Showing 72001 words to 75000 words out of 141487 words
ne daga saman fuskata amma a ƙarƙashin zuciyata kwata kwata ba daɗi.
Washegari da safiyar Talata ya na gida bai fita da wuri ba yana ta aiki a laptop ɗin sa ni kuma ina cikin ɗaki a kwance. Yadda bai tambayeni me ke damuna ba, nima ban faɗa masa komai ba ai ya na da hankali tun da ya ga ina kwanciya ai ya san ba lau ba, amma mutumin nan ko a jikinsa sai ma wanka da ya yi ya shirya cikin manyan kaya ya fice ya bar ni kwance cikin yanayi mara daɗi. Ban taɓa tunanin akwai wata rana da Yallaɓai zai ganni kwance bai fara rawan jikin tambayana lafiya na ke kwance? Me ke damuna? Amma yau sai ga shi kwana biyu ina kwance ban ji daɗi ya fice ya bar ni ko a jikinsa lalle na fara yarda ina da abokiyar zama. Ba ni kaɗai Yallaɓai ke da shi ba, shi ya sa yanzu ba zai cika damuwa da ni kamar a baya ba. Sannan na lura da wani abu tun kwanciya Nene asibiti bai neme ni ba sai ranar da ta dawo gida shima tun daga ranar har yau bai ƙara nema na ba, ni da na san Yallaɓai da bama ɓarnan ruwa muhimmaci amma yanzu kwata kwata ba ya nuna sha'awar haka, ko na daina burge shi ne ban sani ba? Wata zuciyar ne ta faɗa min cewa yanzu ba da ba ne ya na da wata matar, in ma ni bai neme ni ba ita ba zan ba da tabbacin bai samu natsuwa daga wajenta ba.
Ina kwance ina tunanin nan sai ga kiran shi, ina ɗauka bayan mun gaisa shima gaisuwan ni na gaishe shi ya amsa sai ce min ya yi na shirya na je Gwammaja na sake duba Nene ni kuma ban ce masa komai ba na ce to. Na ɗauka zan ɗan rarrafa na je amma kuma sai na kasa gabaɗaya jin jikina na ke yi kamar ba nawa ba, sannan ni ba na so ma ina fita in ina cikin wannan yanayin ganin dai ba zan samu zuwa ba ya sa na yi ƙoƙarin neman wayar Yallaɓai na faɗa masa ban da lafiya amma ban samu wayarsa ba, ban yi tunanin rashin zuwan nawa zai iya zama matsala ba, ban kuma taɓa tunanin Yallaɓai zai iya min fahimtar a bai bai ba.
Ranar Saude ma ba ta zo ba ta je makaranta Marwa na kira ta ce tana asibiti sai 2 na rana za ta dawo sai na ce ta biyo ta gidana ba na jin daɗi. Ita ta zo ta gyara min gida sannan ta yi ma su Jidda girki, ita da kira Ya Aina ta faɗa mata cewa ta na gidana ba na jin daɗi har ta ba ni ita ma muka gaisa ta na faɗan ban da lafiya amma ban faɗa ma kowa ba? Sai na ba ta haƙuri da cewa ba wani ciwo sosai ba ne shi ya sa ban ɗaga musu hankali ba, ita kuma Ya Aina ta kawo maganar cewa daman kwanan biyun nan duk kowa ya ji ni shuru na ce ina nan lafiya ba wani abu ba ne mai tsanani kar ta ɗaga hankalinta. Mun rabu da cewa Marwa ta kwana nan tun da ban ji daɗi na ji daɗin haka tun ballatana da Marwa ta ce Gobe ta na da hutu sai jibi ta ke da aikin dare sai na ji daɗi ko banza za ta ɗebemin kewan zaman gidan ni kaɗai.
