da kallon ta gare shi tayi tace " nayi alkawari " ka tashi please, murmushin farin ciki ya saki yana mikewa tsaye tayi gaba ba tare da kara kallon sa ba, shima barin wurin yayi don yasan yanzu lokacin komawar ta class yayi.

Sai karfe biyu suka tashi da sauri ta fito tana kallon mutanen dake wurin a fakaice bataso ta gamu dashi cikin saa kuwa har ta karasa wurin motar ta ta shiga ta fice daga makarantar, tinda ta fito yake lura da yanayin ta yasan shi take so ta gudarwa shima baiyi tinanin binta ba don bayaso ya takura mata.


Tana zuwa gida ta tarar da Yaya Musaddiq a farfajiyar gidan yana ta zagaye Jin shigowar mota yasa yayi saurin juyowa motar ta yaci karo da ita tana shigowa. Cigaba da tsayawa yayi har ta karaso gurin sa da murmushi a fuskar ta ta ce" Daddyn Twins brka da hutawa, hararar wasa ya balla mata ya ce wacce ta saka ta saurin rufe baki tana waro ido tace " lailah yau mai aka yiwa baban twins?

Hade rai yayi yace" karfe daya kika ce min zaki dawo baki dawo ba sai karfe uku shine zaki fake da yaya na saboda kin raina ni hadda yi min dariya ko? Toshe bakin ta tayi wata dariyar tana shirin kwace mata ta shiga girgiza kai Saida tayi da gaske sannan ta iya saita kanta tace" bamu tashi da wuri ba bane sorry my sweet brother, maimaita yanda tayi maganar yayi a tare suka saka dariya yace " kije ki huta da yamma sai muyi magana" yes sir "tace tana sara masa, girgiza kansa yayi ya bar wajan yana dariyar farin cikin da ta saka shi .

Behaviors dinta suna burgeshi t tana bawa kowa girman sa tana da wasa duk da wasu mutanen sukan ce tana da girman kai, saidai mafi yawan girman kan da maza sukan ce mace tana da shi ba wai girman kai bane na nuna ita wata ce ba, girmama kai ne da tsare mutunci.


Tana shiga ciki Sultan da Sultana suka nufo ta da gudu suna oyoyo Mommah fuskar ta fal farin ciki ta tsuguna tare da ware hannun ta ta hade su ta rungume tare da yi musu kiss a kumatu sannan tace " where is your mom? Tana kitchen tana hada mna abn dadi suka fada a tare dariya tayi don sarai tasan girki akeyi wa Ibrahim abokin yaya Safraz wanda shine akayi musu baiko da khadija shi kansa Safraz din bai sani ba.
Sama ta haye ta rage kayan jikin ta tayi wanka tare da alwala bata tsaya wani shafe shafe ba mai ta murza da powder kadan sai kwalli da white lips , ta canza kaya zuwa atamfa dinkin t bubu tayi kyau sosai, sallar la'asar tayi sannan ta fito da dankwali a hannun ta tana kwana Kiran momyn twins daga kitchen khadija ta fito tana hararar ta tace" ai nasan indai naji irin wannan kiran daurin dankwali ne idan na barmiki gidan sai inga mai daura miki. " Ni sai in koya in dinga daura mata" cewar momy dake zaune a parlon tana duba wasu kaya da aunty Aisha ta turo mata . Dan tsalle Salma tayi tana da yiwa Khadija gwalo tace " oya maza daura " kin dai ji kunya wlh katuwar mace bata iya daura dankwali ba dame zaayi wa miji ado ? Saida ra faki idon momy sannan tace da gashin kaina.


Fuzgar dankwalin khadija tayi tana Jin kmar ta zane Salma don ta gaji da daura mata dankwali kuma idan tace tazo ta kota mata sai tace bata da time. Daurin akayi mata yayi mata cif fuskar nan sai kyalli takeyi ta koma sama ta dakko mayafi da wayar ta ta fito. Ta cewa momy zata je garding ta fice.


A can ya samu Yaya Musaddiq ya canza kaya Yana sanye da bakar shirt da jeans blue gashin kansa yasha gyara ya fito sak jinin fulani, Sallama tayi a bayan sa ya juyo a hankali ya kura mata manyan idanuwan sa har saida ta dan rusuna ta huta masa iska sannan ya dan furgita ya maida kallon sa kan kujerar dake kallon sa, zama tayi suna fuskantar juna tace " to Abban twins gani Allah yasa dai yanzu banyi laifi ba", kinyi mana ko nace ki tsaya yin kwalliya ne? Ni haka nake so kizo ba sai kin lullube natural beauty face dinki da wani abu ba ya karasa fada yana kokarin saka idanun sa cikin nata, kasa tayi da idon ta jikin ta ya danyi sanyi taki bari su hada ido.

