Showing 6001 words to 9000 words out of 118786 words

Chapter 3 - CUTA TA DAU CUTA COMPLET BOOK by billyn Abdull .pdf

12 Jul 2025

4026

idanun yay da ƙyau tare
da motsa jikinsa, jin hannunsa na dama yay masa nauyi sosai ga zafin daya ratsashi saboda
fisgar da yay masa ya sashi ambaton “Wash ALLAH na”.
A karo na farko duk wanda ke ɗakin suka juyo garesa, sai kuma duk suka zabura kowa na
ambaton sunansa. Idanunsa ya sake buɗewa da ƙyau yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.
Mahaifinsu ne, sai yayunsa biyu da abokinsa MB da SJ, sai ƙaninsa guɗa ɗaya. Jin yanda suka
rufesa da tambaya da sannu ya sashi motsa bakinsa da yay nauyi a hankali ya furta, “Abba ina
ne nan ɗin?”.
“Asibiti ne Jazool, an kawoka ne baka da lafiya tun jiya”.
Yayansa ya bashi amsa cike da nuna alhini da tausayawa. Da ɗan sauri JJ ya dubi
hannunsa, ganin ruwa ake ƙara masa ya sashi yarda da zancen yayan nasa. Ƙoƙarin tashi yake

zaune sai dai ya kasa, cikin sauri MB da yayansa na biyu suka kamashi. Zaunen suka tadashi,
tare da jinginasa jikin bango da Nuhu ya gyara filo suna cigaba da masa sannu. Kai kawai yake
iya gyaɗa musu shi dai, ransa fal mamakin miya kawosa asibiti shi kam.. Idanunsa ya rufe ruf,
tamkar wanda ake sarrafawa da remote sai kuma ya buɗe da sauri jin abinda MB ke faɗa... “Sannu kaji abokina, gaba ɗaya ka ɗaga mana hankali, amarya da ya kamata ace ita ke
jiyya sai kuma kai a naku labarin amarcin ya juye kaine kwance a gadon asibiti? Ni dai ALLAH
yasa ba pills ɗin dana baka bane ya jawo maka wannan bala'in tun jiya ake abu ɗaya kamar
bazaka rayu ba”. Rawa jikin JJ ya farayi, ya ɗan juya ya dubi sashen da Abba da Yayunsa suke, can ya
hangosu a bakin ƙofa alamar magana sukeyi, sake maido idanunsa yay kan MB da SJ dake
tare da shi kawai. Muryarsa na ɗan rawa ya ce, “Yaushe aka kawoni nan? Waye kuma ya
kawoni?”. SJ ne ya bashi amsa yanzun kam da “Tun jiya da safe aka kawoka. Amaryarka ce kuma tai
kiran Rabi'ah tana kukan cewar azo a taimaketa ka mutu kamar yanda Nuhu ya sanar mana.
Hankali tashe su Yaya Mujee suka nufi gidanka. Inda aka taddaka yashe a ƙasa baka numfashi
kuma duk an jimaka ciwo a fuska da jikinka kamar da farauta, itama amaryarka jikinta duk jinin
da yake biyo mata ta hanci da gefen baki alamar dukanta akai...”
Da wani irin gudu abinda ya faru tun daga barinsu gidan zuwa komawarsa ciki ya shiga
dawo masa. A take jikinsa ya fara kakkarwa. Muryarsa dake a disashe na rawa ya ce, “Duka?
Ita Alimah ɗin?”.
“Ƙwarai da gaske, dan tare ma aka kawoku asibitin nan, sai dai ita tun jiyan aka sallameta
bayan Doctor ya dubata sosai, ya kuma tabbatar da marinta akai bakinta da ya fashe, jinin
hancin kuma haɓo ne tayi. Kaiko an yayyageka da farauta ne aka jijji maka ciwukan nan. Dalilin
sumanka ne dai har yanzu basu ce komai akansa ba, dan jiyan ma da ƙyar aka samu ka farfaɗo
kusan sha biyun dare, shine sukai maka allurar barci sai yanzu ne kuma kake farkawa”.
Cikin rawar lips mamakin zantukan MB ras akan fuskarsa ya buɗe baki zaiyi magana, sai
dai shigowar likita tare da Abbansa da yayunsa ya hanashi cewa komai. Duk fita likita yace suyi,
yayinda shi kuma ya shiga duddubashi yana jera masa tambayoyi akan yanda yake ji a yanzu.
Da ƙyar ya iya bama likitan amsa da cewar shi yanzu baijin komai, sai kansa da yay masa nauyi
da kuma mararsa.
“Insha ALLAH suma zasu sakeka. Ciwon kan normal ne na daɗewa da kai a sume. Na maran
ne dai ƴar damuwa itama kuma bamai tada hankali ba. Da ka samu kasancewa da matarka
zaka koma normal. Pills daka sha ne suka haifar maka da hakan. Amma sai ka kiyaye gaba dan
bincikenmu ya tabbatar mana daka jima kana amfani da irinsu, hasalima ƙarfin maganin da
rashin sauke nauyin da suka saukar maka ne ya haddasa maka sumar nan kayi kuma nauyin
farfaɗowa. Ka godema ALLAH ma kuma da baka samu haikema yarinya a wannan yanayin ba
tunda naji ance amarya gareka, dan ƙarfin maganin nan zai iya sawa ka mata babbar illa
musamman idan ta kasance virgin. Dan ALLAH ku dinga bincike akan abu kafin kuyisa, dan
hakan wautace sosai. Musamman idan mukai dubayya da su yaran da ake kai muku basu san
komai ba, binsu a hankali akafi buƙatar kuyi tunda al'amarin ba damben gwada ƙwanji bane ba.
Kaga gashi nan wajen ceton kanta ta jijji maka ciwo itama ka jimata ciwon ta hanyar marinta da
kayi. Hakan ai kaga baida amfani sam a daren farko fa kuma....” Likitan ya ƙarasa maganar
cikin zafi-zafi. Shi dai JJ kallonsa kawai yake kansa a wani irin juye. Dan gaba ɗaya yama

