Showing 1 words to 3000 words out of 141487 words
*TKG*
01.
"SADIYA.."
Wannan karon a yanayin yadda ya kira sunana sai da na ji jikina ya amsa da ya sa kaina na ƙasa sai da na ɗago na kalle shi. Tabbas a cikin idanuwansa na hango kamar hawaye sun cika masa kwarmin idanuwa kuma na hango gajiya da haƙuri harda kunya a lokaci ɗaya.
"Sadiya.."
Ya sake furtawa cikin wani irin rauni. Raunin da har ina jin sautin fitar shi daga muryansa.
"Sadiya.."
"Ta.."
Ya sake faɗa ararrabe daga gani ya kasa sarrafa kanshi halin da ya ke ciki na neman tona masa asiri.
Ba na so ko ɗaya na nuna masa na san labarin abin da ke faruwa yadda bai faɗa mini ba nima ba zan nuna masa na sani ba. Tabbas na yi dauriya domin a lokaci ji na ke yi kamar na zube a kan kafafuwana tsabar yadda suke rawa. Ina jin wani irin nauyin jiki wanda na zuciyata ne ya sakar ma gangar jikina.
Na yi iya ƙokarina kar ya fahimci nima a firgice na ke shi ya sa na gayyato mirmishi wanda ka na ganin shi gwara ma kuka a kan shi saboda ba daga ƙarƙashin zuciyata ya fito ba.
Ina yin mirmishin ina kallon fuskar Yallaɓai amma sai na ga yau ba na ganin shi da haske a idanuwana sai ya yi mini wani baƙi kamar ba Yusuf ɗina ba.
"Sadiya ta. Na dawo"
Ya faɗa ya na kallona domin tun ɗazu idanuwanshi suna kaina ne. Ni kuma cikin rawan jiki da na zuciya na buɗe baki dakyar ina jin harshena na karkarwa a cikin bakina.
"Na'am"
Murya ta na rawa ina so na daidaita kaina amma wallahi na kasa. Kai jama'a kishi bala'i ne sai yau na sake samun tabbacin haka duk yadda na so a ro jarumta sai na ji na kasa ji na ke yi wani abu na min yawo a cikin jinin jikina. Kaina ya yi nauyi gabaɗaya ji na ke yi kamar zan faɗi saboda tsabar gigitar da na ke ciki saboda tashin hankali.
"Na'am Yallaɓai n.."
Sai sauran kalamai na suka maƙale a fatar bakina. Na kasa iya kiransa da yau ɗaya da Yallaɓai na. Yau ɗaya da na kalle shi ina jin dukan zuciya da cewa Yallaɓai yanzu ba nawa ba ne ni kaɗai ya tashi da ga mallakina ni ɗaya ya koma mallakinmu ni da wata. Ashe haka sauran mata da dama suke ji in an yi musu kishiya? Na ɗauka in Yallaɓai zai ƙara aure ba zan wani damu ba ashe ashe kishi ba a yi masa da wasa. Tabbas Ubangiji ne ya hallici mu mata shi kuma ya sanya mana kishi a zukatanmu shi kuma kaɗai ya san dalilin shi na haka.
Balle irin auran da Yallaɓai ya yi ban shirya ba. Lamarin ya zo min ne cikin bazata da tsamanin abin da ban taɓa tsammani ba. Ban taɓa zaton a wannan yanayin ne zan fara raba Yallaɓai da wata ba. Ban taɓa tunani ko hasashen haka ba.
Takalmin da ke kafata har ya jiƙe da zufa haka wayar dake hannuna tana maiƙon zufan da ke fita daga jikina
Yallaɓai ya fara taku ɗaya, biyu zuwa gare ni da sauri na yi baya a nufina na guje ma haɗuwar jikina da na shi domin yau kawai na ji ba na so Yallaɓai ya kusantoni. Ƙokarina na yi baya amma jikina ya ƙi ba ni haɗin kai saboda a firgice na ke. Bayan da na yi da sauri ya ja takalmin kafata ya turkuɗe na yi baya zan faɗi ban san lokacin da wayar hannuna ta faɗi ba, sai na ji Yallaɓai ya rike ni gam lokaci ɗaya yana kallona kafin ya ce.
