Showing 24001 words to 27000 words out of 118786 words

Chapter 9 - CUTA TA DAU CUTA COMPLET BOOK by billyn Abdull .pdf

12 Jul 2025

4028

suka shiga fashewa da shi
suna roƙonta tayi haƙuri sun tuba ta yafe musu. Tamkar bata jisu ba ma ta koma jikin bango ta
maƙale.
Shugaban malaman nan ne cikin galabaita da sauke numfashi ɗai-ɗai ya ce, “Baiwar
ALLAH kiyi haƙuri. Ki sani akwai hisabi tsakanin aljan da bil adam. Yanda makomarmu take a
tsakanin aljanna da wuta haka kuma makomarku kenan. Mu bamu zo nan domin cutar dake ba.
Dan ALLAH kema kada ki cuta mana. Bamu san komai tsakaninki da Jazool ba. Amma zamu
roƙeki shima ki yafe masa, ki kuma fita a jikin matarsa dan ALLAH ki barsu suyi zaman aure
kamar kowa.....”
“Har abada hakan bazata faruba! Nace maka har abada! Har abada JJ bazaiyi aure ya
zauna da wata mace ba. Kuma bazan taɓa iya yafe masa ba!!” sai ta fashe da wani irin
mahaukacin kuka daya sake firgitasu da gigita su. Sosai tai kukan kafin ta ɗago kanta dake
lulluɓe cikin dogon gashinta tana kallonsu. Ƙasa duk sukai da kawunansu. Muryarta na rawa da
karkarwa ta ce, “Zan baku dama ta ƙarshe saboda wasu dalilai. A cikinku akwai bayin ALLAH,
akwai masu ƙananan yara, akwai masu taimakon marayu, akwai masu ƙoƙarin bautama
UBANGIJI, akwai masu ƙyautatama iyaye, akwai masu yawaita karanta Alkur'ani. Duk da dai
akwai tamtirai irin JJ kuma sun san kansu. To sunci alfarmarku, zan barku ku tafi, amma ku
sani, duk wanda ya sake gigin shiga gonata saina sabauta masa rayuwa. Alimah kuma kuje JJ
ya fara sanar muku *_WACECE ANOOSH_*, ni da kaina zanzo gareku da Alimah. Kuma ku
sanar masa ko ƙoƙarin yin ƙarya yay akan Anoosh ina gefensa zaisha mamakina, dan duk inda
yake ina a tare da shi kamar yanda zuciyarsa da jininin jikinsa ke tare da gangar jikinsa. Na
barku lafiya”. Ta wani irin harba hannunta kamar mai san ture abu. Sai gasu a tsakar anguwa an
watsosu kamar kayan wanki.
Wayyo ALLAH zo kaga yanda ƴan maza ke rige-rigen tashi suna cika wandunansu da iska.
Sai dai kaji garamm an buga ƙofar gida an shige. Wasu ma ba gidajensu suke ƙoƙarin shiga ba.
Sai mai gidan ya farga ya jawosu waje shi ya shige yana faɗin, “Tafi gidanka”. Su baba da su
Malam daba anguwar sukeba kam sun ma manta da motocinsu kowa ƙafarsa ce motarsa har
zuwa titi. Babu mai sauraren ɗan uwansa kowa ƙoƙarin tare abin hawa yake. Burinsu kawai su
gansu a nasu gidajen suma......✍️


_To Bara nayi takaina Nima dai, malam na neman ƙafar zuwa gida, ni kuma Bilyn
ku fa��_.


Mura ta rikeni kwana biyu���.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
*_Typing_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_� ��� ��_