gagara auna maganar doctor ɗin a muzubin hankali kona fahimta. Shi harma a yaushe yay
yunƙurin yin wani abu da Alimah. Ya san dai yasha pills kam tabbas, yana kuma cike da ɗokin
yin shagalinsa, amma bai ko ɗau hanyaba. Kai shi bama wannan ba fa, abinda ya faru
tsakaninsa da Alimah ɗinne abu mafi girman ɗaga hankali da buƙatar yin tunani, sai kuma
yanda yaji labarin na neman canja kansa zuwa wani bigire daban a bakin wannan likitan. Ɗan
zabura yay zai sauka a gadon har yana buge likitan. Da mamaki ya ɗago da ga rubutun da yake
ya dubesa, ganin yana neman direwa a gadon yay saurin riƙesa da faɗin, “Ya ALLAHU! Lafiya
kuwa?”.
“Babu ita Doctor, Alimah nake son gani”.
A halin da JJ ke ciki da yanda Doctor ya fahimci al'amarin akwai banbanci, dan haka yay
murmushi yana ɗan laɓe bakinsa. “To baban soyayya kwantar min da hankalinka nan Please.
Indai amaryace yanzu zaka ganta har nan inda kake duk da ma dai zamu sallameka ne muma
kaje gareta a yau ɗin nan in sha ALLAHU kaji”. “Doctor plea....”
“Shiii!!!” doctor yay saurin katsesa. Daga haka ya juya yana fuskantar ƙofar da faɗin, “Zaku
iya shigowa”.........✍️


