Showing 51001 words to 54000 words out of 60473 words

Chapter 18 - SALAME COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM SHARIFAT CE.doc

driver dazai kaishi Kano anayin sallah suka dau hanya

Karfe sha daya tayi wa Baffa cikin asibitin Dr mahfooz wanda ya gane shi tin lokacin da aka kwantar da Salma,yana shiga ya kira number Musaddiq ya sanar dashi zuwan sa. Fitowa Musaddiq yayi ya gaida Baffa sannan yayi masa jagora zuwa dakin da Safraz yake.


Da sallama a bakin sa ya shiga dakin Musaddiq zama yayi a reception bayan ya nunawa Baffa dakin idon sa akan gadon da Safraz ke kwance Yana mamakin yanda lokaci daya kamannin sa suka canza . Mikewa Daddy yayi zuciyar sa cike da farin cikin ganin Baffa wanda yake da yakinin zuwan sa zai iya kawo maslaha a cikin matsalar su mikawa Baffa hannu yayi Yana shirin magana Baffa ya daga masa hannu ransa a bace yace " dakata Abdallah ai bansan lusarin namiji bane kai bansan shashasha bane kai sai yanzu ashe dama baka iya iko da gidan ka ? Dama maryama ke juyawa? ashe bakuda hankali kana zaune kana shirmen banaza zata kashe yaro ka zuba mata ido to wlh idan wani abu ya samu yaron nan zakuga fushi na da baku taba gani ba fuu ya fice daga dakin Daddy ya bishi a baya , har ya fita titi yana tarar abin hawa Daddy ya karaso dakayar ya amince yahau motar Daddy suka nufi gida.

Ko sallama Baffa baiyi a parlon ba ya fara kwala kiran maryama, momy tasan waye Baffa tin tana karama ta sanshi mutum ne mai ha?uri da kawaici tinda taji irin kiran da yake mata tasan ba lafiya ba.


Jikin ta ba kwari da guntun murmushin ta sakko tana shirin yi masa magana ya saka mata tsawar da ta saka momy rike karfen jikin upstairs sunkuyar da kanta kasa tayi ta karaso kusa da shi ta zauna idon ta ya ciko da hawaye tace " haba Hamma Jauro kasan irin wulakancin da yayi wa yata kuwa? Kasan irin ciwon da taji ? Kuma ya gudu ya canza rayuwa saboda ya nuna mana zai iya rayuwar sa a wani wurin ko damu ko babu mu, sai yanzu da ya samu labarin daukakar ta shine zai dawo yace yana sonta, bai ji kunyar Ido na ba ni zai kalla yace min yanason Salma haba Hamma ka duba fa yaron nan yaci mutuncin mu ya nuna mu ba komai bane a gare shi meyasa muma ba zamu barshi ba.


Zama Baffa yayi ya fuskance ta ya tausasa murya yace maryama kece kika hakicce shi? Girgiza kanta momy tayi ya dora da cewa kin manta cewa sayyidina Umar Allah ya kara masa yadda kafin ya karbi musulunci yana cikin manyan sadaukan da yahudawa ke alfahari dasu? Kuma kin manta yana cikin manyan sadaukan da musulmai ke jin tsoro? Girgiza kanta tayi ya kasa cewa"lokacin daya musulunta Ubangijin daya halicce shi yace bazai karbeshi ba saboda kuskuren sa na baya? aa tace to bayan ya musulunta zaki iya kirga nasarorin da musulunci ya samu sanadiyyar sa ? Ko kin manta daga musuluntarsa aka fara bayyana kiran sallar? Nan ma girgiza kanta momy tayi jikin ta yayi sanyi hawaye na yawo a fuskar ta Baffa yace " maryama idan har Ubangijin daya samar dakai daga babu zuwa akwai ya baka lafiya ya baka ido don ka gani ya baka kafa don ka taka ta baka hannu don ka taba da niimomin da bazamu iya kirgawa ba dan Adam zai iya bijire masa ya dawo ya tuba matukar tuban na gaske ne kuma yabi sharudan tuba Ubangiji ya yafe karfa ki manta har damarmaki Allah ya bamu ta neman yafiya idan mun aikata laifi , to maryama kinasl ki nuna hakkin ki yafi na mahalicci ne? Da sauri momy ta girgiza kanta have " idan har kin yadda da abinda na fada miki ki tashi muje ki duba jikin sa kuma ki yafe masa.


