Showing 21001 words to 24000 words out of 118786 words

Chapter 8 - CUTA TA DAU CUTA COMPLET BOOK by billyn Abdull .pdf

12 Jul 2025

4008

da amarya Kainaat, dan
haka ya yanke shawarar tunkarar Khadijah da batun nan dan baya so taji a waje. Tayi mamakin
ganin ya dawo aiki da wuri. Dan ana idar da sallar la'asar ya shigo gidan. Wanka yayi yace ta
kawo masa abinci. Bayan yaci ya ƙoshi yana mata ƙorafin ramar da tayi itako tana ɗan
murmushin ƙarfin hali kawai batare da tace komai ba. Bai sake fita ba har akai kiran sallar
magrib sannan, bayan yayi har isha'i ya dawo gidan da tsarabar kayan ƙwalama. Tsareta yay
sukaci tare, ganin kamar ya fara dawo mata a Dafeeq ɗinta na baya taji ƴar nutsuwa harta saki
jiki taci. Bayan sun gama wanka sukayi da brush, tayi mamakin jin yace da wuri zai kwanta,
amma haka ta danne komai na wasi-wasi a ranta ta biye masa suka shige bedroom tun ƙarfe
tara. Tana kwance a jikinsa shiru bayan ya gama biyan buƙatarsa taji ya sauke ajiyar zuciya.
Kallonsa ta ɗan yi, kamar bazatace komai ba sai kuma ta nisa itama tare da sake shigewa
jikinsa.
      “Husby kanada damuwa ko?”.
   Shiru kamar bazaice komai ba, bayan wasu sakanni ya sake sauke numfashi da fuskantar ta
shima. A hankali ya ce, “Tabbas inada damuwa Khadijah, kuma a kanki ne.”
    A zabure ta kallesa tana mai nuna kanta da waro idanunta. “Ni kuma dai? Dan ALLAH
miyasa zaka shiga damuwa a kaina Dafeeq. Wlhy in dai abinda ya faru ne a kwanakin baya ni
na ajiye komai, na kuma maka uziri, sannan ina farin cikin cigaban da ya samemu tunda nasan
duk dan ka faranta minne. Fatana dai ALLAH ya cigaba da rufa maka asiri ta hanyar halak, dan
bana fatan jikunanmu su zama a cikin jikunan da wutar jahannama zataci sakamakon ci daga
haram. Bana zarginka bazan kuma taɓa zarginka ba in sha ALLAH”.
       “Nagode da hakan. Sai dai ni ba'akansa nake damuwar ba. Dan nasan dai hakkin ciyar
dake a kaina yake Khadijah. Sannan inada ƴancin neman arziƙina ko zuwa miki da sabon abu
batare da shakkar karki tuhumeni ba. Abinda kawai na sani bazan taɓa aikata abinda nima zai
wargazamin rayuwa ba akan neman abinda zan ciyar dake ko ƙyautata ratuwarki.”      Duk da maganganunsa sun mata wani iri haka ta danne harda sakin murmushin ƙarfin hali.