Yallaɓai da wuri ya dawo wajen tara na dare. Sai kuma ni da kaina na zauna ina nazarin wani abu. Kwana biyu ya ke yi in ya fita ya na kaiwa dare a Gwammaja kwana biyu kuma sai ya riƙa dawowa da wuri kuma har ya ci abinci sai zuciyata ta zargi kamar ya na raba mana kwana ne ni da Gimbiya duk da ta na can Gwammaja, saboda sai na ga kamar tsarin da ya ke bi kenan ban yi masa maganar rashin zuwana can Gwammaja ba nima kuma bai yi min ba kuma ko da ya ga Marwa a gidan bai damu da ya ji dalili ba sanin daman ai yar gidana ce ta na zuwa sosai shi ya sa hankalin shi bai kawo masa wani abu ba.
Allah sai ya taimakeni washegari na tashi garas kamar ba ni ba, Marwa ta na nan sai yamma ta shirya ta tafi asibiti. Ranar dai mun yi azkar tare da su Jidda har na yi musu karatu ban dai ɗauki Qur'ani ba ne tunda ba ni da tsarki. Domin na ƙara samun tabbaci a kan sabuwar daɓi'ar Yallabai ya sa ban yi barci da wuri ba kuma illau ranar ma da wuri ya dawo na gabatar masa da abinci ya ci ya yi wanka, sannan sai ya jima ya na aiki a loptop har na yi barci na bar shi bai gama ba, washegari na sake zura masa ido sai ya maimaita abin da ya tsara bai shigo gidan ba sai sha ɗaya da rabi na dare ta ma gota ban yi barci ba a raina daman na kudri niyya sai na yi masa mgana saboda a daran na kira Nene na gaisheta na ba ta haƙuri na ce ban ji daɗi ne shi ya sa ba ta ganni ba sai ta yi min sannu ta ce ba ta sani ba domin ba su yi maganar da Tafida ba.
A lokacin na ji maganarsa a ɗakin Nene da na wasu amma ban ɗauki muryan kowa ba sai na shi, kuma a lokacin ko tara bai yi ba kenan a can ne ya ke kwashe lokaci mai tsawo shi a dole mai Mata kawai sai na saka a raina sai na yi masa mgana. Gwara ya riƙa kwana a can duk ranar girkin Gimbiyar in Adalcin ya ke son ya kamanta dakyau, ni ba ma wani amfani ya ke yi min a gidan ba, gwara ya riƙa tsayawa can ya na kwanan shi zai fi sauƙi da wannan ciccin mganin da ya ke dawowa gida ya na yi min ba tare da na san laifin da na yi masa.
Ina kwance a kan gado ya shigo na yi masa sannu da zuwa ya amsa ya na kallona.
"Ba ki yi barci ba?
Ya faɗa lokaci ɗaya ya na cire agogon hannun shi.
"E."
Na bashi amsa a gajarce sai ya jinjina kai kawai ya fice ya shiga tiolet ya ɗan daɗe sannan ya fito bai yi wanka ba na ga dai fuskar shi da ruwa, duk ina zaune ina kallon shi na yi masa ta yi abinci kamar yadda na yi zato sai ya ce min ya ƙoshi ya ci abinci a can Gwammaja.
Sai da na bari ya yi shirin kwanciya ya na zaune gefen gado da wayarsa a hannunsa ya na dubawa ina kallon shi ya na ta mirmishi koma mene ne ya ke dubawa ya na jin daɗin haka.
"Ya jikin Nenen?
"Da sauƙi Alhandulillah."
Ya ba ni amsa amma hankalinshi na kan wayarsa.
"Allah ya ƙara mata lafiya."
Ya amsa da Amin haka a gajarce, sai na ɗan yi shuru kafin kuma na yaye bargon jikina na sauko da kafafuna daga saman gado na sauke a saman cafet ɗin gefe da gefen gadon.
"Yallaɓai."
"Uhm."
Ya amsa min a ciki hankalin shi har a lokacin na kan wayarsa.
