Showing 12001 words to 15000 words out of 118786 words
Chapter 5 - CUTA TA DAU CUTA COMPLET BOOK by billyn Abdull .pdf
samansu tayo baya
da hannunta sai gasu sun biyota ta dire a gaban JJ da ya sake diriricewa. Ƙular data buɗe a
ɗazun yaga shinkafa a yanzu data buɗe sai ga kunamu baƙaƙe kirin na motsi da ransu cike da
kular. Kula ta biyu mai ɗauke da miya kam wani irin abune kore shar baima san yanda zai
fassarashi ba. Kofi mai ɗauke da zoɓo kuwa ya koma jini. A yanzu Anoosh ce ta zuba kunamun
a plate, tare da koren abunnan, Alimah kuma tasa jini a kofi. Jikinsa suka sake matsowa gab
suna wani irin mugun murmushi.
“Haaah!”.
Cewar Anoosh tana ɗebo kunamun nan da wani irin zabgegen cokali zuwa bakin JJ. Kansa
ya shiga jujjuyawa hawaye na zubo masa. Tsawa mai firgitarwa Alimah ta daka masa, tuni ya
wangale bakin yana fashewa da kuka. Anoosh ta zuba masa kunamun a bakinsa. Cikin sauri ya
fara taunawa yana wani kalar ɓarkewa da kukan azaba dan suma kunamun kamar jira suke ana
zubasu suka fara ɗalla masa harbi a bakin.
Cike da shaƙiyanci Alimah ta kai hannunta saman kansa tana shafawa. “Yauwa My D
maza kaci mana kasha magani, ko kanaso Yaya Mujee ya ɗauka banji maganarsa ba. Haba
ɗan sumilmilin mijina ƙyaƙyƙyawa tauraron ƴammata moouuch!!!”. Takai masa wani irin kiss mai
shegen ƙara a gefen kumatu tare da ɗaura masa kofin nan mai ɗauke da jini cikin baki. Wata
iriyar gigitacciyar ƙara ya saki na azaba. A take ya fara zazzago harshe waje zufa na wanke
masa jiki. Sai kawai yay baya zai sume musu..
Saukar ruwa mai masifar sanyi a jikinsa ta sakashi buɗe idanunsa a hankali. Zumbur ya
miƙe yana ware idanunsa, sai kuma ya ƙwalla ƙara da faɗin, “Na shiga uku na lalace ni Jazool.
Dan ALLAH dan ALLAH azo a taimaka min. Wayyo Baba. Na roƙeku ku faɗa min ku su
wanene? Dan ALLAH Alimah ina kika san Anoosh, ta mutu fa ta mutu, kice min ba ita bace
wannan, zaku haukatani wlhy na haukace kodai mafarki nake.....”
“Ai baba bazai taɓa jinka ba anan. Bama shi ba ko maƙwaftan da ke katanga ɗaya da kai
bazasu taɓa jinka ba JJ. Ka ɗauka nan ɗin lahirarka ce, kasan kuwa ai duk wanda ya tafi lahira
ba'a sake jin labarinsa kuma. Anoosh kuwa ashe baka manta da ita ba hhhhhh” Ƙatuwar magen
dake a saman kujera zaune baƙa ƙirin da jajayen idanunta tamkar wuta ta faɗa cikin muryar
Alimah.
Gaba ɗaya ƙarfinsa ya gama ƙare wa. Ga harshensa dake masa wata irin azaba dama
bakinsa gaba ɗaya. Mugun ƙanƙame jikinsa dake karkarwa yake waje guda ko kaɗan baya
fatan ƙadangarun dake yawo cike da falon su taɓashi. Dan a rayuwa JJ na matuƙar tsoron
ƙadangare da mage. Suko sai su taho kamar zasu taɓashi, sai kuma su zagayesa suna kaɗa
kai. Gasu wasu irin tuma-tuma babu ko ƙyan kallo.
“Dan ALLAH ku kasheni kawai na huta. Ku kasheni zaifi min sauƙi da wannan azabar da
kuke min”.
