Showing 33001 words to 36000 words out of 141487 words
ba ta min maganar ba, nima a raina na kudiri niyyar ba zan yi mata ba, daga ita har Munniran muna nan har azahar sai da muka yi salla ne sannan na ɗora mana taliya fara tunda ina da Miya, na dawo falon kenan sai ta ke ce min da wuri za ta koma gida saboda yara yan makaranta za ta je ta yi musu girki, ni kuma sai na ce sai na da fa taliyan da yawa in ɗibar mata sai ta tafin musu da shi.
Nepa sun maido wuta sai na kunna mana kallo a tashar Arewa24 suna haska wani Hausa Film, hiran duniya kawai mu ke yi da Hauwa ta ɗauko min wannan na hira mu bari mu kama wancan. Kuma na lura da magana a bakin ta amma ta kasa yi min kila tana tunanin ko har yanzu ban sani ba ne.
Ni kuma daman na ce ba zan yi musu mgana ba in sun yi min sai mu yi ta kare in ba su yi min ba to sai dai a tafi a haka.
Ruwan zafin da na saka a gas ya tafasa na je na karya taliya na saka sai na kuma dawowa falon na zauna.
Hauwa ta kalleni ni kuma ina ɗan cire abin taliya da ya ɗan shigar min kumba.
"Anty Sadiya."
Hauwa ta kira sunana, na ɗago ina kallonta amma ban amsa ba, itama sai ta kasa ce min komai, sai na mai da kaina kan abin da na ke yi sai da na cire sannan na kalleta ina faɗin" Kin kirani kuma kin kasa cewa komai. Me ya faru ne?
Kai tsaye ta ce min" Wai kina so ki ce min ba ki san wani abu ya faru ba?
Sai da na juya baki sannan na ce" Ban sani ba Hauwa. Wani abu ya faru ne?
Na ƙarishe faɗa ina tsare ta da ido, mamakina ta ke yi, ko a har yanzu Yallaɓai bai sanar da ita ba?
"Hauwa me ya faru ne?
Na faɗa ina katse mata tunani sai ta yi saurin ɗaga hannu kafin ta ce" Ba ruwana. Tun da ba ki sani ba."
Mirmishin takaici na yi ina kallon Hauwa kafin na ce" Me ye ban sani ba! Wai na auran Yallaɓai da Gimbiya?
Hauwa ta zaro ido ta na kallona kafin ta ce" Daman kin sani?
Haushinta ya kamani da sauri na ce" E da ba ku gaya min ba na sani a can duniya ba."
Hauwa za ta kwaso rantsuwa na ɗaga mata hannu raina a ɓace ina faɗin" Daman ina jiran ki Hauwa daga ke har Munnira na yi ta tsumayin ku. Ai na ɗauka ni da ku ɗaya ne in kuka ji wani abu a kaina za ku yi saurin zuwa ku sanar da ni amma sai ga shi an yi min kishiya kowa ya rufeni ciki har da ku Hauwa. Kun bani mamaki kuma wallahi na riƙe ku a cikin raina Ubangiji ya gani na ji haushin ku ƙwarai kun kuma nuna min irin na ku zaman tare kenan."
Na ƙarishe faɗa ina jin takaicin abin na taso min daga ƙasan zuciyata.
Hauwa ta fara rawan bakin rantsuwan itama ba ta sani ba Muttaƙa bai faɗa mata ba daga can Rano ne ƙanwarta ta kira ta faɗa mata. Da ta kira Munnira ta faɗa mata sai ta ce itama ta ji Jamila ta kira ta faɗa mata amma an ce a yi shuru Tafidan bai sanar da ke ba tukunna."
Hararan Hauwa kawai na ke yi ta na mgana ganin haka yasa ta ƙara kwaso rantsuwa ta na faɗin" Wallahi ki yarda da mu. Ta ya ya za mu fara sanar da ke wannan labarin mara daɗin ji? Munnira ta ce kar mu faɗa miki mu jira shi da ya kwanto kuran ya ɗaure ta da kansa."