Cikin son danne hawayen da suka cika mata ido ta ce, “Hakane”.
      Tashi yay zaune fuskarsa babu alamar wasa, hakan yasa itama ta tashi zaunen da ƙyau.
Sai da ya zuba mata idanu na wani lokaci tamkar mai nazartar ta kafin ya ce, “Khadijah!”.
    “Na'am”.
Ta amsa masa cike da girmamawa.
        “Mata nawa akace maza su aura a musulince?”.
    Ƙirjinta yay wata irin muguwar bugawa har sai da ta ɗago a zabure ta kallesa. Ganin yanda
ya tsareta da nashi idanun ta haɗiyi wani abu mai kauri a maƙoshinta tana maida idanunta ƙasa
cikin rawar murya ta ce, “Huɗu”.
      “Masha ALLAH” ya faɗa yana gyara zamansa. Batare da damuwa da yanayinta ba ya
cigaba da faɗin, “To ALLAH ya karrama mijinki da zamowa cikin jerin maza da zasu ƙara aure,
nima zan mallaki mace fiye da ɗaya kenan. Dan na samu wata baiwar ALLAH da muka
dai-daita kammu har jibi juma'a ma za'a ɗaura auren in sha ALLAHU....”      Sosai jikin Khadijah ke rawa Kaff-kaff tamkar wadda aka kaɗama gangi, yayinda idanunta
tuni hawaye ya ɓalle a cikinsu. “Aure kuma Dafeeq!”. Ta faɗa cikin suɓutar baki da rawar lips ga
hawaye share-share. Fuska ya sake tsukewa tamau, cike da gadara ya ce, “Ban cika namiji
bane?”.        Kanta ta girgiza masa da sauri. “A'a ba haka nake nufi ba. ALLAH ya sanya alkairi ya bada
zaman lafiya”.
    A gatsine ya ce, “Amin” tare da komawa ya kwanta ya juya mata baya. Hannu tasa ta toshe
bakinta jin kuka na neman kufce mata. Sai dai duk da haka sai da sautinsa ya shiga cikin
kunnen Dafeeq. Ƙaramin tsaki yaja batare da ya juyoba ya ce, “Malama bana son wata damuwa
fa. Idan kin kwantar da hankalinki ma ita wadda zata shigo ɗin ba sa'ar yinki bace ba. Sannan
bata da lokacin wani yin ƙishi-ƙishin banzan nan dan tanada aji ta kuma san abinda yake yi. Ya
rage naki ki kwantar da hankalinki kici arziƙi kema cigabanki ne”. Daga haka ya juya yay
kwanciyarsa.
Kasa daurewa Khadijah dake jin kanta na juya mata tayi, da sauri ta dira a gadon ta nufi
falo........✍️


_Humm Khadijah _

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
*_Typing_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*

_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_� ��� ��_



_Shafi na goma_



_ADVERT_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA
CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO,
GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL,
AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA
GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN
KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA
KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN
YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and
more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND
YOUR HOME COVERED

