Showing 15001 words to 18000 words out of 118786 words

Chapter 6 - CUTA TA DAU CUTA COMPLET BOOK by billyn Abdull .pdf

12 Jul 2025

4030

baƙin cikin cigaban rayuwata saboda ke
butulu ce. To bari kiji ki kama kanki kafin na sassaɓa miki kamanni a gidan nan. Dan wlhy kaɗan
da ga aikina ne na haɗa miki jini da majina wawuya kawai...” fuuu ya fice kamar zai tashi sama. Ragwaf Khadijah ta zube ƙasa tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya.. Tunda ta baro
gidansu ta biyo Dafeeq yau itace rana ta farko datai mahaukacin kuka na tashin hankali da har
ya saka mata masifaffen ciwon kai tare da jin wani abu kamar nadama nasan ɗarsuwa a ranta.
Dan ko daren farkonsu tayi kukan azabar da taci a hannunsa amma baiko kai kwatankwacin
wannan ba. Ita yau Dafeeq kema gorin bijirema iyayenta ta biyosa nan?, ita Dafeeq ya ɗaga
hannu ya mara. Mari fa, mari mai suna mari da har take iya jin sayin yatsunsa biyar akan
ƙyaƙyƙyawar black beauty face ɗinta. jama'a Dafeeq fa, Dafeeq ɗinta data zaɓa akan iyayenta
da karatunta. Dafeeq data yarda ta bar komai ta koma mara komai ta ɗaukesa. ya arrahaman
wannan wace irin rana ce haka da bata taɓa lissafawa a ciki lissafin rayuwarta ba. ya ALLAH
kasa mafarki takeyi ba a zahiri bane ba. Ta sake fashewa da sabon kuka mai tsananin ƙona
zuciya.....

(Hummm Khadijah kaɗan daga illar bijirema umarnin iyaye kenan. Ƴammata a dinga
sassauta soyayyar da har zata iya saka ido rufewa a bijirema iyaye�� dan zancen malam
bahaushe nan fa na NAMIJI BA ƊAN GOYE bane gaskiya ne akan wasu mazan).


★★★......


Iya jigata da galabaita JJ yayi a wannan dare zuwa safiya. Dan da salo-salo su Alimah suka
dinga firgitashi. Gaba ɗaya ya gama fita a hayyacinsa tamkar wani sabon kamu a hauka. Babu
abinda yake iya ganewa tsakanin rayuwa da numfashi. Rana da duhun dare. Duniya da lahira,
fari da baƙi. Abinda kawai ya sani a garesa komai ya gama ƙarewa kawai. Yayi masifar zama