Ta ga dai in zaune ina karkaɗa kafa ban ce komai ba sai Hauwa ta yi mirmishi kafin ta ce" To ki yi hakuri tun da kin ji zafin mu."
Kai tsaye na ce"Wallahi na ji zafin ku. Kuma waɗanan mganganun ba su saka na daina jin haushin ku ba. Haba a taren mu ya wuce wasa. To ai shi bai faɗa min ba a duniya na ji "
Hauwa ta yi ta bani hakuri na ce ni fa ba zan haƙura ba sun ba ni haushi kuma na riƙe su a cikin raina na kuma ce mata wallahi in ita ce ko Munnira haka ya faru da su ba zan iya yin shuru ba saboda a tunani haɗuwar mu ta bangaren gidan aure ɗaya a shekarum da muka yi tare mun ƙulla kyakyawan alaqa a tsakaninmu da duk iskar ko guguwar da ta tunƙaro wani daga cikin mu sai in da karfin mu ya ƙare, ba su koma gefe su bari duniya na yi min dariya ba."
"Mun ji mun yi laifi. Don Allah ki yi hakuri."
"Ba fa zan haƙura ba. Ko na haƙura to ba zan ɓoye muku ba, na riƙe ku a cikin raina."
Na faɗa kai tsaye ina kallon Hauwa da ta yi kalan Tausayi. Ni kuma na ƙara jadaddamata da cewa na riƙe su a raina ita da Munnira na hakura amma ba zan manta da abin da suka yi min ba, ta na jin haka ta ce to ba za ta iya da ni ita kaɗai ba nan ta ke ta ɗau waya ta kira Munnira ta ce ta zo gidana yanzu a she su suna can suna ɓoye min mganar kar na ji hankalina ya tashi ni kuma ina nan gida na ƙullace su. A cikin wayar ma Munnira ta ji ina mita ina faɗin kwarai Ubangiji ma ya sani na ƙullace ku a cikin raina.
A she duk sun san abin da suka yi mini ba su kyauta ba muna cin abinci da Hauwa sai ga Munnira. Ni da kaina na je na buɗe mata gida ta na shigowa ta fara faɗin" Haba uwargidan Yallaɓai afuwan."
Hararanta na yi kawai na wuce na barta ta biyo bayana itama da na ta mganganun, ni abincin ma duk ya fita kaina ita kanta Hauwa kaɗan ta ci Munnira daman da na yi mata ta yi sai cewa ta yi sai da ta ci abinci ta fito daga gida.
"Haba Sadiya wa zai iya tunkaranki da mganar kishiya? Suna mafi muni a wajen mu mata. Tabbas na riga Hauwa jin mganar nan auran domin a daran Jamila ta kirani ta faɗa min ta kuma ce an ce a yi shuru saboda ba ki sani ba. Na shiga ruɗu da tashin hankali Sadiya lokacin da Hauwa ta kirani da niyyar wai mu shirya mu zo mu faɗa miki na ce a'a kar mu yi haka, ke ba za ki manta da mu a matsayin waɗanda suka sanar da ke labari mafi muni ba, sannan Tafida zai ta ganin baƙin mu. Mazajenmu kuma za su ji haushin mu domin mun shiga hurumin da namu ba. Sadiya ki kalli dalilinmu ta fuskar fahimta ki yi mana uzuri, in kin ƙullace mu wannan ba laifi ba ne hali ne na ɗan adam saboda kina ganin har da mu aka munafunceki, amma kin ji dalilinmu ki yi duba da tsaka mai wuyar da muke ciki ki yi haƙuri zuciyarki ta yi sanyi a kan mu don Allah."
