Showing 78001 words to 81000 words out of 141487 words

Chapter 27 - TURKEN GIDA BOOK 2 COMPLETET BY JANAFTY.txt

Janafty   

18 Dec 2025

868

tafi, sai na rarumi Hijabin Marwa na zura tunda nawa na kai sa cikin ɗaki.

Na ɗauka ma har ya miƙe ne sai kuma na je na gan shi zaune suna hira da Yallaɓai ina daga tsayen na ce" Kawu har an gama yi mana yinin?
Ya na dariya ya ce" Taho ki zauna ai ban ga ta tafiya ba tun da ban yaɗa munafata ba."
Cikin mamaki na zagayo na zauna kujeran zaman mutun ɗaya. Kawu na ke kallo duk da ina ganin mutumin nawa na ta kallona ni kuma sai na ba ma banza Ajiyar a cikin raina ma sai na ɗauka kamar bashi a wajen ba dai ni zai wulaƙanta ba wallahi sai ya ga ne bashi da wayau da ni ya ke zencen ba ya ce Gimbiya ta yi masa komai ba to zan bar shi da ita ta yi masa abin da ma ni ban taɓa yi masa ba.

"Kawu me ya faru?

Na faɗa ina kallon shi, wani lokacin in ce masa Uncle wani lokacin kuma Kawu. Amma dai Uncle ɗin ya fi kama bakina.

"Ba nan muka fara magana na ce miki na ga wani iri a gidan nan ba?
Da sauri na gyaɗa masa kai kawai sai ya cigaba da faɗin" Ga irin nan muna zaune a falon nan ta shigo. Ita ce wacce ki ka aiko ta kawo mana shayi."
Ido na zaro ina kallon shi kafin na yi magana Yallaɓai ya tare ni.

"Wai Marwa?

Ya faɗa ya na kallon shi, shi ma kallon na shi ya yi kafin ya ce" Ina ruwanka? Da kai na ke magana."
"Allah ya baka haƙuri."
Yallaɓai ya faɗa ya na ɗauko wayarsa daga cikin aljuhu ya yi kamar hankalinsa na kan wayar amma ni na san hankalin shi na kanmu ne.

"Sunan ta Marwa ne?

Kawu ya tambayeni ya na kallona cikin mamaki da ya kasa ɓoyuwa a saman fuskata na gyaɗa masa kai kafin na ce" Sunan ta Marwa."
"Ya kuke da ita?
Ina mirmishi na ce" Ɗiya ta ce. Ɗiyar yayarmu ce Ya Aina uban mu ɗaya da mahaifiyarta."
Sai kawai ya koma ya ɗora kafa kan ɗaya kafin ya ce" Alhamdulillah."

Ina dariya amma ban yi magana ba amma ni kaina lamarin ya zo min a bazata Marwa fa? Yanzu duk ƴan matan duniya Kawu Marwa ya gani kuma ya yaba ikon Allah.

"Wato haƙiƙa tun ranar bikin tariyan wannan yaron na ganta lokacin ta kawo mana abinci na yaba da natsuwarta to na ɗauka lamarin wasa ne shi ya sa ban yi magana ba. Sai kuma da na koma gida ina ta tunaninta ta na yawan faɗo min a cikin tunanina na so ma na kira ki a waya sai sabgogi suka sha kaina sai yanzu da na ƙara ganin ta sai na ji zuciyata ta ƙara yin wani nauyi a kanta."

"Uncle.."

Na faɗa ina ta dariya ina jin wani farinciki a ƙasan raina ba ni kaɗai ba hatta Yallaɓai fuskar shi ta cika da Annuri domin ni dai yau ce rana ta farko da Kawu ya zauna ya taɓa yabon wata mace duk wacce aka yi masa tayin ta sai ya kushe ta. Amma wai Marwa ce ta yi masa ikon Allah ya fi gaban wasa.

"Kawu ka ce kawai ka faɗa tarkon so."

DaKafarsa ya zungure shi  ya na faɗin" Wai ba na ce ba ruwanka ba! Ina mgana da surukata kar ka ƙara saka min baki malam."
Yallaɓai na danne dariyan shi ya ce" Kawu"
" Ka sake kiran sunana zan iya yi maka baki."
Ya faɗa ya na hararan shi kafin ma ya ce" Kai tashi ma ka fita"
"Allah ya huci zuciyar ka."
Sai ya yi kyaci sannan ya dawo da hankalin shi kaina ya na gyara zama.

