Showing 117001 words to 118786 words out of 118786 words

Chapter 40 - CUTA TA DAU CUTA COMPLET BOOK by billyn Abdull .pdf

12 Jul 2025

4011

TAWAGAR ZAFAFAN LITTATAFAN NAN NA ZAFAFA BIYAR NAKE
MAGANA SISTER KIN MALLAKA���🤔??_*


*_KIN SAN KUWA A WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA DABBANCE. IDAN NACE DABAN INA
NUFIN DABAN A CIKIN DABAN_*


*_A 2024 ZAFAFA BIYAR ÆŠIN NAN NAKU SUN SAKE ZUWA MUKU DA WASU SABON SALO
NA MUSAMMAN DA ƘAYATARWA AKAN FARASHI KAI SAUƘI DA RAHUSA. DAN HAKA INA
GAYA MIKI ƳAR UWA KADA KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE_*


_Littatafan sune kamar haka 👇🏻_.



*_KWANKWASON JIMINA....._*
_(NA MSS XOXO)_


*_GUDUN ƘADDARA_*
_( NA SAFIYYA HUGUMA)_


*_TSUSTAR NAMA....._*
_(NA BILYN ABDULL)_


*_AMEENATU_*
_(NA MAMU GEE)_




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_

_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_



🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥


_______________


.........Sosai Khadijah tasha kuka da ganin irin wulaƙantacciyar rayuwar da su Dafeeq suke a ciki
shi da Kainaat. Kasa haƙuri tai tun a daren ta kira Alhaji Abaan ta zayyane masa komai. Shima
dai al'amarin ya matuƙar girgizashi. Dan haka washe gari da suka zo ɗaurin aure bayan an
kammala da yamma ya É—auki Khadijah da autansa da autan su Khadijah sukaje har asibiti yaga
su Dafeeq. Kuka sosai Kainaat ta dingayi da ganin Abaan. Ya sake zama babban mutum duk da
shekaru sun fara nuna kansu. Amma dayake akwai kuÉ—i da hutu da jin daÉ—i yana nan a É—an
gayunsa ga aji da rashin son hayaniyar nan tashi. Babban abin sha'awa yanda yake tattalin
Khadijah sa da Æ´aÆ´ansa biyu dake tare da su. Dan Muhammad da Fharooq suna makaranta su.
Kasa iya cewa komai Abaan yay sai rungume Khadijah da Mimi dake kuka yay a jikinsa yana
lallashinsu. Dan bayan komawarsu gida sai da Mimi tai yanda tai Aunty Jamila ta bata labarin
tushen komai da basu taɓa sani ba. Anan ta fahimci tushen rikicin da aka sha a lokacin shirya
aurema Yazeed ita sanda suke a shekarun ƙuruciya. Wanda da ƙyar suka sha a dalilin marigayi