Kallon Munnira kawai na ke yi har ta dire mganarta ban ce komai ba. Ganin haka ya sa ta gyara zama a saman kujera mai zaman mtum ɗayan da ta ke fuskata ta, ta cigaba da faɗin" Ni fa sai dai ki yi ta ƙullatana Sadiya amma Allah ɗaya ne wallahi tallahi ba zan iya fara iya taran ki da labarin Yallaɓai ya ƙara aure ba. Hauwa ma ni na ƙwabeta. Gwara shi da kansa ya sanar da ke zai fi sauƙi."
Kai na gyaɗa kafin na ce" Uhm to ai da ba ku sanar da ni ba shima bai faɗa min ba a daran aka kirani aka sanar da ni."
"Waye don Allah.?
Har Munnira da Hauwa suna haɗa baki wajen tambayata ko wace ce kai tsaye na ce musu Ma'u ce, ita Munnira ba za ta gane wace ce Ma'u a wajena ba Hauwa ta fi sanin ta ita ce ma ta yi mata bayanin matsayin Ma'un a wajena da ta in da suka haɗu da Anty Bahijja suke aminta.
Munnira ta lailaya wata aashar kafin ta ce" Kai mutane ba su da kyau. Ita yanzu sai ta zaɓi bare a kan ki Sadiya? Ta na yar'uwanki ta kira ki ta na sanar da ke wannan baƙin labarin?
Ina murmishin takaici na ce" E mana. Ita ai daɗi ta ke ji,da kuma gayya ta kirani ta sanar da ni hakan"
"Amma wallahi ba ta kyauta ba."
In ji Hauwa.
"Kai gaskiya ta yi asara."
In ji Munnira. Sai kawai na kalle su amma na kasa mgana saboda wannan tuƙiƙin dake zuciyata yanzu ke taso min da aka ta da mganar.
"To wai shi Yallaɓai har yanzu bai sanar da ke ba?
Munnira ta tamnayeni ta na kallona, jikina a sanyaye na ce" Bai sanar da ni da bakin sa ba sai bayan Nene ta zo gidan nan jiya ta sanar da ni da kanta."
Gabaɗayansu suka waro min ido suna haɗa bakin faɗin" Ita Nenen?
Sai suka ba ni dariya har sai da na dara kafin na gyara zama ina ba su labarin abin da ya faru tun ranar da aka ɗaura auran na dai ɓoye musu abubuwan da suka shafi siirun auran mu, amma na sanar da su duka mganganun Nene a kaina da shi kuma abin da Yallaɓan ya ce min a jiya na ƙarishe da cewa" Ni dai har yanzu bai ce min komai a kan Gimbiyar ba."
"Tiƙashi.!"
Munnira ta faɗa ta na sauƙowa ta yi zaman dirshan saman cafet.
Ita daman Hauwa daman tuntuni a saman cafet ɗin ta ke zaune.
"Wai daman ashe haka kishi ya ke? Kishi na da zafi da ƙuna. Wallahi ban taɓa sanin raɗaɗin kishi ya kai ƙunar haka ba sai yanzu da ya faru a kaina."
Na faɗa ina jin numfashina na sarkewa. Hauwa da Munnira suka kalleni cikin tausayawa amma sun kasa mgana.
"Ku yi ta fatan Allah ya bar ku da mazajenku har abada. In kuma kaddara ta saka sun ƙara ku fara addu'an salama da sanyin zuciya tun yanzu domin ban sam da abin da zan yi iya kwantanta muku zafin da ke cikin a yi maka kishiya ba. Ballatana kishiya irin tawa wacce ta zo min a cikin bazata. Wallahi ban taɓa tsammamin Yallaɓai zai ƙara aure a wannan gabar ba. Ban kawo hakan a raina ba kwata kwata ba."
In na so na daure amma na kasa sai kuka, na dukar da kaina a cikin cinyoyina ina ta kuka Munnira ta taso zuwa kusa da ni ta zauna ta na lallashina.
"Ki yi haƙuri Sadiya. Ki daure."