"Kamar dai ina son ta ne fa."

Ni kaina na kasa danne dariya ta sai da na sake ta jin kalaman Kawu har ya na wani gyaran murya, Yallabai ko har ya na duƙewa Kawu ya kai masa naushi sai ya kauce ya tashi ya sauya kujeran zama, sai ya koma ya na kallona kafin ya ce" Surukata dariya kuma kike yi?

Ina danne dariya ta na ce" Na isa Kawu. Yanzu dai ya kake so a yi?
Sai ya yi shuru kafin ya ce" To za ku iya aura mata tsoho kamar ni?
Kai na gyaɗa kafin na ce" Me zai hana in dai ta na son ka?
"To kina ganin za ta so ni? Kalle ni fa ba ma arba'in baya."
"Me zai hana ta soka Kawu? Ai kawai nema za ka shiga yi har sai ciyo mana yaƙin a cikin zuciyarta."

"Ko? Kina ganin zan iya?

Ina mirmishi na ce" In sha Allah za ka yi."

"To kina ganin in ta aminta da ni za ta iya zama a Rano.?

"Me zai hana Kawu? A ko'ina aure ya kaita ai za ta zauna in sha Allahu."

Sai ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Haka ne. Shekaranta nawa ne?
"Ashirin da uku."
"Ta na makaranta ne?
"E. Ta na makaranta koyon aikin jinya a garin tsafe amma yanzu ta dawo gida ne ta na pratical."
"Ta kusa gamawa? Ji na ke yi kamar ba zan iya jiran wani dogon lokaci ba."

Ina dariya na ce" Ina jin ta kusa gamawa gaskiya."
Sai ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Sadiya da gaske ina son ɗiyar ki tun ranar farko da na fara ganinta ban ƙara tabbatarwa ba sai yau da na ganta. Allah ya sa ku ba ni ita."

"In sha Allahu za mu baka ita in rabon ka ne Kawu"

Ina danne dariyata ganin duk ya susuce Yallaɓai ya kalla da ya kasaƙe da waya a hannun shi ya na jin mu.

"Kai wai ba ka so ka yi albarka ne?

"Me na yi kuma?

Ya faɗa ya na danne dariya Kawu Abba ya jinjina kai kafin ya ce" Ka ce wani abu mana. Ko fatan alheri ba za ka iya yi min ba Tafida?
Hannuwana ya ɗaga sama kafin ya ce" In ce me? Ni da ka ce ba ruwana in na ƙara saka maka baki a cikin maganar ka za ka yi min baki?
"To na janye kalamaina saka bakin ka na ji."
"Me zan ce?
Sai kawai ya tsaya ya na kallon shi, shi kuma ya na dariya kafin ya ce" Allah ya ba da sa'a Kawu na."

"Amin to in ma ba har zucci ba ne."
Ni dai ina gefe ina ta faman mirmishi zuciyata kamar farar takarda.
Kawai sai wayar Kawu ta fara ƙara alamun ana kira ya na duba sunan mai kiran ya kalleni sannan ya Kalli Yallaɓai kafin ya ce" Gaskiya Tafida ka cika tsurku"
"Me na yi?
"Me ka faɗa ma Tariq ya ke kirana?

"Ni? Me na faɗa masa kuwa? Ya dai ji kana faɗa da bakin ka"

"Au recording ka yi ka tura masa munafuki da matan ka biyu kana gulma?

"Wani recording? Direct ya ji Soyayya ya fara zautaa ka."

Kawu sai kawai ya tsaya ya na kallon shi har wayar ta katse bai ɗauka ba shi kuma Yallaɓai na yi masa dariya.

"Ɗauki wayarka fatan alheri zai yi maka fa. Ko ba ka so?

"Ina so mana. Ko da bai kai zuciyar ku ba."

Ya faɗa lokaci ɗaya ya na ɗaga wayar amma ya sa ka a speaker.

"Kawu ina kwana."