_Shafi na goma sha ɗaya_



.......Tun daga lokacin bata da wani buri sai na ganin ta samu ciki, amma shiru kake ji malam
yaci shirwa. Tun tana irga wattani har aka koma shekaru babu amo babu labari. Kwaɗayin
samun jika ya fara damun Hajiya Maryam, da kanta ta saka Kainaat da Abaan gaba suka bar
ƙasar zuwa asibi. Doctor ya tabbatar musu Kainaat nada ƴar matsala a cikin mahaifa, dan wani
ƙurji ne ya fito mata, zasu iya mata aiki, sai dai akwai haɗari gaskiya, zakuma su iya ɗorata
akan magani idan da rabo a hakan ma ciki zai iya samuwa. Jin batun haɗari yasa Hajiya
Maryam cewa a bata magani kawai, yayinda Kainaat tace ai mata aikin ita dai, dan tana buƙatar
haihuwa tako wane hali. Amma sai Abaan ya nuna mata bata isa ba, maganar mahaifiyarsa
za'abi. Hakan ya mata ciwo matuƙa suka tattaro suka dawo gida Nigeria ta fara shan magani.
Sai dai a hakan shekaru biyu suka sake shuɗewa babu labari, dan haka Hajiya Maryam tace
Abaan ya ƙara aure, idan da rabo watarana itama Kainaat ɗin zata haifa musu. Tofa babbar
magana, wannan zance ya hargitsa kan Kainaat matuƙa, dan a duniya bayan son haihuwa abu
na biyu shine mugun son Abaan da Kainaat keyi. Tana kishinsa na hauka da ko ita mahaifiyar
tasa da ƙamwarsa baso take taga ya raɓesu ba, tana dannewa ne kawai saboda irin son da
suke nuna mata ga dukiya mai yawa ta mallaka ta dalilinsu. A dalilin wannan batun aure
Kainaat ta fara fiddo da wasu sabbin halaye a gidan marasa ƙyau, tun Hajiya Maryam na kauda
kai har dai ta fara magana, sai Kainaat ta fara mata rashin kunya. Abu kamar wasa ya fara
zame musu kamar gaba a tsakaninsu, har Kainaat na neman raba Abaan da su. Hankalin
Hajiya Maryam ya tashi matuƙa, tako miƙe kan ɗanta da addu'a ta kuma hanashi cin abincin

Kainaat dan Noor ta kamata tana zuba masa abu ranar a kitchen. Rikici tun yana ƙarami har ya
zama babba, a haka akai auren Abaan da sabuwar amaryarsa. Sai dai tunda akai aure Abaan
ya gagara kusantar matar tasa, daga baya ma ta fara wani irin ciwo maiban tashin hankali har
sai da aka raba auren. Ana cikin wannan rikici labari yazo ma Hajiya Maryam kan ainahin
iyayen Kainaat da alaƙarta da mahaifiyar Nadwa. Nan fa aka sake kwasar wani sabon rikici ta
tsare Abaan akan ya saketa, dan ba matar aure bace. Wadda zata iya gudun iyayenta saboda
suna talakawa ta canja iyaye ai komai zata iya aikatawa idan ta samu dama. Abaan baya ƙetare
maganar Mamah, dan haka babu wani ja'in ja yayma Kainaat one shika (inji gwanja ba).
Baƙin ciki da ruɗani suka rufe idanun Kainaat ta hau zagin Hajiya Maryam da tabbatar mata sai
ta sakata nadama akan raba auren nan, Noor batama san sanda ta wawwanka mata mari ba,
yayinda a take nan Abaan ya ƙara mata saki biyu suka zama uku ciff. Abin kamar almara haka
suka koro Kainaat a gidan, sai dai da yake bayin ALLAH nan sun gaji arziƙi duk abinda suka
mallaka mata basu ƙwace ba, hakama wanda ta sata duk suka barta dan su irin arziƙine
gadonsa sukai ba haye ba. Wannan shine dalilin rabuwar Abaan da Kainaat, tunda ta fito kuma
bata dai nema iyayentan ba, saima gida data saya ta tare a ciki, suka kuma cigaba da mu'amula
da su Nadwa, ga company da Abaan ya bata na kawo mata kuɗu sosai, wanda a yanzu haka
shine Dafeeq ke a ciki da kuma burin mallaka shima. Yayinda Kainaat ta aureshi da burin yin
auren kisan wuta, tare da wani burin kuma data baima zuciyarta ita kaɗai. Babban burinta kuma
shine komawa gidan Abaan, kullum saita masa text message naban haƙuri da safe, da dare
kuma na good night daban haƙurin dai. Bai taɓa nuna alamar ya gani ba balle ya kulata, bata
iya kiransa kuma alamar ya tosheta, ya kuma ɗauki matakin hana baƙuwar number kiransa.
hakama duk wani shifinsa na yanar gizo ya tosheta, amma hakan bai hanata cigaba da bibiyar
duk wani motsinsa ta hanyar yaransa ba.....


