Showing 102001 words to 105000 words out of 118786 words

Chapter 35 - CUTA TA DAU CUTA COMPLET BOOK by billyn Abdull .pdf

12 Jul 2025

4029

Maman Dafeeq ɗin ke sata ta sayar basu sani ba. Dama dai kayan Ƙainaat
ne masu daraja a ciki. Ga faɗa kullum kamar kaji. Yanzu basa jin nauyin ɗaga hannuwa su
shararama juna mari. Saboda yana marinta itama take ware hannu ta sauke masa. Sai in zasu
harƙume dambe ne Babansa ya tsawatar tare da tuna musu lalurar dake jikin Kainaat ɗin....
      __________★

         Yau ta kasance weekend, dan haka tun kusan sha biyu Abaan da Khadijah suka fita
domin ɗan hutama ransu. Tunda aka kawota bayan asibiti babu inda ta taɓa zuwa sai yau.
Yawo yayi da ita sosai wajaje daban-daban da suka nema juye kan Khadijah ta sake tabbatar
da ganin Abuja yafi jinta ma. Dan wani wajen ma idan suka shiga ita mantawa take Nigeria ce
fa. Bata wani ɓoyewa taita santi abunta da nuna al'ajabinta. Shiko Abaan na mata dariya da
tsokanarta wai baƙauya. Sunsha hotuna, dan duk inda akeje cewa take suyi hoto dan ta nuna
ma su Ni'ima. Tun yana tayata shikam harya gaji ya miƙa mata wayar tasa ta cigaba da
ɗauke-ɗaukenta. Sai yamma lis suka dawo gida a gajiye. Washe gari kuma yace ta shirya zai
fara koya mata mota. Jitai kamar ta suma a zaune dan sai da ya taɓata tai firgigit. Muryarta har
rawa take ta ce, “Hamma mota fa?”.
      Murmushi ya sakar mata mai sanyi, sai kuma a hankali ya kwanto da kansa saman cinyarta.
Hannunta ya kamo yasa a ƙirjinsa ya rungume. “Ko jirgi kike son koya zan kai ki a koya miki na
sayo miki shi Khadijah. Kin san waye mijinki kuwa. K dai kawai kiyita bani farin ciki wlhy zan
zame miki fiye da bawa. Ba koyan mota kawai ba, nan da sati uku zaki fara zana waec ɗinki in
sha ALLAHU. Dan ina son ki samu kwalin Sakandire sai mu tattara inamu-inamu mu koma
abroad ki cigaba da karatunki har sai kin kammala zamu dawo. In sha ALLAHU sai kin gogema
iyayenki hawayen da kika sakasu zubarwa a shekarun baya. Sai kin zama abar kwatance.
Yanda mutane da dangi suka dinga jifanki da ALLAH wadai a shekarun baya sai sun koma
sanya miki albarka. Yaron nan daya zaluntar min ke sai kin koma kece mai taimakonsa a
rayuwa. Fatana ni dai ki zama mai gaskiya, mai amana, mai kuma jajircewa......”
      A hankali hawayen da suke kwaranyo mata suka shiga ɗiga a kan fuskarsa. Murmushi ya
saki tare da kai hannu ya share mata su. Sai kwai ta rungume kansa ta saki kukan mai ƙarfi.
Tashi yay camak ya ɗauketa yay bedroom da kayarsa. Daga haka labarin ya canja salo...

