Showing 42001 words to 45000 words out of 141487 words
ina jin wani iska na shiga jikina, ina ji in da ace ban zo ba da na yi kewar wannan yanayin na farinciki da na ke cioi mu ne har wajen biyun dare muna hira da Rahila, mu na tuna baya muna ta dariya ji na ke yi kamar baya ta dawo yanzu rayuwar ta fi daɗi.
Ko kafin ranar alhamis ɗin da su Ya Aina suka iso, mun riga mun zama yan gari domin mun sha yawo, mu ne gidajen yan'uwa da suke aure a kusa, sannan har gidan su Gwaggo mun je, sun zo sun iske mu mune ma ke yi musu maraba.
Ya Aina sai Ma'u da Ya Murya, sai Zaitunan Ya Abubakar Gwaggo sai jibi za ta taho tare da su Alhajinmu.
Mun sha biki sai wanda ya gani. Malunfashi a ka kai Amarya ni da Rahila da Ya Aina har da Ma'u mun je kai amarya Ya Murja ce ba ta je ba, ranar lahadi muka dawo Yashe, litini su Ma'u suka koma kano da ya ke biki ne kuma ga jama'a har muka rabu dai ba mu raba hali ba. Ma'u dai ta je ta ga dangin babanta kafin su koma. Baaba ba ta samu zuwa megidanta ba lafiya.
Mu kuma muka ce sai mun cike sati gobe kenan talata, na ji daɗin zuwana Yashe domin ya sa na shafe tunanin auran Yallaɓai a cikin raina muna waya da shi lokaci bayan lokaci yara ma mun yi magana da su sau biyu Baby ce ke ta karaɗin ba ni labarin Anty Gimbiya ta yi musu kaza ta yi musu ita Jidda ba ta da surutu.
Ranar litinin ɗin da yamma Munnira ta kirani a waya ta na faɗa min an kama ma Gimbiya hayan wani gida ita kaɗai a sharaɗa. Ni kuma dai Tauraini ya ce min da farƙo wataƙila wancan bai yi ba ne suka kama wani, ni kuma daman na ce ya daina zaunar da ni ya na faɗa min abin da bai shafe ni ba shi ya sa duk labarin da Munnira ke ba ni na ce mata ban san da labari ba. Ta na ga ya min anan Gwammaja za a yi taron biki, Hajiyar Tafida za ta yi nata acan Rano amma taro na gidan Nene, har da labarin Yallaɓai ya ba ma Gimbiya kuɗi masu yawa na lefe da na hidimar biki. Har Munnira na faɗin" To ke nawa ya baki? Gwara mu ji saboda mu ma mu shirya namu taron ko ya kika ce?
Ina mirmishin ya ƙe na ce" Ni ba na gari ai na zo Yashe biki ƙila sai na koma za mu yi maganar da shi." Mun rabu da ita a kan in na koma zan yi musu waya ita da Hauwa da farko na ji a raina ba zan yi wani taro ba amma ɗazu da muka yi hiran da Rahila sai ta ce na yi domin kauda idon masu mgana gazawata a ke nema abu kaɗan zai zama abin magana nima na shirya taro ni da ahalina domin a zo a ɗebemin kewa sai kuma da ta faɗa na aminta da maganarta sannan mun yi chart da Ant Zabba itama ta nuna min fa'idar haka tace har kunshi da kitso duk na yi na gyara kaina yadda duk wanda ya ganni zan yi masa kwarjini, sai na ji duka na aminta da shawarwarin sa na ɗau damaran in na koma gida za mu yi mgana da Yallabai daman taron gidana ai nawa ne, na su na can Gwammaja.
Na bari sai in na koma Kano sai na kira Inna Mariya na faɗa mata halin da a ke ciki kar su ji a wani waje, su ce ban faɗa musu ba. A daran na ga Yallaɓai ya turamin 1m miliyan ɗaya a acct ɗina, sai na kira wayarsa ba ta shiga ba sai na tura masa saƙo.