★★★_____

Ƴan gidan Baba Hakimi ne sukaima Khadijah karar taruwa a gidan sunata kwantar mata da
hankali, dan a cikin kwana biyun nan ta sake wata irin rama da baƙi tamkar ba ita ba. Bata da
aiki sai kuka, dan gaskiya tana jin kishin mijinta matuƙa. Matsala ta biyu yanda ya tattarata ya
sake watsarwa tun randa ya sanar mata zancen auren zamansu ya sake ɗaukar zafi. Takai
yama bar cin abincin nata, ya kuma daina yini a gidan gaba ɗaya, ya koma kwana a doguwar
kujera a falo. Hatta yau da zai tafi ɗaurin aurensa harya gama shirinsa ya fito ko kallonta baiyi
ba. Sai itace ke binsa da kallo kamar zata cinyesa. Dan yayi mata masifar ƙyau cikin ɗanyar
shaddar da ya saka fara tass. Ga hula ya kafa sai ƙyalli yake kamar namijin ɗawusu.
Ana ɗaura auren ya tura mata saƙo kamar haka _(Duk baƙin cikin tanda dai sai munci
waina. Masu hassada sai a haɗiyi zuciya a mutu. Dafeeq ya zama angon Hajiya Kainaat. Zaɓi
ya rage mutum ya kwantar da hankalinsa a zauna lafiya yaci arziƙi shima ko ya yanki ticket ƙofa
a buɗe take)_ sosai jikin Khadijah ya dinga rawa da ganin wannan saƙo, dole ta shige bedroom
ɗinta jin zata faɗi ga mutane a gida. Kuka taci sosai tana sake karanta saƙon kamar mai bitar
karatu, mamakin Dafeeq na neman halakata. Shin dama haka yake ko yanzu ne ya canja
saboda kuɗi? Dan ita saima yanzu take jin wacece ya aura ɗin a wajen ƴaƴan baba hakimi. Sai
dai har suka gama hirarsu batace komai ba. Jin kanta na neman fashewa ta haƙura da kukan ta

gyara fuskarta ta fito, duk da ba hira take ba tana zaune a cikin su Aunty Kareema dai daketa
cigaba da mata nasiha. Gab da magrib suna shirin wucewa gidajensu Dafeeq ya dawo gidan.
Daka ganshi kaga sabon ango, dan sai ƙamshi yake bazawa. Sama-sama ya amsa tsokanar da
suke masa babu kunya ya shige bayi yin wanka bayan ya shiga ya cire kayan jikinsa yasa
jallabiya. Ganin hankalinsa ma ba'a kansu yake ba suka tattara suka wuce zukatansu cike da
tausayin Khadijah. Koda ya fito bai kalleta ba, sai ma a gadarance yace ya tashi ta ɗiba kaya a
akwati su wuce. Da mamaki ta ce “Ina kuma?”.
A zafafe ya amsa mata da “Ban sani ba. Ban san rainin hankali. Ina faɗa miki ki tashi ki
shirya kina tambayata ma ina?”.
Karan farko taji bazata iya haɗiyewa ba ta ja masa tsaki, a tsiwace ta ce, “Babu inda zanje
to, aikin banza makwaɗaici kaw....”.
Kafin ta rufe baki taji saukar mari. Bata gama dawowa a hayyacinta ba ga sake sauke mata
wani. Sai da yay mata uku a jere masu gigitarwa sannan ya nunata da yatsa yana magana
tamkar zai haɗiyi harshensa. “K! Dan uwar ubanki har kin isa kirana kwaɗayayye? To ubanki
mai ƙaton kan nan da shegen miskilanci ne kwaɗayayye dan uwarki ƴar iska. An gaya miki nima
da sona zan ɗaukeki zuwa inda nake ne banza daƙiƙiya baƙauya da ko secondary bata iya ya
gama ba akan saurayi. Wlhy badan Hajiya ta dage atare dake gidan can ba na tafi sai kinyi
wata bama ki ganni ba balle ki iya mun rashin kunyarki na rashin tarbiyya. Zan kuma tabbatar
miki dani ƙwaɗayayyen ne ƴar baƙin ciki da hassadar cigaban wasu. Yanda ubanki ya ƙare a
talauce haka kike fata nima na ƙare ko. To sai dai ke ki ƙare a wahale wlhy, dan sai kinje, kuma
zakiga hukuncin da zan miki”.
Wani irin kuka mai cin rai da zuciya Khadijah ta durƙushe tanayi. A karo na farko tunda suka
baro gida take jin kewar yin nisa da iyayenta. Gatan da sukai musu ita da ƴan uwanta ya shiga
dawo mata a rai. A wannan halin Dafeeq ya fito cikin sabon ɗanyar shadda yana baza
ƙamshi....