"Lafiyan ki kuwa?
Ya faɗa ya na mai kallona cikin fitan hayyaci na kalle shi sai na ji in na cigaba da kallonsa zan iya fashewa da kuka har na tona asirin zuciyata. Ya ji jikina na rawa ya kuma ya fahimci duk a firgice na ke ba na cikin hayyacina, shi ya na ƙoƙarin ya ta da ni tsaye ya raɓa ni da jikinsa ni kuma hannayen nashi na ke kallo domin sai na ga kamar sun zame min baƙi a cikin idanuwana yau ɗaya kawai sai na ji hannun Yallaɓai kamar baƙo a gare ni da ban san lokacin da na yi gefe ina mai kauce ma riƙonsa baa. Hannun kujera na dafe ina haki sama sama domin na ji tabbas numfashina na cijewa kamar ya na neman ya dawo wuyana.
Yallaɓai ya kalleni a tsorace ya sake kallona kafin ya ce" Sadiya? Kina lafiya?
Ya faɗa ya na ƙokarin ƙara matsowa kusa da ni da sauri na yi baya amma kuma ban saki hannun kujeran da ke gefena ba domin in har na yi gangancin saki ba zan iya riƙe kaina ba.
Sadiya ki yi jarumta Sadiya ki daure. Haka na ji wata zuciyar na faɗa min da ya sa na yi saurin ƙwato numfashina da karfi na sauke ajiyar zuciya ina mai kallon wayata da ta faɗi a ƙasan Tayels. Yallaɓai ya bi in da na ke bi da kallo shi ya duka ya ɗauko min wayar ya riƙe ta a hannun shi.
Kallona ya ke yi yana so ya yi mgana shima bakinsa ya yi masa nauyi kawai sai na miƙa masa hannu ya saka min wayar lokaci ɗaya yana faɗin" Kin tabbata kina lafiya?
Ji na yi kamar in balla masa harara in ko na buɗe bakina na tabbata sai na danna masa ashar na katsinawa. Amma sai ban yi haka ba, na sake gayyato mirmishi ina mai ɗaga masa alamun lafiya ta ƙalau. Ajiyar zuciya na riƙa saukewa a jejjere ina huro iska daga bakina domin na samu natsuwa daga ƙasan raina ina ta mamaita Innalillahi domin Allah ya sake ba ni jarumta.
Cikin ikon Allah na ji na samu natsuwa jikina ya daina rawa. Har na samu daman sakin hannun kujera na tsayu da kafafuwana. Kallonsa na yi ya na tsaye ya harɗe hannuwansa a saman kirjinsa ba ni kaɗai ba shi kan shi ma a firgicen ya ke sannan ba natsuwa a tare da shi. Ban tsaya sake kallon shi ba na yi karfin halin wucewa wajen ledojin da ya ijiye na duka na ɗauka ina faɗin" Su Jidda sun gaji da jira har sun yi barci."
Na faɗa saboda gyara yanayina lokaci ɗaya ina ɗagowa da ledojin ta gabansa na wuce zuwa kan dining na ɗora ledojin amma ban buɗe su ba. Ina so na juyo amma ba na so mu sake haɗa ido da Yallaɓai.
"Ki tashe su mana."
Haka ya faɗa a sanyaye sai na juyo ina mirmishi kafin na ce" Sun riga sun yi barci fa? Ƙyale su kawai."
Shi kuma kawai sai ya saki hannayenshi ya wuce kawai zuwa falo ya na mai faɗin" Wannan babban rana ce a gare mu bai kamata mu yi murnan ba su a wajen ba."
Ya ƙarishe faɗa ya na buɗe kofar falon ya shige ni ban bi bayan shi ba ina ta ƙoƙarin yaji da abin da ke taso min. Ina jin sa daga nan ya na kiran sunanayen su Jidda daman ba ta da nauyin barci. Baby ma ba ta dashi amma ba kamar Jidda ba.