"Ki daina kuka don Allah Anty Sadiya. ji na ke yi kamar na ta ya ki kukan wallahi"
Hauwa ta faɗa a muryanta itama kamar ta yi kukan
Lallashin su ma ƙara sakani kuka ya ke ganin na ƙi yin shuru ya sa Munnira ta ce Hauwa ta tashi su tafi tun da kuka suke sakani jin haka ya sa na haɗiye kukan da ke taso min.
"Gaskiya Nene ba ta kyauta ba. In hae abin da ta faɗa gaskiya ne ba ta ɗauke ki a ƴa ba. In ke yarta ce sai ta saka a yi miki kishiya! Na fi ganin laifinta sama da laifin Yallaɓai, domin ita uwa ce umarninta sama ya ke da umarnin kowa."
"Gaskiya ne. Nima dai haka na ce a raina. Ina laifin ta bari in ya zo ya faɗa miki sai a saka rana tun da ta matsa sai an ɗaura."
Hauwa ta faɗa kai tsaye Munnira ta gyara zama ta na ƙara faɗin" Ni fa ban iya shuru ba, har Nasir sai da na yi ma ƙorafi namiji ne kuma ɗan'uwansa ne shi kan shi ya ce ba a kyauta miki ba, ya kamata a fara ba ma Tafida lokacin da zai yi miki mgana da ke haƙƙin ki ne mganar wai da ke da Gimbiya ɗaya ta ɗauke ku ta faɗa ne kawai amma Ke suruka ce a wajenta matar ɗan ta. Gimbiya kuma ƴa ce a wajenta kuma suruka gaskiyan mgana kenan, sauran mganganunta kuma gaskiya ta faɗa ko Nasir ya ce ya na da kyakyawan shaida a kan Yallaɓai na daraja ki, na yarda da duka Nasabobin da ta ce Ubangiji ya ba ki amma kar ki sake ki ji a ranki da cewa Nene da yayanta za su ɗauke ke da Gimbiya ɗaya. ba gaskiya ba ne Sadiya. Kawai dai a yi sha'ani an cuci na ƙauye."
Duk fa abin da ta faɗa gaskiya ne. Ni daman ban isa na haɗa kaina da Gimbiya ba kuma ko Nene ta so ta ɓoye laifinta gaskiya ɗaya ce daga ƙin ta sai ɓataa ta yi son kai a wannan lamarin daga baya ne ta ji kunya ta zo ta na gyaran zence.
Yadda Munnira ta tsani kishiya ina tunanin in ita ce aka yi ma irin auran Yallaɓai da Nasir da Duniya ta gama jin kansu. Faɗa min ta ke yi na saka a raina kawai ni girman ne Allah ya ba ni na kama kaina amma ba ta ce na zauna a takani ba duk da ta san halina.
Hauwa dai ta na gefe yar cewa gaskiya ne, sun daɗe a gidana sai wajen biyar na yamma na raka su har bakin titi suka samu adaidaita sahu.
Kafin tafiyar su har mganar tafiyata Yashe na yi musu Munnira ta ce wallahi gwara na je na huta ko na samu salama mganar tariya suka yi min na ce ban sani ba Munnira ta ce da an tsaida lokaci na sanar da su za su dawo mu ma shiri za mu yi duk da ta sanni ni ɗin a shirya na ke, sai dai kawai na ƙara sabon shirin.
Na ji daɗin zuwan su kamar kar su tafi haka na dawo gida ni kaɗai duk sai na ji kewa, Allah ya taimake ni Khaleesat ta kirani a waya muka kusa awa muna hira. Kan dai maganar auran Yallaɓai ne itama faɗa min ta ke yi ta yi mamakin auran nan gaskiya. Duk daɗewar da muka yi muna waya shawarwari ta ke ba ni, na kama kaina na ƙi ji na ƙi gani, da sauran shawawarin masu girma ciki daman shi ne haƙuri sai na ninƙa haƙuri domin zan ta ganin abubuwa.