Baba Hakimi. A take Alhaji Abaan yasa aka canjama su Dafeeq asibiti zuwa Abuja kamar yanda
Khadijah ta roƙa. Dan kafin ma su gama shagalin biki su an wuce dasu. An kuma fara basu
taimakon da duk ya dace kodan matsayin Khadijah na babbar likita a asibitin na Abuja. Lokacin
da suka kammala biki suka dawo Abuja Dr Khadijah ta cigaba da treatment É—insu su duka tare
da taimakon likitoci. Yayinda Alhaji Abaan ya zuba maƙudan kuɗaɗe da ake basu cikakkiyar
kulawa ta musamman. Kafin kace mi abubuwa sun fara daidaita a kansu. Dan kuwa an sakama
Kainaat ƙafafun roba duka biyu. Yayinda jikin Dafeeq ya fara murmurewa. Kafin cikar shekara
guda sun É—an dawo hayyacinsu musamman da yake akwai lafiyayyun abinci ga kulawar
lafiyarsu. Sai dai Dafeeq bai iya tafiya sai a wheelchair. Gara ita Kainaat ɗin takan ɗan miƙe
akan sanduna. Sai dai itama tafiyar tata bata wani nisan zango. A kullum cikin kuka suke da
nadamar rayuwarsu musamman ma Kainaat data rasa iyaye da dangi baki É—aya. Dan tun da ta
baro Niger babu wanda ya sake waiwayenta a ƴan uwan nata. Ga rashin ƴaƴa. Ƴar ɗaya tilo ta
musu nisan da ko labarinta ma basu da ƙarfin ikon ji sai kukan zuci. Ko ƴan aiki da Khadijah ta
É—iba musu suke tare da su a É—an gidan da suka basu dan bayan sun sami lafiya Kano aka sake
maidosu haka zakaga suna musu wulaƙanci da daka musu tsawa. Yanda masu aiki ke tsoron
iyayen gidansu su ga waÉ—annan ba haka bane. Iyayen gidan ne ke tsoron Æ´an aikin. Dan basu
musu komai sai hantara da wulaƙanci. Suna zama dasu ne kawai dan amsar kuɗaɗen
albashinsu. Su kuma sun gagara iya gayama su Khadijah gaskiya dan kar suga sun cika ƙorafi.
Saboda komai a rayuwa su Khadijah sun musu bai kamata su damesu ba kuma.
      Lokaci-lokaci idan su Khadijah sun shiga Kano sukan leƙa su duba su. Musamman ma
Khadijah dake yawan shigowa saboda harkar aikinta na likitanci data samu É—aukaka
daban-daban saboda ƙwazonta. A yanzu haka akowane ƙarshen sati biyu akwai jihar da take
zuwa bisitin matsayinta na gawurtacciyar likita da ake ji da ita a Nigeria ma baki É—aya ba Abuja
kawai ba. Ga mijinta daya kasance shahararren É—an kasuwa lamba É—aya musamman a fanin
shinkafa. Dan zuwa yanzu bama a Africa kawai ba, a duniya kamfanin Alhaji Abaan yana cikin
wanda ake matuƙar ji da alfahari dasu a harkar shinkafa. Kuɗi dai kam Alhmdllh akwaisu. Ga
ɗaukaka ga suna ga taimako duk ALLAH ya basu. Dan Khadijah ta kafa wata ƙungiyar wayar da
kan mata musamman ƙananun yara da iyaye akan harkar soyayyar ƙuruciyar nan da dayawa
take kashe rayuwar yaranmu da nakasar zukatan iyaye. Tare da ƙarfafa iyaye akan tsayawa
akan ƙafafunsu wajen ganin sun tallafawa ilimin yaransu musamman mata. Dan ɗiya mace tana
matuƙar buƙatar ilimi kodan sanin yanda zata tafiyar da rayuwar aurenta ma da tarbiyyar
yaranta. Domin kuwa wannan ƙarancin ilimin ya taka rawar gani akan mahaifiyar Khadijah a
lokacin da soyayyar Dafeeq ke É—ibarta. Maybe da tanada ilimi data kasance mai tsayawa da bin
matakan jan ra'ayin É—iyarta. Hakama iyayen Kainaat. Maybe da sunada ilimi da basu yarda
Æ´arsu ta zubar da su ba a idon duniya ta É—auki wasu iyayen barikin. Duk da dai idan mukai dubi
da wani faninin kuma Kainaat nada ilimin ai, amma bai hana Æ´arsu Banan ta bijire musu ba
itama harta maimaita abinda Kainaat ta aikatama nata iyaye. Hakan na nufin koda ilimin sai an
haɗa da ƙyawawan halaye da tsayawa wajen biyayya ma iyaye. Dan iyaye basu kasance abin
wasa ba a wajen kowanne irin ɗa komai lalacewarsu da baƙaƙen halayensu. Dan kuwa dai
Banan taga hakan, dan duk da baƙin halin iyayenta Kainaat da Dafeeq hakan bai hanata itama
ɗan ɗana kuɗarta ba. Tunda da ga ƙarshe ta ɓige da ƙasƙantacciyar rayuwar prison. Ta kuma
ratayama kanta alhakin rai. Inda ta koma ba dukiyar babu iyayen babu nasarar rayuwar.
Hakama a fannin Khadijah sai da ta girbi abinda ta shuka duk da kuwa ita nata iyayyen ma ta

