Showing 1 words to 3000 words out of 118786 words

Chapter 1 - CUTA TA DAU CUTA COMPLET BOOK by billyn Abdull .pdf

12 Jul 2025

4004

*_Typing_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_� ��� ��_



_Shafi na ɗaya_



ِ
مْسِب_* ِ
هَّللا ِنٰ
َمْحَّرلا *_ميِحَّرلا
_Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._


........“Ango! Ango!! Ango!”. Itace kalma mafi rinjaye da tafi fita a bakunan taron matasan dake
cike da ƙofar gidan. Yayinda wanda suketa faman kira da angon bakinsa ya kasa rufuwa dan
farin cikin da yake a ciki a wannan rana data kasance ta aurensa da masoyiyarsa mafarkinsa.
Magana da ɗaya daga cikin abokansa ya gwargwaɗa masa a kunne ta saka shi jan hannunsa
suka koma gefe. Cikin ɗan nuna yanayin damuwa da hasala ya ce, “MB ya akai haka kuma?
Nifa bana son matsala wlhy, duk abinda zan ɓatama Love rai bana son shi musamman a
wannan ranar ma data kasance mana ta daban.....”
      “Na sani kwantar da hankalinka, kaima kasan dai bazan bari wani abinda zai ɓata farin
cikinka faruwa ba JJ. Na faɗa maka ne kawai dan kar kaga an samu canji, dan yanzu haka ma
nariga na daidaita matsalar, wajen da aka samu yanzu ɗin ma yafi wancan komai...”
     “Amma karka manta wajen farkon muka saka a invitation card”.
    “Hakan bazai zama matsala ba shima, dan kusa-da-kusa suke, dabarar da zamuyi zamu
ajiye su Nure a ƙofar wancan hall ɗin duk wanda yazo sai su turosa inda aka canja ɗin. Yanzu
sai ka sanarma amarya kawai, ko hakan baiyi ba?”.
          “A yayi, kunyi ƙoƙari, ALLAH ya bar zumunci bari na sanar mata”.

     *_DINNER HALL_*

       Matuƙar ƙyau da ƙayatuwa wajen yayi tamkar dama tun farko nan suka shirya yin shagalin.
Kalar decoretions ɗin wajen kalar ankon ƴammatan amarya da suka sha ƙyau har suka gaji,
haka suma abokan ango shar da su. Shigowar ango da amarya ta shafe duk wani ƙyawun kowa
a wajen, dan adonsu na musamman ne. Atake hasken flash ya shiga tashi tako ina, tsakanin
wayoyi da camaras, a gefe mc na faman kwarzantasu, yayinda dj ya saki wani cool music mai
ratsa zuciya. Ta ko'ina dai taro ya cika taro kam sai masha ALLAH, abokan ango da ƙawayen
amarya nata taka rawar gani irin na bajinta tare da dangi takowace ɓangare. A yanda aka tsara
komai zaka iya saka masu bikin a layin masu hannu da shuni, sai dai sam ba haka bane ba,
ana dai tsaka tsaki, wato babu tsiya babu hamshaƙin arziƙi. Sai dai akwai rufin asirin ALLAH ta
kowanne ɓangarorin guda biyu. Anyi taro an tashi lafiya kusan ƙarfe ɗayan dare, ango na son
maida amaryarsa gida da kansa yayarta tace karya damu yaje gida ya huta zasu wuce da ita.
Babu yanda ya iya dole ya haƙura suka dunguma shi da abokansa zuwa hotel da suka kama.
Amarya da danginta suma suka wuce nasu gida dan sai gobe in sha ALLAH za'a miƙata gidan
mijinta.....