Kowa fa maganarsa kenan akwai zafi sai na daure, kuma kowa kalmarsa kenan sai na yi hakuri wato an san cewa lamarin akwai zafi akwai ciwo an kuma san zan ta ganin abubuwa sai na yi haƙuri ni dai fata na Allah ya sa har Yallaɓai ya yi gangancin cewa a nan gidan za ta zauna domin a lokacin ne zan yi abin da ba a yi tsammani ba. Gidan nan gidan shi ne amma kuma ya zama gidana tun da domin ni ya gina shi, in ina ma tuna yadda a ka gama gidan har na tare a ciki sai dai kawai na kaina wani abun gwara ka bar shi a rufe bayyana shi ba shi da amfani.
Sai da su Jidda suka dawo makaranta gidan ya ɗan min daɗi. Yallaɓai tun safe da ya fita sai bayan isha'i ya shigo gidan da tarkacen su cakulate da ice crean ɗin da ya siyo ma Baby. Ya na dawowa ya yi wanka sannan ya ci abinci farar shinkafa na dafa masa tun da shi ba ya son taliya, ya na gama ci ya ce su Jidda su shirya za su je Gwammaja domin duba Gimbiya ni har na ma manta da maganar amma shi ya na nan sane.
Yaran ko suna ta murna ni dai ina zaune ina kallon ikon Allah. Yallaɓai ya sha shigan ƙananun kaya rigar fara ce haka wandon kuma baki ne har da saka rufaffen takalmi da daddaren kamar wanda zai je taɗi! A raina kuma sai na tuna ai ya na da Amarya shi ke da ko babban taɗi adon ma domin ita ya yi shi ya sa gabaɗaya na yi kici kicin da raina. Lokacin da za su fita na rakasu har bakin ƙofar falo, har Yallaɓai ya fita yaran sun yi gaba suna ɗaga min hannu har na ba ma Jidda Soyayyen nama na ce ta kai ma Nene ina tsaye riƙe da kofar falo na kasa tafiya sai na ji kamar an dasa ni.
Kawai sai na ga Yallaɓai ya dawo sai ya ganni a tsaye riƙe da ƙofa sai muka tsaya muna kallo kallo.
"Lafiya! Ko ka yi mantuwa ne?
Na tambaye shi ganin ya na kallona. Sai ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" E. Na manto waya ta a ɗaki."
Sai na juya na ce bari na ɗauko masa a can bedroom ɗin mu ya barta ina ɗauko ma sa wayar hannuna tsautsayi ya sa na ta ɓata sai hasken ta ya kawo, idona ya hango min Daugther 3 missed call. Da sauri na danne gefe hasken wayar ta ɗauke, da sauri na koma na kai masa wayar ya karɓa ya na kallona kafin ya ce.
"Thank you."
Ya faɗa lokaci ɗaya ya na zura wayar cikin aljihun wandon shi sannan ya ɗago ya na kallona, idanuwana na ware masa ina kallonsa da sigar tambaya.
"Ba damuwa in muka bar ki a gida ke kaɗai.?
Sai kawai na tsaya ina kallon shi a fuskarsa na gama nazarin abin da ya ke nufi da maganarsa amma ban nuna masa na gane in da ya dosa ba.
"Babu."
Na bashi amsa a takaice, ya fita ni kuma na ja ƙofar zan rufe sai ya kira sunana.
"Sadiya ta."
Sai na dakata ina kallon shi har ina gyarawa tsayuwan yadda zan yi ma Yallaɓai tijara in har ya sake ya ce na shirya mu je gaida amaryansa sai Allah ya ƙwace sa bai ce ba.
"Bar shi ma. In dai na dawo za mu yi mgana."
Sai na gyaɗa kaina lokaci ɗaya ina faɗin" A dawo lafiya."
Daga haka na maida kofa na rufe na koma can falon yara na zauna, ba na son damuwa ya sa na ɗau romot ina yawo a tsakanin tasha she, har dai na tsaya a Mbc2 suna haska wani american film mai kyau shi na tarrara ma hankalina gabaɗaya nan saboda kallon da ya ɗau hankalina ban ma ga daɗewarsu ba, sai da na ji kiran