zuru-zuru cikin ƙanƙanin lokaci. Ba shi kaɗai ba hatta gidan kansa ya gama fita a hayyacinsa
tamkar ba sabo ba, wanda aka ƙawata da kayan alatu.
Dukan gate da akeyi da ɗan ƙarfi ya sashi buɗe idanunsa da sukai masa matuƙar nauyi.
Wani irin zafi da haske suka ratsa idanunsa da jikinsa a lokaci ɗaya. Tamkar wanda aka
bulbulama wani irin ƙarfi ya miƙe zubur. Waige-waige ya fara, tabbas a tsakar gidansa yake
kusa da gate gab. Idanu ya sake warewa na tabbatarwa. Farin ciki ya sake ratsashi ganin fa da
gaske ƙofar gate ɗin ce dai. Ihu ya kurma na tsabagen jin daɗi mara misali, batare da tunanin
komai ba ya miƙe a 360 zuwa jikin gate. Ƙofar ya shiga ƙoƙarin buɗewa yana waigen bayansa
tamkar mai tsoron a biyoshi, yanda yake karkarwa da ƙyar ya iya buɗe ƙofa. Ko kallo bai yima
wanda ke tsaye gaban gate ɗin ba alamar suke knocking ya wani kwasa a bala'in guje ji kake
fiyyy-fuyyyy yana dukan iska, sai ya tafi gaba zai faɗi sai ya damƙi ƙasa ya miƙe yana waigen
bayansa....
Tuni yara da ke wasa a tsakkiyar layin suka fara kwasa a guje suma suna ihu dan ganin
ƙatoton mutum tsirara haihuwar uwarsa na gudu jikinsa yay wani irin butsaaa da ƙuraje ƙanana
tamkar jikin kada. Cikin ƙanƙanin lokaci anguwar ta ruɗe, yayinda JJ ke falfala gudun ceton rai
da iyakar ƙarfinsa. A haka ya kai har titi, bai damu da tare abin hawaba ya ɗauki titin da ƙafa.
Sake ruɗewa mutane sukai ana kiran mahaukaci-mahaukaci. A tare a tare. Sai dai ina babu mai
tarewar sai ma darewa da ake ana bashi hanya a guje. Duk da wahala da jigatar da yay
gudunsa yake sosai batare da nisan hanya da yanda mutane ke ƴar tsere akan ganinsa ya
damesa ba. Sai dai duk mai hankalin daya gansa yasan wannan gudun bana lafiya bane,
sannan ba a cikin hayyacinsa yake yinsa ba dan a haka ya isa har gidansu.
A anguwar tasu ma tunda ya shigo ta rikice da iface-ifacen yara da mata da matasa. Dole
akai dafifi wajen masa tara-tara da ƙyar aka iya kamashi. Ƴan gidansu hankalinsu yay masifar
tashi, wasu ma kuka suke dan tun fitowarsa gida su Rabi'ah dake knocking gate yazo ya wuce
su suna kuka sukai kiran iyayensu suka sanar da su. Tuni wasu sun nufo gidan nashi, sai dai a
hanya suka gamu da shi, dole suka juya gida dan ganin komi zasuyi bazasu taɓa samun kanshi
ba, ALLAH ma ya taimakesu hanyar gida ya dosa ba wani waje daban ba.....

(� Uncle JJ badai kuma ka haukace ba��).


...★...★...★....

Duk yanda ya fito da ga gida da tsananin ɓacin rai gaba ɗaya yaji zuciyarsa tai masa sanyi
a dalilin shigowar kiranta. Cike da girmamawa ya ɗaga tare da kai sabuwar galleliyar wayar tasa
iphone 14 data bashi shekaran jiyannan saman kunne yana ɗan murmushi. Sallamarsa kawai ta
amsa da faɗin “Kana ina ne babban mutum”. Wani irin murmushi ya saki mai faɗi, dan yana matuƙar jin daɗin sunan nan da take kiransa
da shi. Cike da girmamawa ya bata amsa da “Ina gida ranki ya daɗe”..
“A to bara na haƙura wannan lokacin uwargida ne ran gida ai. A gaidamin ita sai da
saf......”
Cikin sauri ya katseta da faɗin, “A haba hajiya, ai ko'a gidan giya akwai babba. Dan ALLAH
kada ki katse ki faɗa min komi kike buƙata zan miki shi yanzun nan”.