Tariq ya faɗa daga can bangaren Kawu ya haɗe rai kamar ya na ganin shi kafin ya ce" kirani Abba na  ko Abdulmu'iz domin ni ba Kawun ka ba ne."
Kaina na ƙasa ina danne dariya Yallaɓai ko har ya na ba ta sauti saboda dariya.

"Mu ba ƴan'uwan juna ba ne?

"Ni ban haɗa komai da kai ba Mallam."

"To na ji ina yi ma Tafida kara ne."

"Shima ai ni ƙanin uwarsa ne ba na Ubansa ba."

Yallaɓai dariya har ya na ƙyaƙyawata ya na kallona da mun haɗa ido sai na haɗe rai na juyar da fuska.

"Haka ne. To a bar mganar."

"Yauwa yi fatan alherin ka ina mgana da Surukata ne ka katse ni."

"Kawu ashe kuma an faɗa tarkon so? Ƴar yarinya ta susuta haka?

"E ko ban kai ta susutanin ba ne?

"Ni? Ban ce ba haba ai ka isa ma har ka gota. Kawu Allah Ubangiji ya sanya alheri ya sa a wannan shekaran za mu sallama ka."

"To Amin."

Ya faɗa ya na ɗan mirmishi kafin Tariq ya cigaba da faɗin" Mutumina kawai Tafida na kirana ina ɗauka ba sai na ji kana ruwan haruffan ƙauna ba. Wai wata yarinya ce ta susuta ka haka! Na san ta kuwa?

"Ba ka san ta ba."

"Tafida."

Tariq ya ɗaga murya ya na kiran Yallaɓai shima ya amsa ya na faɗin" Ɗan'uwa nawa ka tara? Kasan mun yi alƙwarin biyan sadaki da kuɗin gaisuwa fa?

Tariq ya ce" Ai asusu na yi. Shekaru sama da goma. Ka ce lokacin fasa asusu ya kama mu."

"Tabbas. Domin da gaggawa ya ke so da wahala ma ya iya jira."

"Allah. Ka ce Kawu dai ya faɗa
da yawa."

"Ba ma a mgana sai ma ka gan shi duk ya susuce."

"Yo min Video ɗin shi mana."

Kawu sai kawai ya kashe wayarsa Yallaɓai ya kalle shi ya na faɗin" Ya haka? Me ya sa ka kashe?
"Ba ka da waya ne? Ya kira ka ta wayar ka. Ni ka ganni nan ba ni da lokaci ɓatawa a kan ku. Yauwa surukata yanzu ya za a yi ne? Kin ji dai matsaya ta."

Ina mirmishi na ce" Na ji Kawu yanzu ya kake so a yi? Yadda kace haka za a yi."

Sai ya yi shuru kamar ya na nazari ni kuma sai na ce" To ko zan kira ta ne sai mu ba ku waje?
Da sauri ya ce" A'a sai na yi mgana da magabanta ta zan fara mgana da ita.
Sai na jinjina kai kafin ya cigaba da faɗin" Za mu yi waya dai in na koma in sha Allahu."
Ina mirmishi na ce" Allah ya sa. Kar ka ji komai Kawu kana da ni. Kuma Marwa yarinyar kirki ce ga natsuwa ba ina yabon ta ba ne fa."

"Haba na sani. Ai na ga abubuwa da dama a tattare da ita."

Ya faɗa ya na shafa sajen sa, Yallabai na gefe bai saka mana baki ba amma ya na sauraran mu. Tallar hijabai na yi masa sai ya ce" Hijabai kika fara saidawa kuma?
Sai na gyaɗa masa Zaraf Yallaɓai ya ce" Ko za ka siya ma Marwatu ne?
Hararansa ya juya ya yi kafin ya ce" Ina ruwanka? Ba hijabai ba, ka san dai ko kasuwar Hijaban ne zan iya siya mata  ita gabaɗaya ba ko?

"Tabbas ko mai garin Rano Allah ya ja da zamanin ka."

"To ka yi shuru. Ka jira lokaci kawai."

"Allah ya nuna mana lokacin."

