Showing 42001 words to 45000 words out of 118786 words

Chapter 15 - CUTA TA DAU CUTA COMPLET BOOK by billyn Abdull .pdf

12 Jul 2025

4036

da tsoro maigadi ya ce, “Hajiya bakin titi yanzu a daren nan, idan aka kamani fa? Karki
manta mace ce fa wani ma sai ya ɗauka fyaɗe namata ai”.
           “Bamu da wani zaɓi ai Dauri sai wannan. Dan wlhy kaga wannan yarinyar ta mutu a
gidan nan kaima bazaka sha ta daɗi ba. Inada dukiyar da zan iya tsallake ƙasar nan batare da
ansan ina naje ba. Wannan mahaikacin dana jajiboma kaina wlhy a daren nan zai iya haurewa
yabar garin nan shima faɗamin wanene a ruwa?”.       Rawa jikin Dauri maigadi ya fara, dan tabbas gaskiya Hajiya tafaɗa. Shiko idan hakan ta
kasance ai ya shiga uku. Kwata-kwata watansa na biyu kenan da yin aure. Amaryarsa nacan ya
baro a ƙauyensu. Kuma Hajiya tasan garinsu koya gudu zata iya saka ƴan sanda su bishi. Ɗaff
ya raba Khadijah da ƙasa cikin karkarwar jiki yay sauka zuwa ƙasa. Har cin tuntuɓe yake ga
nauyin mutum ko yace gawa dan a yanzu Khadijahn bata da banbanci da hakan. Yana sauka
Dafeeq na buɗe ƙofar ya fito, takarda ya jeho batare daya kalla sashen da yabar Khadijah ba.
“Karna tashi na ganki a gidan nan da safe. Kije na sakeki saki. Abinda zaki tarar acan ɗin ma ya
isheki daga ke har iyayen naki wawuya kawai ƴar iska. Ai ba'a haifi macen da zata maran ta
zagan na barta ba, idan kina tunanin kinyi na farko kinci riba yanzu bazaki cita ba kuwa. Dolene
kije ki ɗanɗana hukunci mafi tsauri dan nasan rabuwa dani shine mafi girman bala'i a rayuwarki,
sai dai ki wuce Legas ki kama ɗaki matsayin karuwa dan waɗan nan iyayen naki masu kama da
kafiran farko musamman ubanki ba sake kallonki zai ba”. Daga haka ya koma ciki tare da bugo
ƙofar da ƙarfi har sai da Kainaat da ke tsaye galala tana kallonsa da saurarensa ta zabura.
Takardar ta ɗauka, cikin matuƙar mamaki ta ware idanunta, dan kuwa da gaske sakin ne har

biyu ya rubuta. Ita dake shirin aje mata wajen malami akan hakan sai gashi ta samu cikin sauƙi
haka. Kai gaskiya ita ɗin ƴar baiwa she ma to. Wani shegen murmushi ta saki mai ƙayatarwa da
sanyaya zuciya, babu tausayi ko ɗar a ranta ta sumbaci takardar da kashe ido ɗaya ta ce, “Kin
zama labari a tarihin rayuwar Kainaat Khadijah. Karki damu nima kwanaki biyar ya ragen na
biyo bayanki, sai dai banbancina da ke ni wajen mijina masoyina abin alfaharina zan koma”.
Dariya ta saki, sai kuma ta dafe bakin da sauri ta sauka ƙasa da gudu. Ta sami Dauri na ƙoƙarin
buɗe ƙofar falo zai fita da Khadijah. Cike da nishaɗi ta saƙala takardar a cikin rigar Khadijahn
sannan ta buɗema Dauri ƙofar da kanta ranta fes babu tausayi ko ƙanƙani a ranta....

     (Hummm).