“A'a ai ba'ayi haka ba Dafeeq. Ka bari kawai gobe ma haɗu” Kainaat ta faɗa tana danne
murmushin ta.
“Hajiya bazanyi jayayya da ke ba, amma dan ALLAH ki bani umarni kawai ni mai biyayya ne
a gareki”.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali. Ta ce, “Okay dama ina son ganinka ne wlhy. Yanzu haka ma
ina office ban wuce gida ba. Idan ban takuraka ba ko zaka sameni?”.
“Yanzu-yanzu kuwa ma Hajiya in ALLAH ya yarda”. Ya faɗa cikin sauri yana komawa cikin
gidan. Ko kallon Khadijah dake durƙushe na kuka baiyi ba ya shige bedroom. Baifi mintuna
bakwai ba sai gashi ya fito cikin sabuwar shiga ta yadi mai ƙyawu sosai dan daga gani ma
kasan sabon ɗinki ne. Sake tsallake Khadijah yay yayi wucewarsa ya barta da ƙamshinsa....
A cikin abinda bai wuce mintinan arba'in ba ya iso. Sakatariyar ta ce ta tarosa har cikin
office ɗin duk da kuwa shima ya sani tunda Companyn ba baƙonsa bane ba. Tunda ya shigo
Kainaat ke masa wani irin shu'umin kallo a ƙasan ido. Tabbas Dafeeq ƙyaƙyƙyawa ne. Dan daka
ganshi kaga bafulatanin usil. Duk da har yanzu shekarunsa basu gama tsayar da shi a namiji
ba, amma kai daka ganshi kasan nan gaba ba ƙaramin ingarma za'ayi ba. Sai dai fa duk da
wannan ƙyawun nashi ko kama ƙafar Abaan ɗinta baiyi ba. Dan Abaan dabanne a cikin dubun
mazaje tsararsa ma balle Dafeeq da'a gabansa bai wuce ɗan tsako haihuwar jiya ba. Wajen
zama ta nuna masa tana mai tattare komai zuwa gefe. Batace da shi komai ba har sakatariyarta
ta ajiye masa lemo da ruwa ta fita. Taja wasu mintuna tana rubuce-rubucen ta kafin ta ɗago.
Ganin bai taɓa komai ba ta ce, “A'a babban mutum ya haka? Ko kana tsoron karna zuba maka
wani abu ne na sace ka”.
Murmushi yayi yana girgiza kai. “Kai haba hajiya wane sacewa kuma. Kawai dai bana jin
shan komai ne dan yanzu na fito daga gida”.
“Okay kace uwargida ce ta cika maka ciki dai kawai”.
Murmushi kawai shi dai yayi baice komai ba. Itama bata sake cewarba sai tasowa da tai ta
dawo kujerar kusa da shi suna facing juna. Lemon da aka ajiye masan ta ɗauka tare da ɓalle
murfin takai baki, sai da tasha kusan rabi sannan ta miƙa masa. Kasa musa mata yay ya amsa
yana godiya. Tai murmushi kawai da gyaɗa kanta. “Nasan kanata makin dalilin wannan kira na ujila. Dan haka bazan so barinka a duhu ba ko
lalube muje kai tsaye ga abinda yasa na kirakan, dan ni macece mara son kwana-kwana ko
kwalo-kwalo. Dafeeq nasan ka sanni kasan wacece ni a companyn nan. Ka mun tambayoyi bila
adadin akan ƙyautar mota da gida danai maka sati ɗaya data wuce. Hakama shekaranjiya
kamin tambaya akan waya duk dai ban amsa maka ba. To ina ganin yau ya kamata na baka
amsa da kuma dalilin komai. Da farko dai magana ta gaskiya *_SONKA_* nakeyi.....”
Da wani irin sauri Dafeeq ya ɗago manyan idanunsa yana kallonta. Sai kuma ya nuna kansa
alamar (Ni). Kanta ta jinjina masa na tabbatarwa. Batare data bashi damar cewa wani abu ba.
Ta ɗaura da faɗin, “Tabbas kai kuwa Dafeeq. Na kuma jima ina jin hakan a kanka tun randa na
fara ganinka a company ɗin nan. Sai dai nata tunanin ta yanda zan tunkareka da batun gudun
kada ka baɗa min ƙasa a ido. Amma dai na baka dama kaje gida kayi tunani dan ALLAH. Da
gaske ina sonka kuma aure nake so muyi nanda ƙanƙanin lokaci. Dan banama son mu wuce
sati biyu. Kada kuma ka damu da duk abinda za'ai na shagalin biki. Aikinka kuma zaka iya fara
zuwa wannan Monday ɗin dan na tanadar maka kayan da duk zaka buƙata da kamfani ya bada

umarnin ai amfani da su. Dan ALLAH kada kace a'a. Amma dai kaje kayi tunani akan maganata
Please. ALLAH dai yasa bazakace na maka tsufa ba”. Ta kamo hannunsa tana murmushi tare
da ɗora masa bandir na dollers. “Ga wannan ka riƙe a hannunka sai na jika. Ni yanzu zan tashi
dan na gaji jikina ciwo yake mun ina buƙatar hutu.” Ta sakar masa hannu tana miƙewa fuskarta
ƙawace da murmushi. Handbag nata mai azabar ƙyau kawai ta ɗauka da tarkacenta batare da
ta sake cewa da shi komai ba tai ficewarta a office ɗin tana murmushi..........✍️


_Na rasa mima zance akanki Kainaat_.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _* 
*_Typing_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_� ��� ��_



