Showing 3001 words to 6000 words out of 141487 words

Chapter 2 - TURKEN GIDA BOOK 2 COMPLETET BY JANAFTY.txt

Janafty   

18 Dec 2025

895

lulluɓe rayuwarsa. Har ga Allah bai taɓa hango rayuwarsa ta yanzu a kusa ba. Ya ɗauka in zai ƙara aure da amincewar Sadiya da yardanta bai taɓa tunanin kaddara za ta juyo masa ta wannan fannin ba. Ya na tsoro ya na tsoro tsoron kar Sadiya ta ji labarin auransa a bakin wani ba abakin sa ba. Ya daɗe a kofar gida a cikin mota amma ya kasa shigowa ciki ya rasa jarunmta da karfin gwiwan da zai iya haɗa ido da Sadiya bayan kuma yau ya munafunceta ya yi aure ba tare da saninta  ba. NENE ce ita ce ta sha gabansa kuma ita ɗin Nene Uwa ce a gare shi da ba zai iya mata musu ko saɓa umarninta ba amma gabaɗaya yau yini ya yi jikinsa ya yi wani irin sanyin. Sanyin da bai taɓa tsintar kansa a ciki ba.

Ya na zaune su Jidda na ta bidirinsu amma ya kasa cewa komai. Har Naman da kazan su kaɗai suka ci shi ya kasa  in zai tuna tun abincin da ya ci jiya da daddare ne bai ƙara saka wani abu a cikinsa ba sai ɗan wannan cake ɗin kuma a yadda ya ke jin cikinsa ya toshe ba zai iya cin wani abu ba.
Wayarsa ce da ke cikin aljihun gaban rigar shi ta yi ɗan kara alamun shigowar sako sai ya yi saurin ɗaukowa ya duba. Musbahu ne.

"Yaya Tafida sun sallama Shagon nan fa. A kan dai yadda kuka yi mgana. Ga ma key din sun ba ni a hannuna."

Daga jiya ne ya ke zumuɗi da fatan su sallama masa wannan shagon amma yanzu komai ya ƙare. Sai ya ji ma abin ya fita kansa. Abin da ya faru yau a Rano ya ɓata komai ɗin da ya shirya a matsayin zai ba ma Sadiya suprise. A cikin shagunan da ke ƙasan Office ɗin su ne wasu suka saki shi kuma ya yi mgana ya na so Saboda Sadiya su kuma masu wajen sun ce mai wajen ne zai yi amfani dashi amma ya na ce ya na so saboda kimarsa kuma akwai kyakyawan alaqa tsakaninsa da mai wajen ya sa suka sallama masa ya so ne ya ba ma Sadiya suprise da niyar in aka bashi kuɗin aikinsa na kaduna zai cika alkwari ya  ba ta kuɗi ta yi oder ɗin kayan da za a sanya a shagon a buɗe shi cikin ƙankani lokaci. Ya san a duniya Sadiya ba ta da wani buri sai na buɗe shagon Saloon da tun da suka yi aure ta ke da wannan burin kuma shi ya karbe mata duka kuɗaɗenta da alƙwarin zai tallafa mata domin cikar burinta.
Amma a wannan lokacin sai ya ji ko ya nuna mata ma ba za ta yi murna ba in ya faɗa mata ya kara aure za ta fassara niyyarsa ta wani siga ne shi ya sa sai karsashinsa ya ragu.
 
"Ok."

Kawai ya tura ma Musabahu daga nan ya maida wayar aljihu.  Kunya ce ko nauyi suka sa ya kasa ta shi ya bi Sadiya cikin ɗaki ya zauna tare da su Jidda har suka gama bidirinsu sannan ya ce su je su yi brush su sauya kaya su kwanta shi kuma suka bar shi da gyara in da suka ɓata sauran cake ɗin da komai ya kwaaso su ya kai kitchen ya tura a cikin fridge. Sai ya leƙa ɗakin su Jidda ya tabbatar da sun kwanta sannan ya rage musu hasken ɗakin ya rufe musu kofa ko'ina sai da ya duba ya rarrage hasken gidan gabaɗaya sannan ya wuce bederoom ɗin su.