Har da nima na amsa da Amin ɗin, cewa ya yi na ijiye masa guda goma na yayyensa da ƙannensa duk zai siya musu har da Innayi.
Yallaɓai na gefe ya ce" Nene ta gode."
"In kai uwarka ce ni yayata ce."
Sai Yallaɓai ya koma kawai ya yi shuru ya na danne dariyan shi, nan ta ke na faɗa masa kuɗin ya saka min ya ce na ijiye masa in zai wuce zai dawo ya ɗauka ina ta masa godiya ya ce.

"Haba bakomai an zama ɗaya.  Kin fara saidawa Hijaban ne ina shagon Saloon ɗin?
Sai na yi shuru ban yi magana ba sai ya juya ya na kallon Yallaɓai kafin ya ce" Kai ya maganar shagon da ka ce min ka kama mata ƙasan offishin ka? Sai na ɗago ina kallon shi domin ni ban ma san da labarin ba.

"Na saka Musbahu a ciki sannan ai na faɗa maka na ɗauki wani yaro Auwalu. Su na gyara ma ƙasa ni kuma ina sama saboda ina so na faɗaɗa kamfanina in sha Allahu."

"Allah ya ba da sa'a. Ita kuma fa?

"Zan buɗe mata in sha Allahu."

Sai ya kalleni kafin ya koma ya na kallon shi lokaci ɗaya ya na faɗin" Mallam ba wani in sha Allahu. Tun yaushe ka ke alƙwari ba ka cika ba? Na san fa ba rashin kuɗi ba ne, Mallam ka samu kuɗi ka san na sani ko?
Yallaɓai ba ya son kallona kai ya kauda kafin ya ce" Ba ni na yi alƙwari ba? To zan cika in sha Allahu."

"Better domin yanzu ina bayan ta ne. Ba zan lamunci ka danne mata haƙƙi ba tsab za  ka iya ji sammaci daga hukumar kare haƙƙin ɗan adam."

"Ba Shakka."

Yallaɓai ya faɗa ya na kallon shi, shi kuma ya miƙe lokaci ɗaya ya na gyara zaman hulan kan shi kafin ya ce" E haka na ce. Sadiya ba ri mu je amma zan dawo kafin na wuce."
Sai nima na miƙe ina musu fatan a dawo lafiya nan na bar su a falon suna ta halin su shi da Yallaɓai ni kuma na koma cikin gida saboda murna kamar na faɗa ma Marwa sai kuma na ce ba ri dai in yi shuru na jira ce shi kamar yadda ya ce kar na yi gaggawa amma ita kanta Marwa sai da ta ce Umma kina ta fara'a ina dariya na ce mata abin fara'an ne ya same ni.

Ba su suka dawo ba sai bayan la'asar lokacin har Marwa ta gama shinkafa da miya da salak, ta kuma gyara gidan ya na ta kamshi, shi kuma Kawu tuni na haɗa masa Hijabansa waje ɗaya kololin daman ni ya ba ma zaɓi na zaɓar masu kyan ciki, ni kaina na ƙara ma na ni da yara har da Marwa na zuwa sallar idi. Bayan sun ci abinci tare da Yallaɓai ya ce zai wuce amma zai shiga Gwamnaja ya duba Nene tare suka sake fita da Yallaɓai ina jin su da na raka su Haraba Yallaɓai na faɗin ya kawo na Nene ya kai mata ya ce ai ya san hanyar gidan haka suka fita suna ta halin su da suka saba.

Sai dare Yallaɓai ya dawo misalin tara da wani abu ashe ma a gidan ya ke ni na ma manta, ni dai ina ɗakin da yanzu ya zama wajen kwana na shi kuma bayan ya yi wanka Marwa daman na saka ta hada masa tea, a falon yara na ji su tare da su suna ta hira har na yi barci ban san lokacin da suka kwanta ba da safe Marwa ce ta yi hidiman gidan da yara har da shi kan shi Yallaɓai domin ina ciki na kulle ƙofa ko ma ya zo ba zai tarar da shi a bude ba sai da ya bar gidan sannan na fito.