"Na ga saƙo Yallaɓai na mene ne?
Da ya saƙon ne ya kirani, ni kuma na gaji na kwanta da wuri sai da safe na ga kiran shi da saƙon shi.
"Na ki ne. Yau dai za ku dawo ko? In kin dawo sai mu yi mgana."
Ko bai faɗa min ba na san na faɗan kishiya ne, tun kana ji abin daga nesa ga shi yanzu har ya zo kaina wai Yallaɓai ya turamin kuɗi amma kuɗin na faɗan kishiya ne, duk dauriyata sai da na shige makewayi na ci kuka na ƙoshi, da zamu koma gida fitan safe muka yi Baba Aminu ya ba mu wake mai yawa ni da Rahila mu ne barkoni waken suya,daddawa kuɓewa zogale bushasshiya, da sauran su duk mun yo tsaraban shi ko da la'asar ta yi muna Ɗorayi sai yamma Yallaɓai shi da yara da ya biya Gwammaja ya ɗaukosu suka zo suka ɗauke ni zuwa gida.
In ka yi tafiya duk sai ka ji gaɓɓanka sun saki, barci na yi ta yi kamar wata mattaciya kuma Alhamdulillah natsuwan da na je domin na samo kuma na samo ta, sosai na ji zuciyata ta samu sauƙi, bayan na huta da kwana biyu muka yi mgana da Yallaɓai shi ne ma ya ke faɗa min ya samu wasu kuɗi daga aikin su na Kaduna ne, na yi haƙuri da kuɗin hannuna na siya abin buƙata na kaya da sauran su , na yi ƙokarin nuna masa bakomai cikin raankwafa na yi masa godiya.
"Na gode Yallaɓai. Allah ya ƙara buɗi"
"Amin. Ki yi hakuri kin ji ko?
Ya sake faɗa ya na mai kallona sai na girgiza masa kai kafin na ce" Kar ka damu bakomai."
Na faɗa ina danne yanayinaa shi kuma ya yi shuru ne kawai rasa abin cewa tun da na dakatar da shi faɗa min halin da Gimbiya ke ciki, ni dai a falo na bar sa ya shiga zurfin tunani na koma ɗaki kawai na yi tagumi, in lissafina ya yi dai dai saura kwanaki kaɗan tariyan Gimbiya. Kenan ya dai tabbata Yallaɓai ya zama namu ya tashi daga nawa ni kaɗai.
Na kai tunani zurfi na tuno lokacin da muka tare a wannan gidan. Lokacin da ya ya ma aka ƙarisa aikin gidan? Dakyar ne da soɗin goshi, sannan kuma lokacin ba ni da komai daga ni sai gado sai kujeru. Allah ya taimake ni yan'uwana suka tallafamin na fita kunya. Kayan ɗakina na siyar aka yi min sabon gado da kujeru, gadon shi ne a bedroom ɗin mu sai kuma kujerun a falon Yallaɓai, ɗakin yara kuma Ya Auwal ya taimaka min da kuɗi na yi musu gadajen ne, sai kuma na Ya Hamza shima da ya bani, na siya kayan kitchen ko na ce na ƙara sai cafet ɗin falo sauran kayan duk a hankali a hankali na riƙa siyan su, ko falon yara adashe na shiga na tara su kuɗi na yi kujerun nan da cafet sai dispanser abin da Yallaɓai ya siya daga Tv sai fridge duk ni na gama faɗi tashina kuɗaɗena duk suna kan shi, in na yi magana sai ya ce zai ba ni zai buɗe min shago in aka biya su, sai ga shi kuɗin aiki nawa a ka biya shi? Yanzu ba ta ni ya ke ba komai da ya samu kan maganar Tariyan nan ce a gabansa.