_�To JJ dai ALLAH yasa kar a nuna hali anan ma_


https://chat.whatsapp.com/ImF9JpXmBISJCvMBGkTKLc


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

*_Typing_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_� ��� ��_

_Shafi na huɗu_



https://chat.whatsapp.com/ImF9JpXmBISJCvMBGkTKLc


........Dafeeq dai shima ɗaya ne daga cikin ɗaliban makarantar su Khadijah. Yaro ne mai ƙwazo
da maida hankali a karatu sai dai baya jin magana. Shekara ɗaya ne tsakaninsa da Khadijah a
makarantar, dan shi a yayinda ta shiga ss2 shi kuma sune suka shiga ss3. Yana ɗaya daga
cikin waɗanda aka bama prefect, yana kuma cikin masu manyan muƙami. Sun haɗu ne a
sanadin sayayyar kayan ƙwaɗayi da aka san ƴan makaranta a lokacin break. Tana tsaye gaban
mai awara ita da ƙawarta Aminatu Dafeeq ya iso wajen tare da tawagarsa su huɗu shi na biyar.
Shine a gaba suna take masa baya tamkar wani saraki ko malami. Hakan ba sabon abu bane,
dan Dafeeq suna ɗaya daga cikin tsagerun ɗalibai, sai dai ƙoƙarinsa yasa malamai basa iya
masa komai. Tunda ya shigo makarantar kuma da rashin kunyarsa ya shigo, dan baifi sati ɗaya
ba wani prefect ya dakesa akan makara a wajen ya riƙe bulalar ya murɗesa ya amshe shi ya
shiga zabga masa. Al'amarin ya bama kowa mamaki, dan kowa yasan dai akwai seniority a
school ɗin musamman prefect nada ƙarfin iko sosai akan hukunta na ƙasa da su. Abinda yay
yasa sauran prefect ɗin dake wajen rufesa da duka har sai da malamai suka fito aka dakatar da
su da ƙyar. An hukuntashi akan wannan laifin tare da bashi suspecsion har na sati biyu, bayan
yaje yayo babansa da aka buƙaci gani yazo ya bada haƙuri. Tun daga wannan abun da yay ƴan
ss3 suka tsanesa, hakama ss2 suna cike da burin sauke masa iskancin kansa. Adalilin hakan
yasha wahala sosai a cikin makarantar shima kuma ya wahal da wanda suke wahal da shi ɗin.
Dan babu fashi ka dakesa a cikin makaranta kai kuma a waje zai saka a maka duka ko kuma
shi ya maka da kansa. Daga baya ma daya haɗa daba sai yazam tare suke aikin su biyar.
Wannan tsagerancin nasu da ƙoƙarin ya sakasu yin ƙaurin suna a school ɗin. Sannan kuma a
wajen sayen kayan break basa saya, sai dai su saka yara su loda musu kaya su cinye suƙi
biyansu. Idan an kai ƙararsu wajen malamai ana gama musu hukunci aka sakasu biya dole ana
fita wajen makaranta suma yaro ko yarinya duka su amshe kuɗinsu. Tun suna ss1 suke
halayyar nan har zuwa yanzu, su kansu masu tallan har sun gaji da kai ƙarar tasu idan sunzo
sai su zuba musu kawai dan a zauna lafiya.
     Khadijah bata da yawan hayaniya, ba kuma ta da yawan shiga sabgar mutane. Dan haka ba
wani sanin Dafeeq tayi sosai a fuska ba, sai dai takan ji ana labarin rashin jinsu a makarantar.
Sai kuma duk sanda za'ai hutu idan an musu taro takan ga fuskar idan zai amshi ƙyauta dan
duk tarm kam hakan baya wucesa saboda ƙoƙarinsa. Amma ita dai ALLAH bai taɓa haɗasu
face to face ba balle magana ya shiga tsakaninsu sai yau ɗin nan da ya sameta a gaban mai
awara ita da Amina. Ta juyo zasu bar wajan shi kuma ya kawo jikinsa duk da kuwa ya ganta
sarai kuma ya fahimci ita bata lura da mutum a gabanta ba suka bangaji juna. Ledan hanunta
ne ya faɗi, awaran ciki ya watse a ƙasa. Tsabar wulaƙanci Dafeeq yabi takansa ya wuce yana
wani busar iska da fesarwa tamkar baiyi komai ba. Khadijah nada haƙuri, amma bata ƙaunar

