Showing 48001 words to 51000 words out of 141487 words
katifa yara ta kasa sai Marwa da Saude daman sun shimfiɗa sun kwanta sauran yaran kuma sun kwanta tare da su Jidda. Ni kuma na shige ɗakin mu na kwanta gefen Yallaɓai da har ya yi barci ma.
*****
Asabar.
28. Dec 2015.
Ranar asabar mun tashi da taron biki, ni dai kamar muka tsara haka tsarin ya tafi. Su Munnira su ka yo waina su Amina kuma suka yi miya da zoɓo anan gida sai kuma Alele ba dai da yawa ba na ce su Saude su wanke wake a yi. Da safe dai Tea muka sha sai buredi sannan aka soya ƙosai. Da ya ke ba wasu jama'a na gayyata ba ƴan'uwana ne, dangin miji kuma suna can Gwammaja suna na su taron
Tun 11am na safe muka yi wanka gabaɗaya gidan kowa ya shirya. Tun da tun safe an gama komai, zuwa sha ɗaya da rabi su Munnira sun iso da waina Yallaɓai kuma tun safe Kawu Abba da Tariq suka zo suka fita tare da shi, ashe Tariq tare suka zo da Farida anan garin ya kwana ni ban ma sani ba sai da safen da suka zo gidan ya ke faɗa min, anan ma suka karya sannan suka fita, Yallaɓai an sha wanka da fararen kaya har da babban riga, ni kaina na jinjina ma kaina kamar an ƙwara min ƙwarin gwiwa na yi mamakin yadda na tashi cikin kuzari da dakiya.
Kawu Abba ya ce min na kwantar da hankali na su suna bayana kuma matukar Tafida ya yi min wani abu da ban gane ba kawai na kira shi zai yi min mganin shi, na ce an gama mgana zan ko kira shi suna ta dariya shi da Tariq.
Abin mamaki Ya Murja da wuri ta zo ita da yaranta gabaɗaya Anti ce ba ta zo ba amma ta ce ta je makarantan hadda ne in sun ta so ta ce mata ta same ta a gidana abin da ya ƙara ba ni mamaki da ita shi ne har awara ta yo min mai yawa ta zo min da shi, har sai da idanuwana suka ciko da kwalla da Ya Balki ta ba ni kula cike da awara ta ce Ya Murja ta yo min ta zo da shi.
Na kalleta cikin wani yanayi kafin na ce" Ya Murja ashe dai ba Ma'u kaɗai ki ke so ba. Nima kina so na."
Na faɗa cikin wani yanayi a muryanta su Ya Aina suna ta mana dariya ita ko harata ta yi kafin ta ce" Ji wata magana mutun ya taɓa kin ɗan'uwansa ne Sadiya? Ni fitinarki ne ya ba ma shiri amma ki sani ke ɗin fa jinina ne, jinin da ke gudana a jikinki da jikina bai kai wanda ke gudana a jikin Ma'u ba Ki daina gasa da ita ni duka ɗaya na ɗauke ku."
Sai kawai na rumgume Ya Murja ina ƙokarin maida ƙwallar da ta kawo min
"Na gode Ya Murja. Allah ya bar zumunci."
Ta amsa da Amin Amim ta na dariya su Rahila na ta ya mu, haƙiƙa ba abin da ya fi ka ga ɗan'uwanka ya zo ta ya ka farincikin ko aka sin shi, duk da dai ba ma shiri da Ya Murja yau sai ta nuna ma duniya ni ɗin jininta ne Ma'u ce bare domin da ake mganar jiya ba ta zo ba, Amina ta yi karaf ta ce an ce ta je can gidan dangin mijina Walima, kuma ni na faɗa mata yau da safe da na ji ta na cigiyar Ma'u.
"Gaskiya ba ta kyauta ba. Duk zumuncin da ke tsakaninta da yayar mijin Sadiya ba kai kwatan alaqan da ke tsakaninta da Sadiya ba. Maganar gaskiya ba ta kyauta ba."