"Na ce ba."
Sai ya ji na yi shuru sai ya juyo ya na kallona bayan ya ijiye wayar a gefen shi, ya na mai kallona kafin ya ce.
"Ina jin ki. Kika ce me?
Kai tsaye na ke kallon shi kafin na ce" Wata shawara na ke so ba ba ka Yallaɓai."
"Ina sauraran ki."
Ya faɗa ya na mai ƙureni da ido amma fa ya wani haɗe rai kamar ya san abin da zan faɗa
"Me zai hana duk ranar girkin Gimbiya ka riƙa kwanan ka kawai a can Gwammaja."
Giransa ya tattare waje ɗaya ya na min wani kallo amma ban fasa mgana ta ba.
"Zai fi tunda akwai ɗakuna a can"
"Me ya kawo wannan mganar kuma?
"To ai na ga kana raba mana dare ne da ita. Da zuwan da kake yi kana raba dare barci kawai ke kawo ka nan shi ne na ce duk ranar girkinta ka riƙa kwanciyarka a can har ta koma gidan ta."
Ya daɗe ya na kallona bai ce min komai ba, ni kuma ganin ya yi shuru ya sa na tashi zan fita zuwa tiolet har na ɗan gota shi zaune a gefen gado.
"Kin gama mganarki?
Sai na juyo ina kallon shi kafin na ce" E. Na gama."
Sai kawai na ga ya miƙe ya wani harɗe hannuwansa a saman kirjinsa ya fara takowa gabana cikin wani yanayi, sai na tsaya kawai ina kallon shi ba tare da na yi mgana.
"Sadiya."
Ya kira sunana a kausashe bai ma jira na amsa ba ya ce" Kishi ne ke rufe miki ido ko?
Cikin mamaki na kalleshi ina shirin mgana kawai ya wani ɗaga min hannu a fusace ya ce" Ke kaɗai ce mai bakin magana!? Ko ke kaɗai ce ake yi ma ba dai dai ba? Ko ke kaɗai ce ake zalunta ehe?
Ya ƙarishe faɗa ya na mai yi min tsawa, sai na yi baya kawai ina kallon Yallaɓai na kasa mgana.
"Ko domin kin ga bana son ina yi miki faɗa? Ko kina tunanin ina tsoron ki ne? To bari ki ji na faɗa miki ba ki isa ba, ba ke kike aurena ba ni na ke auran ki Sadiya saboda haka ki shiga hankalinki tun kafin ki ɓata min rai na buɗe miki bakina ba za ki ji daɗi ba."
Sai na fara mamakin sa? To wai ya na jira na ne, me na yi masa da zai wani fara balbaleni da masifa daga faɗin gaskiya ni ma ko a fusacen na kalle shi kafin na ce" To wai me aka yi maka? Daga faɗin gaskiya sai ka fara wasu mganganu da ban gane musu ba! Ni na ce ka yi laifi ne! Rayuwarka ce yadda ka so ai haka za ka tafiyar da ita. Kuma da kake maganar za ka buɗe bakin ka in ka bude ba zan ji daɗi ba, to don Allah Yallaɓai ka buɗe bakin naka ka yi mgana mana sai me?
Na faɗa ina watsa hannayena daman raina a ɓace ya ke kuma a kusa na ke.
"Kika ce sai me ko Sadiya?
Na taso masa ina faɗin" E sai me in ka buɗe bakin? Me za ka faɗa min wanda ayyukan ka ba su nuna min ba. Koma za ka ce ka ce gaskiya na faɗa ina lura da kai kwana biyu nan kake cin abinci kuma ka dawo a kan lokaci kwana biyu kuma kana can Gwamnaja sai dare ka ke dawowa in na yi maka ta yi abinci ka ce ka ci a can, me ya sa ba zan yi tunanin ka raba ma kwanan ba ne kar a cuceta? Ni fa mafita na kawo maka domin kar ma ka yi tunanin alfarma ka ke yi min da kake kwana ranar girkinta a gidana shi ya sa na ce ka je can ka kwana ko ka riƙa tafiya can gidan nata kana kwana babu ruwana tunda in ba ka kwana a nan ɗin ba ba mutuwa zan yi ba, sannan kwanan ma da ka ke yi anan ɗin ba wani amfani kake tsinana min ba."