Na ci kukana na share hawayena ni kaɗai ba wanda ya sani. Tariyan ya kama 28 ga wata ne, na kira Inna Maariya na faɗa mata ta ce za su zo in sha Allahu. Sannan ba tunanin auran nan da Yallaɓai ya yi ba ne zai saka ni gyara ba domin ni ɗin daman mai gyara ce na kira Surayya Halin yau na ce ina son haɗin uwargida, ta ce an gama sannan na sake siyan man gyaran jiki a wajen Aisha Lame, saboda ko Yallaɓai ya sha ce min fatata kamar ta Baby saboda taushi. To mayuka Aisha lame ni masu saka taushin fata da santsi, a can group din gida na sanar da tariyan Yallaɓai na kuma ce ina gayyatan kowa da kowa a ranar a gidana zan yi taro, Ya Auwal ya kirani ya ce Laila za ta zo garin daman suna da biki itama na ce na ji daɗin haka Amina ma da ban yi zato ba, sai gashi ta kirani ta na faɗa min a bar ta za ta zo, kuma haƙiƙa na ji dadin jin haka har Faridan Tariq ma ta ce za ta zo kuma ta ce min a gidana za ta sauka tabbas na yaba da wannan karamcin.
Na kira Hauwa da Munnira sun zo mun yi shawara. Suka ce na siya kaya sabbi na ɗinka saboda in shiga in fita, haka ko aka yi na siya kala biyar atamfa uku leshi ɗaya, material ɗaya sai yara ma na yi musu duk da Yallaɓai ya yi mana shadda da ni da shi da yaran gabaɗaya. Ni ban ma san wa ya faɗa musu Abban su ya auri Anty Gimbiya ba sai da Jidda ta tambayeni na ce hakane ina tunanin lokacin da na je Yashe ne aka faɗa musu a Gwammaja ko baban na su ya faɗa musu da kanshi ban dai sani ba, maganar taron da zan yi kuma da kaina na samu Yallaɓai na faɗa masa ina so na yi taro ƴan'uwa ba su zo su taya ni zama da nuna masa farinciki.
"Shi ne ba ki faɗa min da wuri ba?
Ya faɗa cikin nuna mamakinsa ko bai yi tunanin zan yi taron ba ne.
"Na ɗauka ka san uwargida na yin taro ko?
"E. Amma ban ɗauka ke za ki yi ba."
Hararan wasa na yi masa kafin na ce" Ban kai yadda ka ke tunanina ba."
Mirmishi ya yi nima na ta ya shi, mun tsara za a yo cefane tunda muna da shinkafan tuwo za mu yi waina sai Nama da za a kawo da kayan Miya sannan shima ya ce min Kawu zai zo shi da Tariq suma suna son wainar na ce ba komai sai a yi da su gabaɗaya.
Ko bai faɗa min ba na san ya ji daɗin yadda ya ga ina ta masa dariya ina ta kuma shirye shirye, tun yana sharewa har dai ya furtamin da kansa.
"Na gode Sadiya ta. Ina ƙaunarki saboda Allah."
"Nima ai saboda Allahn na ke sonka ko Yallaɓai?
Na faɗa ina masa fari. Lokacin da daddare ne na fito wanka da sauri Yallaɓai ya ta so ya rumgume ni ya na shinshina min wuya, cakulckuli ya fara min na fara dariya ina ture sa.
Allah sarki rayuwa. Yanzu fa nan da kwanaki sai dai Yallaɓai ya zo mu gaisa da safe in dai ya na gidan Amarya.
Tabbas kishi ya na da zafi. Kuma zama Turken gida abu ne mai matuƙar wahala.
*Janafty*
*TKG*
08.
Ranar alhamis su Jidda suka yi hutun makaranta. Jidda daman ita ce ta ke ɗaukan first postion a ajinsu Baby kuma Third, sun karɓo kyatuttuka tunda an yi speach and prize giving day ban je ba amma Yallaɓai ya je musu tare ma suka dawo.