___________★

Sosai Anoosh ke laulayin cikin nan. Ga JJ yaƙi zuwa har kwanaki biyu sun wuce. Kullum
cikin kiransa Hajiya Lailah tare yana kawo mata uziri. Ganin an tafi sati uku baida alamar zuwa
ta fahimci yawo kawai yake da hankalinta. Ranta ya sake kaiwa ƙololiwar ɓacin da ta kasa
cigaba da riƙe abinda ke ranta ranar tai masa wankin babban bargo a waya. Tare da tabbatar
masa saita wulaƙanta rayuwarsa fiye da yanda ya wulaƙanta mutuncin ɗiyarta. Dan haka ya
saurari sammaci.
Ko tari JJ baiyi a wayar nan ba yayinda Hajiya Lailah ke masifa, sai da ta gama tsaff yaja
tsaki kawai tare da kwashewa da dariya ya ce, “Lallai Hajjaju baki san wanene ni ba kenan. Ni
kike tunanin wai ki wulaƙanta? To bissmilla ga fili ga mai doki saura sukuwa. Ƴarki kuma da kike
maganar na shiga mutuncinta ki tambayeta ai tare muka ji daɗin, hasalima da kanta take kawo
min kanta. Dan haka sai ki shirya wulaƙantani da wulaƙantata dan a tafin hannuna take saboda
ni bana ƙwaina sai da zakara Hajiya. Ki duba WhatsApp naki ga saƙonan na tura miki, sannan
ki shirya taki wulaƙantar ke da ballagazar ƴarki kafin ki shirya wulaƙantanin kinji. Dan na fahimci
kin manta duk abinda NAMIJI yayi ado ne, MACE ita ce cikin ruwa tsundum. Na barki lafiya,
idan ta haihu namiji a saka masa sunan babanta, idan mace ne kuma Lailah. Kar kuma a
haifamin bebiya dan ALLAH hhhahahah”. Ya ƙare maganar da wata irin mahaukaciyar dariya
data saka jikin Hajiya Lailah rawa. Gaba ɗaya ma ita ta kiɗime, tsabar yanda komai ke neman
juye mata ta rasa ina zata kama. Da ƙyar ta iya kaiwa zaune ta shiga WhatsApp jikinta na rawa.
Gigitacciyar ƙara ta saka mai firgitarwa tare da sakin wayar ƙasa ta sulale a sume. Da gudu
Anoosh dake kwance a ɗaki cikin bargo ta fito, zubewa tai gaban mahaifiyarta tana mai kwala
kiran sunanta da girgizata. Babu alamar numfashi a tattare da ita, baki ta sake buɗewa zata
ƙwala kiran sunanta mararta tai wani kalar masifar ƙullewa. Da sauri ta saketa tare da dafe cikin
da duka hannayenta biyu. Azaba ta sata kwanciya ta naɗe jikinta waje gudu hawaye masu zafi
na tsiyaya a idanunta. Shirun ta ya sata jiyo sautin muryarta daga cikin wayar mahaifiyarta,
sauti ne mara daɗin ji da gigitar ta tunani, duk da azabar da take ciki haka takai hannunta dake
rawa da ƙyar ta ɗauka wayar, (innalillahi...) Kawai ta iya ambata a zuciyarta wayar na suɓucewa
daga hannunta. Ɗaukewar numfashinta dai-dai da ɓallewar jini da ga jikinta tamkar an buɗe
fanfo...

Hajiya Lailah ta fara farfaɗowa gabannin asubahi, yayinda tana buɗe idanunta da ƙyar ta

