Showing 48001 words to 51000 words out of 60473 words

Chapter 17 - SALAME COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM SHARIFAT CE.doc

sa shine a cikin mawuyacin hali amma an rasa mai kusantar sa.

Kara kiran number Daddy yayi cikin saa kuwa ya dauka da sallama,kasa amsa sallamar yayi ya cw "haba alh Safraz fa danka ne Koda a hanya kuma tsince shi a halin da yake ciki bai kamata a tafi a barshi ba bare Safraz first born din ka idan ma akwai wani Abu sai a barshi as family issue bai kamata a kyale shi ba.


Mamaki ne ya kama Daddy don shi gaba daya a tinanin sa Safraz ya farfado an sallame shi ya tafi gida muryar dr mahfooz ce ta katse masa tinanin sa inda yace " muna bukatar ku yanzu alh yana fada ya kashe wayar, da Ido kawai Daddy yabi wayar jikin sa yayi sanyi lakwas ya kira Musaddiq yace ya dakko mota zasuje unguwa momy yace tazo su tafi khadija da Salma hadda twins sukace zasuje cikin kankanin lokaci kowa ya shirya suka fice, tinda suka karaso asibitin momy ta fara kokarin balle murfin motar zata fice Daddy yace " ba gurin Safraz nace kije ba rakiya nace kiyi min idan na isa shiri tayi ta dakata da kokarin fitar saidai kana kallon ta kasan ranta a matukar bace yake.


Suna shiga suka tarar da Dr mahfooz a reception sama sama suka gaisa yace su biyo shi har dakin da aka kwantar da Safraz ya kaisu suka zauna akan kujerun dake dakin momy kuwa a tsaye ta tsaya ranta a hade zama Dr yayi ya fuskance su yace " kamar yanda na fada maka Alh Safraz yana cikin mawuyacin hali don a halin yanzu lakar sa ta baya ta lalace ina nufin bazai iya tashi ba bazai iya motsa jikin sa ba abinda kadai zai iya shine amfani da hannun sa kafar sa ma iya yatsun sa ne zasu motsa sa kuma kansa zai iya magana amma daga nan babu inda zai kara motsi daga jikin sa.


Sample din wata cocaine aka kawo gidan su Karima inda zaa fitar da ita zuwa saudia kuma a karkashin Karima, karfe goma jirgin su zai tashi tin karfe tara ta shirya inda tayi cukon mazaunan ta da cocaine din wani wando ta saka 3 quarter mai aljihu da baya guda biyu gaba ma guda biyu manya inda ta cika su day hodar iblis din sannan ta saka wani dogon ta dora doguwar riga tayi rolling mayafin rigar, sai da suka sai hanya sannan ta nufi airport, karfe goma suka tashi sai jidda sun sauka lafiya ta sauka a hotel din da suka saba sauka idan suka zo ta canza sim ta fara kiran mutanen su na saudia.

Bugun da akewa kofar dakin nata ne yasa ta kashe wayar ta shu a fusace ta bude kofar waro Ido tayi cike da rudu ganin jamian tsaron saudia a kanta babu alamar sassauci a tare da su, bincike suka farayi a dakin Saida suka yi filla filla da komai sannan suka dawo jikin ta matan suka caje ta tsaf aka fito da cocaine din da ta shigo da ita suka tasa ta gaba , kafin ta shiga kungiyar su saida ta amince da sharadin su koda an kama mutum kada yace komai idan kuma yayi magana kaf dangin sa sai an kashe su.


Hanan wajan sati biyu kenan bata ga alajin ta ba wato minister duk da har yanzu akwai manyan kudade a account dinta sannan akwai shopping mall dinta yana tafiya saidai wani irin kaikayi take ji a duburar ta da gaban ta musamman idan tana zauna haka zataji kmar an mintsileta da sauri zata tashi ta kama sosa bayan ta tin tana jurewa har ta fito ta sanar da mama , shawarar zuwa asibiti mama ta bata a cewar ta bazai wuce inspection ba gara tin kafin yayi mata karfi tayi maganin sa.