Raina ne ya ɓaci na riƙa sakar masa mganganu na gama na juya zan bar masa ɗakin sai ya saka hannu ya fizogoni ya dawo dani cikin ɗakin da karfi har ya na hankaɗani na yi baya Allah ya sa ban faɗi ba.
"Ina za ki je! Tun da kin gama fadin na ki sai ki jira nawa Malama."
Ya faɗa ya na nuna min yatsa, sai kawai na koma na yi tsaye na harɗe hannuna a ƙirji ina girgiza jikina kafin na ce" Ai ban hana ka mgana ba."
"Me ke damun ki? Me kuma kike taƙama dashi ne? Tun da na yi auran nan kike bi na da fitina ina ƙyaleki saboda ina ganin kamar ni ne ban yi miki dai dai ba, amma me ya sa haka! Me ya sa kike da ɓakin kishi ne Sadiya?
Na buɗe baki na rufe ya fi sau uku ina rufewa na kasa mgana.
"Ni ke kake kira da mai baƙin kishi Yusuf?
"E mana baƙin kishi ke damun ki, kin ƙi ki kwantar da hankalinki ki yi ta zarge zarge. Kar ki manta itama Matatace kamar yadda kike matata kuma auren da na yi zunubi ne? Ko Allah ya hana ne?
Ai sai kawai na rufe bakina na yi shuru, ganin idanuwan shi sun rufe ya na zaro maganganu.
"To ba ri ki ji na faɗa miki ba ki isa ba. Ke in har kina da tunani za ki kawo wannan mganar? Gwammaja nan ne gidan Ubana kuma uwata ce ba lafiya ta ke jinya. Gimbiyar da kika saka ma ido kike kishi da ita ita ce ta bar komai na ta har da ni mijin da kike takama da ni ta je ta zauna ta na kula da mahaifiya ke ina kike? Ba kina gida akwance ba? Kin taɓa tunanin cewa bari ki je ki taimaka mata! Ko shekaranjiya da na kira ki na ce ki je kin je! Kin je? Na ce kin je?
Ya ƙara daka min tsawa sai na saka hannuwana duka biyu na toshe kunnuwana saboda sosai ya yi min ihu a saman kaina.
"Ki saki kunnuwan ki saurareni da kyau. Daughter ta yi min komai kuma komai za ki ce kin daɗe ba ki ce ba. Kwana kuma babu ruwanki ba ke za ki faɗa min abin da ya kamata in yi ba, in ina son kwana a can ke ba ki isa ki sani ko ki hana ni ba, shawara da zan ba ki ki riƙa saka alheri a cikin zuciyarki Sadiya saboda wata rana kar ki ji kunya."
"Ba ni da alheri a zuciyata ka ke son ka ce mini Yusuf?
Na faɗa muryata na rawa ina nuna kaina.