___________


.......Ƙarfe ɗaya da mintuna goma sha shida duk wanda ke a massalacin ya shaida ɗaurin auren
Dafeeq Abubakar Ja'e da amaryarsa Kainaat Usman akan sadaki naira dubu ɗari biyar.
Kasancewar massalacin a anguwar su Kainaat yake gane wanene angon nata ya haddasa
ƙananun maganganu a bakunan mutane. Kainaat sananniyace a anguwar tun tana budurwa,
duk da mahifinta talakane ta tashi irin yaran nan marasa jin magana da son ƙarya. Za'a iya rasa
masarar tuwo a gidansu Kainaat ka ganta da dressing na kusan dubu ɗari biyu a jiki. Gashi bata
da mutunci ko kaɗan, dan ko gittawa tai ka gaya mata cuta sai ta dawo ta gaya maka mutuwa.
Yanda Kainaat ke fantamawa a cikin dukiya yasa tuni kowa ke mata kallon ƴar iska. Sai dai
kuma a baɗini sam ba haka bane. Dan duk rashin jin Kainaat bata aikata zina, amma fa ko kai
waye a wayo in har ta ƙwallafa maka sai taci kuɗinka. Zatabi tako wace irin hanya taci saboda
shegen wayonta. Kainaat ƙyaƙyƙyawa ce sosai, dan ta kasance buzuwa, sai dai anan Nigeria
aka haifeta, dan nan ta tashi taga kanta da iyayenta nan kuma kaɗai ta sani ko Niger da aka
san asalin buzaye suke basa zuwa. Ƙawayen Kainaat duk ƴaƴan masu kuɗine, ta kuma samosu
ne a yazon bin joint-joint ɗinta. Dan duk inda tasan ƴaƴan manya suke nan ne wajen zuwanta. A
wannan kutse-kutsen nata ta tattara ƴaƴan manya suka zama abokanta. Sometimes ma sune
ke saya mata sutura, dan in har zasu shiga shopping to itamafa dole a mata. Tayi samari kala
daban-daban kama daga kan alhazawan birni har zuwa matasan masu kuɗi dama yaransu, sai
dai taci kuɗinsu ta gudu. Da taimakon Nadwa ta koma makaranta, dan ta kammala secondary
ɗinta tuni. Nadwa mommy's girl ce. Dan babanta ya jima da rasuwa, kuma mai kuɗine sosai, ita
kaɗai ya haifa dan haka ya barsu da tarin dukiya itada mahaifiyarta. Tunda taga Kainaat ALLAH
ya ɗaura mata sonta, dan ita mutum ce mai son ƙyaƙyƙyawa. Tare suka fara karatu, daga baya
Mommyn Nadwa ta turasu abroad. Da ƙyar baban Kainaat ya yarda, dan sai da Mommyn
Nadwa ta lallaɓashi.
Su Kainaat na shekarar ƙarshe a school Abaan yazo yin wani course na wata shida. Tunda
Kainaat ta ɗaura idonta a kansa ta haukace. Haka ta addabi Nadwa sai da ta binciko mata shi
ɗin ɗan waye. Hankalin ta ya sake tashi jin bama ubansa ba, shi akaran kansa gayyane. Dan
matashin mai kuɗine a harkar noman shinkafa da shigo data waje gida Nigeria, ya kuma fitar da
ta Nigeria waje. Kai a taƙaice dai shine kankat a harkar shinkafa a Nigeria bama arewa kawai
ba. Wannan shine irin mijin da Kainaat ta jima tana burin mallaka, matashi ga kuɗi ga ƙyawu.
Uwa uba miskilanci. Dan kallon fuskar Abaan kawai ya isa tabbatar ma da mai hasashenshi shi
ba kanwar lasa bane. Duk da jikin Kainaat ya ɗanyi sanyi kaɗan da jin shekarunsu ɗaya na
haihuwa, amma da ga baya sai ta ware akan hakan ba komai bane. Kainaat ta fara ƙoƙarin
shiga jikin Abaan sai dai ko kallo bata ishesa ba, hasalima an sanar mata shi fa mata basa
gabansa sam. Mahaifiyarsa da ƙanwarsa ne kawai taurarinsa a duniya. Jin wannan batu yasa
Kainaat shiga ta fita harta jawo hankalin P.A nashi kanta, da taimakonsa ta fara kusanta kanta
da Abaan, sai dai nan ɗin ma babu nasara, ganin bazai kulata ba ta canja alƙibla zuwa kan
ƙanwarsa da mahaifiyarsa bayan sun dawo gida Nigeria sun bar Abaan acan. Yanda Kainaat ke
kwantarma Hajiya Maryam kai yasa ta fara jin sonta a zuciyarta, gata kullum cikin shigar
kamala. Noor ce dai ma aka ɗan sha wahala da ita, dan da ƙyar ta fara kula Kainaat saboda
faɗan da Hajiya Maryam ke mata. Da taimakon Mommyn Nadwa Kainaat ta sake samun shiga

