Showing 90001 words to 93000 words out of 141487 words

Chapter 31 - TURKEN GIDA BOOK 2 COMPLETET BY JANAFTY.txt

Janafty   

18 Dec 2025

866

su saboda in dai na je sai ta tambaye su. A waya na kira shi na ce ya dawo da wuri na gama sannan mu tafi da yara asibiti tun a cikin wayar na ji muryan shi cikin farinciki bayan kuma da ya dawo bakin sa ya ƙi rufuwa. Bini bi ni sai ya yi ta min godiya na ce kar ya damu ai mun zama ɗaya.

A daran muka je asibitin ni da shi da yara na kai mata faten mun iske ma Maman farko da Nene wanda suka zo tare da Hajiya da Musbahu anan ne na ji suna hiran mutanen Rano sun zo amma ba wacce ta kwana sun ce komai Gimbiya ta ke bukata ta samu ba amfanin zaman su ni ko a raina na ce ba shakka ita da ta ke da uwa a gindin murhu ai ba ta da matsala. Gimbiya ta ji daɗin faten nan ta sha da yawa ta rage ta ce na safe ne har da Nene a masu yi min godiya saboda Yallaɓai ke ba da labarin ya na zuwa ya faɗa min Gimbiya na son fate sai na ce ina da tsakin da yakuwa na kuma ce zan yi.

"Sannu Sadiya kin kyauta."

In ji Mimisco.

"Ai Sadiya ba ruwanta nima nan kullum safiya ita ke fara kawo min abin karyawa da daddare ma za ta ba ma Tafida ya kawo min kuma sannan kullum sai ta zo asibitin nan."

"Gaskiya ta kyauta. Allah ya ƙara muku zaman lafiya."

"Amin Amin."

Aka amsa gabaɗaya. Nene ce sai daga baya ta yi magana bayan na yi mata gaisuwan ta na dabam ina tambayan jikin ta.

"Jiki da sauƙi na gode Sadiya da kulawa."

"Allah ya ƙara miki lafiya."

Ta amsa da Amin kafin ta ce na sunkuyo sai na duka a gabanta abin da ya sa hankalin waɗanda ke ɗakin ya dawo kan mu kenan

"Sadiya."

"Na'am."

Na amsa ina mai kallonta kawai sai ta bubbuga kafaɗata ta na faɗin" Na gode Sadiya. Daman na faɗa miki ina da kyakyawan tsammani a kan ki sai gashi ina ta ji da ganin abin da daman na yi tsammani daga gare ki."
Mirmishi kawai na yi ba tare da na yi magana ba sai kawai ta ƙara dan buga kafaɗata kafin ta ce.

"Allah ya yi muku albarka gabaɗaya."
Na amsa Amin a hankali suma na ɗakin suka amsa da Amin Amin sannan na tashi. Ina ɗagowa muna haɗa ido da Yallaɓai sai ya yi min mirmishi nima na mayar masa. Gimbiya kuma ta na tare da Baby a saman gadon suna ta hira.

"Ke Baby sauko kar ki danne Antyn ta ki mana."

Na faɗa ina kallon su da sauri Gimbiyar ta ce" Ƙyaleta ai ba ta matse ni ba."
Maman farko na dariya ta ce" Ina ruwan Maimunatu ba ruwanta dai ba irin Jidda ba ce ita akwai baki "
Mimisco ta ce" Jidda Tafida ne in suka so hira suna yi in suka so miskilanci suna yi. Baby kuma ta wani bangaren Sadiya ne ta wani bangaren ta ɗauko hallayan mai suna domin Maimu ma akwai surutu."