In ji Ya Murja, Ya Aina ko cewa ta yi" To in ma an gayyaceta can ɗin me ya hana nan ɗin ma ta leƙo? Kome ke tsakaninsu Sadiya zumumci ya wuce wasa"
Rahila ta karɓe da cewa" ballatana ita Sadiya ma tun da Alhaji ya yi sulhu shike nan ta daina faɗa da Ma'u. Ta kira ta a waya ta faɗa mata tana gayyatan ta ita da shema'u.
Amina ta kaɗa kai kafin ta ce" To gulma ce ya kai ta amma in ba haka me ya sa sai ta je! Wannan ma fa kamar cin mutumci ne wallahi."
Ya Balki kuma tace wallahi in ta zo sai ta yi mata mgana Ya Aina ta ce ta ƙyaleta ita da kanta za ta yi mata mgana, ni dai ina gefe sun tare min faɗa ban ce komai ba ina ta mirmishi. Daman muna cikin bedroom ɗina ne mun bar su Hauwa acan falon su Jidda suna hira tare da su Farida. Jama'an da na gayyata sun yi min kara sun zo min kaf iyalan Inna mariya da na yan gandun albasa sun zo min, har da matan su Kawu Tasi'u kuma da wuri suka zo, Sameena da wuri ta baro Gwammaja ta dawo gidana da kayanta ta ce nan za ta kwana sai gobe za ta je Rano daga can za ta koma gidan mijinta haƙika na yaba da karamcinta.
Iya imu muka ci taron bikin mu, mun ci waina da alele da zoɓo sai son barka. Ma'u sai wajen uku na rana suka zo ita da Shema'u sun saka kaya iri ɗaya sun chaba kwalliya tare da kanwarta Zainab da Alhaji ƙarami. Ni da ya ke na daina saka sha'anin Ma'u a gabana da fara'a ta na tarbesu lokacin na sanya leshina riga da sikat kayan kuma sun zauna a jikina adon leshin ja ne, domin ni daman ina son jan abu, sai leshin ya yi min kyau na yi kwalliyata mai sauƙi na kashe ɗauri bayan na cire atamfar da na saka da safe na tabbata daga Gwammaja ta ke, kuma a yanayin da suka ganni cikin fara'a da gayu na ya yi musu baza ta sun ɗauka za su zo su ganni cikin kuka da baƙinciki ne, ina lura da su sai bi na suke yi da kallon mamaki ni kuma ina juyi da mazaune na domin akwai su Allah ya ba ni.
Shema'u za ta min shaƙiyanci da cewa" Uwargida a gidan Yallaɓai wannan ba za kalan fa? Ina mata fari na kaɗa mata kugu sannan na juya wuyana gashina da ya sauka ya karkace na baza shi da gyara tsayuwata kafin na ce" Ke ma ba ki ji abin da kika faɗa ne. Uwargida a gidan Yallaɓai fa, kin kuma san cewa daman tun can matar Yallaɓai akwai kashe kala ba sabon abu ba ne wannan."
Munnira na gefe ta ranguɗa ta na faɗin" Wannan gaskiya ne ta Yallaɓai ita belbela daman ai da farin gashin ta a ka gan ta."
Sai ta mika ma Hauwa hannu suka tafa, Faridan Tariq na gefe ta miƙe ta yi juyi kafin ta riƙe hanci tana faɗin" Jama'a ku ta ya ni rangaɗa ma duk wata uwargida guɗa."
Kafin kace me su Munnira sun rikita falon da guɗa, ni dai ina ta dariya ganin har da Ya Balki a masu guɗan. Ni dai na saka Amina ta zubo ma su Ma'u waina da alele, na ɗauka za ta ce sun ƙoshi sai na ga ta fara cin alalen. Amina ce ta yi mata tsiyan sai da yamma ta ke zuwa bikin gidn su?
"Na ɗan je Gwammaja ne. Kin san ni duka tudun biyun nawa ne Uwargida da Amaryan."