Nafisa ta zama manyan mata yanzu yayan ta biyu Amir shine Babba sai Amira, gidan man da Sulaiman yake aiki duba da kwazon sa da amanar sa mai wajan ya maida shi md ya canza musu gida yasai mota hankalin su akwance suke yaruwa mai cike da tsafta Sulaiman yayi mata halacci baya manta kalubalen data fuskanta akan soyayyar sa yanzu babban damuwar ta shine batasan inda su mama suke ba duk da mama batason ganin ta amma takanje tsohon gidan su ta tsaya daga baya wani lokacin tana ganin Hanan wata Rana ma har da maman lokaci daya taji tashin su a wurin makotan su kuma babu wanda yasan inda suka koma..
Mrs Sharif ce
' *SALAME*

OUM SHARIFAT CE>??
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE



Kuyi hakuri da wannan =?O?

Wani irin tashin hankali ne ya ziyarce su ita kanta Salma sai da taji wani abu ta darsu a zuciyar ta wanda tabar hakan a matsayin tausayin musulunci.

Sultan sultana kuwa basu San menene abinda ke faduwa ba wasan su kawai sukeyi a jikin gadon.

Yana kwance sambal kamar gawa idanun sa a rufe bakin sa ya fara motsi alamar yanason cewa wani abu da ido Daddy ya kalli momy yayi mata alamu da ta karasa gare shi da sauri ta mike ta fice daga cikin dakin fuskar ta babu alamun sassauci, gaba daya da kallo suka bita dukkan su sun san Safraz ya aikata babban laifin daya cancanci hukunci, saidai suna ganin halin da ya tsinci kansa a ciki ma hukunci ne daga Ubangiji yakamata ta yafe masa tinda Allah ya hukuntashi, yaya Musaddiq ne ya matsa kusa dashi ya sunkuyar da kansa saitin bakin sa zuwa lokacin muryar sa ra fara fitowa ta ynda idan mutum ya nutsu zai iya jin abinda yake cewa gaba daya shiru sukayi suna sauraren abinda sukeji tamkar tatsuniya daga bakin sa " ki yafe min bazan sake ba kiyi duk wulakancin da kika ga dama amma kar kice ba zaki zauna dani ba inason ki badon kyawun ki ba Ina son ki badon daukaka ba banson kece Brr Salma ba tinani da kokarin kare mutunci yasa nake son ki, dukkan su jin maganar suke kmar zafin ciwo da kuma rashin sanin inda kansa yake.

Dr mahfooz ne ta shigo yaji abinda Safraz yake cewa ya dubi Daddy ya ce " tin yana cikin suma yake furta wannan kalaman kuma wannan yana nuni da cewa zuciyar sa ce take fada ba kalaman bakin sa bane Alh idan da hali kuyi masa abinda yake so kafin nan ma yakamata a fitar dashi inda zaayi masa aiki.

Momy tana fitowa ta nemi kujerar da aka jera don hutawar masu jinya ta zauna tare da dafe kirjin ta, batasan mai take ji ba so take ta karyata zuciyar ta wacce take fada mata taji tausayin ta wani irin abu take ji tin daga saman kanta har karkashin kafar ta so take ta sanar da zuciyar ta haushin sa ta kara ji ba tausayin sa ba, numfashi ta dinga ja tana saukewa saida ta saita kanta ta karfafa zuciyar ta akan batajin komai game dashi duk da akwai wani rauni a sashin zuciyar ta wanda ta kasa gane ko menene.

Tashi tayi ta koma dakin, duk abinda Dr mahfooz ta fada taji, "" babu inda za'a kaishi suka jiyo muryar momy daga bakin kofa da kallon mamaki suka bita gaba daya bata damu da kallon da suke mata ba ta ce " kuma idan har akan Salma yake wannan sambatun karyar to gara ya mutu ya huta ciwo kuma yayi tayi idan kun gaji da ajiyar sa ku jefar dashi ku kuma ku tashi mu tafi dangin daya sauya suzo suyi jinyar sa.