Na ji takun sa zai shigo da sauri na shigar da kaina cikin bargo na lafe kamar mai barci. Ahalin kuma ba barci na ke yi ba. Na ji shigowarsa kuma na ji tsayuwarsa a kaina na wani lokaci na ƙara lafewa ina nunfashi kamar mai barci sai kuma bai tashe ni ba can na ji ya buɗe kofa ya fita. Sai kuma na ji ya shiga tiolet leƙo da kaina na yi ina sauke numfashi tunda na shigo ɗakin nan tiolet kawai na shiga na kama ruwa na dawo na saka kayan barci na kwanta ina faman tunani na ɗauka in na keɓe ni kaɗai zan samu daman kuka sai kuma na kasa ashe ma kukan rahama ne suya kawai kirjina ke yi, wani tuƙuƙin abun da ya tokaremin a zuciyata tun a lokacin da Ma'u ta faɗa mini ya kasa wuce min. Na san Yallaɓai zai iya ƙara aure kuma na saka a raina zai iya auran Gimbiya amma ban ɗauka yau ba. Ban kuma kawo sa gobe ko jibi ko nan kusa ba. Lamarin ya shammace ni shammatan da ya firgitani matuƙa sai kuma yadda Yallaɓai ya munafunce ni? Zan hana shi kara aure ne? Ko zan hana shi yin abin da ubangiji ya ce ne? Takaicina ɗaya yadda na yarda dashi na ke yi masa kyakyawan zato daga karshe ya ci amanata ya yi aure ban sani ba. Ni kuma na yi ma kaina alƙwarin in dai bai buɗe baki shi da kanshi ya faɗamin ba zan ta ɓa nuna masa na sani ba zan jira na gani ina da sauran ƙima a wajensa da zai zaunar da ni ya faɗa min ya ƙara aure sannan ta yadda auran na shi ya zo bakatatan! Ko kuwa zai bar ni a rufe ne ya na yaudarata da kalaman bakinsa na ƙarya da munafunci.

Ina jin zai buɗe kofar tiolet ɗin sa na koma da kaina cikin bargo na lafe. Wallahi ban iya barci ba duk ina jin kai da kawonsa har ya gama ya zo ya kwanta ina jin sa a kusa da ni ya na kiran sunana na ƙara lafewa domin a ji a raina yau ko nema Yallaɓai ya yi sai dai tsinuwan mala'ikun su hau kaina amma ba zan iya yi masa wani amfani ba.
Ina jin sa sarai ya na ta kiran sunana na yi kamar mai barci har bargon ya ye min daga fuskata yana leƙani na yi bakam na ƙi motsi sai da dai ya ga kamar na yi barci. Sai ya gyara min kwanciya ya sake rufamin bargo amma bai rufe min fuska ba.

Kamar ya san ba na buƙatar sa bai raɓu da ni ba sai ya koma gefe ya kwanta. Na daɗe ina jin karin maganar nan ta hausawa da sukan ce yadda na ga rana haka na ga dare a baya in ta tunanin kawai sai ka kwana ba ka yi barci ba? Sai yau na samu tabbacin hausawa fa sun yi gaskiya domin nima yau ɗin nan yadda na ga rana haka na ga daren. Barci ko na minti ɗaya bai ɗauke ni ba Yallaɓai ma ya kusa raba dare ya na juye juye amma daga baya ya samu barci ni ko a kunnena aka fara kiran sallar farko na asuba a kuma lokacin ne na yaƙi sheɗan na miƙe na sauko daga kan gadon ina mai kallon Yallaɓai sai na ji wani shashi na zuciyata na ji tausayinsa yadda ya kwanta ya takure jikinsa sannan ni ya bar ma blanket ɗin bai rufu da shi ba. An ce mata da miji sai Allah sai na ji a wani shashe na zuciyata na yi ma Yallaɓai uzuri. Wani shashen kuma na ce min Yusuf ne fa! Wanda ya fi kowa fahimtar ki.