Ta fada ta na wani mirmishi, wanda na tabbata na yake ne, to ba nasara ta ga abin da ba ta yi tsammani n gani ba. Nan ta ke Ya Aina ta ce mata in ta gama cin abinci ta na so za ta yi magana da ita sai ta ce ti, sun yi dai hira da su Ya Murja ba wanda ya nuna mata ko a fuska, ni dai sai faman bina da kallo suke yi ita da Shema'u ganin yadda na ci kunshina baƙi da ja haka ma yara su Jidda su kansu sun sha gayu, suna falon sai ga su Suwaiba da Jamila sun leƙo min biki suna shigowa suka hau faɗin" Ina Uwargida a gidan Ya Tafidan ne! Ta fito mu tantance tun da mun gama gano gayun amarya saura na uwargida."
Sai suka ci karo da ni ai sai suka ɗau shewa daman Jamila shaƙiya ce ta karshe zagaye ni ta fara yi ta na faɗin" Kai jama'a cancanɗi. Ni fa na kasa gane ki. Anty Sadiya kin gama cinye wannan gasar."
Ta faɗa ta na buga shewa ta ba ni hannu muka kashe Suwaiba kuma sai zama ta yi kan kujera ta na faɗin" Ke ce ma Amaryan Ya Sadiya to ai ko Gimbiya sai dai ta nuna miki makeup ɗin da mai kwalliya ta yi mata. Amma tabbas Uwargida ta Yallaɓai wanka ya rusuna jama'a."
Sai ta karkace hanci ta saki guɗa su Munnira na ta ya ta falon ya ɗau ihu, ina gefe ina ta dariya. Allah ya ɗauke min hamdala kawai na ke yi a cikin raina ashe da ban yi taro ba haka zan zauna baƙin ciki ya kashe ni kaɗai a gida. Suma nan suka zauna suka ci waina ana ta hira ana shewa yau dai gabaɗaya ranar ta uwargidaye ne, su Ma'u ana gefe duk an muzanta. Wannan muƙamin na manyan mata ne, sai mai nasibi ubangiji ke ba ma wannan sarautar in ji Ya Balki nan ko aka saka mata guɗa ana faɗin kwarai ma da gaske Yayarmu, ni dai ba na mgana sai dariya Suwaiba ke faɗin Yallabai na can Gwammaja ana ta hotuna ta na ma cikin faɗa ne wayata na hannun Marwa ta kawo min ta ce Yallaɓai na kira suna ko jin haka suka ɗau ihu suna faɗin.
"Yallaɓai dai bai manta da matar Yallaɓai ba duk da ya ga Amarya."
"Ita kanta Amarya in ta zo sai dai ta yi mana mubaya'a. "
In ji Munnira sai suka ƙara saka shewa suna tafawa ita da Suwaiba daman mutuniyarta ne, Jamila ta mike ta na faɗin" Wai ya ne? Gidan Uwargida ba sauti?
Ya Balki yar ta ya ɓera bari ta ce" Shi ne da ya kamata sa kar mana sauti mu yi takun uwar gida ran gida Yallaɓai ya na yi ma Sadiya rawa."
Ni kaina wannan karon na kasa rike kaina sai da na fashe da dariya a jikin Tv falon yara akwai wajen saka flash Amina na da shi aka yo dowloading ɗin wakar Uwar gida suka kunna mana sauti, Suwaiba ta ce duk wacce ta san ita ɗin ba Uwargida ba ce ta koma gefe wannan filin na uwargidaye ne.
Sai kawai suka miƙe suna takawa, ni dai na shige ɗakin su Jidda ina amsa wayar Yallaɓai tunda ya sake kira.
"Yallabai na"
Na faɗa har daga ƙarƙashin zuciyata kuma a cikin wayar ma har ya tona asirin halin da na ke ciki na farinciki.
"Matar Yallaɓai."
Ya faɗa daga can bangaren, ina jiyo hayani ya tabbata har lokacin ya na can Gwammaja ɗin.
"Na'am mijin Sadiya."
Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce" Me kika samu ne? Na ji ki cikin farinciki ne'
Ina mirmishi na ce" Farinciki mana. Yan'uwana ke nan suna saka ni farinciki."