Gaba sukayi jiki ba kwari wata dabara ce ga fadowa Yaya Musaddiq yayi can gaba ya danna kiran layin Baffa ,bugu biyu ana uku aka dauka bayan sun gaisa ya sanar da baba komai tin daga dawowar Yaya Safraz hankalin Baffa ya tashi sosai kuma ransa ya baci akan abinda momy tayi shiru yayi yana nazari kafin yace " Musaddiq kayi wa mahaifiyar ka biyayya ka tafi amma ka nemi wanda zai kwana dashi gobe in sha Allah nima ina tafe sai yanzu Yaya Musaddiq yaji wani sanyi a ransa nan take ya kira wayar Ibrahim ya sanar dash???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i komai tsananin tashin hankalin da Ibrahim ya shiga bazai fadu ba kashe wayar kawai yayi ya sanar da momyn sa halin da Safraz yake ciki ya nufi asibitin.


Daddy aka bari a zaune kan kujera yana tinanin abin yi maganar gaskiya Safraz ya shuka laifi Mai girma a zuciyar mahaifiyar sa saidai ga ciwon da basu tsammanin wanzuwar sa a cikin ahalin su ba ya faru dashi ciwo mafi hatsari ko wannan bai isa ya tabbatar wa momy cewa Ubangiji ne ya hukunta Safraz ba? Gashi da ransa amma ko kafarsa bazai iya dagawa ba wayewae da yake takama da ita a yanzu babu kuzarin da zai nuna ta, ilim da yake takama dashi gashi ya kasa yi masa amfani wannan ya isa ya gane shi din bakowa bane mai yasa momy ba zata barshi da iya hukuncin Allah ba ? Kasa kunnen sa yayi Jin Safraz yana mgna a hankali. " Koda zan dawwama da wannan ciwon bazai dame ni fiye da fushin ki ba momy nasan ni mai laifi ne amma gudu na zai iya tarwatsa zuciya ta momy banida wani abn so a duniya sama dake kece farin ciki na momy Ni kaina na tsani kaina banaso na rayu ban cancanci zama dake ba saidai bazan iya rayuwa kina gudu na ba momy ki yafe min in mutu plx momy sambatu yake tayi sai kuma ya fara daga kansa yana bugawa a jikin gadon hakoran sa suka fara kakkarwa ya fara tauna harshen sa nan da nan gadon ya fara rawa da gudu Daddy ya fita yana kwala kiran Dr daidai nan Ibrahim ya karaso Dr ya fito a rude a atare suka shigo dakin ganin halin da Safraz yake ciki yasa dr sallamar su gaba daya ya kira nurses suka turashi akan gadon marasa lafiya aka bar bangare gaba daya dashi..

Halin da Ibrahim ya tarar da Safraz ba karamin tada hankalin sa yayi ba abin ya wuce yanda yayi tinani wasu hawaye masu dumi suka zubo masa " cikin zuciyar ya fara magana"" wannan yana da alaka da hakkin Salma da kuma fushin momy menene amfanin rayuwar yau wacce zata hana ka tina gobe? Yanzu ina ilimi ina iko ina mukami ina wayewa duka suna tare da shi amma ba zasu ita taimakon sa da komai ba ina amfanin bijirewa iyaye? Zamewa yayi kasa ya zauna kmar karamin yaro ya fashe da kuka yana tina wannan fa shine Safraz wanda duk inda zaije convoy din motoci ke biye dashi wanda aka zaman awanni ana jiran umarnin sa wanda ke takawa da karfin sa yau ina karfin ina kafar takawa shi kansa Daddy kukan zuci yakeyi a zahiri na gaskiya ya zubar da makaman sa zuwa yanzu tausayin dansa ne fal a ransa da kuma tinanin hanyar nema masa lafiya so yake a shawo kan wannan matsalar ya fita dashi ayi masa aiki.