Gabaɗaya muka yi dariya kuma haka ɗin ne, domin Anty Maimuna akwai mgana ita Anty Bahijja shisshigi ne da saka ido, muna asibitin har wajen goma har su Nene ma sai da suka riga mu tafiya da za mu tafi Gimbiya ta kalleni ta na faɗin" Na gode Madam. Faten ya yi daɗi"

Ina mirmishi na ce" Ko? To ko gobe a sake yo miki wani ne?
Kanta na ƙasa ta ce" In ba zai zama takura ba ina so."
"Wani takura. Bakomai zan yo miki in kuma akwai wani abun da kike so ne ki faɗa min ko shi sai ya faɗa min sai na dafo miki."
"To na gode."
Ta faɗa ta na mirmishi.
Daga shi har Maman Farko suna jin mu amma ba su yi magana ba suna ta dai mirmishi sallama muka yi musu Baby Yallaɓai sai da ya ɗauketa daga zuwa dubiya ta haye gadon asibiti ta na sharan barci. Bayan mun koma gida Yallaɓai sai wani nan nan ya ke yi da ni a raina na ce Namiji. Namiji sai shi wai saboda ina ma matarsa kirki shi ne na zama fara yanzu a idon shi haka ya riƙa nanike min da daddare ya saka mu ɓarnan ruwa haka ma bayan salla asuba shi dai kawai na lura ya na cikin farinciki har wani suna ya sauya min ya na maƙale murya da kirana Abar ƙauna a raina na ce daga baya kenan an yi sadaka da bazawara.

Kamar yadda na yi alƙwari na sake yi mata faten Yallaɓai ya kai mata ta kirani ta na ta min godiya na ce bakomai ranar ban je asibitin ba sai washegari na iske Naja'atu da wasu ƙawayen Gimbiya har da abokan aikinta haka na ji Najan na faɗa ma Maman farko na dai shiga mun gaisa na fito domin na ga ana ta nuna ni, ko ba a yi mgana ba na san sai na fita za a ce ita ce kishiyar ta ki? Ranar ma mun sake haɗewa da Anty Bahijja ina kuma asibitin sai ga Ma'u ta zo tun ina mamakim munafunci Ma'u har na zo na daina amma ta ba ni mamaki da na ganta sanin ni dai ban faɗa ma kowa ba sai Ya Aina ita ma Marwa ce da muka yi waya na faɗa mata sai ta sanar da ita shi ne ta kira ta ji, har ta ce ko za ta yi ma su Ya Balki mgana ne su zo asibitin su duba ta na ce su yi zaman su ai ta ji sauƙi haba abin sai ya yi yawa gani ni ina ta zarya sai kuma na gayyato dangina.

Na san za ta sani tun da ta na tare da Anty Bahijja amma zuwan na ta ne ya fi ba ni mamaki kuma ita kanta ta ɗan yi wani iri da ta ganni.
Mun gaisa da ita sama sama ina mai mamakinta Anty Bahijja ta yi mata jagora zuwa ciki ba daɗewa sai ga su sun fito har da ma wasu ƙawayen Gimbiyar da ita Naja'atun a gabansu Anty Bahijja ta kalleni ta na faɗin.

"Sadiya ashe ba ki faɗa ma kowa a gidanku Gimbiya ba ta da lafiya ba?

Sai na kalleta amma ban yi magana ba saboda na ga renin wayan ne ya yi yawa. To Gimbiyar uwata ce da zan yi she ɗan ciwonta a dangi ko Yallaɓai ne ai sai na ga daman na faɗa ballantana ita.

"Sai da na kira Ma'u ina ta mata tsiyan ba ta zo ba shi ne ta ke min rantsuwan ba ta sani ba. Kai tsaye na ce to laifin Sadiya ne wannan ita ce ba ta sanar da ku ba."

Ma'u na yi ma wani kallo kafin na sauke kallona kan Anty Bahijja kafin na ce" Ban faɗa ba amma tun da ita ta sani gashi har ta zo na wakiltata ta sanar da su."
Daga haka na juya fuskata ina kallon wani bangaren raina kawai na ji yana tafasa ji na ke yi kamar na je na shake Ma'u.