Ko da suka dawo mai kitso ta zo, da mai ƙunshi har an yi min ƙunshi saura kitso.
Marwa daman ta na nan domin ni na ce ce ta tattaro, ta dawo wajena sai an gama biki, Amina ma ta iso tun azahar Hauwa da Munnira suna gidan suma tun safe sai zlZaitunan yaya Abubakar.
Sameena ta kira ni ta ce suna nan tafe gobe ina mata tsiyan ita ko yar gidan amarya ce tana dariya ta ce.
"Matar Baba akwai amana ni ai ina bayan uwargidan Yallaɓai."
Haka dai muka gama wayar muna ta barkwanci, a bakin su Hauwa na ke jin mai gyaran jiki daga maiduguri Anty Bahijja ta ɗauko ma Gimbiya tun ana saura sati ɗaya ta sauka a gidan Nene. Taro ne Gimbiyar ta shirya sosai tun da ƙawayenta duk na Rano da Abuja da nan kano za su zo baban aminiyarta Naja dai daman suna tare ko da yaushe, tun da ba ɗaurin aure taron gabaɗaya na mata ne.
Ƙannen Gimbiya da matan yayyenta duk Kano za su zo, can Rano sai dai manya dangi dai na can amma taron gabaɗaya ya na nan ne, a ranar alhamis ɗin ma aka je aka gyara gidan Amarya Halima ta biyo daga can zuwa gidana ta ke faɗe, ni dai ina gefo ban ce komai ba,
Ban gayyaci kowa daga dangin Yallaɓai ba, sai wanda ya ga niyya ya zo. Amma ni dai na gayyato kaf ahalima har da Ma'u saboda na tusa mata haushi na ce ta gayyato min Shema'u.
Na kuma san ita kanta ta yi mamaki, na kuma san za ta je can ɗin za kuma ta zo nan tunda Anty Bahijja kamar ita ce ma uwar Amarya saboda yadda ta ke rawan jiki kan auran nan, daman burinta ne da daɗewa na daina juyi a gidan ɗan'uwanta ni kaɗai gani ta ke yi kamar wata tsiyar Ɗan'uwan nata ya ke ba ni, ni fa shi ya sa har gwara Anty Maimuna a kan Anty Bahijja matar nan sam ba ta da hali mai kyau akwai baƙin ciki amma ita ta na can gidan wani a dangi wasu ta na abin da ta ga dama.
Ni da ya ke ko a waya na rufe ta ba zan ga status ɗin ta saboda ina da tabbacin da gayya za ta yi ta ɗora abin da zan gani na ji haushi, ni kuma ba na so damuwa shi ya sa na kama kaina, ita kanta Gimbiyar ban san dalili ba ina jin ta aure min miji na goge lambarta a wayata cikin zafin ƙishi.
Kamar na san haka za ta faru Ranar jumma'a sun gudanar da walima anan haraban gidansu Nene a Gwammaja duk sun sha abayoyi sun sha kyau, tsabar ma renin hankali Anty Bahijja ta ce ma Yallaɓai wai nima na zo wajen Waliman tunda malama ce za ta zo ta yi wa'azi a kan aure, shi kuma da ya ke ya san a yanzu ina kan tsini ne magana ma ta arziƙi ta tsiya na ke mayar da ita sai bai yi min magana ba ya ce ta rabu da ni kawai su yi abin su.
Ni ban ma sani ba tunda Yallaɓai bai yi min maganar ba sai a safiyar jumma'an ta kirani a waya kuma daman na san da batun za su yi walima tunda Halima ta faɗa min, har ga Allah lokacin da na ga kiran Anty Bahijja a wayata sai da na ra ya a raina ba alheri a cikin kiran nata, amma ban ki ɗauka ba illau ko sai gashi ta na faɗa min wai ta aiko Tafida bai faɗa min saƙon ta ba ne?