Tsayuwa na neman gagarata ya sa na samu ɗaya daga cikin kujerun falon na zauna ina sauke numfashi. A baya in yi ta ganin laifin matan da mazajensu ke ƙara aure su yi ta hauka sai da ya zo kaina na fahimci yanayin tabbas kishi ke haukata mata ya kuma sa ka kasa mallakan kanka, ina zaune a in da na zauna ya dawo falon tare da yaran dukkansu ya na riƙe da hannun su. Baby ce sarkin surutu sai faɗi ta ke yi.
"Abba yaushe ka dawo?
"Ban daɗe da dawowa ba Baby"
Ya ba ta amsa dai dai suna zama kan kujera mai zaman mutum huɗu.
"To ina ka je Abba?
Baby ta faɗa tana mai hawa jikinsa ya na shafa kanta ya ce" Na je Rano ne."
Ya ɗago kenan muka haɗa ido da shi sai na yi saurin kauda kai daman ina so na ji me zai ce? Tabbas can ya je kuma ya dawo da kyakyawan tsaraba na ce a raina a lokacin da na ji Baby na tambayan shi ya siyo mata tsaraba. Sai ya nuna mata ledojin kan Dining ya na faɗin ga tsaranbanta ca.
Daga shi sai Baby suke hiran su ni da Jidda kamar ba ma falon ita ta na gefe sai hamma ta ke yi daga gani barcine a idanuwanta ni kuma ina zaune ina fama da turirin zuciya.
"Duk Umma ce ta haɗa wannan?
Ya faɗa ya na nuna cake ɗin da ke gabansu.
Da sauri Baby ta ce" Umma ce da Yaya Jidda. Abba ni ma zan ci Cake ɗin"
Ta faɗa tana leƙa Cake ɗin . Na ji ya kalleni a cikin jikina ni kuma sai ban juya na kalle shi ba, ina kallon gefe ina ƙokarin sakin fuskata na nuna komai bai faru ba amma ina jin kamar ba zan iya nuna komai ɗin bai faru ba.
"Sorry Jidda barci ko?
Na ji ya faɗa sai na ji ita kuma ta na faɗin" A'a Abba."
"To Hammar kuma ta mane ne Jidda?
Ya faɗa ta gefen ido na kalle su sai na ga ya na jan hancinta ita kuma tana mirmishi. Yana ɗago kansa zuwa gare ni na yi saurin ɗauke kaina kamar ban san suna wajen ba.
Ƙila ya daɗe yana kallona domin falon ya yi shuru sai karakainan Baby kawai ke tashi a falon ni kuma na yi matukar ƙokarin sassauta fuskata.
"Yaran nan fa na jin barci ta so su mu yi abin da ya kamata su je su kwanta."
Ya faɗa a sanyaye. Ni kuma sai na yi kamar ban ji ba sai na maida kaina can gefe kamar ina kallon Tibi ahalin Tibin ma a kashe ta ke.
"Sadiya"
Shima yau ɗin ya raba ni da wata ni ai ba Sadiyarsa ba ce ni kaɗai ya na da gimbiya shi ya sa yau Yallabai ya ke kirana Sadiya gatsal ta sar ma ya kasa ma minibwannan karan. Ji na yi kamar na fashe da kuka saboda baƙin ciki.
"Sadiya.'
A wannan karon da ɗan karfi ya sake kiran sunana. A sanyaye na kalleshi kuma kallon bai yi yawa ba na yi saurin kauda kaina ina ƙoƙarin miƙewa sai na ji duk jikina ya saki. Amma hakanan na miƙe ina ƙokarin dai dai ta kaina ina gani ya na nuna min gefensa na yi kamar ban gani ba na zagaye shi na isa kujera mai zaman mutum biyu dake gefen su na zauna. Ban kalle shi ba sai na sadda kaina ƙasa ina wasa da zoben azurfan da ke hannuna.
"Sadiya ta."
