Showing 27001 words to 30000 words out of 118786 words
Chapter 10 - CUTA TA DAU CUTA COMPLET BOOK by billyn Abdull .pdf
burge ƴammata.
A hankali JJ ke murza steering fuskar yarinyar na masa waiwayi a cikin idanu, ko sau ɗaya
ya gagara saka baki a zancen su MB har sai da yaji SJ ya ce, “Ai inaga fa Gwaggo Ladi na
mutunci da mutanen gidan, dan ina ƙyautata zaton ko abincin data bamu take faɗin daga
maƙotan can natane masu farin gate to daga gidanne kuwa”. ƙuwww!! Kake ji JJ ya taka birki. Har sai da sukai gaba su duka suka bigi jikin motar. MB
dake baya ya dafe goshinsa yana murzawa a hasale ya ce, “JJ halan kana hauka ne nikam?
Yanzu dan ALLAH saboda mace kake neman kashemu a ranar salla”. Shima dai SJ masifar ya
balbalesa da shi, amma a mamakinsu ko'a jikin JJ, sai ma ƙoƙarin gangarawa gefen titi da yay
saboda yanda ake masa horn ya tsarema mutane hanya.
“Wai lafiya kake kuwa?”. MJ ya sake tambaya a ƙufule. Kai JJ ya girgiza musu a karo na
farko. Muryarsa na ɗan rawa ya ce, “Gidan Gwaggo zamu koma dan ALLAH”.
Kallon juna MB da SJ sukayi. Sai kuma suka kwashe da dariyar shaƙiyanci. JJ bai damu ba,
da kuma kafiya-lafiyane masifa zai fara musu. Suna ji suna gani ya karya kan mota suka koma
gidan Gwaggo Ladi. Shi ya fara fita a motar ya nufi gidan, dan ba baƙonsu bane ba kasancewar
sun saba zuwa duk salla. Wani irin zuzuzu JJ yaji sakamakon yin tozali da yarinyar nan zaune a
tsakar gidan Gwaggo tana cin abinci. Fuskarta ƙawace da wani irin murmushi da ya sake fiddo
ƙyawunta.
“Jazool kunyi mantuwa ne?”.
Gwaggo data farga da shi ta faɗa. Cikin sauri yarinyar ta ɗago kanta, dan sam ita ba ƙofa take
kallo ba. Idanu ta waro, sai kuma ta fisgi hijjab ɗinta dake saman jarkar ruwa a gefe ta shiga
kiciniyar sakawa. A dai-dai nan su MB suka shigo suna dariya. Suma turus sukai da ganin
yarinyar, sai kuma suka wayance tare da kamo hannun JJ da yay sumar tsaye baima amsama
Gwaggo Ladi tambayarta ba. Shigewar yarinyar falon Gwaggo ya Bama SJ damar matsawa
kusa da Gwaggo yana ƴar dariya. “Gwaggo ɗanki fa yay gamo, dan yarinyar nan fa ta dawo
damu”.
Da mamaki Gwaggo Ladi ta dubi hanyar falonta, sai kuma ta juyo ta kalla Sj. “Wai
Anoosh?!”.
“Wannan dai data shiga falonki yanzu. In dai sunanta kenan to ita”. Tsaff ya kwashe komai ya
sanarma Gwaggo. Murmushi Gwaggo keyi tana kallon JJ. Sai kuma ta kamo hannunsa ta
zaunar kusa da ita. “Kaga kwantar da hankalinka Jazool. In dai Anoosh ce da yardar ALLAH ka
samu kuwa. Na kuma tayaka murna dan yarinya ce mai tarbiyya da hankali. Sai dai bebiya ce
dan bata magana amma tana ji. Tana kuma iya baka amsar da zaka iya fahimta ta motsin
laɓɓanta. Zanfi kowa farin ciki da wannan al'amarin kuwa”.