Kamar zan ƙyale shi sai kuma na fasa zuciyata mai imani da tausayi wacce ta gaza ganin baƙin Yallaɓai ta rinjaye ni na isa gare shi na ja bargon na lulluɓa masa sai na ga ya yi motsi ya ɗan gyara ya miƙe kafarsa. Ina tsaye ina kallon shi duk da akwai ɗan duhu amma hasken kwan lantarki haraban gida ya na shigo mana ta cikin bedroom ɗin mu.

Juyawa na yi na fita daga bedroom din Tiolet na shiga na ɗauro alwala sai da na fito ne na duba agogon wayata 4:30am na asuba sai na shimfiɗa darduma na saka hijabi na tada sallah.
Sai da na yi raka'a huɗu sannan na zauna ina salatin Annabi da istgifari a cikin raina rokon Allah kawai na ke yi ya ba ni juriya domin na ji kamar zan gaza na ji kamar ba zan iya ba kuma gashi ina so na iya ina so na daure. Bayan na yi addu'o'ina na neman sassauci wajen Ubangina yau rana farko da na yi addu'a ban yi ma Yallaɓai ba  kawai sai na ji gwara na yi ma kaina da ƴaƴana tunda yanzu Yallaɓai ya zama mallakinmu ba mallakina ba

Na tashi na sake tada salla Yallaɓai ya farka da fitilan wayarsa ya haskoni sai ya ga ina salla, ni kuma ina ganin ya farka saboda ba na son mgana ya sa ina sallamewa na sake miƙewa na ƙara kabbarta wata sallar. Sai na ga ya sauko daga kan gadon shima ya fice ashe alwala ya ɗauro ya dawo ya saka jallabiya ya zo kusa da ni ya shimdiɗa sallaya dai dai ina sallame raka'a ta biyun da na faro.

"Me ya sa ba ki tashe ni ba?

Sai na ji na kasa mgana a da na saba in dai zan tashi sallar dare ina ta da Yallaɓai mu yi tare yau kuma ban tashe shi ba. Saboda kar na yi masa mgana sai na sake miƙewa na kabbarta salla da ƙarfi na ce." ALLAHU AKBAR."
Ni na san Yallaɓai ya bi ni da kallo kuma ya na ɗan fara shan jinin jikinsa. Ban bi ta kansa ba sai da na sake yi raka'a huɗu sannan na zauna ina jan casbaha Yallaɓai ma raka'a shidda ya yi lokacin har an fara kiran sallah na biyu sai ya miƙe ya je ya ɗauko hula ya saka da casbahansa hasken ɗakin ya kunna ya na kallona kafin ya ce.

"Na tafi masallaci."

Kaina na gyaɗa masa ina ɗaga masa carbin hannuna alamun ina lazimi bai ce komai ba sai ya kaɗa kai ya fice daga bedroom ɗin ya ma mai rufo min ƙofar bedroom kamar an ƙwace ni haka na sauke ajiyar zuciya ina ta fitar da numfashi ta baki ina tunanin shi ya ta da yara bayan ya fita saboda ni ban fita ba sai bayan na idar da sallar asuba sai na leƙa su na ga sun tashi suna salla a ɗakin na zauna daman na zo da Qur'anina na fara karatuna so na ke yi zuciyata ta samu salaman da zan yi ma kaina tunani mai kyau kuma alhamdulillah na samu.

Sai da na gama karatun nawa a cikin suratul Maryam sannan na yi ma Jidda na ta karatun tare da Baby ina cikin yi ma Baby ne Yallaɓai ya shigo ɗakin daman sun san na hana su tashi in muna karatu daga zaunen suka gaishe shi ya amsa ya na daga ƙofar ɗakin bai shigo ciki ba hankalina da idanuwana na kan Qur'anin da ke gaba na na ce.

"Ina kwana."