roƙa gafararsu kuma sun yafe mata kafin subar duniya. Amma duk da haka sai da UBANGIJI ya
É—anÉ—ana mata irin wannan zafin data É—anÉ—anama iyayenta domin taji ta tabbatar da iyaye ba
abin wasa bane ba. Hakama bijire musu babbar musiba ce kuma illa ga rayuwa. Sai dai ALLAH
ya taimaketa kasancewa mijinta mutumin kirki mai tsarkin zuciya yasa komai ya daidaita cikin
sauƙi suka cimma burinsu na aurar da ƴarsu cikin salama ga wanda taso kuma yake sonta a
kuma lokacin da sukai fata. Haka dama rayuwa take cike da ƙalubale kala-kala da kuma
nasarori. A wasu lokutan gaggawarmu ke hanamu zuwa ga nasarorinmu. Wani lokacin kuma
son zukatanmu ke yanke mana igiyoyin nasararunmu. Mun manta cewar UBANGIJI ya
ƙaddarara dukkanin ƙaddaririn namu tunkafin haihuwarmu. Babu kuma mahaluki ko alkalamin
da takardar da suka isa canjawa daga abinda zuciya ke so zuwa ga abinda ke a rubuce a taskar
ALLAH. Dan haka mu kasance masu tsoron UBANGIJI a duk inda muke a kuma duk yanda
muke. Mu kasance masu jin soyayyar MANZON ALLAH a zukatansu akowane hali dan ita a
garemu wajib ne. Mu kuma kasance masu biyayya da hakuri da iyayenmu koda abinda suke so
mu bai mana ba mu so shi in sha ALLAHU zamu ribatun a wata rana koda ƙasa ta lulluɓe
idanunsu. Sannan namu Æ´aÆ´an muma zasu kasance masu biyayya a garemu.
       Ya rabbi ka shiryemu ka shiryamana yaranmu. Ka tsaremu katsare mana zukatanmu.  Ka
saka gaskiya a harshenmu, ka saka gaskiya a zukatanmu, ka saka gaskiya a ayyukanmu da
gaɓɓanmu. Ya rabbi ka hanemu saɓa maka da ganganci ko akan rashin sanin ka tsaremu daga
aikata ZINA. ka shiryi masu aikatawa idan masu shiryuwa ne. Idan ba masu sjiryuwa bane ya
rabbi ka nisantamu da su ka nisantasu da Æ´aÆ´ayenmu. Ya rabbi ka shiryi masu irin halayyar JJ
idan masu shiryuwane. Idan ba masu shiryuwa bane ya rabbi mun kawo ƙarar su gareka ka
fimu sanin yanda zakai mana da su.. Ya rabbi ka gafarta mana baki É—aya. Ka É—aukaka
ayyukanmu da rahamarka.í ½í¹í ½í¸­âœï¸.

*_ALHAMDULLAHI!!_*

    Ya rabbi Nagode maka daka bani ikon kammala wannan ɗan littafi nawa. Kuskuren da nayi a
ciki rabbi ka yafe mini ni da masu karantawa.🙊
Duk wanda na ɓatamawa a yayin rubuta wannan labari ya yafe Mani. Nima na yafema kowa.🙊
Ina sake tallata muku littatafan ZAFAFA BIYAR dake shirin zuwa muku da wani sabon salo na
musamman masoya. Dan tafiyar wannan shekarar fa tanada banbanci da saura matuƙar
banbanci. Soyayya ce za'a shata kwarya-ƙwarya😋 babu algus. A fanin ilimin ma mun tanada
muku romo mai yawa. Hakama faÉ—akarwar munzo da sabon tanadi. Kai cakwakiyar ma fa da
zamantakewar rayuwa duk ba'a barmu a baya ba. Kudai kawai ku kasance da zafafan biyar É—in
nan naku domin samun nishaɗi fiye da yanda aka saba.���

Masha ALLAH sai mun haÉ—u a ZAFAFA BIYAR dan suna nan shirye tsaff da zafinsu. Kuma gab
suke da zuwa gareku in sha ALLAHU suma�🙊
        

    
Bilyn Abdull ce🤙.




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_



🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu í ½í¸­í ½í¹_*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login