Har akayi sallar azahar shiri gaba daya jikin su ya gama yin sanyi sun hakikan ce shikenn sun rasa shi wajan karfe uku aka turo gadon hannun sa daure da drip yana bacci a tare Daddy da Ibrahim suka sauke ajiyar zuciya sannan suka bi bayan Dr suka shigo dakin.

Kallon Daddy Dr yayi yace " Alh muje office kafin ya rufe baki tini Daddy ya mike da sauri yayi hanyar office din Dr ya bishi a baya,
matsawa kusa da gadon Ibrahim yayi ya kurawa fuskar Safraz ido yana mamakin yanda yayi wata muguwar rama yayi baki kmar ba Safraz ba.



A office din Dr Daddy ne zaune ya kurawa Dr Ido da kunne yana son jin halin da Safraz yake ciki " Alh menene abinda ya faru har ya jawo masa wannan jijjigar? shiru Daddy yayi can ya nisa yace " Dr sun dan samu misunderstanding da mahaifiyar sa ne har takai ma yanzu taki saurarar sa shine abin da yake ta sambatu akai har kuma ya fara jijjigar , jijjiga kansa dr yayi yace " okay to gaskiya ayi kokarin taya shi bata hakuri zuciyar sa cike take da fargaba da kuma tsoron wani abu wannan dalilin yasa bata bugawa yanda yakamata idan tsoron ya cigaba zuciyar zata iya tabuwa daga nan kuma gaskiya komai zai iya faruwa tinda zuciyar ta riga tayi rauni.

Iska mai zafi Daddy ya furzar kansa na wani irin sarawa ya lumshe idon sa ya bude su a hankali ya ce " nagode dr in sha Allah hakan ma bazata faru ba yanzu dai ya zaayi da maganar aikin lakar tasa? Zaayi maganar aiki Alh amma bazaiyiwu ba har sai zuciyar sa ta dawo tana bugawa daidai yanda take a baya.

Mr sharif ce
' *SALAME*
74

OUM SHARIFAT CE>??

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI



(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE

Shikenn Dr in sha Allah ba zamu bada gabar da zaa samu matsala ba, musabiha sukayi da Dr sannan Daddy ya fito ya koma dakin . Idan ba cikakken sani kayi wa Safraz ba baka isa ka gane shi yayi duhu sosai yayi wata irin rama ya kara tsaho yanda yake kwance akan gadon zaka iya tinanin gawa ce gefen gadon Ibrahim ne zaune hannun sa cikin daya hannun na Safraz wanda baa daurawa drip ba jiki ba kwari Daddy ya zauna ya dubu Ibrahim yace " sannu Ibrahim kaga halin da dan uwanka ya tsinci kansa ko? Kaga illar biyewa zuciya ko? Idanuwan daddy sunyi jawur yake magana.

Murmushin yake Ibrahim yayi zuciyar a cunkushe ya dubi Daddy yace" bawa baya kaucewa ?addarar sa Daddy kuma wannan abun ba komai bane a wurin Allah zai bashi lafiya cikin kankanin lokaci, taimakon da zakayi mana Daddy ka koma gida ka roka mana momy tayi hakuri ta yafe masa nasan Salma zata yafe masa. Girgiza kansa Daddy yayi yace " kayya dai Ibrahim maryama ta sha saudaukar da mafarkan ta saboda farin ciki na maryama ya zabi nutsuwa ta fiye da tata bata iya musawa umarni na a wannan lokacin inajin kunyar tursasata ne, sasauta murya Ibrahim yayi yace "" Daddy wannan karon idan ka tursasa momy na tabbata nan gaba itama zatayi alfahari da tursasawar da kayi mata Daddy ka dauki wannan a matsayin ceton rai. Dakyar Ibrahim ya shawo kan Daddy ya tafi gida ya barshi zai kwananda Safraz amma fur yaki amincewa ya turasasa momy.