Sai yanzu? Sai yanzu ne ya gane ni tasa ce kafin ya samu wata. Haka na faɗa a raina sai na ɗago idanuwana da na ji har nauyi sun yi min ina kallon shi, shima fa karfin hali ne amma kunya da nauyin Sadiya da ya ke ji sun hana shi sakewa.
"Na tambaye ki meke damun ki, kin ce min bakomai."
Ya faɗa ya na mai kureni da ido a cikin zuciyarsa kuma na san bugu ta ke yi saboda nima ƙura masa ido na ke yi ina hasashen shike nan yanzu wai kwana zan riƙa rabawa da wata a kan Yallaɓai ko? Shi kenan mun tashi daga Family of 4 mun koma Family of 5 ƙilama kafin a rufe shekara ta haihu za mu hauhawa. Sai na ji kuka na taho min amma na yi saurin kannewa.
"Me ke damun ki? Ko an faɗa miki wani abu ya faru ne?
Shike nan ya fara kama kanshi da kanshi. An ce mara gaskiya ko a cikin ruwa ya ke gumi ya ke yi. Da gangan na kalle shi sai na ga ya daburce yana ƙokarin gyara mganarsa.
"Nufina ko can Ɗorayi su Alhajimmu duk lafiya ko?
Mirmishin takaici ya kwace min. Yallabai ya na so ya raina ma kansa ma wayau. Ya na tunanin abin da ya rufe bai faɗa min ba ya na ji a ransa zai tabbata a rufe ne ni ban sani ba.
Sai kawai na yi masa wani kallo kafin na ce" Ko ɗaya. Ba abin da ya faru kawai raina ne ya ɓaci ba ka dawo da wuri ba alhalin kasan tun karfe nawa muka shirya ni da yara muna zaman jiran ka?
Na faɗa hawaye na ciko min a ƙwarmin idanuwana. Ƙura masa ido na yi sai na ga ya sauke ajiyar zuciya irin na samun salama ya na neman ɗauko mgana na yi saurin tare shi da faɗin" Mu yanka cake ɗin ina jin barci.'
Na faɗa ina mai kauda kaina saboda ƙokarina na maida hawayena sai ma na ga sun koma da kansu ba tare da na yi yinƙurin maida su ba.
"Sadiya"
Ya sake kiran sunana a zafafe na juya na kusa na ce ya daina kiran sunana haka tunda ba shi ya raɗa min ba amma sai ya yi sauri tare ni da cewa.
"Ta so ki zo nan ki zauna kusa da ni."
Ya faɗa ya na nuna min gefensa. Kamar na ce bar ni anan sai kuma ban ce ba na tashi na koma kusa da shi na zauna amma ban matso kusa da jikinsa ba sai shi ne ya sauke Baby da ke kan jikinsa gefen Jidda sai ya ƙara matsoni ba zato kawai na ji ya sunkuya ya sumbaci kuncina kallonsa na yi bai bani zarafin mgana ba ya yi mirmishi kafin ya ce.
"Ki yi hakuri Sadiya."
Kallonsa na ke yi amma na kasa mgana sai ya ƙara marairaicewa ya na ƙara matso ni a jikina.
"Sorry ba na ce ki yi haƙuri ba? Kin ji ko?
Ya faɗa ya na ƙoƙarin saka hannu ya ɗago haɓata da sauri na kauda kaina ina faɗin" Nima ai na ce komai ya wuce ko?
Sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Yaushe kika ce! Yanzu dai ko?
Ban iya ma yi masa mgana ba ya dame ni kamar na ce ya matsa baya amma na kasa. Shi bai san ni yanzu ba na so ma ina zuwa kusa dashi ba a raina na ke jin duk abin da na ke tunanin ni kaɗai ke da shi yanzu ya tashi a mallakina nawa ya koma mallakinmu kuma namu. Ya yi ƙokarin ba ni haƙuri amma kuma ya kasa bayyana uzurin da ya zaunar da shi tun safe sai dare, Me ya sa Yallaɓai ya boye min ? Zan hana shi aure ne? Ni a cikin zuciyata na fi jin zafin munafuntata da ya yi sama da auran shi. Har Ma'u ta na murna ta samu makamin da za ta ya ƙe da shi ni kuma na ce ƙaryanta ba zan taɓa bari ta samu wannan damar ba.