"To ina alherin. Kin bi kin kwazzabi kan ki tunda na yi auren ba ki bar ni na huta ba daga kice na yi miki kaza sai kice ƴan'uwana sun yi miki kaza duk dai na biki da ki yi hakuri saboda a zauna lafiya. In ba zuciyarki ba ta saƙa miki alheri ba yanzu ya kamata a wannan halin ki tare ni da wannan mganar? Gimbiyar da kika tsana ita ce ke son ki tsakanina ga Allah ƴaƴanki kamar na ta ta ɗauke su amma ke ko sau ɗaya a zuciyarki ba za ki ɗan mutuntata ba? Ta na can ta na wahala da mahaifiyata ko sau ɗaya kin ji a ranki ya kamata ki gode mata! Ai ba ita kaɗai ba ce matata ke ma ɗin matatace kuma akwai haƙƙin mahaifiyata a kan ki Sadiya, kin je? Ba daina zuwa duba ta kika yi ba amma kullum anan gida na ke barin ki kwance amma saboda ba ki da kunya har kina tara ta da wata mganar banza saboda kin ga na yi miki shuru? To ki fita daga idanuwana ki kuma fita daga abin da ya shafe ni da matata babu ruwanki, kamar yadda kema kika ce na daina saka ki a lamarinta tun a baya to kema babu ruwanki da sha'aninta ko wani abu dake tsakanina da ita. Ni ne na ijiye ki, da ni za ki yi ba ita ba."
Ko kafin ya gama mganganunsa na durƙushe a ƙasa ina kuka mai sauti lalle duniya juyi juyi wai ni yau Yallaɓai ke faɗa ma ba ni da alheri a zuciyata.
Ina kuka na ɗago ina kallon shi hawaye wani na koran wani cikin shaƙewar murya na nuna kaina ina faɗin" Ni ka ke faɗa ma ba ni da alheri a cikin zuciyata Yusuf? Ni Sadiya?
"E ke kika ja. Me ya sa zuciyarki ba ta ba ki damar ganin alherin mutanen da ke tare da ke? Kishi hauka ne Sadiya?
Ya sake taso min babu nadama ma a cikin maganganun sa sai kawai na sake fashewa da kuka wani abu mai ɗaci na sukan zuciyata.
kawai sai gani na na yi na miƙe ina faɗin" Yau ni kake yi ma gorin ban kula da Nene ba Yusuf? Ni kake yi ma gori?
Sai ya yi shuru bai yi magana ba sai kawai na yi murmishin takaici ga hawaye wasu na korar wasu, sai kawai na kaɗa kaina kafin na ce" Zan faɗa ba domin ina so ka yarda da ni ba. Tunda Nene ta kwanta asibiti har ta dawo gida ban taɓa fashi ba, ko ban je na kwana da ita a yanzu a baya in ka manta na yi ƙila sama da abin da ka ke jijiyan wuya matarka ta yi. Mganar ban je Gwammaja ba ranar kuma ba ni da lafiya ne kwanciyar da ka ga ina yi ba ta lafiya ba ce, kuma na yi ta kiran wayar ka na faɗa ban samu ba ne, shi ne ka ke tunanin da gangan na ƙi zuwa? Kai iya naka zuciyar alherin kenan Yusuf?
Na faɗa ina kallon shi, ina kuka saboda zuciyata ma zafi ta ke yi min ina numfashi sama sama kamar mai ciwon Asthama."
"Wa kika faɗa ma ba ki da lafiya! Kin faɗa min? Ko ina da Allah musuru ne da zan san ba ki da lafiya.?
Ya faɗa ya na kallona amma ya ɗan sassauta muryan shi.
Kawai sai na kalle shi, sai ji na yi kamar juwwa za ta kwashe ni sai kawai na taka na fice daga ɗakin ina ji kuka na taso min daga ƙasan raina falon yara na koma na zauna na ci kukana kamar zan shiɗe, na tabbata in na cigaba da kuka nan zafin da zuciyata ta ke yi za ta iya bugawa na mutu Yusuf ba shi da asara. Ni wai yau Yallaɓai ya kalli tsabar idona ya na faɗa min Gimbiya ta yi masa komai wato ni kuma ban yi masa ba kenan ya manta tarin alherina a gareshi yau ni ce na zama mara zuciyar alheri, ina hawaye ina tuna baya, akwai wani lokaci a baya lokacin na haifi Jidda Nene ta yi wani ciwon kafafu mai zafin da ko bayi sai an kaita ni na koma Gwammaja da ga ni har Yusuf muna kwana acan