saukesu akan fuskar Anoosh dake kwance hawaye duk sun bushe mata a ƙyaƙyƙyawar
fuskarta. Ƙarnin jini da laimar da taji tana ciki ya sata zabura a firgice. Sai dai da ƙyar ta iya
tashi saboda nauyin da kanta yay mata ga jiri na ɗibarta. “Ya ALLAHU Sadiyya!”. Ta kira ainahin
sunan Anoosh ɗin da ƙyar jikinta na ɗaukar sabon rawa. Hannu takai da niyyar taɓata sai dai ta
kasa, dan ƙirjinta wani irin bugawa yake da sauri-sauri. Yaraf ta koma ta kwanta, dai-dai da
shigowar wasu ƙartan maza huɗu cikin falon fuskokinsu a rufe da ƙyalle. Dishi-dishi take iya
ganinsu, amma hakan bai hanata ƙarfin halin ambaton, “Su wanene ku?”. Ba
Ƙyallen ɗaya da ga ciki ya janye daga kan tasa fuskar yana wani kalan taunar cimgam
kamar ɗan daudu. Ya kalleta sheƙeƙe yana kaiwa zaune tare da dire kakkaifar wuƙarsa ƙasa
yana jujjuyata. Wuƙar Hajiya Lailah ta zubama idanu, sai kawai bugun zuciyarta ya ƙaru. Hannu
biyu tasa ta dafe ƙirjinta, sannan ta fara magana da ƙyar. “Na roƙeku idan kashemu kuka zo yi
kada ku aikata hakan, idan kuma yazama dole ne, ni ku kasheni ku barmin yarinya ta rayu. Dan
ALLAH ku barta ko zamu samu mai mana addu'a ni da mahaifinta. Ita ɗin yarinya ce mai raunin
ji da gani, bata san komai ba sai mu da neman ilimi. Na roƙeku kumin hukuncin da duk zaku
mata duk da ban san laifin da mukai gareku ba......” tari ne ya sarƙe ta ta kasa cigaba da
magana. Maimakon suji tausayinta ma sai suka kama dariya, tare da ɗaukar wayarta suka
shiga kallon videon Anoosh da JJ dake cikin wani yanayi, sai dai ba'a ganin fuskar JJ ɗin sai
Anoosh. Wani irin ihun shaƙiyanci suka saka daya ƙara ƙarfin bugun zuciyar Hajiya Lailah, a
take ta fara aman jini. Sai lokacin sukai kanta, wanda ya buɗe fuskar tasan nan dake tabbatar
da ogansu ne ya riƙota ya rungume yana wani abu na ƴan iska da faɗin, “A bari nima na more
anan dan naga uwar da ƴar duk jirgi ɗaya ne, ba oga JJ bane kawai zaisha romon nan”.
Dariya yaran nashi suka shiga yi, babu alamar tausayi a tattare da shi ya bama yaransa
umarnin zuwa su bincike gidan duk wani abu mai muhimmanci su kawo masa shi, shi kuma ya
shiga aikata sheɗanci da Hajiya Lailah da ita tuni ma ta fita a hayyacinta dan zuciyarta ta buga.
Ko a lokacin daya ɗaga daga jikinta da alama rai yayi halinsa ma. Amma babu ko tausayi da
imani tattare da shi, da alama ma baisan ta rasuba tsinannen..
Raba jikinsa da nata dai-dai da dawowar yaransa da tarkace a hannunsu. Na takardu dana
wasu abubuwan daban-daban masu alaƙa da dukiya. Sai kuɗi da basu wuce 200k ba da suka
samu a gidan. Cikin yaransa wani yaso haikema Anoosh shima amma ganin jinin dake fita a
jikinta ya sashi haƙura cike da takaici ya shureta a ciki da shegen takalminsa yana faɗin,
“Shegiya ƴar baƙin ciki”. Komai sai da suka tattare har wayoyinsu sannan suka kunna candles
guda biyu suka ajiye a kusa da carpet da kujera, basu fita ba har sai da wutar ta fara kama
kujerar sannan suka gudu lokacin anata kiran sallar farko ta asubahi.

Ƙauri da hayaƙin wutane ya fara kai hankalin mutane masu fitowa sallar asubahi. A take
aka fara binciken ta ina hayaƙin ke fitowa. Kafin hankali ya kai gidan wuta ta fara ci sosai.
Kusan gaba ɗaya rukunin gidajen wajen aka ruɗe. Tuni har mata sun fara fitowa a guje da yara.
Kafin kace mi an ɓalle ƙofar gidan da ƙyar aka shiga, tako ina ƙoƙarin kashe wutar akeyi, dan
iya falonsu kawai ta kama bata fara zagaye gidan ba. Dalilin wani ma'aikacin ƴan kwana-kwana
dake anguwar yasa aka samu nasarar isowarsu da wuri dan shi yay waya. Zuwansu ya bada
gudunmawar samun nasarar kashe wutar akan lokaci, yayinda aka fito da Anoosh da Hajiya
Lailah jikinsu duka a saɓule ko iya shaidasu ba'ayi. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Wannan
tashin hankaline da ba'a taɓa ganin makamancinsa ba a anguwar, an wuce dasu asibiti duk da

ba'a da tabbacin ma suna numfashi. Yayinda mutanen anguwa keta faman kuke-kuke. Dan
Hajiya Lailah mutuniyar kirki ce, sannan Anoosh yarinyace mai tarin nutsuwa da hankali,
sannan a dunƙule ma rayuwarta abar tausayice ga duk mai imani kasancewarta bebiya ga
raunin gani, ga rauni na kasancewarta ɗiya mace. Kai koda maƙiyinsu a yau hankalinsa tashe
yake. Gashi babu wanda yasan danginsu sai Gwaggo kuma itama ALLAH yay mata rasuwa.
Sai kuma wanda kowa yasan Anoosh zata aura wato JJ. Dan haka ma wanda suka ɗan sanshi
musamman waɗanda Hajiya Lailah ta wakilta suka amshi kuɗin auren Anoosh hankali tashe
suka nemosa a waya, tare da faɗa masa ya maza yazo su Hajiya Lailah sunyi gobara.........✍️