"Alhamdulillah na ji daɗin jin haka."
"Ya Hidima Yallaɓai?
A amsa min da Alhamdulillah.
"Sadiya ta yunwa na ke ji tun fitan mu fa ba mu ci wani abu ba."
Da sauri na ce" Me ya sa ba ku ta ho gida ba! Tun ɗazu aka kawo waina alelen ma an gama fa."
Da sauri ya ce" To in zo za ki ba ni?
Ina dariya na ce" Ni na isa na hana Yallaɓai abinci? Sai kun taho zan shirya muku na ku in sha Allahu."
Da haka muka yi sallama, ko da na fito falo waje ya cika da shewa ga kiɗa. Har da su Ya Balki ana cikin fili ana takawa da, ban ga Ma'u da Ya Aina kenan ta ja ta gefe suna mgana. Amina na yi ma mgana abinci su Yallabai daman an cire musu, tare muka shiga kitchen ɗin ina ganin abin da ta ke haɗawan, ina cikin kitchen ɗin Munnira ta zo ta ja ni ina faɗin ta bari ina zuwa amma ba ta saurareni ba, sai tsakiyar falo ta kuma riƙe hannuna ta na rawa da ni farida ta mike ta na min liki, Shema'u na ga ta na kallona sai kawai na sakin hannun Munnira na fara takawa, suna min shewa da guɗa hana ni saƙat suka yi har su Jidda fa sun shige rawan suma sun ce ba za a bar su a baya ba.
Muna can muna bidiri ko shigowar su Yallaɓai ba mu ji ba, sai da ya leƙo da kansa ya na faɗin" Ku ce shasu kuke yi kenan"
Ai su Suwaiba suna ganin shi suka rufe shi da guɗa, ya na kare fuskarshi ya ke faɗin" Wai guɗan nan ba ta ƙarewa ne Suwaiba?
"Wanda muka yi maka a Gwammaja na Amarya ne. Wannan kuma ai sautin na uwargida ne."
Suwaiba ta faɗa ta na ƙara sakin masa guɗaa akai, ya dafe kansa ya na dariya Jamila ma ta kama Munnira na ta ya ta, Sai ga Kawu da Tariq sun shigo. Kawu shi cewa ya yi" Danƙari Tafida ka ce ga in da ake biki."
Tariq kuma ya ce" Shi fa Tafida duka amare gare shi."
Ya faɗa ya na kallona ni kunya ma na ji na sauke kaima ƙasa, Suwaiba ta fara yi ma kawu shaƙiyanci wai shima Allah ya sa baɗi uwar haka suna Rano sun je suna ya zabga mata harara kafin ya ce" Sai dai in da cikin ta zo ko?
Ni kaina sai da na yi dariya daman kawu akwai yanka mgana gaisuwa suka yi da su Ya Balki da su Inna Mariya ƙin barin shi suka yi suka ce sai an yi mana hotuna, haka nan suka tsaida mu suna ta ɗaukan mu hoto har da Tariq shima da wayarsa shi da Faridan sa, sai da na ce musu su yi haƙuri, Ango fa na jin yunwa a yi masa afuwa na bashi abinci ai sai su Suwaiba suka ƙara ɗaukan shewa suna dariya.
"Allah ya shirye ki Suwaiba."
Haka Tariq ya faɗa ya na girgiza kai. Dakyar Yallaɓai ya samu ya ƙwace suka koma falon shi sai na saka Marwa ta kai musu abincin da komai da komai a falon na Yallaɓai, bayan sun gama ci sun ƙoshi har suka bar ma gidan ban sani ba muna can ana ta hira da shewa, Ma'u dai tun da ta dawo falon ba ta ƙara dariya ba, ga ta nan dai zaune ta na bin kowa da kallo, muna nan tare da su Suwaiba har dare bayan mangariba na sauya kaya na saka material
Ya Aina da Ya Balki har da Ya Murja da Zaituna da mutanen Gandun albasa sun koma gida sai aka bar su Rahila, Ma'u ma da kawarta ba su tafi ba, da daddaren Halima ta zo ita da ƙawarta ta ce daga nan gidan Amarya za su wuce domin an tafi da ita tun mangariba ta zo min ne kawai na ce mata na gode. Haka ma Lailan Ya Auwal a lokacin ta zo ita da ƙanwarta na yi mata uziri tun da suna da hidima.