“Hhhh mutuwa kuma. Ai idan ka mutu a yanzu JJ kaci riba kenan. Dan koba komai ka
kuɓuta da ga tari-tarin buhunan azaba dake zaman jiranka. Yanzu lokacin ɗaukar darasin
rayuwane bana mutuwa ba.” sai tai wani irin kuka na maguna da ya sashi fashewa da kuka. A
take ƙadangarun nan suma suka shiga rige-rigen nufar JJ. Ihu yake sosai yana ƙanƙame
jikinsa. Suko suka shiga hayesa yuuuuu kamar an kori tururuwa da ga rami. Tsaff suka
yanyamesa yanda kiyashi ke yanyame abu mai maiƙo. Wasu har cikin wandonsa da rigarsa.
Harsunansu suka shiga zarowa suka fara lasheshi. Yayinda wasu ke ƙoƙarin shiga masa cikin
bakin daya wage yana ihu iyakar ƙarfinsa. Miƙewa yay ya shiga zagaye falon yana tsalle-tsalle
da ihu da ƙoƙarin kakkaɓesu a jikinsa. Da ƙayar ya iya kama rigarsa ya saɓule ya watsar ƙasa.
Wandon ma ya saɓulesa. Cigaba yay da dire-dirensa yana kaɓar dana jikinsa. Sai da ya gama
galabaita da jigata ƙarfinsa ya ƙare tasss ya zube ƙasa yaraff sannan magen nan tai kuka
ƙadangarun suka ɓace ɓat. Gaba ɗaya jikinsa raɗaɗi yake masa na bala'i. Dan duk sun
karceshi da jikinsu da farcinansu. Da ƙyar yake numfashi idanunsa nayin kamar zasu rufe sai
dai sun gagara rufuwar. Sai buɗesu yake da rufewa kamar mai shirin suma. Ji yay ana wani
kalar siɗeshi tun daga yatsan ƙafarsa. Yunƙurin zabura yayi sai hakan ya gagara. Da ƙyar ya iya
buɗe idanunsa da sukai masa masifar nauyi da ƙyau kan abinda ke suɗesan. Wata irin
mummunar hallita ce da tunda uwarsa ta haifesa bai taɓa gani ba duniya. Jikinta tamkar jan
nama, kai irin na jaki, fuskar mutane da ƙahuna irin na shanaye. Tayi wani kalar tsaho mara
misali da daɗin kwatamtawa. Idan ta lashesa ta lasa ta lasa saita fesa masa wani irin ruwa a
bakinta mai azaba da raɗaɗi aka ciwukan nashi kamar ruwan attaruhu. Azaba ta hana JJ ko
kuka. Jikinsa kam ya gagara koda motsawa. Sai hawaye da ke rige-rigen sakko masa a
idanunsa. Zuciyarsa na addu'a da zuwan mala'ikan mutuwa ko hakan zai zama sauƙi a gareshi.
Ji yake inama uwarsa bata haifeshi a wannan duniyar ba. Inama ya mutu kafin ya girma.....
(JJ na buƙatar malamai a gidansa)
★★★★....
“Dan ALLAH ka taimakeni ka faɗamin yanda akai Husby. Wlhy gaba ɗaya zuciyata ta kasa
samun nutsuwa, a tsorace nake, a firgice nake.”
Sai da ya haɗiye laumar shinkafa da waken da ya zuba a bakinsa sannan ya saki ƴar
dariya idonsa a kanta. Cikin nuna alamar rashin damuwa ya ce, “Tsoro kuma Dijoh, minene abin
tsoro ko firgita anan. Gida fa nace miki an bamu halak malak da motar hawa ga kuma aiki da
za'a dinga biyana albashi mai tsoka. Ai nakega abin muyi farin ciki ne mara misali”. “Dafeeq wake garemu a garin nan dazai mana duk wannan? Sannan karka manta iyakar
karatunka secondary ne kawai balle muce ko girman takardunka zai baka wannan nasarar.
Dafeeq ka faɗa min gaskiya mana!”.
Yanda ta ƙare maganar kamar a tsawace ya sashi tsayawa cak da ga yunƙurin kai abincin da
ya ɗibo bakinsa ya kalleta. Spoon ɗin ya ajiye a hankali yana mai harɗe hannayensa a ƙirji ya
cigaba da kallonta. “Khadijah!” ya kirayi sunanta a hankali idanunsa na sake tsatstsareta. Nata
idanun ta rissinar ƙasa, sai kuma ta amsa shi a hankali. “Ihu fa kike min kamar?”.