Ban san yanayin sa a lokacin ba ya dai amsa nuryansa a sanyaye.

"Lafiya lau. Kin ta shi lafiya?

Ban amsa shi ba na cigaba da biya ma Baby karatu gajiya ina ga ya yi da tsayuwa ya fice sai dai na ji ƙaran rufe kofarsa na raka shi da harara ƙasa ƙasa.
Bayan na gama musu karatun sai muka yi azkar sannan na bar su na ce Jidda ta yi ma Baby wanka su shirya ni kuma na cire hijibina na ijiye anan ɗakin yara na shiga kitchen na dafa musu ruwan tea sai na soya musu kwai na ce su karya da shi sannan kuma su tafi dashi yadda na ke jin kaina ba zan iya firan dankali ba kai aiki mai wahala ba na son yi saboda duk jikina ya mutu.

Yau tare da yarana na karya ban ko jira Yallaɓai ba. Ban kuma koma ɗakin ba sai da Salisu ya zo suka tafi sannan na koma ɗakin ni dai na ji sa ya na waya sanda na shiga a mganar da na tsinta na karshe ce ya sa fahimci da wanda ya ke wayar. Uncle Abba ne domin na ji ya na faɗa min" Na kasa. Na kasa zama jarumi a gaban Sadiya Abba"

Daga nan na shigo ɗakin sai kuma ganina ya sa ya yi saurin cewa" In na fita za mu yi mgana"
Da kuma sauri ya katse wayar ya na kallona. Ni ko sai na yi masa mirmishin ya ƙe kafin na ce" Wanka za ka fara yi ko sai ka karya?
Cikin ƙaramin sauti ya ce" Mu dai fara karyawa amma zuwa anjuma ko?
Kai tsaye na ce" To. Amma ni na riga na karya tare da yara.'
Ban bashi zarafin mgana ba na yi fit na bar masa ɗakin na faɗa tiolet ruwan zafi ya ƙare a tiolet sai da na fita kitchen na jona a buta ya tafasa sannan na juye na yi wanka da shi lokacin da na fito zan shigo ɗakin saboda ƙofar ba ta rufu ba sosai na ji sa ya na mgana kuma again kamar a waya ce.

"Haba Anty Bahijja ba na roƙe ku da kar ku bari  maganar auran nan ta fita ba tare da na faɗa ma Sadiya ba? Me ya sa kika yi status in ta gani fa?

Ban san me ta ke ce masa ba amma dai na ji ya amsata da cewa" Ko da kin cire ta don Allah ki goge. In ita ba ta gani wani na ta ya gani ya faɗa mata fa? Da wani ido zan kalleta? Duk bayanin da zan mata ba zan iya wanke kaina ba don girma Allah ku bari ni na samu jarumtar da zan iya faɗa mata ku bari ni mijinta ta fara jin mganar nan daga bakina."

Ban yi niyyar labe ba amma sai na ji ina so na ji har karshen mganar ta su. Kenan shima ya ga status ɗin da ta yi? Uhm wato ta cire ni amma ta manta ba ta cire yar'uwata Ma'u ba. Ko ta manta zan iya sani ta hanyarta ne? Jin ban ƙara jin mganarsa ba ne ya sa na san sun gama wayar kenan shi ya sa na yi gundubalan tura ƙofar na shigo ciki, ba shi da gaskiya shi ya sa ya wani firgita da ya ganni na shigo.
  Ta gefen ido na kalle shi sai kuma na basar da shi na isa kan kujeran madubi na ja na zauna ina shafa mai ina hangensa ta madubi wayarsa ce a hannunsa amma kuma hankalinsa na kaina ya kasa iya buɗe hira a tsakaninmu ni kuma daman tun a jiya na ji kamar an shimfiɗa wata tazara mai yawa a tsakaninmu na yi shuru kawai ina shafa mai bayan na gama na warware gashina na gyara sannan na tashi na isa ga wardrope na dauko wata doguwar rigar atamfata na saka ina cikin ɗaura ɗankwali na ji mganarsa.