_Shafi na takwas_



INA ƳAN KASUWA MASU SON ƘAWATA KASUWANCINSU TA HANYAN GRAPHIC DESIGN,
DA MASU SHIRIN BIKI, KO SUNA, DA MASU SHIRIN WALIMAR SAUƘA, DA MASU SHIRIN
YIN BIRTHDAY, KAI HARMA DA MASU ANNIVERSARY

MAZA KU GARZAYO "UMMUH FARUQ GRAPHIC DESIGN "TA TANADAR MUKU DA
HAƊAƊƊUN DESIGN MASU ƘAYATAR DA MAI KALLONSU.���

KAMA DAGA
*FLYER

*3D MOCKUP LOGO
*2D MOCKUP LOGO
*NORMAL LOGO
*IMAGE LOGO
*BANA
*STICKERS
*ADVERT VIDEO
*PROFESSIONAL INVITATION
*INVITATIONS CARD
*BIRTHDAY VIDEOS
*POSTER
*CERTIFICATE.AND MORE......

CONTACT ME ON

09035390383

___________


........Cikin ƙarfin hali ta ƙarasa duka aikin da ya kamata tayi taja jikinta da ƙyar zuwa falo ta
kwanta. Sosai kanta ke mata ciwo saboda kukan da tasha. Barci ya ɗan fara figarta sama-sama
ya shigo gidan. Ciki-ciki yay sallama batare da ya kalli inda take ba. Har ya wuceta sai kuma ya
dawo da baya yana kallonta. Gabansa ne ya faɗi ganin yanda idanunta sukai tulu-tulu alamar
taci kuka, ga jijiyoyin kanta da sukai ruɗu-ruɗu suma.
“Yanzu ke akan wannan ɗan abunne kika zauna kikai kuka har idanunki suka kumbura
haka?”.
Idanun ta buɗe a hankali ta sauke kansa, maimakon amsa masa sai ma ga wasu hawayen
na zaryar sakkowa. Da sauri ya kauda kansa yana jan ƙaramin tsaki zai bar wajen ta riƙo
hannunsa caraf. Cak ya tsaya, sai dai bai juyo ya kalleta ba. Ƙasa ta zamo daga kujerar ta
durƙushe tare da sake fashewa da sabon kuka hannunta biyu riƙe da nasa. “Dan ALLAH kayi haƙuri ka yafemin, nasan nayi kuskure amma in sha ALLAHU bazan
sake ba, kada kayi fushi dani mijina na tuba”.
Idanunsa ya lumshe yana jan ajiyar zuciya, kamar bazai kulata ba sai kuma ya juyo gaba
ɗayansa. Idanu ya zuba mata na tsawon mintuna biyu. Ita dai tama durƙushe tana kuka mai ban
tausayi. Kamata yay ya miƙar, batare da yayi magana ba ya zaunar da ita a kujera shima ya
zauna. Nan ɗin ma baice komai ba ya dai zuba mata ido tana cigaba da kukan har tsawon wani
lokaci kafin ya ɗan tsuke fuska da faɗin, “Amma kin san bana son kuka ko! To na gaji daji haka
nan”.
Da sauri ta shiga goge hawayenta, dan tasan tunda ya faɗi hakan to ya huce kuma
kenan. Cikin dasashiyyar muryarta ta ce, “Nagode mijina.”
Bai tanka mataba nan ma, bata kuma damu ba ta sake cewa, “A kawo abinci? Abinda kafi so
na dafa maka”.