“Kayi haƙuri. Wlhy hankalina ne a tashe. Ina jin tsoro Dafeeq matuƙar tsoro. Karka manta
nabar komaina da kowa saboda kai tsahon shekara uku batare da nasan yaya suka kasance
ba. Taya kake tunanin bazan shiga ruɗani ba a lokacin da naga sabon abu a wajenka tunda
nasan mun bar komai namu ne a yanzu kuma bamu da komai sai kammu.” “Humm hakane, na fahimce ki. Sai dai ki sani barin komai da mukayi bashi ke nufin bazamu
samu komai ba a gaba. Itafa duniyar nan da kike gani Khadijah tamkar tsanin hawa gini take. A
lokacin da kika bar step 1 zaki ci karo da step 2 ne har zuwa ƙarshe kafin ki kai ƙarshen ginin da
zai kaiki rufin soron. Naji bamu da wani karatu mai zurfi da zai iya bani aiki mai girma haka,
amma kada ki manta mutanen kirki basa ƙarewa, sannan nasan abinda nakeyi fa ni ba shahsha
bane.....”
“Miya kawo zancen shashanci anan kuma. Indai maganata ce nikan ta ɓata maka rai
ALLAH ya baka haƙuri. Gida da mota kuma bazan sake magana a kansu ba ALLAH ya sanya
alkairi. Ya kuma sa matakin nasararmune su ɗin”.
A ɗan gatsine ya ce, “Amin”. Da ga haka ya ɗauka spoon ɗin ya cigaba da cin abincinsa
fuskarsa a ɗaure, bai kuma sake kallonta ba duk da ita yana jin idanunta a kansa alamar shi
take kallo. Tsaff ya cinye abincin dan yana cin abinci sosai dama shikam. Batare da ya sake
mata magana ba ya miƙe ya haye doguwar kujera ya kwanta ya lumshe idanunsa. Nata idanun
kawai ta zuba masa zuciyarta na rawa sosai....
________★
“Wai mi kike shirin yi da wannan yaron da kika danƙarama wannan ƙyautar haka? Kainaat!.
Ni gaba ɗaya kin birkita min lissafi wlhy”.
Murmushi ƙyaƙyƙyawar matar da zata iya kaiwa shekaru talatin da huɗu ta saki. Sai kuma
tai wani irin juya lafiyayyar kujerar office ɗin nata da salo irin na isa da ƙasaita tana kai bayanta
kwance da lumshe idanu. Tsahon mintuna biyu kamar bazatace komai ba sai kuma ta buɗe
idanunta a hankali akan wadda tai mata tambayar. Murmushi ta sake saki da motsa lips ɗinta
dake ta shining na jambaki maroon ta ce, “Nadwa!”.
“Na'am”.
Nadwa ta amsa mata idanunta ƙyar a kanta.
“Auransa zanyi”.
Ta faɗa kanta tsaye babu shakku ko nuna damuwa balle kwana-kwana a zancen nata.
A zabure Nadwa ta ce, “Aure!! Fa Kainaat? Da wannan abun dana tabbatar kin girma da
kusan shekara goma? _Don_ ma da kuke shekarunku dai-dai da shi an miki sutu balle wannan
jaririn. To ke da baki gama idda ba ma miya kawo miki wannan tunanin haka?”.
Murmushi Kainaat ta saki tana wani limshe idanunta da sake buɗesu cike da yanga da
ƙasaita. “Nadwa kenan, ai ƙarancin shekarun nasa ne suka ja hankalina da yin hakan garesa.
Dan zan samu damar tafi da shirina yanda nake so. Rashin gama iddata kuwa ba matsala bace
tunda ba yau nace a ɗauran aure da shi ba. Ina yin sharar fage ne kawai yanzu dan so nake ina
gama idda a washe gari a ɗaura min aure da shi”.
“Hummm wannan wane irin tunani ne yazo miki na rashin mafaɗi Kainaat? Kamarki matar
riƙaƙƙen attajirin matashi ɗan ƙwalisa irin _Don Abaan_ ki rasa a inda zaki ƙare sai auren
wannan gajan yaron da ko shekarun balaga bai gama cikawa ba. Anya duniya bazata miki
dariya ba da kallon kinyi faɗuwar baƙar tasa kuwa? Ai shi kanshi Abaan zai sake jin izza da
yarda ya fi ƙarfin naki kamar yanda yay iƙirari. Uwar tashi da ƙanwarsa da suka zama sanadin
rabakun kuma sunci riba.”