"Yau sai aka karya a ka bar ni ko?

Ban juyo ba na ce" Tea kawai na sha."
Ya kasa mgana ni da na san Yallabai da hira amma yau kalaman bakinsa sun kare duk ya wani kama kanshi saboda na ƙure shi sai na juyo ina kallonsa kafin na ce" Lafiyan ka?
Da sauri ya ce" Me kika gani?
Cikin ido na kallesa kafin na ce" Bakomai."
Daman na latsa sa ne sai kuma bai bani kunya ba.
 
"Ni? Bakomai ke ce ma na ga tun jiya kin yi wani sanyi sanyi kamar ba ki da lafiya."

"Ko?

Na faɗa ina masa wani kallon tara saura kwata. Sai ya amsa da min E. Kafin ya ɗora da fadin" Ko duk laifina ne na jiya ba a gama hucewa ba?
Sai kawai na rausayar da kai kafin na ce" Ko ɗaya ni fa lafiyata kalau. Kai ne dai na ha kamar a firgice ka ke."
"Ni?
Ya faɗa ya na kallona sai na gyaɗa mai kai kafin na ce" E.  Ka na yin abu kamar mara gaskiya. Yallaɓai me ka je ka yi ne ban sani ba?
Da gayya na tsare shi da ido ai sai Yallaban ka ya daburce yadda ya yi min kaɗan ya rage ban yi dariya ba.

"Rashin gaskiya kuma? Me kuwa zan yi miki ni Sadiya.?
A duburce ya ke mganar da ka ganshi za ka gane bashi da gaskiya sai na yi mirmishi kafin na ce" To na sani. Maza ai ba ku da gaskiya barin ma in kuka so ƙara auro."
Wallahi na hango tashin hankali ƙarara a idanuwan Yallabai mganta ya kashe masa jiki da ya sa ma ya kasa mgana.
Ni kuma saboda na kauda wannan firgicin ya sa na ce" Ranar Mandoy ina da komawa asibiti fa."

  "Allah ya kaimu. An gama duka gwaje gwajen ne?

Ina ɗaukan wayata dake gefen in da na kwanta na ce" Saura ɗaya."
Ina jin ajiyar zuciyarsa kafin ya ce" Allah ya kaimu."
Na amsa masa da Amin sai na fice ina faɗin" Ina falo."
Ban jira cewarsa ba na fice ina danne leɓena na ƙasa a raina ina tunanin to wai daman akwai irin wannan hanyar na cin uban maza da zullumi mata ke hauka? Ai wannan bakam ɗin kaɗai ya ishe su ba sai ka wahalar da bakin ka wajen faɗa ba.

Falon yara na koma na zauna sannan na kunna datar wayana. Duk da ina jin faɗuwar gaba ban fasa ba. Na kuma kasa iya sarrafa kaina sai da na je na ƙara duba sreenshoot ɗin da Ma'u ta turamin sannan na girgiza kaina na koma na duba status ɗin kaf yan gidansu Yallaɓai ban gani ba da gaske kenan sun ji roƙon sa? Ita kuma Anty Bahijja kamar yadda ta ce ne ta rufe ni ban gani ba.

Saƙon Munnira ne ya ɗau hankalina da ya sa na fara zargin ta san abin da ya faru.

"Matar Yallaɓai kina lafiya kuwa?

Haka ta rubuta mini sai na sha jinin jikina. To ni na ji ballatana ita? Ko mijinta bai faɗa mata ƴan'uwansa mata za su iya kirnnta ta su faɗa mata tunda an san muna tare. Na shiga na ba ta amsa da ina nan lafiya sai na fita ga waya a hannuna amma na kasa yin wani abu da ita ji na nake yi kamar ba ni ba, sai na ke jin kamar ba wancan Sadiya ba wannan Sadiyan da Yallaɓai ya gama shayar da ita mamaki ne.

Vibration ɗin wayar a hannuna ne ya sa na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login