Sai wajen tara na dare gidan ya yi shuru, su Suwaiba sun koma Gwammaja su Ma'u sun tafi, Haka ma su Hauwa da Munnira daga ni sai Amina sai Rahila sai Sameena da ta yini ma kwance ba ta jin daɗi duk shewan da aka yi ta na ɗaki, sai Saude da Marwa sai su Jidda har maman Saude da mai yi mana kitso sun zo min biki.
Su suka gyara gidan ma ya yi kintsi sai gidan ya koma ya yi shuru kamar ba shi ba ne ɗazu ya cika da hayaniyar mutane ana ta hidima sai kuma da ya yi shurun na fara jin wani iri a cikin ƙasan raina.
Ranar da na ke gudu ce yau ta zo. Ranar da Yallaɓai zai je ya kwana da wata mace ba ni ba. Tirƙashi.
*Janafty*
*TKG*
09.
*Assalamu alaikum!*
*Ina muku gaisuwa irinta addinin musulunci da fatan masoya labarin ƳAR KARUWA suna cikin ƙoshin lafiya,baya ga haka ina muku albishir da cewa free pages na labarin ya ƙare mun shiga asalin labarin wanda ya kasance shine part 2 na labarin.*
*Karku manta bamu ce komi ba a free page's na labarin domin kuwa yanzu nema za a fara wasan,don haka karku bari ayi tafiyar babu ku masoya.Ku hanzarta ku shigo cikin tafiyar ARCH.AMMAR CHIROMA TARE DA HAFSAT KABEER CHIROMA,Tabbas a cikin wannan tafiyar akwai tarin faɗakarwa,zazzafar soyayya,ƙiyayya mai zafi da kuma halacci.*
*Paid page's sun fara sauka a manhajar whatsapp da kuma Telegram,masu biyiyar arewabook tuni labarin part 2 ya fara nisa a can,sai ku garzaya domin Shan karatu.*
*Ku biya kuɗinku ta wannan asusun Kamar haka👇🏻*
For VIP on Telegram Pay 1k for Whatsapp group Pay 500 in to this account 👇🏻
7087809778
Aisha Dansabo Ibrahim Opay,evidence of payment to 08167768704.
*Masu buƙatar free pages na labarin ku tuntuɓeni ta wannan line ɗin 08167768704.*
Ƙarfe tara da rabi na dare sai ga Yallaɓai ya dawo shi kaɗai ya ce min ya ba ro su Tariq a gidan mai za su saka mai amotar shi kuma sai ya hau adai daita ya taho gida ya yi wanka ya shirya kafin lokacin sun taho sai su raka shi can gidan Gimbiyar.
Kamar ya sani bai ko neme ni na haɗa masa ruwan wanka ba, ba domin in ya ce na yi ba zan yi ba sai domin zuciyata a lokacin ba ta cikin sukuni, muna gama maganar nan da shi ya shiga wanka ni kuma sai na koma can falo wajen su Rahila ba na so na zauna ni kaɗai tunani da damuwa su taru su ƙara ruguza ɗan sauran kuzarina.
Duk hiran da suke yi na kasa saka musu baki, zaune kawai na ke kamar mutum da mutumu ba na ma fahimtar hiran da suke yi, tun da ni nawa tunanin ya yi zurfin tunanin yau fa Yallaɓai ba anan zai kwana ba, yau ɗin wata rana ne da zai je ya kwana da wata mace ba ni ba, tuna haka kawai in na yi sai na ji numfashina ya sarƙe. Zuciyata na harbawa da sauri sauri ina dai zaune ne ina wasa da yatsun hannuna amma ni kaɗai na san