Murmushi Kainaat ta saki saki mai faɗi har ƙyawawan farare haƙoranta dake jere reras na
bayyana. Idanu ta zubama aminiyar tata cike da ƙasaita. “Nadwa kenan, na fahimci har yanzu
baki gama haddace ilimi akan halayena ba kenan. Ban so nace miki komai ba a wannan gaɓar
amma ya kamata nace mikin domin ki tabbatar da ni Kainaat ba shasha bace. A tunaninki zan
iya haƙuri da 1-0 a fagen wasa ne? Ai in har ba'ai 2-0 ba sai dai ayi draw wlhy, ko kuma a tashi
babu ko ɗaya zai fi sauƙi ga abokin karawa. Bari na fito miki a mutum, saki ukun da Abaan yay
min zan gyara na sake komawa gidansa dan aure ni da shi yanzu ne zai fara. Wlhy wlhy kinji na
rantse, sai na raba Abaan da uwarsa da wannan shegiyar ƙanwar tasa mai kama da aljanu har
abada. Sai na sakashi ya wulaƙantasu fiye da yanda suka sa ya wulaƙantani. Sai na shafe
babinsu a zuciyarsa fiye da yanda ruwa ke shafe garin da aka gina akan hanyar wucewarsa.
Zan ɗanɗana musu azaba sannan na wawashe kaf abinda ya mallaka a duniya ta yanda
almajirin saman titi sai ya fisa kima da darajar kallo. Zan tabbatar musu ni Kainaat annoba ce a
rayuwarsu. Talauci ga talaka kuma ba tambari bane adone”
“Kin daina son Abaan ke nan?”.
Wata siririyar dariya ta saki mai faɗin gaske. Kafin ta furta, “Bazan taɓa daina son Abaan ba
har ranar mutuwata, sai dai kuma hakan bazai hana ni ɗan ɗana masa hukuncin laifinsa ba da
na uwarsa da ƙanwarsa dan sabo da kaza a wajena baya hana na saka mata wuƙa a maƙoshi
na yanka banza nai farfesunta na cinye”. “Humm amma kin san shi wannan yaron da kike son aure yana da mata? Sannan ba ɗan
garin nan bane zuwa sukai nan aka ɗaura musu aure a gidan hakimi saboda mugun son da
sukema juna shi da matar tasa”.
“Wannan dalilinne yasa na zaɓesa ai. Batun matarsa kuwa idan ta kwantar da hankalinta
ƙaruwarta ce. Dan bani da wata matsala da ita sai idan ta shiga gonata ne fa tabbas bazan
barta ba koda ace zaman sati ɗaya nayi niyyar yi da mijin nata kuwa. Soyayya da kike magana
kuma ni ban yarda akwaita ba. Dan naga abubuwa masu yawa a cikin idanun wannan yaron na
hatsabibanci. Inda ace sonta yake da gaskiya bazai rabota da iyayenta ya kawota nan ya aura
ba. Da sonta yake bazai dinga zubar mata da ciki ba a duk sanda ta samu....”
“What! Zubar mata da ciki fa kika ce? Ke ko ina kika san duk wannan Kainaat?”.
Wani shegen murmushi Kainaat ta saki tare da maida bayanta jikin kujerar ta wani
kwanta........✍️
_(Tofa wata sabuwa. Khadijah da Dafeeq laila da majnoon yaya dai?)._
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
*_Typing_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_ _
_Shafi na bakwai_
INA ƳAN KASUWA MASU SON ƘAWATA KASUWANCINSU TA HANYAN GRAPHIC DESIGN,
DA MASU SHIRIN BIKI, KO SUNA, DA MASU SHIRIN WALIMAR SAUƘA, DA MASU SHIRIN
YIN BIRTHDAY, KAI HARMA DA MASU ANNIVERSARY
MAZA KU GARZAYO "UMMUH FARUQ GRAPHIC DESIGN "TA TANADAR MUKU DA
HAƊAƊƊUN DESIGN MASU ƘAYATAR DA MAI KALLONSU.