"Ai ko zan faɗa ma su Ya Murja. Don dai dubiya mene a ciki? In sha Allahu na san za su zo"
Ni dai ƙala ban ƙara ce musu ba har suka gama mganan da ƙawayen Gimbiyar za su tafi kamar Anty Bahijja ta kwanta musu haka ta raka su ta na yi musu godiya ni fa matar nan har mamakinta na ke yi, ba ta da yadda za ta yi dani ne da tuni ta saka an koreni Gimbiya ta mamaye komai sai dai kuma ta Allah ba ta ta ba na riga na zame mata ciwon ido.
Ma'u da za ta tafi har da ba da kuɗi ina zaune ina ganin ikon Allah da ta yi min sallama ina ji amma ban amsa mata ba na haɗe rai suka fice ita da Anty Bahijja na raka su da harara kafin na ja tsaki.

Ranar kafin na bar asibitin nan sai da raina ya ɓaci Anty Bahijja daga ganin sauran fate da na yi ma Gimbiya jiya ta ce a bata ta shanye ta fara faɗa ba fa komai ne za ta riƙa sha ko ci ba kar ta manta ta na da juna biyu kuma ta na ƙarkashin kulawan likito ci ne.

"Ke Bahijja to ai fanten ne ta ke samu ya zauna mata. Kuma Sadiya ce ke yo mata ta na aikowa dashi wani zubin ma da kanta ta ke kawowa."

"Koma wace ce dai bai kamata a barta ta sha ba. Abu tun jiya duk ya yi sanyi sai kuma a bar ta tasha? Ai sai ya jawo mata wani illar Allah na tuba"
Sai ta ɗanɗana faten da sauri ta furzar ta na faɗin" Tabɗijan wannan kaifin tsamin kawai ya isa ya zubar da ciki."
Ina tsaye a ɗakin ina kallonta kuma ina jin ta amma matar nan ba ta fasa yada min mgana ba.

"Anty Bahijja ni na ke son tsamin fa.'

Gimbiya ta faɗa a hankali ita Maman farko shuru ta yi ba ta ƙara mgana ba.

"Kuma Likitoci sun ce ba wata matsala ko Mama?

Naja'atu ta faɗa ta na mai kallon Maman farko da ta yi kamar ba ta ji ba saboda abin ya ba ta haushi. Amma Anty Bahijja ƙiri ƙiri ta hana Gimbiya shan faten nan ta ce ba za ta sha ba.

"To wanne zan sha?

"Ba dai fate ba. Zan saka Suhailat ta yo miki ba shikenan ba"

Har Gimbiya sai da ta kalleta amma ba ta yi mgana ba. Nima ban ce komai ba na tattara kololina na saka a kwando na yi musu sallama shi ne Anty Bahijjan ta ke ce min" Ba raina ƙokarin ki na yi ba. An gode amma ya yi tsami da yawa ne kin gane?
"Kar ki damu. Ki cigaba da yi mata mara tsamin wanda ba zai zubar da ciki ba."
Ina gama faɗin haka na fice ina yi ma Maman farko sai anjuma ta amsa min da cewa na gaida gida.

Muna tafe acikin adaidaita ina jin ƙuna a raina na kuma ce tunda shi alheri ya koma sharri shike nan kuma an gama daman ni saboda Allah na yi da kuma Yallaɓai amma tunda lamarin ya zo da cin mutumci an gama mgana. Tun daga ranar ban ƙara dafa wani abu da sunan Gimbiya ba amma kuma ban fasa kai ma Maman farko. Gimbiyar da kanta ta kirani a waya ta na bani haƙuri na ce kar ta damu bakomai.
Kawai ranar da Gimbiya ta cika sati a asibiti sai ga kiran Yallaɓai a waya wai don Allah na taimaka na yi ma Gimbiya faten wake kai tsaye ba kwana kwana na ce.

"Gaskiya ba zan yi ba Yallaɓai. Amma ka kira Anty Bahijja ta yi mata daga gidan ta."

"Saboda mene?

Ya tambaya cikin mamaki kai tsaye na ce" Saboda ba na son ƙananun mganganu ka kuma sanni ba ni da haƙuri kamar zawo na ke yi in raina ya ɓaci"

"Me ya faru?