jikin Hajiya Maryam, danta alaƙantata da cewar ɗiyar ƴar uwarta ce. Duk da Hajiya Maryam ba
damuwarta dole sai ɗanta yay auren ƙwarya tabi ƙwarya bane sai taji ta amince Abaan ɗinta ya
mallaki Kainaat matsayin mata. Dan koba komai ƙyaƙyƙyawace kuma nutsatstsiyar yarinya.
(Nace Humm). Daga ƙarshe dai anyi auren Kainaat da Abaan badan yana sonta ba sai dan biyayya ga
mahaifiyarsa. Yayinda komai akayisa a hannun Mommyn Nadwa matsayin itace uwa gareta
iyayenta sun rasu. Mahaifiyarta tayi kuka sosai da irin wannan aure, dan tana son ƴarta, amma
gashi a dalilin auren mai kuɗi ta kashesu ta ɗauki matar data santa da girmanta. Haka dai aka
sha shagalin biki iyayen Kainaat basu da wani power a ciki. Amarya ta tare, sai dai babu kulawa
daga miji, hasalima randa aka kaita yabar ƙasar, hakan ya ƙonama Kainaat rai sosai, taci kuka
bana wasa ba, sai dai Mommyn Nadwa nata kwantar mata da hankali ta waya. Hakama Hajiya
Maryam tasa Abaan ya dawo dole bayan tafiyarsa da kwanaki uku. Anan ɗin ma Abaan bai
niyyar shiga sabgarta ba, amma babu wanda yasan yanda akayi kwanakinsa biyu da dawowa
yakai kansa gareta har ma ya angwance a wannan dare. Samunta da budurcinta ne abu na
farko daya kankaro mata mutuncinta a wajensa, duk da kuwa asiri na cinsa, dan kai kansa da
yay gareta kam tabbas magani yaci a cikin abinci. A watan da Kainaat taje bata tsallake na ciki
ya bayyana, kowa murna yake tsakanin Abaan da mahaifiyarsa da Ƙanwarsa. Tattalinta sukeyi
kamar ƙwai, dan ko motsi tai sai ance mike damunta. Wannan al'amari yayma Kainaat daɗi, sai
ta dinga langaɓe musu kuwa fiye da jin jiki na laulayi suko suna rawar jiki. A haka ALLAH yakai
ciki watan haihuwa, ta ko haifo ɗanta namiji mai kama da ubansa sak. Farin cikin wannan family
bama zai misaltu ba. Amma abin baƙin ciki mahaifiyarta da ƴan uwanta da mahaifinta sai zuwa
sukai dubata a matsayin wai dangin babanta ne dake Niger, Mommyn Nadwa itace komai.
Ranar ma mamanta sai da tai kukan baƙin ciki, yayinda ƴan uwanta sukai alkawarin bazasu
sake raɓarta ba, dan yanda ta amshesu a wulaƙance ya ƙona musu zuciya sosai. Suna baro
gidanta suka tattara kayansu dama gidan da suke gidan haya ne sukai tafiyarsu Niger. Wannan
shine silar rabuwarta da iyayenta da ƴan uwanta, har yanzu bata kuma nemesu ba suma basu
sake memanta ba.
Ranar suna an zubar da kudi na tashin hankali, yayinda yaro yaci sunan Kakansa wato
mahaifin Abaan da ALLAH yayma rasuwa tuni. A wannan ranar ne Abaan yayma Kainaat
ƙyautar companyn nan, tare da maƙudan kuɗi daga mahaifiyarsa, ƙanwarsa Noor ma ba'a barta
a baya ba ta siya mata danƙareriyar mota duk da kuwa Kainaat ɗin nada har guda biyu na lefe
da aka saka mata da wadda Abaan ya bata matsayin tukuycin kai masa budurci. Ansha shagali
an kuma samu dukiya sosai daga abokan arziƙi, dan kwarai da gaske yaro yayi goshi, Kainaat
na alfahari da haihuwarsa. An fara rainon yaro matsayin ɗan gata, sai dai kuma ashe bamai
zama bane, dan watansa ɗaya da kwanaki a duniya ya rasu sakamakon mura da dama aka
haifesa da shi, dan Abaan nama shirin suje suga likita ne a waje ashe babu rabo.
Kuka na tashin hankali Kainaat ta dingayi, dan kuwa dai taga samu taga rashi, harta fara
alfaharin dukiya ta zama tata ta gida gaba ɗaya. Abaan da Mamah suka koma lallashinta ita da
Noor, dan kuka suke sosai. Ansha fama Kainaat harda kwanciya asibiti kamar ba mutuwar
ƙaramin yaro ba, da ƙyar ta dawo hankalinta.....
___________★