      Kamar yanda yay alƙawari ya fara koya mata mota da kansa. Sai dai a wajen koyar motar
nan ma babu abinda ake sai shan soyayya ziryan. Komai suna yinsa cike da farin ciki da
nishaɗi ne. Cikin sati guda ya fara sakar mata steering. Khadijah mai ƙwazo ce tun acan baya.
Kawai taso zubar da damarta ne a dalilin busar shaiɗan data Dafeeq. Sai dai yanzu kam
alhmdllh. Lokacin da ta cika sati biyu ai sai dai ace Alhamdullah. Bata motar ake ta fita ita kaɗai
ma. Sai dai abinda bata sani ba Abaan na biye da ita a ɓoye. Dan shi dai a tsorace yake. Sai da
ya tabbatar komai Alhmdllh sannan ya iya dinga daina binta. A haka ta fara exam. Abinka da
makarantar masu kuɗi komai ya riga ya mata da kansa, sai abinda ba'a rasaba ne ya kaita ta
ƙaƙƙarasa yi kafin farawar, ya kuma dage da koya mata abubuwa shi da Noor. Kai har Mamy
ba'a bari a baya ba ta bada tata gudunmawar. A haka dai ta fara jarabawar, cikin amincin
ALLAH kuma suka kammala lafiya. Tana cigaba da zuwa ganin doctor duk sati, dan gaskiya
zubar mata da ciki da Dafeeq ya dingayi da abinda suka saka mata a jiki yaso mata illa. Amma
Alhmdllh da yake akwai kuɗi yanzu kam Abaan ya dage sosai. Sai dai bai taɓa sanar mata
abinda Doctor ɗin ya faɗa mata game da matsalar da taso samu ba a mahaifarta. Dan har ɗan
ƙaramin aiki sukai mata batare da an warware mata al'amarin kai tsaye ba. Ya kuma gargaɗi
likitan akan kada ya taɓa sanar mata komai ya riga ya wuce kawai.

      Watansu uku da aure ya ɗauketa suka nufi Kano. Inda ta samu iyayenta cikin ƙoshin lafiya
da wadatar zuci. Ga gidansu yasha gyara sosai kamar bashi ba. Babanta na sake samun
kulawa ta musamman ashe har Egypt Abaan ya kaisa amma yace kar a faɗa mata. Sai da suka
zo ɗin nan ta sani a bakin Jamila. An buɗema Baba ƙaton store na shinkafa a bakin titi. Aiko
bawan ALLAH yay fes da shi kamar bashi ba, duk da dai har yanzu yana ɗan tafiya da sanda
haka dan ƙafarsa na shagiɗawa. Jitai kima da darajar Abaan da mahaifiyarsa ya sake girma a
idonta. Kai ita kam bata san mizata sakakankama mutanen nan da shi ba a rayuwa.
     Tururuwa matan anguwa da yara da ƴammata suka dingayi ganinta. Dan tuni anguwa ta
ɗauka Khadijah tazo a wata mahaukaciyar mota. Dan tsiyar da Abaan yay musu ita kaɗai ya
bari ta shiga anguwar tasu a wata zazzafar mota yace mata zuwa dare zai ƙaraso dan yana da
meeting a gidan gwamnati. Aifa ta janyo magana, dan har gidan su Dafeeq aka kai ma
mamarsa labari. Sai ta dinga koro mutane da zagin cin mutunci da tsinuwa. Mutane kam nata
mata dariya sun maidata mahaikaciya. Alokacin Dafeeq da Ƙainaat na asibiti sun je ganin
doctor dan sam bata jin daɗi, cikin na matuƙar wahalar da rayuwarta, gashi a bayan mahaifa, ta
kumbura matuƙa babu ƙyan gani. Koda suka dawo kuma dare yayi, Mama ta katsatstsare dan
kar Dafeeq yaji labarin Khadijah tazo. Washe gari da asuban fari ta sashi gaba suka tafi wani
ƙauye wai amsar magani, sai da tai yanda tai suka kwana acan. Sai washe gari suka dawo a
randa su Khadijah suka wuce.........✍️


*_NACE KIN MALLAKI NAKI�??._*


*_NAKI NAKE NUFI KIN MALLAKA KUWA�??_*

*_TIKITIN SHIGA JIRGIN TAWAGAR ZAFAFAN LITTATAFAN NAN NA ZAFAFA BIYAR NAKE
MAGANA SISTER KIN MALLAKA���??_*


*_KIN SAN KUWA A WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA DABBANCE. IDAN NACE DABAN INA
NUFIN DABAN A CIKIN DABAN_*


*_A 2024 ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN NAKU SUN SAKE ZUWA MUKU DA WASU SABON SALO
NA MUSAMMAN DA ƘAYATARWA AKAN FARASHI KAI SAUƘI DA RAHUSA. DAN HAKA INA
GAYA MIKI ƳAR UWA KADA KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE_*


_Littatafan sune kamar haka _.