"Komai ma ya faru. Na yo fate Anty Bahijja ta hana Gimbiya sha ta ce ya yi tsami da yawa wannan zai iya zubar mata ciki ma."

"Ita Anty Bahijjan ta ce?

"Ya wuce wai."

Na faɗa ina kaɗa kafa kamar ya na ganina.

"To ina ruwanki da ita? Ai ba don ita kike yi ba."

"Don Allah na ke yi amma ba shi zai saka na zauna ana ci mun mutumci ba. Daga alheri sai ya koma tsiya kuma?
Na ƙarishe faɗa a fusace shi kuma ganin na fusata ya sa ya sassauta murya ya na faɗin" Na ji to ki yi hakuri kin ji ko?
"Na yi haƙuri amma girkin ne ba zan yi ba."
"To ni ne na ce ko Daughter? Bai kamata ki damu da mganar Anty Bahijja kin san halinta."

"Dole fa na damu. In wani abu ya zo ya faru ba fata ake yi ba mganganu suka tashi fa? Kasan ba zan zauna a ci zarafi ba in kuma na yi magana a ce na cika ƙorafi daga na ce an yi min kaza sai na ce an yi min kaza."
Da gayya na daba masa mgana kuma na san ya san dashi na ke yo ina dalili daga abin arziki ban da ma ina da zuciyar Imani ni har wata kishiya ne zan zauna ina ma girki ina zuwa kai mata asibiti duk wannan sadaukarwan da na yi ba ta gani ba ta na neman ci min mutumci to ba ta isa ba mganin ayi ma to kar ma a fara shi.

"Ki yi hakuri na ce ko?

"Na faɗa maka na haƙura."

"To za ki yi ɗin?

"A'a."

"Me ya sa?

"Ai na faɗa maka dalilina."

Ina ji ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Duk na ji kuma zam mata mgana amma dai yanzu ki yi hakuri saboda ni saboda Daugther ki yi mata don Allah."
Sai na yi shuru ban yi magana ba amma ina ta ƙunƙuni.

"Abar ƙaunata ki yi don Allah. Ni na yarda dake shi ya sa a komai nawa na ke sakawa a ciki. Da gaske na ke ke ɗin amintattaciya ta ce Sadiya."

Nan ma na yi masa shuru har dai ya gaji ya ce" Kin ji ko?
"Na ji."
"Za ki yi ɗin?
"Uhm."
Ina jin sautin mirmishin shi kafin ya ce" Yauwa Abar ƙaunata. Allah ya yi albarka."
"Amin."
Na amsa da Amin aciki ciki shi kuma har da yo min kiss ta cikin waya kafin ya ce" Sai na dawo."

Ko amshi ban yi ba na kashe wayata ina ƙunƙuni ina dalili Yallaɓai na neman ya maida ni yar aikin matarsa daga abin arziƙi ban so yi ba amma haka nan na tashi zan yi mata ban kalli kowa ba sai shi. Mijina ne a kowani hali zan cika Umarninsa, ko faɗa muka yi da Yallaɓai sai dai na yi gaba dashi da kaurace masa amma ba na hana shi abinci zan yi masa komai da na saba, ina bin Umarnin shi saboda na san haƙƙin mijina a kaina shi ya sa na danne komai na yi mata fanten wake ya aiko da hanta da allayahu na saka mata a ciki da ya dawo bayan isha'i ya yi wanka ya ci abinci ya je ya kai mata a wayar ma ya kira ni ta karɓa ta na ta min godiya na ce mata bakomai an zama ɗaya. Bayan mun gama wayar na daɗe zaune ina tunani sai na tuna mganar Alhajinmu da ya ce na yi mata alheri na kuma zauna da ita da alheri in ma ta na da wani sharri Allah zai mayar mata da kayanta.