           *_WASHE GARI_*

   A kaf ƴan rakkiyar amarya babu wanda baiyi santin gidan da aka kawota ba. Dan kuwa dai
gida ya cika ya tunbatsa komai zam. Tabbas angon yayi ƙoƙari sai kuma fatan a zauna lafiya.
Bayan kammala ƴan kai da kawo na al'ada da rabe-raben kayan gara kowa ya kama gabansa
aka bar amarya da ƙawayenta. Sune suka sake gyare mata gida ana faman raha da wasa da
dariya komai ya koma kan saitinsa. Sai dai amarya bata da wani kuzari tattare da ita, ba komai
ya jawo hakan ba sai ƴar fargabar da aka san duk wata amarya kamila da ita a irin wannan
ranar, dama ita gata bamai yawan hayaniya bace, ko ƙawayen ma ba wasu ne daban ba, daga
ƴan uwa sai maƙwafta da aka tashi tare. Bayan idar da sallar magrib kowacce ta shiga sake
gyara kwalliyarta sukai zaman jiran abokan ango. Ƴan halak ɗin kam basu taushe hannu ba,
dan idar da sallar isha kaɗan suka iso gidan. Amarya dai na lulluɓe, yayinda ango yay tsallen
turare ɗan goma zuwa inda take ya zauna kusa da abarsa kamar zai rungume, itako tana ta
faman matse jiki waje guda abinka da farin shiga ga kunyar baƙunta. Suko abokan ango nata
faman masa shaƙiyanci da ido yana musu daƙƙuwa ta ƙasan riga da sakin murmushi. A haka
dai akai ƴan abubuwan daya dace tsakanin abokan ango da na amarya, zuwa tara da rabi ango
da yaga basu da niyyar basu filin ya murje idanu ya korasu waje. Sun fito suna dariya, yayinda
MB babban amininsa ya sinna masa wasu ƙwayoyin magani tare da miƙa masa gorar ruwan
hannunsa yana faman ƙyafta masa idanu da masa magana a hankali. “Adai yi tuƙi a hankali,
dan wannan motar ƙirar larabawa ce, idan bakai wasa ba amaimakon horn ƙira'ar Alkur'ani
zakaji”. A tare suka kwashe da dariya tare da cafkewa bayan ya afa maganin batare da
tambayar na miye ba ya kora da ruwa. Ango JJ ya ce, “Shege abokina, kune malaman duniya,
dan shugaban mai jan ƙyalli ma a ƙarƙashin koyarwarku yake baza komarsa”. Dariyar suka
sake kwashewa a tare, MB yay gaba yana saɓa babbar riga da faɗin, “Idan da matsala kai dai
kai kirana da wuri na turo makanike dan ka samu damar fita shan iskar yammaci, na barka