*_KWANKWASON JIMINA....._*
_(NA MSS XOXO)_


*_GUDUN ƘADDARA_*
_( NA SAFIYYA HUGUMA)_


*_TSUSTAR NAMA....._*
_(NA BILYN ABDULL)_


*_AMEENATU_*
_(NA MAMU GEE)_




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NE_






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

*_Typing_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_� ��� ��_



_Shafi na talatin da tara_



Follow this link to join my WhatsApp community:
https://chat.whatsapp.com/F7aIYP99bGn9mIqLhjUWKR MUNA SAYAR D KAYAN KITCHEN D
FURNITURES N TURKEY D ABAYA AKAN FARASHIN SARI DA CAPSULES MASU KYAU D
INGANCI.
___________


........Rayuwa taima ango Abaan daɗi fiye da yanda yay hasashe. Hakama amarya Khadijah
dake samun kulawa a garesa da ahalinsa. Idan kaje gidan dolene rayuwar cikinsa ta burgeka
musamman yanda kowa ke girmama ɗan uwansa. Tsakanin ango da amarya kam ai ba'a cewa
komai. Dan soyayya ce mai tsafta da tarin birgewa, tuni Abaan ya kaɓar da ƴar sauran kunyar
Khadijah musamman idan an shiga daga ciki. Yanda soyayyarta tai tasiri garesa haka itama
tashi tuni ta mata shigar sauri saboda nagartattun halayensa. Bayan sun dawo Kano ya bar
ƙasar. Ya barta da damuwar rashinsa kusa da kaɗaici, sauƙinta ma ta koma zuwa wata babbar
islamiyya anan kusa da su. Sashenta kawai masu aiki ke gyarawa, nasa kuwa ita da kanta take
wannan aikin batare da jin gajiyawa ko ƙosawa ba kullum duk da baya nan. Takan shiga sashen
Mamy susha hirarsu, dan Noor ma tana zuwa aiki. Satinsa biyu ya dawo aka cigaba daga inda
aka tsaya. Ita ke tsaye kan hidimar mijinta da safe. Hakama idan lokacin ɗora abincin rana yayi
tayi musu da kanta dan in har Abaan na Abuja zuwa ake a amsar masa abincin rana daga gida
akai masa office. Dan haka nan ma ta riƙe ragamar girkin rana. Bana safe da rana kawai ba, na
daren ma ita ke shirya musu abincin mara nauyi, sannan ta koma sashensu tarbar mijinta duk
da in har ya shigo gidan ƙa'idarsa ce sai yazo ya fara gaishe da mahaifiyarsa sannan, hakama
idan zai fita sai yazo ya mata bankwana. Idan sun kamala ƴan hidimominsu kamar taimaka
masa yay wanka da sauransu zai wuce massalaci har sai anyi isha'i ya dawo. Sukan nufi
sashen Mamy ita da shi suyi dinner acan. Daga haka ai zaman hira. Goma nayi Mamy ke
korosu, wani lokacin ma tara da rabi tace suje sashensu su ƙarasa hirar acan tagode. Noor kan
dinga musu dariya dan su sunfi son ayi hirar anan. Saboda Mamy mace ce data san kanta.
Dolene ma idan ka zauna da ita komanta ya dinga birgeka. A koda yaushe cikin gyara Khadijah
take batare da Khadijahn ta farga ba. Dan ita dai sai dai kawai a bata abu ace ta shanye ko ta
ci. Ita kuma saboda biyayya bazata taɓa tambayar Mamyn minene wannan ba balle ta musa
sha kota zargi wani abu. Halayen Khadijahn na sake saka ƙaunarta a zuciyar mijinta da
mahaifiyarsa harma da ƙanwarsa ɗaya tilo data zame mata ƙawa a yanzu duk da ta girmeta.
      A wannan hali kwanci tashi Khadijah da Abaan suka cika wata goma da aure. Akan samu