Mrs Sharif ce
' *SALAME*
75

OUM SHARIFAT CE>??

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI


(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE


Sunkuyar da kanta momy tayi tace na dade da yafe masa hamma kawai idan na kalli Salma sai in dinga jin kamar Ina da hannu cikin zalintar ta, Inna ta ma zata yafe masa tinda dan Adam ne shi ajizi kuma dukkan abinda zai faru da bawa tin kafin yazo duniya a rubuce yake so nake ki tashi muje asibitin ki fada masa da kanki. Kafin momy tayi maganar wayar Daddy tayi kara sunan Musaddiq ya gani yana yawo ajikin screen din wayar dauka yayi gabansa yana faduwa ya saka wayar a handsfree, ko sallamar da Daddy yakeyi Musaddiq bai amsa ba cikin muryar kuka yace " Daddy shikenn yaya zamu rasa shi wlh Daddy Yaya Safraz yana cikin matsanancin hali so yake momy da Salma su yafe masa kar ya mutu da hakkin su yanzu haka bamusan halin da yake ciki ba Daddy numfashin sa tafiya yakeyi yana dawowa cikin kidima kowa ya mike momy ta manta da fushin da takeyi da Safraz da sauri ta mike dama da hijab a jikin ta suka fice Daddy ne ya jasu zuwa asibitin.


Suna zuwa suka samu Dr ya fito daga dakin ransa a bace yace "gaskiya Alh kun bani mamaki ai na zata ko dabba kuka ajiye a cikin mawuyacin hali haka zakuso ganin ta samu salama wai ko wani ya kashe muku ne kuke so kuma ku kashe shi? Daddy bai tsaya jin karashen kalaman Dr ba ya fada dakin.

Safraz a kwance idon sa a bude yana kallon pop dake cikin dakin hawayen nadama ne ke bin gefe da gefen idon sa, kusa dashi Baffa ya karasa ya kama hannun sa ya rike ya jawo hannun momy ya hada yace " dana Safraz ka kwantar da hankalin ka ga momyn ka nan ta yafe maka ta daina fushi dakai kmar an sakawa Safraz shock haka yaji ya damke hannun momy yana so ya dago kansa ya ganta sosai amma ya kasa sai momyn ce ta koma gefen da fuskar sa take , yafi sanda ta barshi ramewa kmar ba Safraz dinta ba Jin muryar sa tayi a kunnen ta yana fadin momy na kin yafe min? Kin daina fushi dani ? Zaki dinga kulani? Kawar da fuskar ta momy tayi zuciyar ta na lugude, matsanancin so da tausayin danta yana ratsa ta tace"" e na yafe maka saidai cigaba da kula ka kamar da zai kasance ne bayan kabi sharadi na, gaba daya dakin saida suka juyo kan momy, shi ko Musaddiq haushi ya fara ji akan abinda momy takeyi ransa a dan bace yace " haba momy daga masa hannu tayi, kafin tayi magana Safraz yace " ka bari Musaddiq kar ta sake yin fushi dani na amince momy ko menene idan har zaki yafe min ki kulani zanyi ko menene".


Ka cire Salma a ranka ka dauke ta a matsayin kanwar ka ka janye kudirin sake rayuwa da ita, wannan shine sharadi na , tari Safraz ya fara kamar bazai daina ba daga can ya lafa cikin wata irin murya can kasa yace "na amince momy daga yau Salma kanwa ta ce koda sonta zai kashe ni bazan sake bayyana shi ga kowa ba zan roki Allah ya cire ta a raina " gaba daya dakin ji sukayi sharadin momy baiyi musu dadi ba ciki kuwa hadda Yaya Musaddiq da yake jin wani iri a ransa yasan dai yanason Salma amma ya kasa gane farin ciki yake da sharadin momy ko bakin ciki.