_________★

Tuni anguwar su JJ ta ɗauki ɗumi akan abinda ya faru daren jiya. Dan su baba da wanda
suka bisu gulma da ƙyar suka sami kansu a safiyar yau. Masu baƙin surutu suka kasa haƙuri
suka shiga bada labari. Kowa jinjina al'amarin yake da mamakin mi JJ ya aikata haka shi kuwa
da zafi? Babu mai basu amsar nan sai JJ ɗin, shi kuma yana kwance babu lafiya. Dan mafi
yawansu ana idar da sallar asuba mazan anguwa da sama suka shiga gaisheshi kamar yanda
al'adar anguwar take. In dai baka da lafiya aka kuma sani to maza kan shiga dubaka bayan
kowacce salla daga massalaci.
Duk wanda ya shiga yakan samu JJ na kuka da ihun jikinsa naci da wuta. A taimakesa a
zuba masa ruwan sanyi kada ya ƙone. A zahiri kam babu wani abinda ke faruwa da shi.
Hankalin ahalinsa gaba ɗaya ya ƙara tashi, a take yara da manya suka taru a kansa ana masa
addu'a. Da ƙyar aka samu kansa kusan sha ɗaya na safe. Yay shiru sai wani irin mugun zufa da
yake yi dan cikin duk bayan mintuna ashirin yakam jiƙe abinda aka shimfiɗa masa kamar wanda
aka watsama ruwa, sai an ɗauke an canja da wani. Yayi wata irin muguwar rama ta tashin
hankali jikinsa yayi baƙi sosai duk da kuwa JJ fari ne sol da shi. Tuni ƙyawun fuskar nan tashi ta

gushe, baƙin sajen nan dake ɗaukar hankalin ƴammata kamar ma ya fara furfurar wahala. Baka
iya hangen komai a tattare da JJ sai ƙwala-ƙwalan idanu da haƙora tamkar dillalin aljanu. Baba
dake share hawaye cikin kasa daurewa ya ce, “Jazool mika jawoma kanka haka ne da zafi?
Mika aikata ne da har muma yake neman shafarmu? Jibeka dan ALLAH cikin kwanaki uku
kacal halittarka ta canja gaba ɗaya. Jazool ka faɗa mana mika aikatama bayin ALLAHn nan?
Wacece Anoosha? Miye haɗinka da ita da ka shiga irin wannan bala'i a dalilinta ne?”.
Duk da azabar dake ratsa JJ da wahalar ciwo a firgice ya kalli Baba jin ya ambaci sunan
Anoosh. Yaya Inusa ne ya karɓe da faɗin, “Ba kallonsa zakai ba Jazool, ka sanar mana wacece
Anoosh? Kamar yanda baba ya buƙata. Minene haɗinka da ita? Dan bayin ALLAHn nan sun
tabbatar mana da har sai ka sanar mana wacece Anoosh sannan zasu bada matarka. Dan
ALLAH ka sanar mana ko muma ƴan uwanka zamu sami nutsuwar zukata da kwanciyar
hankali. Jiba kaga Baba ko taka ƙafarsa baya iya yi saboda wahalar da mukasha tsakanin
safiyar jiya zuwa yammaci. Jibi fuskar Mujetapha yanda ya kwaye kumatu saboda gudun ceton
rai. Kalleni kaga raunuka biyu naji a tsakanin hannu da gefen cikina duk a dalilin gudun kuɓuta
daga gidanka. Dolene akwai abinda ka aikata Jazool, in ba hakaba miyyasa saboda kai duk
zamu shiga bala'in nan. Hatta su baba liman basu tsira ba suna gidajensu suna jiyyar kansu.
Mazan anguwar da gidanka yake ɗai-ɗaine jiya basuyi fitsari a wando ba banda tashin hankalin
da idanunmu ya gani. Jazool wacece Anoosh! Mika aikata mata ne!!”. Yaya Inusa ya faɗa cikin
ƙaraji da kaushin murya jikinsa har yana rawa. Shima JJ ɗin rawa jikinsa ya farayi yana mai
kallon duk wanda ke ɗakin. A ƙufule Yaya Mujee ya amshe da faɗin, “Garama ka faɗa Jazool,
kai dolene ma saika faɗa mana mika aikata. Dan tace idan ma ka ɓoye wani abu tana anan tare
damu dan akoda yaushe tana kusa da kai. Ya rage naka ka faɗa da arziƙi koka faɗa da wahala.
Dan kaga dai yanda ka koma a cikin kwana uku kacal tamkar wani dilallin aljanu. Har muma
ana neman sabauta mana rayuwa a dalilinka”.
Wasu irin hawayene masu zafi suka shiga ziraroma JJ a idanu. Tamkar wanda ake
controlling murya na rawa ya ce, “Anoosh budurwata ce. Mun haɗu a ranar babbar salla ta
shekarar 2020 da ƙarfe huɗu da rabi na yamma. Dan fitowarmu da ga salla kenan ni da su MB
a anguwar su Gwaggonsa da mukaje gaidawa.......”✍️
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
*_Typing_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_� ��� ��_