sassaucin yawan faɗa ko rigima ta ma'auratan zamani, ba komai yasa hakan ba sai
kasancewar su su duka biyun masu haƙuri ne. Sannan Abaan ya girmi Khadijah nesa ba kusa
ba, takanyi abu da yawa yay masa kallon ƙuruciyace kawai ya share. Wanda kuma ya zama
dole yay magana a kansa sai ya zaunar da ita cikin nasiha ya ankarar da ita kaza ba dai-dai
bane kazane dai-dai. Hakan da yake na ƙara saka girmansa da kimarsa a wajen Khadijahn, dan
takanyi ƙoƙarin ganin ta kiyaye duk abinda zai ɓata masa rai. Takanyi waya da iyayenta a
wayarsa, dan ita har yanzu bata da waya, bai siya mataba ba kuma ta taɓa masa magana ko
nuna ta damu da son a sai mata ba duk da tana buƙatar hakan. Ko magana yake son yi da ita
idan yana office sai dai ya kira wayar Mamy yace ta bata dan yasan da rana suna a tare idan
bataje islamiyya ba. Idan kuma zatai waya da ko su Zuhrah ne tashin take amsa kota Mamy ko
Noor. Bata taɓa nuna damuwar hakan ba garesa ko waninsa ko taji a ranta ana raina mata
wayo. Sai dai ma takan ɗan ji kunyar cewa su ara mata tai wayarne wasu lokutan, koda tana da
buƙata sai kawai ta haƙura.
      Abinda Khadijah bata sani ba Abaan na gwadata ne kawai, dan Mamy tasha masa faɗan ya
saya mata waya sai yace tayi haƙuri zai saya akwai abinda yake yi ne. Mamy tasan halinsa, dan
haka ta saka masa ido kawai akan hakan. Dan daga baya itama sai ta fahimci dalilinsa akan ƙin
sayen wayar. Ana cikin haka yay tafiya waje ya barta bata jin daɗin jikinta, takuma ƙi yarda suje
asibiti, to anan ne fa shima abin ya fara cin ransa. Dan da rana dai yakan kira su Mamy su bata.
Da dare kam yana son waya da matar tasa ko zaiji raguwar kewarta da lafiyarta babu dama. Da
farko ya fara saka Noor ta bata tata, sai kuma nata saurayin yayta kira, wani lokacin kuma
sanda shi zai kira saurayin Noor ya riga ya kira sai hakan ya ƙona masa rai. Ai fa babu arziƙi
kwanansa goma sha biyu sai gashi ya dawo. Sam babu wanda yama san da dawowar tasa, dan
ita Khadijah ma ranar jikinta ya takura mata ko sashen Mamy bataje hira ba, tadai je ta gaisheta
ta dawo sashenta ta kwanta.
    Cikin barci sama-sama take jin ƙamshin turarensa na hawar mata kai. Idanunta da sukai
matuƙar nauyin barci ta buɗe a hankali. Lumshewa ta sake yi, sai kuma ta sake buɗewa domin
tabbatar da shi ɗinne ko mafarkin data saba take yi. Shi ɗinne dai ba mafarkin take ba. Tashi tai
da sauri, sai dai mi, ƙamshin turarensa na bugarta a guje ta nufi toilet sai amai. Hankalinsa ya
tashi, ya taimaka mata ta gyara jikinta suka fito yana mata faɗan ya akai take barin ƙofa buɗe
sauro na shigowa, dan shi zatonsa malleria ce, tunda yaga sanda aka kawota haka taita amai
tana zazzaɓi. Ita dai batace da shi komai ba, sai faman toshe hanci ma takeyi.
Karon farko Mamy tazo sashensu tunda Khadijah tazo gidan, itace ta fahimci halin da
Khadijahn ke ciki, tai mata tambayar ƙamshin miye bata so. Da ƙyar ta sanar musu turaren jikin
Hamma. Idanu sosai ya waro waje, mi Noor zatayi inba dariya ba. Har sai da ya harareta
sannan ya miƙe fuuu ya fita shi yaji haushi. Ita kanta Mamy sai da tai murmushi. Koda ya fitan
ma Khadijah ta kasa sukuni, dan tace har lokacin tana jin ƙamshin. Dole aka haɗa turaren wuta
da yawa Noor ta saka ako ina. Sai da aka ɗauki lokaci ga ac sannan tace ta daina ji, lokacin
kuma Mamy ta kira Abaan da tunda ya tafi sashensa bai dawo ba tace yay kiran doctor.