lafiya a tuna da maƙota kar'a ishesu da...” bai ƙasa ba ya wani kashe masa ido ɗaya yana
ficewa a gate ɗin. Shi dai ango JJ rufe gate ɗin yay yana cigaba da dariyarsa. Kafin ya juya
cikin gidan ransa fes yau ranar baje koli ta duniya a cikin rayuwar sa...
     Shuuu!! Aka gitta kamar ta gefensa a dai-dai yana kai hannunsa ga handle ɗin ƙofar, kamar
zai share da tunanin iskar sanyi data fara kaɗawa ce sai kuma dai ya ji an sake gitta masa yana
ƙoƙarin tura ƙofar. Wawwaigawa yay damansa da haggu sai dai kuma babu kowa, cikin nuna
halin ko'in kula ya ɗage kafaɗu da taɓe baki ya ƙarasa shigewa a falon.      “Amarya kin sha ƙamshi, amarsu baƙya laifi koda kin kashe ɗan masu gida!”. Ya jero
kalaman kirarin tamkar shine ya fara ƙirƙirarsu saboda tsaruwarsu a bakinsa kai kace waƙace a
bakin shata ko barmani coge. Bai damu da jin ba'a amsa mar ba, ya murzawa ƙofar key harda
gyara labulaye da ƙyau. Turus yaja ya tsaya ƙirjinsa na bada wani irin turururumm tamkar sautin
gangar Ado gwanja a tsakkiyar filin biki. Wayam falon babu komai, duk kayan alatun nan da aka
ƙawata falon da shi  tamkar wata almara babu su babu alamar su. (Kai ina, wannan almara ce
JJ dawo hankalinka) wata zuciya ta ayyana masa. Yawu ya haɗiye da ƙyar, tare da sakin
murmushi mai kama da kuka shi adole yana son dawo da hankalinsa jikinsa. Bakinsa na rawa
da karkarwa ya furta, “L-o-v-e!” a rarrabe yana runtse idanunsa da ƙarfi. Ba'a amsa mar ba
yanzun ma dai, dan haka ya sake ƙarfin halin buɗe ido ɗaya da ƙyar, da sauri ya sake buɗe
ɗayan ma ya shiga waige-waige yana haɗiyar yawu da sauri-da-sauri. Yanzu kam falon komai
ya dawo kamar yanda yake a da, sai dai kuma kalar kayan ta canja. (JJ! Farin ciki fa ke neman
juyar maka da brain, ka daidaita kanka mana). Kansa ya shiga gyaɗawa kamar tsohon
ƙadangare cike da son gamsar da kansa akan dole, sai kuma kamar wanda aka ingiza ya nufi
bedroom da sassarfa, yana tafiya yana waigen falon. Har ɗan datse hannunsa yake wajen
ƙoƙarin rufe ƙofar bedroom ɗin da danna mata key saboda yanda jikinsa ke rawa. Cikin dauriyar
azabar dake ratsa masa hannun da ya datsa ya jingina da ƙofar yana sauke nannauyar ajiyar
zuciya irin ta na sha da ƙyar ɗin nan. Yakai minti ɗaya a haka kafin ya dai-daita kansa da ƙyar
yana sauke ajiyar numfashi a jajjere. Kasancewar sai ka ratsa ɗan lungu daga jikin ƙofar kafin
ƙarasawa tsakkiyar bedroom ɗin sosai saboda bathroom dake a wajen ya bashi damar share
gumin ɗaya tsatstsafo masa da dai-daita yanayinsa da ƙyar sannan ya cigaba da tafiya a takun
da bai gaza huɗu zuwa biyar ba. Bedroom ɗin ƙato ne, ga kayan gado yaji masu ƙyau dan
iyayen amarya sun taka rawar gani suma. Ƙoƙarin hana kansa kallon komai yake saboda
abinda ya baro baya, dan haka ya nufi gadon kansa tsaye dan yasan dai anan zaiga amaryar
tasa sarkin kunya da nutsuwa. Sai da ya kai zaune yana faɗin, “Afuwan Love na barki ke ɗaya,
na sallami waɗan nan ƴan matsalar ne, kin san in su MB na waje bakin mutum baya hutaw......”
     Ya kasa ƙarasawa sakamakon abinda idonsa ya gane masa. Wata irin murɗaɗɗiyar macijiya
ce baƙa ƙirin an mata wata kwalliya da kalar jaja-jaja mai haske kamar ƙwan lantarki. Ba'a
labaran tatsuniyoyi da wasanni ba, ko'a film ɗin ƴan India da suka sabayin na macizai bai taɓa
cin karo da irin wannan maciji mai girma ba. Rawa jikinsa ya farayi kamar mazari, har takai yana
zamewa a saman gadon zuwa ƙasa batare daya farga ba. Gab ya kusa kaiwa ƙasa daɓar yaji
an riƙoshi...
       “D lafiya kuwa? Miya faru kake irin wannan kakkarwar har kana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa?”.
   Nutsatstsiyar muryar amaryarsa ta ratsa masa kunne, yayinda lallausan tafin hannunta da
tunda ya riƙesa a wajen dinner jiya abin ya kasa barin ransa ke riƙe da shi a yanzu ma. Kusan a
tare ita da shi suka zube a ƙasan, dan ya riga ya taho gaba ɗayansa, sannan ya fita nauyi.