Baffa ne yaja Daddy da momy waje shima Musaddiq jikin sa duk ba dadi ya koma reception ya zauna Ibrahim kadai ya rage a dakin sai sultan da Sultana suna buga game a wayar Ibrahim.

Sultan yana ganin su momy sun fita ya tashi yazo wajan gadon da Safraz yake kai ya kama hannun sa ya rike , Safraz daya lula duniyar tinanin yanda zaiyi ya iya rayuwa ba tare da Barr ba yaji hannun yaro a nasa hannun juyo da kansa yayi daidai saitin da sultan yake ya sakar masa murmushi, Sultan kuwa kurawa Safraz ido yayi cikin tsamin bakin sa yace" mai yasa kake kuka? Ba kuka nake ba cewa Safraz yana sake kakalo murmushi" zaro ido yaron yayi yace Mamy ta ce karya haram Allah zai kona mai karya a wuta kuma Sultan baya karya kai kuma kayi.

Ajiye wayar hannun ta sultana tayi ta karaso ta kama hannun sultan cikin fada fadan ta wanda ya bayyana Salame tsaf a tare da yarinyar tace " kai sultan ba Aunty ta hana mu kula wanda bamu sani ba kwace hannun sa sultan yayi yace " ba momy da Baffa sun taba shi ba , sake tankwabe hannun sultan tayi daga na Safraz tace" idan mukaje duba mutane dama ba momy tana taba kansu kuma ta basu kudi ba nidai na tafi idan ya yanka maka kankan shikenn, sultan jin anyi maganar yanka masa kansa da sauri ya saki Safraz ya fice da gudu ko waiwaye babu.

Hawayen takaici ne suka zubiwa Safraz yace " ka gani ko Ibrahim kaga karshen abinda na aikata ko yara na fa Ibrahim sune suke gudu na sune suke min kallon mugu amma kuma basuyi kuskure ba ni mugu ne na zalinci mahaifiyar su na samar dasu cikin mugunta zalinci bnkasance tare dasu sun bude ido sun ganni ba ban kasance cikin masu rike hannun su wajan koya musu tafiya ba banida hannu cikin ilimi da tarbiyyar su na tafi a lokacin da suke da bukatar na zauna a tare da mahaifiyar su har suzo su same mu tare na dawo a lokacin da suda mahaifiyar su basa bukata ta.

Ganin yana neman sake dawo da damuwar da ake so ya kawar yasa Ibrahim ya shiga bashi baki tare da nuna masa muhimmancin yadda da kaddara.


Baffa ya zauna da Salma ya nemi ta yafewa Safraz inda ta tabbatar masa ya jima da yafe masa tin ranar da ta ganshi a asibiti, kashe gari karfe takwas na safiya a Nigeria jirgin Safraz ya tashi zuwa kasar masar cikin kulawar likitoci don yi masa aiki tare da rakiyar Musaddiq da Ibrahim, bayan sun tashi suka dawo gida saida Baffa ya sake yiwa momy nasiha sosai mai ratsa jiki sannan drivern Daddy ya tafi kaishi ruga.


Karima bakar wahalar da tasha a hannun askarawa ne yasa ta fallasa siriirn kungiyar su cikin ikon Allah kuwa aka kama bangaren su saidai a kawai manya manyan kungiyoyin wadanda Karima bata san su ba kuma sune jigo masu bada umarni wannan taasar da Karim tayi ne yasa suka binciko iyayen ta har gidan da suke ciki.