Ba JJ ba hatta su MB kallon Gwaggo suke jin wai Anoosh bebiya ce. Sai dai a cikinsu babu
wanda yace komai. Gwaggo da bata lura da yanayin nasu ba ta ɗaga baki ta kira Anoosh dake
cikin falo. Kusan mintinan biyu sai gata ta fito tana rabe-raɓe. Fuskar Gwaggo da murmushi ta
nuna mata su JJ. “Anoosh waɗan nan ƴaƴana ne, sun zo min gaisuwar salla ne”. Jin jina kai Anoosh da idanunta ke ƙasa cikin gilashi tayi, sai kuma ta motsa ƙyawawan lips
ɗinta a hankali alamar gaisuwa a garesu. Gwaggo ce ta sanar dasu tana gaishesu, cikin rawar
lips suka amsa su duka, JJ kam yama kasa sai kallonta da yake kamar idanunsa zasu zubo
ƙasa......
____________★
Wani irin shurinta yay da ƙafa tare da cilla mata mayafi yace, “Tashi dan ...” ya mulmula
mata ashariya. Ganin bata da niyyar tashi yay wani irin fisgarta tana tirjewa yana janta kamar
wata dabba har waje. Kasancewar anguwar babu wuta gashi wata yay nisa ya buɗe motarsa ya
cillata baya ya rufe. Gidan ya kulle shima ya zagaya mazaunin driver yaja motar a fisge. Har
suka iso katafaren gidan Khadijah na kuka. Maigadi ya wangale musu gate ya shige. Koda ya
fito nan ɗin ma janta yay zuwa ciki kamar abar banza, a wani haɗaɗɗen falo ya shigo da ita,
ɗaki na farkon shigowa ya buɗe ya cillata ciki ya maida ƙofar ya kulle ya wucewarsa sama
abinsa...
Gaba ɗaya kukan da take ya tsaya cak saboda azabar wahalar buguwar da kanta yayi da
gado a dalilin wullota da Dafeeq yayi. Tuni goshinta ya fara ɗigar da jini saboda fashewar da
yayi. Kwanciya kawai tai yaraf tana sauke wasu irin ajiyar zuciya kamar wadda numfashinta ke
barin gangar jikinta. Kafin dogon lokaci jikinta ya ɗime da zazzaɓi mai zafin tsiya. Gab-gab ta
fara rawar ɗari saboda ac dake aiki a ɗakin. Tana kwance a cikin wannan wahalar take jin
shigowar motoci da guɗe-guɗe alamar yanzu ne ma ake kawo amaryar. Zuwa can taji sun shigo
falon. Yanda suke shewa da arerewa yasata fahimtar bama su da yawa ƴan rakkiyar amaryar.
Zuwa can taji kiɗa ya fara tashi, sai kuma ta jiyosu suna ihu da shewar ango-ango. Hakan ya
tabbatar mata da Dafeeq ne yaje inda suke kenan, da alama ma rawa yake shi da amarya
kamar yanda take ji a kalamansu. Kusan awa biyu da wasu mintinan suka ɗauka a gidan, dan
sai sha ɗaya taji gidan ya ɗauki shiru. Daga haka bata sake jin motsin kowa ba har dare ya raba
tana dai kwance a wajen jinin dake ɗiga a goshinta ya fara rinjayar idanunta alamar jiri...
A ɓangaren amarya Kainaat da ango Dafeeq kam bayan wucewar ƙawayenta su Nadwa
cak ya ɗagata daga tsakkiyar falon cikin kuɗin da suka musu liƙi yay sama da ita. Dan Kainaat
dai bata da jiki sosai can, amma fa a murjenta take suɓul-duɓul kamar alalar gwangwani. Kai
tsaye ɗakinsa ya wuce da ita suna faman sakarma juna murmushi, ya direta a tsakkiyar gadon
yana hakki, dan duk da bata da ƙiba tanada nauyi, ƙarfin haline kawai da son ya birgeta ya
sashi jurewa har ya kawota nan. Haƙuri ya bata akan bari yaje ya ɗakko wayoyinsu. Ta jinjina
masa kai tana murmushi. Gudu-gudu sauri-sauri ya dawo falon, sai da ya waiga bayansa ya
tabbatar Hajiya bata biyosa ba sannan ya durƙusa ya tattare dollars ɗin da ƙawayenta suka
musu liƙin da ƴan dubu-dubu sabbi ƙal. Taf ya cika hularsa harda dannawa da ƙyar, bakinsa a
washe dan yasan waɗan nan kuɗin ba ƙaramin kuɗi bane ba. Wayarsa da tata dake a Centre
table ya ɗauka ya koma saman bayan ya kashe fitulin falon da kwasar ledojin kayan sayen baki.