Kai tsaye na ce" Wani saƙo kenan? Domin ni dai ba mu yi maganar wani saƙo da shi ba."
Lokacin ma bai jima da fita ba, ya tashi yau ɗin da cewar ba ya jin daɗin jikinsa na ɗauka munafuncin su na maza ne sai da na ji jikinsa ya ɗau zafi sannan na yarda. Ya dai sha paracetomol ya fita da cewar zai je a duba shi.
"To na aiko shi ya sanar da ke yau akwai walima a Gwammaja"
Mamakin ta ya kamani to in akwai walima ina ruwan Sadiya a ciki?
"Bai sanar da ni ba, amma na ji a bakin mutane."
Ba ba ta amsa a saukaƙe domin raina har ya fara ɓaci, ban yi ma ƙaninta bore don zai ƙara aure ba, amma ba shi zai ba ta damar ta zagayo ta na ƙokarin ci min mutumci ba, ba yayar mijina ba ko uwarsa ce zan nuna mata na san darajan kaina, sannan komai ya tsaya a muhallinsa zai fi alheri gare mu gabaɗaya.
"Duk ɗaya. Ki shirya ki zo kema a yi walimar da ke. Karfe huɗu ce kuma wa'azi ne za a yi muku kan zaman aure da zamantakewa."
"In shirya in zo kuma?
"E."
Ta ba ni amsa a takaici ina ta jin hayaniya ƙila ma ta na Gwammajan ne a gaban Gimbiyar da sauran su an saka ni a seaper za a ci min zarafi, cije leɓena na saka na yi, a ina tunani a cikin raina matar nan ba ta sanni ba ne, Ma'u ba ta ba ta cikakken labarin ni ni ba na barin ta kwana, kuma wanda ya ce da ni kule wallahi komai girman shi sai na ce da shi cas sai dai a yi wacce za a yi.
"In ji wa.?
Nima na tambaya a takaice, cikin fusata ina jin ta daga cikin wayar ta na faɗin" In ji ni, ko ban isa ba ne."
Mirmishi na yi yadda zan kunnata kafin na ce"Ba maganar isa ba ce. Ko shi ƙanin na ki da na ke zaune domin shi ya ce na je zan ga ya masa ya yi hakuri ba zan je ba, ke ma kuma haƙurin zan ba ki ba zan samu zuwa ba, domin ni a lokacin aurena na yi walima kuma an yi min wa'azin aure da zamantakewa, bayan haka kuma Iyayena ba su kawo ni haka ba sun yi min shekara goma sha biyar da aurena kin san sai dai na zaunar na karantar da wani ba dai ni na zauna ana karanta min wani abu akan aure da zamantakewa ba wallahi."
Na faɗa kai tsaye kuma ko a jikina. Ina ji ta yi shuru kafin ta ce"Me kike nufi Sadiya?
"Abin da na ke nufi shi ne ba zan zo ba. In ina bukatar walima na shiryata a gidana mana? Sannan ni ba na bukatar walima da wa'azi ita dai wacce ta ke bukatar wa'azin ba ka ga shi kin kira za a yi mata? Me ya sa za ki gayyace ni cikin sha'anin da ni na riga na girme shi Anty Bahijja?
Magana na yayyaɓa mata kuma na san sun yi mata zafi shi ya sa muka gama wayar kowa ran shi a ɓace.
"Ba wani kin girma. Da ɗan abin da kika sani na cikin cokali kike cika ma mutane baki! Ke dai kawai malama zafin kishi ba zai bar ki ki zo ba ne. Kuma sai haƙuri Gimbiya zama daram a gidan Tafida in sha Allahu.'
Ni kuma sai na maida mata da cewa" Nima ina fatan su zauna tare har mutuwa. Kuma kishi ai halas ne in ma ya hana ni zuwa na yi dai dai. Amma ga saƙo ki faɗa ma ita Gimbiyar ta ki, ta yi hakuri domin