_Shafi na goma sha biyu_



..........Tafe take cikin nutsuwarta tamkar wadda ke tsoron taka ƙasar. Hijjab ne a jikinta har ƙasa
fari tas. Idanunta da siririn farin gilashi da kasancewarsa bai hana bayyanar ƙyawun idanunta
da girmansu ba gamai kallo. Sam bata da alamar hayaniya akan fuska, sannan da ga ganinta
kasan bata da yawan magana akwai kuma kunya da tarbiyya tattare da ita. “Woow! Ya arrahaman kaga wata halitta!”. SJ ya faɗa. Da ga JJ har MB ɗagowa sukai suka
kallesa. Dan su hankulansu nakan wayar JJ ne suna kallon hotunan da suka ɗauka a wajen idi.
Maimakon magana ita ya nuna musu da yatsa, dan harta gotasu kaɗan. Su dukansu babu
wanda zuciyarsa bata harba ba, sai dai kafin su farga har JJ ya zabura zumutt, tamkar
ƙyaftawar ido sai gashi a gabanta.
“Assalamu alaikum ƙyaƙyƙyawa”. Ya faɗa cikin wani irin murya mai taushi da amo. Ko
kallonsa batai ba, sai dai ta motsa jajayen ƙananun laɓɓanta da babu komai a kansu sai lips
gloss alamar amsa masa sallamarsa batare da yaji sautin muryarta ba. Rabashi tai ta wuce,
kafin ya zabura ta buɗe wani farin gate dake gab da su ta shige abinta. Kansa ya dafe cike da
takaicin kansa da kansa. Yayinda MB da SJ ke faman masa dariyar ƙeta. Yana tsaye a wajen
suka ƙaraso suna cigaba da dariyarsu. SJ ya ce, “Tuku-tuku mugun icce! daga ganin sarkin
fawa sai miya tai zaƙi. Banda ma cin amanar abota nifa na fara ganin yarinyar nan amma ka
zabura kamar wani kafilfilo kazo kamun yankan baya. To sai ka kama kanka ai dan wannan fa
ba irin motocin titi bace ba”.
Harararsa JJ ya ɗan yi, batare da yace komai ba yaja guntun tsaki ya barsu wajen. Inda
motarsu ke ajiye ya dawo, ya jingina cike da damuwa yana mai lumshe idanunsa. Sake biyosa
su MB sukai nan ma suna dariya, har sai da ya ƙufula ya shige mota. Ganin zai tada suka shige
suma, dan kaɗan daga aikinsa ya tafi ya barsu a wajen duk da kuwa motar tasu ce su uku, dan
tare suka haɗa kuɗu suka saya dan kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login