Duk wata kadara da Karima take da ita a Kano Saida suka kwace tare da cikakkun takaddu har gidan da suke ciki mama taso tayi rashin mutunci saidai ganin harkar ta masu jajayen kunnuwa ne yasa ta bisu da kuka da Allah ya isa anan kuma take jin labarin kama Karima da hodar iblis a saudia, mama ta gama gigicewa ta fita hayyacin ta toilet kuwa batasan adadin shigar ta ba ita kanta Hanan ta gama rudewa duk wasu manya da ta sani ta nemi taimakon su akan abun amma daga mutum yaji ance saudia sai ya zame daga karshe ma suke yanke alaqa da ita don kar ta jawo musu masifa, katon shopping mall din da minister ya bude mata saida ya kwace shi tare da mota har account dinta yasa aka rufe don kar a gano ya taba tura mata kudi.

Daya account din Hanan ne kawai keda kudi sai gidan ta guda daya daya rage mata wanda wani dan kasuwa ya siya mata can suka koma da zama har lokacin mama bata daina tsinuwa da laanta akan wadanda suka kwace musu gida ba gefe guda kuma ga yarta mafi soyuwa a ranta cikin kurkukun saudia, rabon data daga hannu ta roki Ubangiji wani abu har ta manta saboda ta sakankance tana da Karima wacce take yi mata komai ta manta cewa Ubangiji shine kadai madauwami baya gazawa kamar yanda baya kasawa.



Mrs Sharif ce
' 76
OUM SHARIFAT CE>??
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE


Ciwo ne ya dami Hanan ta shirya ta tafi asibiti ta samu ganin likita akayi mata gwaje gwaje aka gano wasu kananun tsutsetsi dake yawo a cikin duburar ta sune suke cizon ta take kasa zama firgicin da Hanan ta tsinci kanta a ciki yafi na Jin rahoton kama Karima hawaye na zuba a fuskar ta zuciyar ta tana tafasa bakin ta yana daci idon ta yana rufewa yana budewa cikin kuka da sarkewar murya take tambayar likita mafita, tabbatar mata likita tayi akan idan akayi zata samu lafiya ba tare da wani dogon tinani ba ta tambayi kudin aikin bayan sun fada matata tura kudin aka bata receipt ta dawo bayan an saka ranar aiki nan da kwana uku saida ta dawo gida take sanar da mama halin da take ciki sai a sannan mama ta iya sanar da Hanan matsanancin kaikayin da take ji a gaban ta tare da wani ruwa kore da yake ftowa mai wari a take Hanan ta gane inspection ne ya samu mama kuma tasan a jikin mijin ta ta same shi, kwantar wa da mama hankali tayi tare da siya mata magungunan da zai kashe ciwon.


Bayan kwana uku akayi wa Hanan aiki cikin ikon Allah akayi aiki cikin nasara kwanan ta biyu suka sallame ta suka hado kayan da suka zl dasu suka nufo gida tin daga farkon layon mutanen unguwar suke kallon su har suka karaso kofar gidan da take a rushe babu alamar gini komai an rushe kasa tsayuwa Hanan tayi ya ja baya da sauri ta rike kofar gidan dake kallon rushashshen gidan nasu wani yaro ne yake Basu labarin jiya wani mutum yazo tare da wata mota aka rushe gidan, ko tantama Hanan batayi ba ta tabbatar wanda ya bata gidan ne ya rushe shi, kwantar da kanta tayi akan kafadar mama wacce batasan a wane yanayi take ciki ba ita dai tana ganin wata rayuwa daban da waccce take ciki a baya kuma tazo da salon kaskanci fiye da wanda suka kasance a can baya.

" Kinga abinda Karima ta jawo ko mama? kinga yanda tasa muka tozarta a titi ko? Mama bata iya bawa Hanan amsa ba don ba abinda take ganewa tayi zurfi cikin tinanin irin juyin da duniya tayi musu, tabbas duniya batada Amana cewar mama da batasan ma a fili ta furta ba.


Wani makocin su ne ya fito ya shiga dasu gidan sa ya ba basu hakuri.