“Ba yanzu ba, bani ruwa kawai”. Ya amsa mata cikin sauƙaƙa murya yanzu kam.
Zaram ta miƙe baiwar ALLAH har tana cin tuntuɓe, ALLAH dai ya taimaka bata faɗi ba. Yanda
bai motsa ba haka bai tanka mata ba, sai binta da kallo da yay harta fice. Bayansa ya kai jikin
kujerar a hankali ya kwantar yana sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanunsa, tabbas yana
son Khadijah, duk da kuwa faɗa ne ya fara haɗasu, ya kuma fara jin sonta ne akan bigiren
sha'awa, dan a lokacin daya yaga mata hijjabi a wancan lokacin yay tozali da cikakken halittar
ta yaji wani abu da bai taɓa jiba akan mace ba ya tsarga masa, bayan an musu sulhu hararar
da take masa da murguɗen baki a duk sanda suka haɗu ya dasa masa soyayyarta, dan duk da
yaji sha'awarta a waccan ranar bai taɓa sama ransa wani mummunan al'amari a kanta ba.
Tabbas son Khadijah yake, ya kuma yanke shawarar su gudo suyi aure ganin iyayensu sunƙi
fahimtarsu. To a yau kuma ga Hajiya Kainaat a rana tsaka. A wata gaɓa da shi kansa yasan
yana buƙatar kuɗi, dan kuwa bashi da wani buri a mataki na biyu bayan samun Khadijah da
yaso sai mallakar dukiya. Sun baro iyayensu sun gudo nan sunyi aure, yasan dolene watarana
su buƙaci waiwayar gida, komawa da tarin dukiya a wani matsayi shine abu mafi muhimmanci
da iyayensu zasu kalla suyi saurin amsarsu. Wasu sukance idan aka samu akasi a irin auremsu
da an haihu aka koma ga iyaye sukan amsheka dan waɗan nan ƴaƴan, sai dai kuma kash shifa
magana ta gaskiya baya buƙatar haihuwa a yanzu, yo ALLAH na tuba shekararsa nawa ne ma
kwata-kwata da zai yarda ya haihu a yanzu duk ya tsofe. Ita kanta Khadijah ya barta ta fara
haihuwa ai sai tazo ta koma wata babarsa ne, shiyyasa ma yake zuba mata ƙwaya a duk sanda
ta samu ciki batare data fargaba ta sha a lemo cikin ya zube. Da ga ƙarshe daya fahimci ba
daina ɗaukar cikin zatai ba sai kawai ya saka likitan ya saka mata robar hana ɗaukar ciki tana
tsaka da magagin ɓarinta na ƙarshe, sai bayan wani lokaci idan aikinta ya ƙare zai bi wata
hanyar a sake saka mata wata batare data sani ba, dan ko zai yarda ta haihu gaskiya sai nan
da shekara goma sha biyar haka sun gama more rayuwarsu. Amma yanzu baya buƙatar takura,
ƴaƴa takurane kawai da salon tsofar da mutane, gashi ka zama wahalalle dan dole ka nemo
suci ka biya musu kuɗin makaranta idan basu da lafiya kaine, kai abunfa ba sauƙi. To amma
yanzu ga babbar dama ta samu, wato samuwar dukiya, dan duk da Kainaat ƙyaƙyawar mace ce
fara tass shi baiji zai iya sonta ba, yo dakaɗan fa Ummansa ta girmeta, dan Ummansa ta sanar
masa tana da shekara goma sha biyu akai mata aure kasancewarsu fulani, ta tare tana da
shekara sha uku, ta haifesa tanada shekara goma sha biyar, yanzu shekararsa ashirin da huɗu,
Ummansa nada shekara talatin da tara, matarnan zata iya kaiwa talatin da biyar, shekara huɗu
Ummansa ta bata fa kawai. Taɓɗi babbar magana, yo ai koda take da ƙaramin jiki duk wanda ya
kalleta yasan ba yarinya bace ba wlhy, amma kuma bazai bari damar nan ta kuɓce masa ba,
dan a yanda ya fahimceta zata iya bashi dukiya mai yawa akan son shin da take, sannan in har
ya mallaketa wannan companyn kansa da akace nata ne da tsohon mijinta ya gina mata zai iya
mallakesa batare data farga ba....”
Wani irin murmushi ya kufce masa har haƙoransa na bayyana. Idanu sosai Khadijah da tun
ɗazun ke faɗa masa ga ruwa ta kawo bai jiba ta sake zuba masa. Mamaki na ƙara baibaye
mata zuciya, dan yanayin nashi na sake tabbatar mata akwai abinda yake ɓoye matan tabbas.
Amma tana jin tsoron cigaba da masa bore, dan haka haƙuri da shanyewa ta zubama sarautar
ALLAH ido kawai ya kamata gareta a yanzu.
“Ga ruwan”.
Ta sake maimaitawa a hankali. Idanunsa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login