Kuma ni dai ba ta min komai ba. Laifinta ɗaya ta aure min miji amma ko bayan auran ta na girmamani ta na sona ta na son ƴaƴana ko da ya ke dole ta so ƴaƴana tun da ta na son ubansu sannan nima ta na girmamani sosai sai dai kishi na yau da gobe amma ba zan ce ga wani laifin da ta taɓa yi min ba, tunanin haka ya sa na watsar da mganar Anty Bahijja a cikin raina kuma Yallaɓai in dai bai manta ba sai ya yi mata mgana daman gashi ba shiri ita ta saki nono ya kama akwai faɗan saƙo da saƙo a tsakanin su.

Kafin Yallaɓai ya dawo Marwa na kira da wayar Ya Aina ina tambayanta yadda suke ciki da Kawu nan ta ke faɗa min ma gobe ya ce zai zo ya kawo mata waya ina dariya na ce" To Madalla haka na ke son ji."
Ita kunya ya hana ta mgana sai Ya Aina ta ba ma wayar muka gaisa.

"Ya jikin abokiyar zaman ki? Ɗazu Murja ta kira ni wai Ma'u ta faɗa mata kishiyarki ba ta da lafiya ta na kwance a asibiti ya kamata mu leƙa."

Ban yi mamakin abin da Ma'u ta ce ba kuma ban yi ma Ya Aina munafunci ba kai tsaye na ce" Ya Aina kar ku wani zo don Allah ta ji sauki kuma ga ni ina zuwa Ma'un ma ta je duk bai isa ba! Sai kun zo?

"Kuma fa haka ne. To shikenan kya mata sannu. "
Na amsa mata da zan faɗa mata.
"Me ke damun ta hala?
"Ciki gare ta sai ya ɗan samu rauni an dai ce ta samu cikakken hutu."
Ya Aina ta ce Allah ya ingata ya raba lafiya.
Daga nan muka yo sallama ba daɗewa Yallaɓai ya dawo ya na faɗa min na ga yadda Gimbiya ta sha fanten waken nan kuwa?

"Ko?

Na faɗa ina kallon shi, ya na zama saman kujera ya ke sake faɗin" Wallahi. Ta yi ta santi ta ce na ƙara gode miki."
"Ayya ai bakomai."
Na faɗa kai tsaye akwai sauran ragowan faten wake sai na kawo ma Yallaɓai ya sha kaɗan sai ya ɗan sha ruwan zafi ko da ya dawo su Jidda sun yi barci ni da shi ne muka yi ta kallo muna hira sai wajen sha biyun dare muka kwanta.

Da safiyar asabar ba makaranta Tahfez kuma yara sun makara ya sa na ce su haƙura sai gobe kawai. Yallaɓai ya fita ba daɗewa sai ga shi ya dawo ina kitchen ina wanke wanke Saude ba ta nan sun je ƙauyen Gwarzo biki, Jidda na can ɗakin su na ce ta gyara Baby kuma na gaban Tibi ta na kallon Cartoon
Ashe mantuwa ya yi ya dawo ɗauka a lokacin ne ya ke faɗa min suna saka rai yau ko gobe za a sallami Gimbiya na ce Allah ya sa domin ta fi sati a asibitin kuma ta ji sauƙi alhamdulillah.

Ranar ban ma saka a raina zan je asibitin ba sai da Hauwa ta zo ta ce ba ta je ba, saboda ba ta nan taje Rano, jin haka ya sa na ce bari na shirya muje tare har ma Hauwa ta kira Munnira ita kuma sai ta ce shekarajiya Jamila ta biyo mata suka je amma tun da za mu je ba ri ta shirya mu jira ta sai mu tafi gabaɗaya. Haka ko aka yi sai da muka jira ta ta zo muka tafi tare na bar ma Jidda gidan ita da Baby.

Mun je mun iske asibitin cike da mutane su Anty Bahijja ne da su Anty Maimuna. Halima Suwaiba, Nasara sai Jawaherr da ta ce jiya ta zo gida hutun semister, Maman farko ba ta nan ta koma gida ta yi wanka ta huta, mun gaggaisa da kowa da kowa cikin sakewa amma ita Anty Bahijja sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login