Duk wanda ke a cikin wannan ahali yau kasan yana cike da ɗunbin farin ciki mara misali,
dan hatta doctor daya tabbatar da ciki a jikin Khadijah yasha ƙyaututtuka. Tuni Abaan ya
rungume Khadijah a gaban Mamy babu ko kunya, turaren ko da tace bata son ƙamshinsa duk
da tsadarsa haka ya ɗauka ya bama Awwal shi, yace an bar sakawa. Sai ya koma idan ma zai

saka turare sai ta zaɓi wanda ƙamshin yay mata koda shi baya so kuwa. A haka ta cigaba da
rainon cikinta da kulawa, dan kowa tattalinta yake kamar ƙwai a cokali a gidan. Batun tafiya
karatunta kuwa dole ya tsaya dan boss yace sai ta haihu kuma. Bata damu ba, dan abinda
mijinta ke so shi take so itama. Cikinta na wata shida Ni'ima ta haihu. Da farko dai Abaan yaso ya hana zuwan, amma ta
saka masa rigima dan tunda sukai aure zuwanta ɗaya Kano bata sake ba. Sai dai Auta da
Jamila sun zo mata hutu sau biyu, yanzu haka ma so take jamilar ta dawo kusa da ita saboda
yanayin cikinta. Sai da Mamy tasa baki ya yarda taje jin cewa har Mamy zata je. Haka suka
ɗunguma sai Kano ta dabo.
Sun sami tarba ta mutunci da girmamawa. Dan Mama tata roƙon Mamy akan su sauka
anan, hakan kuwa akayi. Kasancewar ana gobe suna suka je washe gari tunda safe suka nufi
gidan Ni'ima mai jego, inda suka sami itama Zuhrah na fama da nata cikin, dan tsakaninsu da
Khadijah kaɗan ne. Babu zato sai ga Abaan, ta dinga harararsa dan bata san zai zo ba. Shiko
yana mata dariya ƙasa-ƙasa dan yana tare da su Adams ne da wasu abokansu. Yaro kuma an
masa takwara da Abaan ɗin ne. Zokaga murna wajen Khadijah da Abaan. Aiko yaron nan
yasha ƙyautuka. Suna ya ƙayatar sosai, Abaan yasa rigimar ranar zai koma da matarsa har sai
da Mamy ta tsawatar masa. Aiko yace in dai bazata koma Abuja ranar ba shima bazai koma ba
yana nan Kano har sai sanda zasu tafi. Mamy tace yaje ya ƙarata.
Kwanakinsu uku a Kano sukai shirin dawowa Abuja. Kusan sha ɗaya na safe Khadijah ta
shirya dan zuwa ta gaida wani kawunsu dake can ƙasan su. Hakan yasa Abaan da yazo yace
tazo ya kaita. Dama tare suke da Noor. Tafe suke a mota cike da nishaɗi suna hirarsu. Da wani
kalar sauri Abaan ya taka birki dan kaɗan ya rage ya buge wata yamutsatstsiyar mata goye da
yarinya a baya ta fito a wani gida a guje da icce a hannu tana ɗura ashar manya-manyan. A
harzuƙe ya taka birki, sai dai kafin yay magana sai ga wani mutum shima ya fito da nasa iccen a
hannu yana zagin shima na rashin mutunci. Matar ya wulwuloma iccen, saura kaɗan akan
Khadijah da ke ta saitinsu tayi zuru tana kallonsu kamar mai son tuna ina ta sonsu.
Tofa, an taɓo abinda Abaan bazai iya haƙuri ba, tuni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login