Haka a daran ma lokacin da ya dawo na shige ciki Marwa kawai ya gani da yara. Tun ya na ɗaukan lamarin wasa har dai ya fahimci na riga na hau dogin zuciya har ya bar gidan ya koma can ni ba na mgana da shi, ban ma yarda mun haɗu ba saboda ba na so ma na gaishe shi, Marwa ta koma gida ni kuma ina ta zaman jiran Kawu amma shuru sai dai na yi ta saka ma abin albarka na yi addu'an in da alheri Allah ya tabbatar tun da na gama al'adata har na yi wankan tsarki tun jiya.
Hijabai sun ƙare na ci kasuwar salla,  na yi magana za a kawo min wasu amma sai bayan salla har Ma'u ta aiko Zainab ta karban musu guda biyar, har Baaba ta siya mawa kuma Alhamdulillah ina samu sosai ɗan riban da ba za ka raina ba.

Har Yallaɓai ya sake dawowa gidana ba na masa mgana. Rana ta farko bai neme ni ba sai ana biyu shima na son saboda matsowan sallah ne, ina ɗakin da na mai da shi nawa da daddare Jidda ta shigo ta ce wai Abban su na kirana a falon shi, kamar na yi fuska na ƙi zuwa sai na fasa na tashi na saka mayafi na fita falin na same shi zaune ya na kallo amma ga wasu manyan lodoji a gabansa kamar na wani tambarin kamfani amma ban tsaya na duba ba.

Sannu da zuwa na yi masa ya amsa yana kallona ni kuma sai na kauda kaina a tsaye na tsaya ban ko da niyar zama.

"Madam ki zauna mana."

In dai Yallaɓai ya san ya tafka rashin kirki ya iya kame kame, in ka ji ya na cewa Madam ya cuce ni ne zai yi min ƴar murya. Kamar ba zan zauna ba sai dai na dofana ɗuwawuna a saman kujeran da ke gefensa.
Shuru na wani lokaci ya kasa mgana kunya duk ta kama shi.

"Har na fara barci Jidda ta taso ni."

Na faɗa ina kallon shi fuskata ba Annuri sai ya nuna min ledojin gaban shi kafin ya ce" Na ku ke da yara"
Abin sai ya ba ni mamaki, amma ban yi magana ba na sunkunya na jawo ledojin ina dubawa na ga dai abaya guda biyu ta manya sai na yara sai takalma sai kuma pakiatan na yara na su Jidda kenan sai reborn da man kitso da ɗan kunnaye.
Ban tambayi daga ina ba kawai na maida su leda ina faɗin" Mun gode Allah ya sa albarka."

"Amin. Rigunan da takalman ni na siya muku Daughter ta yi oder din su daga Epgyt sai na ga sun yi mini kyau sai na ce a cire muku sauran kuma ita ta ce na kawo ma su Jidda su yi kwalliyan sallah."

"Allah ya saka da alheri."

Na faɗa kai tsaye sannan kuma na mike nan na bar masa kayan zan wuce sai ya kira sunana.

"Sadiya."

Sai na juya ina kallon shi, ni ya ke kallo kur kafin ya ce" Ki dawo ban gama mgana da ke ba."
Sai na koma na zauna ina kallon gefe ina jin sa ya na mirmishi kafin ya ce" Uhm Halimatussadiya. Sadiya ta Yusuf shi kaɗai duk fushin ne ba a gama ba?
Kamar ya na mgana da dutse ko motsi ban yi ba.

"Ya mganar shirye shiryen salla? Me kika shirya ne?

Sai na kalle shi kafin na ce" Shiri ai ya na hannun ka."

"Ke fa? Ai  mun saba ke ce ke shirya komai."

Kallonsa kawai na yi ban yi mgana ba da dai ya ga ba yi zan yi ba sai ya gyara zama ya na faɗin" Lokaci ya ƙure ku yi hakuri na so na ƙara muku kaya ko ɗaya ne."
Ban ce masa komai ba sai ya cigaba da faɗin" Musbahu zai kawo cefane, sannan zan yi layya ke ma zan yi miki in sha Allahu."

"Allah ya saka da alheri."

"Amin My Sady."

Ko kallon shi ban yi ba sai ma na ce" Ka gama mganar zan iya tafiya?
Sai ya gyaɗa min kai na miƙe zan tafi ya sake kirana bayan na juyo sai ya ce" Ba ki ɗauki kayan ba to."
Shi ya sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login