_Nagode da addu'oin ku tare da kiran wayoyinku_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

*_Typing_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_� ��� ��_



_Shafi na goma sha takwas_


______________

https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr


*_Assalamualaikum warahmatullah_*

*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*

*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA
HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU
QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA
MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har
zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*
_________________________


......A matuƙar hargitse JJ ya iso anguwar. Hakan ya tabbatar da dama yana gari babu wata
Kaduna da yaje. Amma da yake su basu san komai akan batun ba sai tausayin yanda yake
kuka ana riƙesa kamar wani mace ƴan anguwar sukeyi. Da yaje asibiti yaga su Anoosh kuwa
sai ya yanke jiki ya faɗi wai ya suma. Sai da aka yayyafa masa ruwa tare da bashi gado. Dan
da gaske razana yayi ganin Anoosh bata mutu ba ita. Sai dai bata san inda kanta yake ba tana
cikin wani hali mai wahalar fassara...

JJ shine ya zama tamkar ɗan uwa na jini wajen jana'izar Hajiya Lailah, dan shine akan gaba,
sannan shine ma ake ma gaisuwar. Shine ya kawo ƴan sanda akan shi bai yardaba sai a
bincika a tabbatar da dalilin gobarar da alamu da yawa suka nuna akwai lauje cikin naɗi. Ba
komai ya saka JJ yin hakan ba sai tsoron kar Anoosh ta rayu al'amari ya zama wani abu daban.
Ƴan sanda sunyi bake-bake akan case ɗin, yayinda cikin ikon ALLAH suka samu wani ɗan
alama da ya sakasu jin cewar lallai maganar JJ nada ƙamashin gaskiya, dan haka suka jajirce
akan son binciko komai. A zahiri JJ na sake ingizasu da tsayawa tsayin daka akan binciken, a
baɗini ko hankalinsa tashe yake da bin matakan toshe komai da zai bayyana gaskiya, tsabar
son a yadda da shi ya kawo iyayen ƙaryar nan dai an ɗaura masa aure da Anoosh dan ya
tabbatar musu da akowane hali take shi dai yana sonta. An jinjina ma wannan sadaukarwa tashi
ƙwarai da gaske a anguwar, duk da ma auren an ɗaurashi ne kawai bayan idar da sallar magrib
kamar yanda ya buƙata tare da waliyansa na ƙarya. Komai na Anoosh ya koma ƙarƙashin JJ
batare da sanin kowa nashi ba, dan hatta ƴan san jin yanda akai idan sun so yin magana da shi
baya yarda sai ma ya hau musu kuka akan shi su barshi yaji da abinda ya damesa. A haka
Anoosh ta kwashe tsahon shekara kusan ɗaya kwance a asibiti. Tako ina al'umma na kawo
taimako da gudunmawa, duk kuma abinda aka bada kai tsaye a asusun JJ yake tafiya. Duk da
dai ana cire wasu ai hidimar asibitin. Tana da shekara ɗaya da wata uku likitoci suka bada
shawarar fita da ita ƙasar waje yimata wani ai. Ɗari bisa ɗari JJ ya yarda da batun, har ma an
fara shirye-shiryen hakan, sai dai kwanaki uku dayin maganar ALLAH yay mata rasuwa. Ta rasu
idanunta ƙyam akan JJ tana hawaye.
Yanke jiki JJ yay ya faɗi a wajen, sai da doctor ya tsaya kansa ya farfaɗo. Yanda yake wani
irin kukan tashin hankali dole ka tausaya masa, dan harga ALLAH da gaske kukan yake yi. An
kai Anoosh makwancinta na gaskiya JJ na a wani hali, bai kuma samu kansa ba sai a washe
gari. Kamar yanda ya zama komai a yayin rasuwar Hajiya Lailah a ta Anoosh ma dai shi akema
gaisuwar har akai addu'ar uku. Bayan ƙura ta lafa ya ɗan cigaba da zuwa anguwar har bayan
wasu watanni, dan haka gidan su Anoosh ya cigaba da kasancewa a ƙarƙashin kulawar ƴan