KAMA DAGA
*FLYER
*3D MOCKUP LOGO
*2D MOCKUP LOGO
*NORMAL LOGO
*IMAGE LOGO
*BANA
*STICKERS
*ADVERT VIDEO
*PROFESSIONAL INVITATION
*INVITATIONS CARD
*BIRTHDAY VIDEOS
*POSTER
*CERTIFICATE.AND MORE......
CONTACT ME ON
09035390383
____________
.......“Please Kainat yaya kika san duk wannan wai?”.
“Humm Nadwa kenan. Na faɗa miki Kainaat ba shashasha bace ba ai, kin san dai bazan
jashi jikina ban san wanene shi ba. Inama da fiye da wannan game da shi, sai dai lokaci ne zai
sa ki san sauran gaba ɗaya ba yanzu ba”.
Idanu kawai Nadwa ta zuba mata cike da mamaki da tsoro. Maganar gaskiya bata son
ƙawar tata tace zata shiga tsakanin waɗan nan ma'auratan dake tsaka da cin ƙuruciyar
soyayyarsu. Amma ta santa tasan halinta, in har tace tana son abu sai ta cimma burinta a
kansa, dan ita shaidace ko akan Don Abaan da yanda ya fara sonta har sukai aure shirine
babba...
★★★.....
“Ina ganin zuwa jibi zamu koma sabon gidan can dan mu samu albarkacin juma'a”.
Da wani irin razana Khadijah ta jiyo tana kallon Dafeeq da ke magana a dake hannunsa riƙe
da rigarta data miƙa masa zai shanya a igiya. Babu alamar wasa a kan fuskarsa ga shi ya wani
tsareta da idanu. Nata idanun ta rissinar ƙasa tana ƙoƙarin saita rawar da jikinta ya fara. Sai
kuma ta shiga jinjina masa kanta dan in har tai magana sai hawayen da take riƙewa sun zubo
mata.
“Miye wani ɗaga kai baki da bakin magana ne wai? Khadijah nikam wlhy na gagara gane
miki gaba ɗaya. Da ace wani kemin wannan sabon halin naki sai na ɗauka baƙin cikine ko
hassada. Gaba ɗaya kin hana kanki zama lafiya. Ki duba fa jiya na shigo da waya gidan nan
amma koda na nuna miki baki ko taɓata ba a tsatstsaye kika wani ce ALLAH ya sanya alkairi
kika kwanta...”
Duk yanda taso riƙe kukan ta gagara yin haka a wannan gaɓar saboda yanda yake mata
magana a zafafe kamar ba Dafeeq ɗinta ba. Miƙewa tai da sauri daga gaban kayansu da sike
wankewar ta nufi ɗaki da gudu hannunta toshe da bakinta. A zafafe shima Dafeeq ya miƙe, tana
shiga falon yana shigowa shima. Wani kalar fisgota yay baya tai taga-taga zata faɗi ya
hankaɗata saman kujera. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunsa sun gama kaɗewa, cikin nunata da
yatsa tamkar zai mareta ya ce, “K! Wai mi kike nufi dani ne? Dan Kinga ina lallaɓaki kike ganin
kin samu hanyar wulaƙantani da jana a ƙasa. Ubanmi na miki ba dai-daiba anan?”.
Kuka sosai Khadijah ta sake fashewa da shi, sai kuma ta kai hannu ta hankaɗashi baya iya
ƙarfinta tana ƙoƙarin miƙewa. Taga-taga yay zai faɗi ƙasa ALLAH ya taimakesa ya dafe kujera.
“Taauuu!!”.
Kake jin wani lafiyayyen mari a fuskarta. A gigice ta dafe kuncinta tare da fashewa da wani
sabon kukan. “Dafeeq ni ka mara?!”.
“An mareki ko zaki rama? Ke har kin isa ki dinga jana a ƙasa kamar wani yaronki! Har kina da
ƙarfin min wannan abun. Ko kuma dole sai nayi abinda kike so saboda haihuwata kikayi ƴar
marasa tarbiyya”.
“Dafeeq nice ƴar marasa tarbiyyar?!”.
“Kina da ita ne. Ko ƴa mai tarbiyya ce zata bar uwarta da ubanta ta biyo namiji wata uwa
duniya. K! Nifa na fiki iya iskanci. Har ni zaki dingama