Da dabara ya zira hannu daga waje ya kashe wutar ɗakin sannan ya shiga, kai tsaye gaban
gadon yaje ya tura hularsa mai ɗauke da kudin nan ƙarƙashin gadon sannan ya ajiye sauran
kayan yana ƴar dariya da faɗin wasu maganganu wa hajiyar tashi irin shi ya kashe fitilar ne duk
a cikin soyayya. Kainaat bata damu ba, dan itama dai zuciyarta ta tafi wajen tunanin ta yanda
zata zille masa ne. Sai da ya gama ɓoye kudinsa da ƙyau ya kunna fitilar...
Anci ansha tsakanin amarya da ango. Sannan ya buƙaci suyi salla. Kai tsaye tace masa
tana period. Ƙarara taga damuwa a fuskarsa, a ranta tace shege ai maganinka zanyi, dan daga
gani mayen yaro za'ai anan. Suna haɗa ido ta sakar masa murmushi, shima dai mayar mata
yayi cikin yaƙe. Jiki babu laka ya tashi ya canja kayansa zuwa na barci, itama yaje ɗakinta ya
ɗakko mata. Amsa tai ta shiga bayi ta canja, bata fito ba sai da ta turama Abaan saƙo kamar
yanda ta saba a kullum naban haƙuri da good night. Koda ta fito bata kula Dafeeq ba ta kwanta,
dan zuciyarta ta tafi wajen Abaan ne kamar yanda ta saba a kowane dare bata iya barci sai da
tunaninsa, mafarkinsa shine abin yinta a kullum kuma. Babu zato babu tsammani taji Dafeeq a
jikinta, hankalinta ne ya tashi, ta shiga son turesa, amma ya tabbatar mata shifa ko rage zafine
sai yayi gaskiya. Bataƙi ba anan, dan koba komai tana kewar abokin rayuwarta, musamman
daya kasance ita bata iskanci ko'a yanzun.
Dafeeq shegen yaro ne, dan sai da yay yanda yay ya shagaltar da Kainaat har ya binciketa
yaji babu wani period da takeyi batare data fargaba sai jinsa tai yana ƙoƙarin kai hari.
Hankalinta ya tashi matuƙa, ta shiga turesa amma ya nuna mata shi sabon jinine, sannan ƙarfi
ba'a shekaru yake ba, namiji kuma duk ƙankantarsa dai sunansa namiji...