sanda da dattijan anguwar. JJ ma dake zuwa jefi-jefi ya rage zuwa. Watanta bakwai da rasuwa
ya haɗu da Alimah. Ƙyaƙyƙyawar yarinya mai kama da larabawan Sudan. Dan Alimah ba fara
bace, sannan bata kasance baƙa wulik ba. Mace ce har mace a tsaye da sura ga ƙyawun fuska
da ko mace ta kalleta sai ta sake kallo. Alimah dai ƙawa ce ga Rabi'ah ƙanwarsa. Department ɗin su ɗaya a F.C.E. A wata ranar
babbar salla tajema Rabi'ah yawo gida sukaci karo da JJ a ƙofar gida. Cikin masifa ya ɗago a
zatonsa a cikin ƙannensa ne. Amma sai yaci karo da halittar data nema gigita rayuwarsa. Dan
kuwa dai sumar tsaye yayi har Alimah ta gama magiyar bashi haƙuri baima san tanai ba sai da
Rabi'ah ta taɓashi ya dawo hayyacinsa. Bai iya cewa komai ba, face gyaɗa kai tamkar wani
dole. Bayan shigewarsu gida sai shima ya fasa fitar ya koma ciki. Zama yay a falo tare da su,
dukkan wani motsin Alimah akan idonsa ne. Tun ma bata farga ba har dai ta tsargu. Al'amari
kamar wasa dai sai ga magana ta zama babba, dan lokacin da Alimah da ƙanwarta suka tashi
tafiya sai JJ ya dage akan zai kaisu gida. Badan taso hakan ba ta amince aka tafi harda Rabi'ah
suka maidasu gida. Wannan shine sanadin da JJ yasan gidan su Alimah. Bayan sun dawo gida
kuma ya titsiye Rabi'ah da tambaya akan Alimah. Itako ta sanar masa komai. Tun daga lokacin
JJ ya koma kai Rabi'ah makaranta da kansa, yakan je kuma ya ɗakkota duk dan Alimah, sai dai
duk yanda yaso Alimah ta kulashi hakan ya gagara, iyakarta da shi gaisuwa matsayin yayan
ƙawarta Rabi'ah.
Irinsu JJ idan ALLAH ya tashi kamasu ba'a magana, dan kuwa dai da gaske neman
zaucewa yake akan Alimah, yayinda itako ta cigaba da jansa a ƙasa. Bawai wulaƙanci take
masa ba ko zaginsa, kawai dai bata shiga sabgarsa ne bayan gaisuwa. Taƙi kuma bashi fuskar
tunkararta koda da magana ne. Haka ya cigaba da haƙuri da jurewa dan so yakema Alimah na
gaskiya, soyayya ta aure. Har faɗama abokansa su MB yake shikam ya samu matar aure.
Hakama gidansu kowa yasan yana son Alimah. Dan danan JJ aka fara gini, sannan ya rage
abubuwa da yawa musamman akan harkar mata. Da farko iyayensa sunyi mamakin inda ya
samu kuɗin gini haka, dan filin kansa ba wannan suka sani nashi ba. Amma sai ya musu bayani
akan kasuwanci ya shiga shi da wani uban gidansa aka samu yay albarka, hasalima ubangidan
nasa ne ya bashi filin. Sanin wanda yake kira da uban gidan nashi yasaka su yarda, duk da
kuwa ya kamata a matsayinsu na iyaye su bincika uban gidan nasa tunda bawai ya wani jima
da kawoshi garesu ba ne. Amma tunda kudi na shigowa yana ɗaukar wasu daga cikin
ɗawainiyarsu sai babu wanda ya sake masa magana akan hakan.
Ya cigaba da ginin gidansa da yaƙin campaign ɗin soyayyar Alimah, wadda da ƙyar da ƙyar
ya samu ta fara kulashi. Ya fara rawar jikin kashe mata kuɗi mahaifinta ya taka masa birki,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login