Faɗowarta jikinsa ya sakashi sakin wani irin ihu tamkar wanda aka farkar a barci da ruwa mai
sanyi. Yay wani irin mamuƙeta illahirin jikinsa na rawa. A hankali ta saki ƙara da faɗin, “Wayyo D
zaka karya min awazzu.”
     Kafin yau idan yaji wannan zazzaƙar muryar tata ji yake yafi kowa sa'a a duniya. Amma a
yau maimakon hakan wani irin rawa da kakkarwa jikinsa keyi, ga zufa ta wanke masa illahirin
jikinsa tamkar wanda yay wanka. Zumut ya miƙe tamkar wanda aka zabura ya shiga
waige-waige, sam babu komai a gadon, sai ma gyaran da yasha na musamman ga filos da aka
jera a kansa tamkar an zana a takarda. Sake juyowa yay da sauri yana kallonta da nuna gadon
da yatsa, sai dai bakinsa ya kasa furta komai, sai ma rawa da pink lips ɗinsa sukeyi. Cikin
rashin fahimta take kallon gadon itama, sai kuma ta dubesa da alamar tashin hankali a tattare
da ita. “D! dan ALLAH miya faru, wlhy kana sake rikitani nikam. Jibafa yanda kake zufa. Kana
nuna min gado kuma ni banga komai ba a wajen.”
        (JJ ka nutsu, karfa ka ɓata wannan daren mai muhimmanci a gareka mana) wani ɓangare
na zuciyarsa ya faɗa cikin tsawatarwa. Kansa ya shiga jinjinawa tamkar zuciyar tasa na
kallonsa ne, ya haɗiye busashen yawu tare da sakin murmushin yaƙe ga amaryar tasa. “B..ba
komai Love, dama fa ina gwada ki ne kawai naga amaryar tawa jaruma ce ko matsoraciya.” ya
ƙare maganar yana damƙo hannunta cikin nasa da ƙyau. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi, sai
kuma ta duƙar da kanta tana ƙoƙarin janye jikinta daga nashi dan kunya. Yanayin nata ya sake
sakashi dawowa hayyacinsa da tuna masa shi ɗin fa ango ne. Ƙoƙarin haɗiye komai yake yi,
duk da hakan abune mai wahalar gaske a garesa, amma dai zai gwada yin wannan jarumtar ya
gani. Ayatulkursiyyu ya karanta a zuciyarsa yana tattofawa a kaikaice. Sai da ya tabbatar ya
ɗaure ɗakin ɗamm acewarsa, kafin ya ƙara ɗan samun nutsuwar sake maida hankalinsa ga
amaryar tasa da kanta dai ke a sunkuye.
      A karo na farko ya jawota jikinsa ya rungume tsam yana sauke tagwayen ajiyar numfashi,
yayinda ita kuma ta shiga masa rawar jiki irin na farin shiga, sai dai bata hanashi ba ko yunƙurin
janye jikinta har kusan mintuna biyu daya saketa dan kansa. “Yau dai ga ni ga Love a gida
ɗaya, ɗaki ɗaya a matsayin ma'aurata”. Ya faɗa yana sake riƙo hannunta duk biyu cikin nasa da
ƙyau tare da gyara zamansa ya fiskanceta. Murmushi ta saki tana ƙara ƙasa da kanta tare da
jan mayafinta ta rufe fuskarta. Shima sai ya saki wata ƴar siririyar dariya cike da nishaɗi, hannu
ya kai ya yaye mayafin yana mai ɗago haɓarta ta yanda zaiga fuskanta da ƙyau.. Wata
muguwar zabura yayi baya yana mai waro duka idanunsa waje jikinsa na karkarwa batare da ya
ma sani ba ya furta, “Anoosha!!”.
       Cike da salo tai masa luuu da idanu tare da sakin sassanyan murmushin da a fuska ɗaya
ya sanshi kuma ya taɓa ganinsa, bai kuma sake ganinsa ba. Tsabar kiɗimewa da shiga ruɗani
har yana bugewa da gado wajen zabura da ƙoƙarin tattara babbar rigar jikinsa alamar zai kwasa
a guje yaji caraf an riƙesa.......✍️

       *_��Tofa babbar magana, wai ango JJ mijin amaryar da ko sunanta bamu sani ba mi
shika hwaruwa ne hakanga kuma? Anya kuwa ba....�Bara dai na iya bakina abinga walle bana
hiɗi bane._*

   _Alhamdullahi inata alƙawarin gareku na yin free book ALLAH bai ƙaddara hakan ba sai

yanzu. To Amin afuwa gani zan cika alkawarin in sha ALLAH. Ina fatan wannan littafi zai
ƙawatar da ku tako wace fiska, cakwakiya, nishaɗi, ƙalubale, ƙaddara, son zuciya, kai
abubuwane da yawa ya wawuso tako wace fuska, zakuma ku fahimci saƙon da yake son
isarwa, dan salon na musamman ne, idan nace na musamman ina nufin na musamman a gaba
ɗaya musamman ɗin�.