★ Busowar iskar asuba mai sanyi da ni'ima ta farfaɗo da Khadijah. A hankali ta shiga buɗe
idanunta tana karanto addu'a. Ganinta ba'a ɗakinta take ba ya sata maida idanunta ta rumtse
komai na dawo mata dalla-dalla. Hawayene suka shiga sakko mata, itafa har yanzu kallon
komai take kamar almara. Sannan wani gefe na zuciyarta na tabbatar mata Dafeeq ɗinta baya
cikin hayyacinsa. Dole ne matar nan asiri ta masa. Ɗari bisa ɗari ta yarda da wannan tunanin,
dan haka ta yinƙura ta tashi da ƙyar. Goshinta ta shafa, jinin ya tsaya, sai dai wajen ya mata
nauyi kuma yana mata raɗaɗi. Mikewa tai gaba ɗayanta cikin ƙarfin hali ta nufi bayi. Bata damu
da kallon ko'ina ba dan komai baya birgeta a gidan duk da ita kanta tasan ya haɗu. Ta jima tana
kallon kanta a madubi kafin ta wanke busashen jinin goshinta zuwa fuska. Ashema raunin da
taji ba wani babba bane can sosai. Alwala tayo tazo tai sallar asuba. Daga haka ta jingina da
gado ta fara rera kuka, sai da taji kanta na barazanar tarwatsewa sannan ta haƙura. Har rana ta
hasko windown ɗakin bataji motsin kowa na gidan ba, ga shi ya kulleta ta baya, dole ta haƙura
ta zubama sarautar UBANGIJI ido kawai.......✍️
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
*_Typing_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_ _
_Shafi na goma sha uku_
_ADVERT_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA
CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO,
GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL,
AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA
GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN
KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA
KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN
YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and
more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND
YOUR HOME COVERED
_____________
.........A ɓangaren amarya da ango kuwa kowa ya tashi da mabanbancin yanayi. Ango na cikin
farin ciki da nishaɗi, duk da kuwa ya shaida ya kuma tabbatar da amarya fa batako kama ƙafar
Khadijahn sa ba. Dan a daren jiya ya tabbatar da zancen nan na mata sun bambanta. Tunda
yake da Khadijah bai taɓa ganin tasha wani magani domin gyara jikinta ba yanda yake jin mata
nayi, har bincike yasha mata amma bai taɓa cin karo da komai ba. Amma yarinyar nan ALLAH
yay mata baiwa ta musamman da shi kaɗaine yasan wannan sirrin. Amarya kam da fushi ta
tashi, duk da ango yayi wasan kura da ita tamkar ba ƙaramin yaron data raina ba taji a ranta
Abaan ɗinta daban ne. A lokacin data samu kanta a hannun Dafeeq hawaye taitayi, dan gani
take taci amanar Abaan ne. Ta jima tana hawayen kafin barci ya saceta. Basu farka ba sai
yanzu da hasken rana ya hasko windown ɗakin. Itace ta fara tashi, ta zubama Dafeeq dake
barcinsa hankali kwance ido ƙurr tamkar mai son tantance wani abu a jikinsa. Zuwa can kuma
taja siririn tsaki tana ƙoƙarin sauka a gadon caraf taji an riƙe mata hannu. Da sauri ta jiyo, sai ko
suka haɗa idanu da Dafeeq. Murmushi ya sakar mata ita kuma ta ɗan kauda kanta. Lips ɗinta
dake motsi alamar tana son yin magana ya zubama ido, kamar wanda ya gama karantar abinda
take son faɗa ya wani fisgota ta dawo baya. Idanunta ta rumtse da ƙarfi, cikin son sassauta
fushinta ta ce, “Ranafa tayi, gashi bamuyi sallan asuba ba”.
Bai tanka mata ba, sai ma shigewa jikinta yay da jan bargo ya rufesu yana magana cikin
kunnenta a hankali. Idanu ta waro waje tana turesa a jikinta. Amma ko gezau, sai ma abinda
yay niyya ya fara aiwatarwa. Tana ji tana gani sai da yay yanda yake so da ita kafin ya kalleta
yana dariya cike da shaƙiyanci. “Hajjaju karfa ki manta sadaki na biya”. Harara ta zabga masa, a zuciyata tana faɗin (kaji ɗan iskan yaro. Ka biya kona biya maka)
kamar yasan mi take faɗa, ya wani lakace mata hanci da faɗin, “Duk da fa ke kika bani na biya
ni ne dai na biya a idon kowa”.
“Hummm”.
Tace kawai tana mai yunƙurawa ta tashi, da kallo ya bita harta shige toilet. Jin ta rufo ƙofar
harda murza key yay wani kalar kwashewa da dariya. Sauka yay a gadon ya jawo handbag
ɗinta mai ƙyau sosai. Tsaff ya bincike jakar, babu komai a ciki sai gold nata da ƴan kunne da
sarƙa da su awarwaro data sanyo jiya da dare, ya jima yana kallonsu kafin ya wani taune lips ya
maida ya ajiye. Da kansa ya gyara gadon, gamawarsa dai-dai tana fitowa. Baiyi magana ba ya
shige bayin. Shima dai wankan yay ya fito, bata ɗakin, ta kuma ɗauke handbag ɗinta. Salla ya
gabatar, sannan ya jawo hularsa dake ƙarƙashin gado ya shirya ƙuɗaɗen jiya tsaff ya nufi
wadrobe ya ajiyesu a ƙasan kayansa. Cikin ƙananun kaya ya shirya. Kai tsaye ƙasa ya sauka
yanata bulala ƙamshi, ɗakin da ya jefa Khadijah jiya ya nufa, yasa key ya buɗe...