Janyo kujerar sa gaba yayi daf da guiwar ta cikin wata kamalalliyar murya yace" Salma inaso na fadi wani abu a karkashin abun kuma akwai roko banaso ki dauki abin a matsayin alfarma saboda alfarma tana tilastawa mutum yayi abinda bashida raayi saboda jin kunyar wanda ya nema, wannan yasa banson alfarma duk abinda zaayi min inaso ayi min cikin jin dadi da cancanta ta akan abun.
Saida ya nisa ya kara cewa Salma a karo na biyu yanda yaja sunan ya saka ta dagowa ta zuba masa kyawawan idanuwan ta na yan seconni sannan ta sunkuyar da kanta kasa cikin kasalalliyar murya tace " inajin ka yaya" yanayin sanyin muryar da tayi amfani dashi ya saukar masa da wani sanyi har cikin bargon sa ya lumshe ido ya bude su fes akan fuskar ta yace " Rayuwa kmar littafi ce idan page din farko ya burge ka to na biyu zai bata ranka ida kuma ya bata mata sai kika na gama yayi maka dadi , koda bakaji dadin ba hakan baya Hana ka bude na gaba ko da zaka dace da raayin ka.

Salma nayin dakon soyayya shekara biyar da suka wuce na cire soyayyar a raina saboda igiyar aure saidai rabon samun abincin ruhi na ya tsinke igiyar auren daga nan zuciya ta tace min abinka ya dawo hannun ka.

Tinda Yaya Musaddiq ya fara magana Salma take so taji karshen zancen bata jin soyayyar sa ko kadan a ranta, amma a iya zaman ta a gidan ta fahimci irin tsantsar soyayyar da yake nuna mata ta kuma ci alwashin duk ranar daya furta zata amince dashi kuma zata koyawa zuciyar ta kaunar sa domin ya cancanta idan akwai abinda yafi zuciya gangar jiki da ruhi ya cancanta ta bashi.

Bata karasa jin kalaman sa ba sai tsintar kalmar data tsayar da tinanin ta tayi a cikin kunnen ta " ina matukar kaunar ki Salma kar ki ji kunya ta ban fadawa kowa ba har sai naji ta bakin ki, karki cutar da zuciyar ki, kiyi mata adalci karki kaita inda batada bukata. Amma nidai inason ki inamiki son da bansan adadin sa ba.

Dago kanta tayi a hankali ya saci kallon sa cikin saa kuwa suka hada ido ta turo dan karamin bakin ta tace " ni ka daina kallo na" juyawa yayi da kujerar sa yana murmushin hango nasara saidai yana kallon ta ta gefen idon sa a hnkali ta mike ta zura da gudu tana dariya, shima tashi yayi ya biya ta fada parlo tana dariya momy da sauri ta mike tana kallon Salma kafin tayi magana Yaya Musaddiq ya fado cikin dakin yana murmushi, hararar sa momy tayi tace kai kuma fa? Dan sosa kansa yayi yana dariya kallo daya zakayi masa ka hangi nishadi a tattare dashi don ko baa fada ba yasan ya samu shiga saura shirin aure, ficewa yayi daga parlon yana jin dama baiga momy ba da sai ta fada masa abinda take ji a kansa.

Sakin baki khadija tayi tana kallon Salma da har yanzu take murmushi tace " tooo yau naga ikon Allah soyayya har cikin parlo ? Murguda mata baki tayi ta haye sama da gudu, momy kuma murmushin itama ta saki tana komawa wurin zaman ga cikin zuciyar ta take godewa Allah da suke shirin hada kansu da kansu.


Da daddre saida ta gama duk abinda ta saba tayi shirin kwanciya sannan ta bude data ta bude what's app, messages ne suka fara shigowa can taga number Yaya Musaddiq yayi mata magana , da sauri ta bude tana gyara kwanciyar ta , sallama yayi mata sannan ya dora da maganar sa " A cikin halittu Allah ya halicci mata , ya suranta su cikin halitta mafi kyau, ya ware wasu daga cikin su ya kyautata surar su, ya zabi wasu daga cikin su su zama mafifita a cikin kyawawan, a cikin su kuma ya zabi Salma ta zamo mafi kyawu a c Ido na, ya zage wannan Salman tawa da masoya kmar dai zinariya a tsakiyar masu haka, kowa burin sa ya zamo wanda zai mallaki wannan zinariya ya bata kulawa, amma cikin hikimar Allah sai ya zabe mi matsayin wanda zai bawa wannan zinariyar kulawa, ba kuma don ni nafi kowa ba, sai don nine wanda rabo na ya koka aka samu Salma , Salma kw rayuwa ta ce, ke farin ciki na ce, kece mafarkin da nake son cimmawa a rayuwa ta, mafarkin da nake so wata rana ya zamo gaskiya a gare ni, Salma inason ki kmar nayi hauka, Ina matukar kaunar ki Habeebty.

Ta maimaita sakon yafi sau goma tana jin sanyi ma ratsa ta bata samu damar maida masa amsa ba don bata san mai zata ce ba haka ta rungume wayar har bacci ya dauke ta.

Kashe gari da sassafe ta shirya ta tafi school tana da lecture na safe , sai karfe goma suka fito tare da faiza suka wuce inda suka saba zama yauma kmar jiya basu dadeba Jay yazo wurin faiza ta tashi yayi mata godiya ya zauna .

" Barka da hutawa Queen ya fada yana murmushi yawwa kawai tace ba tare da ta juyo ba, bai damu da hakan ba saima kara gyara zaman sa yayi yace " Queen ya maganar soyayyar mu ko ince ma auren mu? Sai yanzu ta ajiye littafin da take dubawa ta juyo ta fuskance shi sosai tace "jay kasan ni musulmace ko? Yes up course na sani amma ai wannan bashida alaka da soyayyar mu. Yana da alaka jay don ni addini na bai amince na auri wanda ba musulmi ba , bata fuska yayi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login