     *Kumuje zuwa gidan ango muji yaya zai ƙare da wannan daren farko nasa, dan naga na
musamman ne fa .*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
*_Typing_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_� ��� ��_



_Shafi na biyu_


........“Ai babu gurin zuwa, saboda da hannunka ka rufe duka ƙofofin guduwar Mr JJ ango mijin
amarya Alimah”. Muryar da baya jin zai manta a rayuwarsa ta ratsa kunnuwansa. Dauriyarsa ta
ƙare, hakama ƙarfin halinsa ya kai ƙarshe. A take jikinsa ya fara rawa kar-kar. Gashi an riƙesa
irin riƙon da ko numfashin kirki ya gagara yi. Jin saukar numfashin mutum a fuskarsa ta saka shi
buɗe idanunsa da sauri. A matuƙar razane ya fasa gigitacciyar ƙarar data ɗauke numfashinsa
gaba ɗaya sai gashi ƙasa wanwar a sume.....

A firgice ta buɗe idanunta itama tamkar wadda aka farkar da ga nannauyan barci.
Waige-waige ta fara ƙirjinta na wani irin luguden daka. To ita yaushe ma barci ya ɗauketa ne, ba
yanzu babu jimawa suka shigo ɗakin nan tare da angonta JJ ba. Dan fitarsa babu daɗewa
rakkiyar abokansa ko cikakken minti biyu baiyi ba ya dawo, batama jin yabar jikin ƙofar falon.

Cike da zumuɗi da aka san duk wani ango da shi ya koma ya zauna inda ya tashi a kusa da ita.
Batare da yayi magana ba kawai ya jawota jikinsa ya rungume yana shinshinar wuyanta. Kunya
ta sakata shiga wani yanayi, a take jikinta ya fara mazari ta shiga noƙewa. Dariya ya sakar mata
cikin kunne da faɗin, “Ai yau dai kunya ta ƙare Love, miya rage kin zama matar JJ, JJ ya zama
mijinki. Please ki ajiye wannan kunyar da safe ƙya maidata dan kin san yau ɗin ta musamman
ce fa”.
Bata iya tace da shi komai ba, dan a matsanancin tsorace take ga kuma kunya. Sai dai
hakan baisa ta hanashi yin yanda yaso da ita ba. Bayan ya gama shinshinar ta ne da
rungumeta ya ɗakkota cak zuwa wannan ɗakin yana faɗin, “Yanzu dai muje muyi sallah kafin
komai ko. Dan nasan matar tawa ustaziya ce”. A karo na farko ta sakar masa murmushi, tare da tura kanta a jikinsa dan kunya takeji matuƙa
kamar me. Dan tunda take a rayuwarta bata jin wani ya taɓa riƙe mata hannu, sai a jiya wajen
dinner da JJ ya aikata hakan gareta. To ita dai tasan sun shigo ɗaki, daga haka kuma bata san
miya faruba sai ƙarar ihun nan da bata san daga ina ya fito ba da ya farkar da ita, a yanda kuma
taga kanta alamu sun nuna barci tayi. Gadon ta sakko da sauri, sai kuma tai tsamm ta dakata
saboda jin motsin ruwa a toilet ɗin ɗakin, hakan na nufin JJ na ciki kenan. Numfashi ta ɗan
sauke a hankali, tare da komawa ta zauna tana gyara mayafinta, zuciyarta na tabbatar mata
wanka ya shiga kenan, ita kuma barci ya ɗauke ta, ihun da taji kuma maybe a maƙwafta ne. To
amma abin mamakin anan taya tayi barcin? Haka cikin ƙanƙanin lokaci? Rashin amsa ya
sakata ɗan sauke numfashi kawai.. dai-dai nan JJ ya fito a toilet ɗin babu alamar wanka yayi sai
dai ko alwala. Kanta ta duƙar ganin ita yake kallo, shi kuma ya saki murmushin da har ta iya jiyo
sautinsa da ga inda take tare da faɗin, “Naga a takure kike, jeki falo ki jirani”.
Kamar mai jiran jin hakan ta mike zumbur, har harɗewa take wajen fita tana mai sauke ajiyar
zuciya, sai dai mamaki fal kanta dan sai take jin kamar wani banbarakwai hakan nan....

(Bake kaɗai ba amarya, ni kaina fa man kai na ya tsiyaye. Dan na gagara fahimtar komai,
shin JJ ɗin ne ba mutum ba ko ke kanki? Masu karatu ko akwai mai amsa min?�).

★★.....

A ɓangaren JJ ango kam zubur ya miƙa tare da sauke nannauyan numfashi alamar farfaɗowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login