Mun yanka Cake amma wannan shekaran Walimar tamu ba cike take da farinciki ba. A fuskata za ka fahimci ba na cikin farinciki shima kuma haka su Jidda ne kawai ke ta murn. Ko wajen yanka cake ɗin ma hannuna saman na Jidda na ɗora sai shi ne ya ɗau hannuna nawa ya ɗora saman wukar sannan ya kama sai ya ce yaran su ɗora saman na shi. A haka muka yanka cake ɗin kuma wajen ba da wa yarana na fara ba mawa sannan shi na karshe in da a ce zan yi masa kutumar uba wallahi ko kallo bai isheni ba amma hakanan na daure ma zuciyata. Shi ko ni ya fara yankawa ya saka min a baki wanda dakyar na buɗe bakin duk ma ya shafa min a gefem baki ya na ƙokarin ya saka hannu ya goge min na goge da kaina sai ya koma ya na ba ma su Jidda cake ɗin suma suna bashi suna ta dariyan farinciki ina kallonsu a cikin raina ina tunanin shike nan Yallaɓai ya yi sanadiyar lalatamin farincikina na wannan ranar. Daman ya ce zai ba ni suprise lalle na karɓi babban suprise da ba zan manta da shi ba a rayuwata ba.
Na gaji so kawai na ke yi na keɓe ni kaɗai. Shi ya sa kawai na mike na isa ga ƙwalin agogon da na siya masa ban jira na bashi a hannunsa ba na ijiye masa a gabansa ina faɗin" Gift ɗin ka"
Na ga ya yi shuru ya na kallona ni ko sai na yi saurin kallon su Jidda ina fadin" Oya tunda an gama ku je ku kwanta."
Da sauri ya ce" Ba mu gama ba. Ba mu yi ciye ciye ba Madam."
Ina kallonsa ina shirin mgana da sauri ya ce" Kuma na siyo kaza gasashiya da tsire ba ki duba ba."
Sai na fara hammar ƙarya ina faɗin" Ina jin barci Yallaɓai."
Haka na faɗa kawai sai na ga ya miƙe ya na mai ɗaukan kwalin agogon ya bude ya na gani kafin ya kalleni ya na min mirmishin da ni yanzu ya daina yaudarata.
Ban tammaci haka ba. Shammata ta ya yi ya kawo min rumguma lokaci ɗaya yana faɗin" Thank you so much. Happy marriage Anniversy MRS YUSUF INUWA."
Haka ya faɗa ya na kamkame ni kamar sanda haka na tsaya masa, illa hannuna na dama da na saka kaɗan na dan rike shi kaɗan na ƙosa ya sake ni sai na fara mutsu mutsu shi ya sa ya sake ni amma sai ya sumbace ni a kumatuna sannan ya bi ni da kallo kafin ya ce" Thank you for coming in to my life Halima."
Yaƙe kawai na yi domin ni kalamansa ba sa wani shiga ta. Su Jidda na kallah suna ta cin nama da cin cin ita da dai Baby duk ta yi dama dama da Cake jin na ce ina jin barci sai ya ce na je na kwanta shi in sun gama shi da yara zai gyara wajen sannan ya zo ya same ni kaina na gyaɗa masa kamar akan ƙaya na ke na yi saurin barin musu falo ina ji a jikina ya bini da kallo ni dai na fita na jawo musu kofa ba tare da na juyo ba.
Ƙaran ƙofar dai dai da sauke ajiyar zuciyarsa. Komawa ya yi ya zauna ya na jin zuciyarsa na rawa. Gabaɗaya yau sai ya ji ya kasa mallakan kansa. Ya kasa yin wata jarumta yau sai ya ke jin kamar ba Namiji ba duk da haramci ya yi ba amma yau ya fahimci abin da ake kira kunya da nauyin Sadiya sun gama