Tana zaune a inda tai salla har yanzu, gyangyaɗi take ga hawaye sun bushe mata a
fuska. Idanu ya zuba mata na tsawon minti ɗaya. Haka kawai yake jin wani iri a ransa mai kama
da tausayi. Da kyar ya ture tunanin gefe dan kuwa duk abinda ya shirya bazai fasa ba. Khadijah
tana cikin plans ɗinsa akan mallakar Hajiya da komanta, sannan ita kanta Khadijah yay
alƙawarin sai yay punishing nata akan baƙin ciki da hassada da kuma maganganun data gaya
masa jiya dan nan gaba ta kiyaye. Saboda shi dai yasan wannan yaƙin da zaiyi sai tafi kowa
mora ai.
Saukar mari ya saka Khadijah farkawa a gigice. Yanda take shuri yasa Dafeeq daka mata
tsawa. Babu shiri ta nutsu, dan harga ALLAH tana tsoron Dafeeq. Saboda tafi kowa sanin baida
mutuncin. Gaidashi ta shiga yi jikinta na mazarin rawa. Bai amsa ba, sai harara daya zuba mata
ya juya zai bar ɗakin yana bata umarnin ta biyoshi. Sai da ta share hawayenta sannan ta miƙe
ta biyoshi, dan tayi alƙawarin matar nan tasa bazata taɓa ganin kukanta ba, yanda ta ƙwace
mata Dafeeq da asiri itama zata ƙwato abinta da addu'a. Babu kowa a katafaren falon, sai
ƙamshi mai daɗi da sanyin safiya. Wani banzan kallo yama Khadijah da nuna mata wata hanya.
“Ga kitchen, ki haɗama amaryata break fast mai ƙyau da daɗi, awa ɗaya na baki. Bake kina da
bakin yimin rashin kunya ba, zaki gane kuranki ne”.
Komai batace masa ba ta raɓa ta gefensa ta wuce. Da kallo ya bita ƙasa-ƙasa harta shige,
sai kuma ya kalli inda Hajiya take tsaye tamkar sai yanzu ne ya ganta. Kainaat da tun fitowarsu
da ga ɗaki itama take sakkowa ƙasa da mamaki take kallon Dafeeq da shima tun fitowar tasu ya
ganta amma ya basar. Kamar bazatace komai ba, sai kuma fuska a yamutse ta ce, “Dafeeq
wannan fa?”.
Tasowa yay ya kama hannunta, kamar wata ƴar yarinya ya kawota ya zaunar a cikin
kujera. Zama yay shima kusa da ita yana wani kwanta mata a jiki. Idanunsa a lumshe yana
shinshinar ƙamshinta ya ce, “Uwargida”.
Idanu ta waro sosai, dan duk da tasan matarsa ance mata yarinya ce batai zaton haka
sharaf ba sosai. Dan Khadijah nada ƙaramin jiki, sannan bata cika tsayi ba can. Idan ma baka
sani ba bazakace takai 19years ba yanzu. Tana kallon fuskarsa sosai ta ce, “Haba Dafeeq.
Yaya zaka saka matarka mana girki. Ni fa ban aureka dan ka wulaƙanta matarka ba, fatana ma
mu haɗe kai mu zauna lafiya”.
“Nima burina kenan hajjaju, sai dai ta nuna ita ba haka take buƙata ba. Jiya ban san
munafukin daya kai mata hotonki ba na samu bata gida da yammar nan bayan gama ɗaurin
aure. Sai bayan magriba ta dawo bata san zata saman a gida ba. Koda na tambayeta