Su Safraz sun sauka a asibiti lafiya misalin karfe daya na dare aka shiga dashi dakin tiyata.

Musaddiq Ibrahim har ma mutanen Nigeria sun dukufa wajan nemawa Safraz sauki ciki hadda Salma wacce ta kasa fahimtar dalilin damuwa da lamarin sa, cikin kwanakin nan takan samu kanta cikin fargaba da faduwar gaba batasan dalilin su ba saidai ta dage da addua tana samun saukin halin da zuciyar ta take ciki.

Saida safe Musaddiq yake sanar da su fitowa da Yaya Safraz cikin aminci kuma ana saka ran zai tashi ya dawo kmar yanda yake da da izinin Ubangiji, hamdala kowa ya farayi cike da farin ciki suke dokin ganin samun saukin Safraz komai ya fara saituwa farin cikin da gidan ya rasa a hankali ya fara dawowa sai yanzu suka fahimci da can akwai gibi a cikin gidan, shi kansa Safraz zaman sa a Cairo taurin zuciya ne kawai irin na soja amma Koda yaushe zuciyar sa fal take da begen iyayen nasa shiyasa a yanzu da ya samu damar goge laifin sa ya dauki damarar hakura da komai don ganin ya dawo da soyayyar sa a zuciyar iyayen sa , bikin su Salma aka kara wata daya sakamakon angwaye suna jinya.

Kwanci tashi akace asarar mai rai yau saura kwana bakwai bikin kuma yaune brigedier Safraz Abdallah yake Shirin dawowa Nigeria daga kasar masar bayab samun sauki daga aikin spinal cord, gaba daya gidan ya dauki harami ana aikin abinci kala kala tini suka manta da shine wanda suka tsana suke kuma Jin haushin sa sosai momy ta zage tare da Khadija da Salma da made din su suke shirya masa kayan tarba.

Yamma likis jirgin su ya sauka a filin jirgin malam Aminu kano motocin gurd dinsa Dana Daddy ne suka zagaye wurin da ake parking don jiran masu dawowa, yana sanye da bakin jeans da t shirt blue black hannun sa daure da bakin agogon rado ya kara haske gashin kansa baki sidik yayi luf dashi wanda ya kara kawata hasken fuskar sa kmar balarabe , su Musaddiq ma sunyi kyau kasar ta karbe su sosai, wurin motar Daddy suka nufa yana tsaye yana jifan su day kyakkyawan murmushi a tare suka tsuguna suka gaida shi zuciyar sa cike da farin cikin ganin yayan nasa ya tashe su ya shiga hogging dinsu daya bayan daya har Ibrahim da yake matsayin suriki Daddy matsayin da yake daukar sa ba suriki ba. Gwanin shaawa haka suke farun cikin su Daddy da Safraz suka shiga mota daya Musaddiq da Ibrahim suma mota daya gurd din Safraz suka saka su a tsakiya sannan aka saki jiniyar dake nuna Brigadier general Safraz Abdallah ya dawo daga jinya.


A can gida kuma sun gama shirya komai sun jere aka katon daining tablet din dake daukar family guda, suna shigowa suka tarar da gaba daya mutanen gidan a compound suna jiran isowar sa, parking din motocin sukayi sannan suka fara fitowa kallom kowa yakeyi cike da mamakin tarbar da baiyi tsammanin ta ba , shi dan gata ne ahalin sa suna son sa amma ya shuka musu gubar bakin ciki a zuciyoyin kunya tare da wata nadama suka sake dirar wa zuciyar sa ganin hadda Salma a cikin masu tarbar sa a boye yasa babban dan yatsan sa ya goge kwallar data zubo masa.

Bai sake cika da mamaki ba Saida yaga irin welcoming din da Momy tayi masa hakika uwa uwa ce duk duniya babu mai so da tausayin ka kamar ta son zuciya da rudin shaidan kadai ke sawa a bijire mata, part dinsa nada suka kaishi shida Ibrahim yasha gyara komai tsaf kmar da mutum

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login