Guri ɗaya suka sake dunƙulewa sosai. Dan hatta malaman kansu a wannan gaɓar
zukatansu bugawa suke da sauri-sauri. Sai dai basu yarda sun saki addu'oi ba. Masu ragguwar
zuciya kam tuni fitsarin daya taru musu ya fara ɗiga, wasu ma gab suke da fashewa da kuka
tsabar tashin hankali. Dan wannan al'amari ne da a film kawai suka sanshi bawai zahirin rayuwa
ba.
Tsahon mintuna biyar wutar ta sake kawowa. Wani irin ihu mai jijjiga gida suka saki kusan su
duka idan ka cire Baba da malaman nan sakamakon bayyanar Alimah a mummunar siffar
horrors dan bata da maraba da su. Fuskarta da jikinta sunyi wani irin fari tamkar an baɗa mata
hoda. Wajen idanunta yay wani zummm kamar wadda tai kukan jini, hakama bakinta duk jini ne,
ga gashi a wargatse da uban tsaho har yana jan ƙasa, ta saman kanta akwai ƙahuna guda biyu.
Hakama ƙafafunta kofataine, hanyenta da wani irin farcina zaƙo-zaƙo tako ina dai bata da
ƙyawun gani. Dan su kansu tunda sukai mata kallo guda idanunsu suka rumtse babu wanda
yay gigin sake maimaitawa.
Shuuuuu!! Ta wani irin zagayesu kamar mai tafiya a takalmin taya tana ɗaura zabgegen
yatsanta a saman baki da faɗin, “Shiiiii!!!” alamar sumata shiru daga ihun da sukeyi. A tare suka
shiga haɗiye ihun sai hawaye dake fita a fuskokin masu raguwar zuciyar cikinsu. Jaruman kuwa
rawar jiki kawai suke yi, gashi a zagayesun da tai ɗin nan ashe ɗauresu tayi da igiyar da sudai
basu gani a hannunta ba.
Kwas! Kwas!! Kwass!! Ta dingayin wani taku tamkar wadda ke jerin gasar ƙyau ta duniya.
Sai kuma ta wani kwashe da dariyar data nema fasa zukatan su. Sai da tai mai isarta tana
faman zagayesu kafin ta tsagaita, da wata kalar kakkausar murya ta ce, “Ku miyasa bil adama
kuke da son shiga abinda babu ruwanki ne? To gashi nan shishshigin ku ya jawo muku
mutuwa!!!”.
Cikin rawar baki da suɓutar baki Baba ya ce, “Baiwar ALLAH kiyiwa ALLAH ki haƙuri. Wlhy
mu muzo ne domin ceton matar Jazool. Amma ki taimaka ki yafe mana”.
“Hahahaha tsoho! Idan kai wannan ya kawoka su waɗan nan miya kawosu? Sannan da
kukazo ɗazun ban muku gargaɗin farko ba?!”.
“Kin mana wlhy, kin mana. Dan ALLAH kiyi haƙuri. Babu wanda zai sake maimaita kuskuren
nan”.
“Wanda ma ke son maimaitawa ya maimaita. Dan ganin gawawwakin ku sai ya saka ƙafar
wani bazata sake tako cikin gidan nan ba. Ɗanka kuma yanzu ya fara amsar sakamakonsa a
hannunmu, dan sai ya tabbatar da bakowace mace ake taɓawa a zauna lafiya ba. Sai mun
barma ire-irensa tarihin tunawa a wannan duniyar”. A yanzu kam idan ka cire baba da malaman nan kowa kuka yake jin wai zata kashesu,
sukam ganin ƙwam bai musu rana ba. Wata irin gigitacciyar tsawa ta daka musu. Sake
dunƙulewa sukai waje guda suna mai sake ƙan ƙame junansu, masu fitsari na sake sakin
second round. Cikin ƙarfin hali shugaban malaman ya fara karanto suratul baƙara. Da rawar jiki
wanda suka iya suka fara suma. Kecewa da dariya Alimah tayi, sai kuma ta haɗe rai tare da
tafa hannunta ta buɗesu. Sai ga bakunansu sun ƙage kowa ya kasa magana.
“Hahaha!! Ni zakuma karatu. Ni nan kuke tunanin ƙonawa? To kafin ku ƙonani ni bari na
shafe babinku.” ta wani irin sake tafa hannaye sai ga wasu mugayen halittu na fitowa ta cikin
bangwayen gidan a kowace kusurwa. Gaba ɗayansu sun gama rikicewa. Hatta da su baba a
wannan gaɓar kam babu sauran jarumta a tattare dasu. Kowa zufa yake kashirɓan jiki na rawa

Kaff-kaff kamar waɗanda aka kaɗama gangi. Yanda suke sake curewa waje guda sai sun
matuƙar baka tausayi. Masu ƙarancin ƙarfin zuciya tuni sun fara sumewa dan ganin halittun nan
kawai ba ƙaramin tashin hankali bane mai rikita tunani. Balle kaga kai suke dimfarowa tamkar
mayuntan zakuna suna wani irin nishi da fesar da wuta a bakunansu. Suna gab da isowa
garesu ta sake tafa hannayenta suka ɓace. Dariya ta shiga ƙyalƙyalawa tana kallonsu. Kafin ta
wani irin fesa musu ruwa da hannunta data ware a kansu kamar mai musu daƙuwa. Sharaf
suka jiƙe, waɗanda suka suma duk suka farfaɗo. Kuka ƴan maza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login