wulaƙanci. Ga shi kuma a yau tana cikin yanayin period sai zuciyarta duk take a ƙuntace kuma
a kusa. Ranta a ɓace ta ɗago, sai dai har ya gotata zai wuce hankalinsa kwance. Hakan ya
ƙona mata rai, batare datama san mitake ba a ƙufule ta furta, “Kai wane irin wawan daƙiƙin
mutum ne mara sanin muhimmanci da kimar ɗan adam balle daraja abinci haka!”.      Cak Dafeeq da yaji abin tamkar daga sama ya tsaya. Yayinda wajen yay tsitt a ƙanƙanin
lokaci kasancewar a tsawace Khadijah tai maganar. “Kan babbar u.... can”. Ɗaya daga cikin
abokan nashi ya faɗa yana wani kallo da ɗaga hannu zai zabgama Khadijah mari. Caraf ta riƙe
hannun nasa tare da hantsilashi tana huci duk da ya fita tsayi sai dai shima babu ƙiba
kasancewar dukansu yara ne. Jikin Dafeeq da bai juyoba ya faɗa har kansu na gware. Sai
lokacin ya juyo a harzuƙe jin ƙarar da Hadiy ya saki sakamakon murguɗewa da ƙafarsa tai
dalilin hankaɗawar da Khadijah ta masa. Tarosa Dafeeq yayi ya miƙar, dai-dai Khadijah na
ƙoƙarin barin wajen yay wani kalar fisgota baya. Keeeee!! Kake ji hijjab ɗin jikinta ya yage har
zuwa ƙasa jikinta da dogon gashinta suka bayyana kasancewar babu ɗan kwali akan nata sai
hula. Fisgarta da yay kuma ya haɗo da hular. Taga-taga tai zata faɗi ciki rawar jiki Aminatu ta
riƙeta, tana ɗagowa babu wani lissafi ganin hijjab ɗinta ƙasa wanwar jikinta da gashinta a buɗe
ido a rufe ta ɗaga hannu ta sauke ma Dafeeq yatsunta biyar a saman fuska. Bai gama dawowa
a hayyacinsa ba ta kuma ɗaukesa da mari na biyu hawaye masu zafi na wanke mata fuska.
Dan a duniya babu abinda Khadijah ta tsana sama da aga jikinta. Itafa ko'a gida bata zama
babu hijjab balle anan cikin makaranta da ko salla bata yarda tayi ba. Shiyyasa da'an tashi bata
zama take ɗaukar hanyar gida dan ta samu damar yin sallarta acan.
     Tsitttt wajen yayi baka jin komai sai sautin kukan Khadijah, kowa ya zubama Dafeeq ido
yaga wane mataki zai ɗauka akan wannan mari, wanda bai ragama senior ɗinsa ba taya jenior
ɗinsa zatai masa wannan al'amari a zauna lafiya. Ganin yanda Dafeeq yay tsaye ƙiƙam tamkar
wani soja ko wanda yay sumar wucin gadi yana kallon Khadijah kawai dan koda ta maresa baiyi
ko gezau ba sai idanunsa da sukai matuƙar kaɗawa jazur, gaba ɗaya sauran abokansa 3 sukai
kan Khadijahn a harzuƙe matuƙa. Sai dai da sauri ya ɗaga musu hannu alamar karsu taɓata.
Basu iya ƙin bin umarninsa, sai dai da mamaki suke kallonsa. Ya wani kalar lumshe idanunsa
da buɗesu a lokaci guda kan ƙirjinta da gashin kanta yana taune lips nashi na ƙasa. Sai kuma
ya juya yana kallon sauran ɗaliban wajen. Cikin sauri suka shiga fashewa dan mugun tsoronsa
ake saboda rashin mutuncinsa. A dai-dai nan ma aka kaɗa ƙararrawar komawa aji......

        ★★★★

   Daga shi har doctor ɗin ƙofar suka zubama idanu. Sai dai ba kamar yanda yay tsammani
bane da tunanin ganin Alimah. Abbansa ne da yayansa. Doctor ya dubesa yana murmushin.
Sai kuma ya ɗauke idanun ya maida kan su Abba dake jerama JJ ɗin sannu da jiki. Kai kawai
yake iya ɗaga musu, yana mai jin wani iri a ƙasan zuciyarsa. Bayani Doctor yay musu a taƙaice,
tare da tabbatar musu zai iya sallamarsu daga yanzu zuwa kowane lokaci. Idan kuma babu
damuwa su bashi matarsa, kar suyi dubi da abinda ya faru, wannan ba komai bane akan
ma'aurata sabbin aure. Nasu kawai su musu nasiha ne musamman ita yarinyar. Sosai Abba ya
gamsu, yayinda JJ kansa ya sake kullewa gaba ɗaya, sai dai kamar an ɗinke masa baki ya
gagara cewa komai har Doctor ɗin ya gama bayaninsa ya fice.
      Zama Abba da yayansa sukai kusa da shi suna sake jera masa sannu, yayinda yayansa ke