Khadija ce zaune akan gadon su ta kurawa gefe daya ido tati zurfi cikin tinani Salma data fito daga wanka ta dafa ta da sauri khadija ta fara goge hawayen fuskar ta tana kokarin kirkoro murmushi. "" Nagani ai kuka kikeyi aunty Khadija tin dazu nazo bakisan nazo ba kuma nasan abinda ya saka ki kuka, duk abinda yake faruwa nice sila inda baa daura aure na da Yaya Safraz ba da yanzu kuna rayuwar ku cikin farin ciki sanadi na mahaifiya ta juya baya ga danta sanadina ta jefa shi cikin mummunan ciwo, nayi nadamar kasancewa ta! bata karasa fada ba khadija ta rufe mata baki tana girgiza kai tace " ba kece sila ba shine silar komai shine ya bijirewa momy shine ya cutar dake nasan cutarwar da yayi miki shine babban abinda momy ta rike ba bijiremata da yayi ba.


Sababbin hawaye ne suka sake gangaro wa daga idon khadija ta kama hannun Salma ta rike gam tace "kiyi hakuri Salma na kasa zamewa bangaren jikin ki na kasa dorewa da fishin da nakeyi dashi zuciya ta tausayin sa take ji zafi nake ji akan halin da yake ciki nayi kokarin cire tausayin a raina amma yaki fita Ina son Yaya Safraz shidin mutumin kirki ne kuskuren daya tafka shine yake jijjiga rayuwar sa a halin yanzu.

Goge nata hawayen Salma tayi tace" wlh Aunty Khadija wanda ya rabi gidan nan ya wuce hakana wuri na na yafe masa kuma nima ina Jin tausayin sa har cikin zuciya ta inajin makamancin abinda kikeji koda bansan shi ba kuma ko mai yayi min bazan iya jure ganin sa a wannan yanayin da hakki na akan sa ba idan da akwai yanda zanyi da zan saka momy ta yafe masa amma tsoro nake ji tinda Yaya Safraz ya dawo taki bawa kowa fuskar da zaiyi mata maganar sa.


Daddy tinda ya dawo yake neman fuskar da zaiyi wa momy maganar saidai yanayin ta ya nuna kamar ba wani da yake faruwa a gidan duk abinda ta saba yi masa saida tayi kafin yayi magana take rigashi yi har ya hakura ya zubawa sarautar Allah ido tex yayi wa aunty Aisha ya fada mata duk halin da ake ciki sannan ya ajiye wayar ya kwanta badon zaiyi bacci ba sai don jikin sa yana bukatar kwanciyar, da sassafe ya shirya ya koma asibiti yanda yabar Safraz haka ya same shi ko motsawa baiyi ba Dr dai yace bacci yakeyi jigum jigum suka zauna sai wajan karfe tara khadija Salma da musaddiq suka zo kawo abinci.

Musaddiq lokaci daya ya rame ya rage walwala damuwa ta bayyana karara a fuskar sa da gangar jikin sa. Aunty Aisha kuwa tin karfe 7 tazo ta saka momy a gaba hadda kuka amma duk inda tabi sa momy ta zame daga karshe da fada suka rabu ta mike ranta a matukar bace tace" shikenn yaya kiyi yanda kike so in sha Allah yaro na zai samu lafiya tinda ransa ba a hannun ki yake ba tana gama fada ta share hawayen daya wanke mata fuska ta fice daga parlon, tashin motar aunty Aisha shine ya dawo da momy daga duniyar data lula ba tinani takeyi ba kuma batasaky mai ya tsayar mata da jinta da ganin ta na wani lokaci ba, danshi taji a fuskar ta ta saka hannu ta taba ta kalli abinda ke hannun ta hawaye ta gani a take ta fara tambayar zuciyar ta na menene bata da amsa sai girgiza kanta kawai takeyi , hayewa sama tayi tana jin wani dunkulallen abu a ranta wanda ya hana hawayen da take son sanin dalilin zubar su fitowa.



Bafaa tinda ya fito masallaci bai koma gida ba dama yayi bookin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login