haɗa masa shayi kamar yanda doctor ɗin ya bada umarni. Bayan ya kammala ya kawo masa
tasan asibiti ya wanke bakinsa sannan aka bashi tea ɗin. Ya ɗanyi nisa da shan tea ɗin
zuciyarsa duk a birkice da tunani kala-kala Abba ya katsesa da faɗin.
         “Jazool!”.
    A hankali ya ɗago idanunsa ya zubama Abban. Kafin ya ɗaga baki da ƙyar ya amsa da
“Na'am Abba”. Nisawa Abba yay da cigaba da faɗin, “Jazool sam banji daɗin abinda ka aikata
ba. Banda wauta irin taku ta yaran zamani abu kamar cin rabo. Yarinyar nan fa a gidanka take
kuma tazo kenan har abada bawai damar daren shekaranjiyan ne da kai ba kawai. Yanzu da
iyayenta fitinannu ne kana ganin maganar nan zata zama mai sauƙi ne kamar haka? Duk da
kuwa sun riga sun mallaka maka ita. Auren soyayya fa kayi bana ƙiyayya ba balle kace taƙi
amince maka zaka haike mata ta ƙarfi. Ka godema ALLAH daya kasance tai hankalin kiran ƴar
uwarka ba wani ɗan gidansu ta kira ba ya ganku a wannan halin. Ina mai baka shawara da
kazama namiji a gidanka, dan shi namiji mai dattako aka sanshi ba barahaza ba. Idan ka bita a
sannu cikin lalama sai ka kai ga inda kake so batare da ita kanta tama san ta mallaka maka kan
nata ba. Ban son na sake jin irin haka ta sake faruwa, in ba haka ba ranka zai ɓaci. Yara baku
da hankali sam gaba ɗaya kun koma gina aure akan sha'awa kawai soyayyar ciki ƙalilance...”
nan dai yay masa tass da faɗa da nasiha. Ya kuma hanashi cewa komai saboda shi Abba suna
kallon komai ne a yanayin da suka fahimta kawai. A ta wani ɓangaren kuma shi kansa JJ ɗin
bakinsa yay masa nauyin da ya gagara iya cewa komai batare da yasan dalilin hakan ba. Sai
ma zaƙuwa da ɗokantuwar son ganin Alimah kawai yake a ransa....

      Zuwa bayan la'asar aka sallamesu. Kamar yanda Doctor ya bada shawara gidansa aka
wuce da shi. Sun sami mutane uku da suma suka dawo da Alimah babu jimawa dan tunda abin
ya faru bayan an kaisu asibiti doctor ya tabbatar da ita bata buƙatar a kwantar da ita can
gidansu JJ aka wuce da ita. Ƙannensa ne guda biyu sai sep mom nasu. Tana zaune a falo
Alimah a kusa da ita tana mata nasiha, yayinda Rabi'ah da Sadiya ke tsaftace gidan duk da
bawani datti yayi ba. A kusan tare JJ da Alimah suka kalli juna, tai saurin rissinar da nata kan
cikin yanayin jin kunya da tsoro, shiko ya kasa yin hakan dan har sai da yayansa ya kamasa ya
zaunar. Bayan Alimah ta gaida Abba da yayansa shi ta gaida da masa yaya jiki kamar yanda taji
Umma ta faɗa cikin jajantawa. Itama da kai kawai ya amsa mata kamar yanda ya amsawa
Umma. A haka su Rabi'ah ma suka fito suna masa sannu da yaya jiki. Suma amsa musu yay da
kai.
        Nasiha mai ratsa jiki Abba yay musu su duka, itama Umma ta ɗaura da nata. Sun sallami
Alimah ta koma cikin bedroom wajen su Sadiya, suka sake rufuwa akan JJ a matsayinsa na miji
babba da ya fita shekaru. Shi dai saurarensu kawai yake dan baima san yaya zai fassara
al'amarin ba. Zuciyarsa gaba ɗaya a rufe take ruff, babu wani abu a jikinsa dake aiki a sashen
tunani irin na masu hankali. Abinda kawai ya sani yana jinsu yana kuma ganinsu da idanunsa.
Rabi'ah Umma ta ƙwalama kira, ta fito aɗan gaggauce tana amsa mata.
       “Ki faɗama Alimah ta haɗa masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login