Showing 84001 words to 87000 words out of 141487 words
Ni Allah na tuba ina ga ita ce baƙuwa a harkan ni ba domin ya matsa min ba wallahi bai dame ni ba. To wai mijin kan shi fa raba shi kake yi da wata to mene ne a cikin zama a gaban mota? sai na ke ganin shi wannan ai ba wani abu ba ne.
Muna dawowa muka sulala indomie muka ci, sai can da rana Musbahu ya kawo kayan ciki na Yallaɓai da nawa sai naman ragon da ya yi min layya daman duk shekara yana yi min in kuma bai da shi ya yi nashi shi kaɗai. Kuma in dai ya yi min to ni ake kawo ma Naman na diɓan ma gida sauran kuma mu yi amfani da shi a gida na Yallaɓai kai da kafa kawai ake gyarowa aka wo naman kaɗan ne ake kawowa duk sai ya ce ya yi sadaka da shi. Yau ma ɗin haka na yi na diɓar ma Gidanmu na ba ma Marwa na adaidaita ita da Jidda suka je suka kai musu muna gida ni da Baby muna jiran su yaran nan sai yamma suka dawo suna faɗa min gida cike da matan su ya Hamza ana ta hidima sai na ji kamar na yi tsuntsuwa na ganni a gida, Alhajinmu ya ba ma Jidda goron salla ya ce Baby ta nemi na ta mijin ya ba ta, Baby na jin haka ta fara rigima sai ta je mu na yi mata dariya.
Sai dare muka dafa shinkafa Jalop da nama, muna ma cikin ci ne sai ga Yallaɓai ya shigo gidan bai ma wani tsaya ba ko abincin da na yi masa ta yi bai ci ba ya dai sha ruwa sai nama ya ci, cincin kuma da na ɗibar masa a leda ya ce na saka masa ya tafi da shi, ina jin haka sai na ɗibar ma Gimbiya kar ta ga ya je da shi ita ban kai mata ba, tunda ni ma ta na kawo min abubuwa in dai ta yi har soyayyen naman ma na ɗibar mata ya ko karɓa ya na ta murna har ya na ce min.
"Allah ya saka miki da alheri Sadiya ta."
Na amsa masa da Amin to har ya tafi fa sai ga shi ya kirani a waya wai zai zo na zuba masa abinci Gimbiya ba ta yi girki ba saboda ba ta jin daɗi. Na ce to ya zo ba daɗewa sai ga shi, a raina na ce shi ma dai da gulman shi na fa yi masa ta yi da farko ya ce ba zai ci ba ya ɗauka ta dafa masa ne in ya koma kar ya ce mata ya ci a wajena ta ji haushi sai kuma ta ɓare da shi a babba kula na saka musu mai yawa ya na ta min godiya.
"Godiyar nan ta yi yawa Yallaɓai sai ka ce na yi maka wani abu."
"Wani abu ne mana. Ke dai kawai Allah ya yi miki albarka."
Na amsa da Amin Amin sannan muka yi sallama ya tafi, ko washegari da ya ke gidana ma sai da ya karɓan mata tuwon shinkafar da na yi miyan agushi, ya na faɗa min ba ta yi girki ba ai ba ta son kamshin girki a raina na ce ko dai ciki ne? Amma ban furta masa ba amma dai na ce ya kamata su je asibiti ya ce za su je in sha Allahu.
Tuwon da ɗan yawa na yi na aika can Gwammaja sai Hauwa da Mutaƙƙa ya zo ya karɓan mata sannan Musbahu ya zo da wani abokin shi, suma sun ci na saka musu cincin da Nama, da daddare ma sai ga Adnan ya na gidan sai ga Datti ya zo Allah ya sa da sauran shi sai na saka musu da ya ke kuma sun san juna suna ta hira. Wannan salla ban samu wasu yan yawon salla ba da rana dai Firdausin Ya Balki ta yo min zuga ƙawayenta da ƴan'uwanta bayan sun ci abinci da za su tafi na ba su 2k goron sallah ina ta tsumayin ƙannen Marwa amma ba su zo ba ranar salla ta uku kuma Gwammaja muka yi ni ban tsaya dafa wani abinci ba tea muka sha da safe muka tafi suma can ɗin cike gidan ya ke can na iske Gimbiya ina ganinta na fahimci ba ta da lafiya ta yi zuru zuru sai kwanciya ni dai kamar shigar ciki na gani tare da ita amma ban yi mgana ba haka ma kowa ke faɗi in ya ganta su Anty Bahijja ne yan faɗin in sha Allahu ma cikine za ta faɗa ma Tafida ya kaita asibiti a tabbatar.
Har su Hauwa sai da suka ce min kamar Amaryan ki na da shigar ciki na ce ban sani ba wallahi
Munnira ta kalli Gimbiya ta sake kallonta kafin ta ce" Ke Sadiya na ba ki tabbacin Amaryan Tafida ciki ne da ita."
Duk da acan ƙasan raina na ji wani iri amma ai tunda an yi dare ni na san garin zai waye komai daran daɗewa shi ya sa na yi mirmishi kafin na ce" Ina musu fatan haka"
Saboda ni na san Yallaɓai na son haihuwa Allah ne kawai bai bashi masu yawa ba na tabbata zai fi kowa farinciki da hakan shi ya sa a ƙarƙashin zuciyata na yi ta karfafama kaina Gwiwa in ma ta na da cikin. Cikin na Yallaɓai ne kuma ni da na sha yi ma kaina alƙwarin in Yallaɓai ya ƙara aure har ya samu ƙaruwa zan fi shi murna da farinciki sannan zan so duk wani abu da ya fito daga jininsa ko tsatson sa. Shi ya sa na yi ta kiran sunan Allah a raina har ya kawo min agaji na ji na samu salama.
Muna Gwammaja har tara na dare da ɗaya da ɗaya kowacce mazajensu na ta zuwa ɗaukan su. Wannan karon dai Cincin kawai da nama na kawo ma Nene ta yi ta saka albarka, Hajiya Iya da Maman farko sai na kai musu cincin kawai suma suna ta godiya da faɗin" Sadiya ba kya gajiya? Ina zan gaji ina ganin su ne kamar iyayena mijina suma yadda zan kyautata ma Nene haka suma na ke yi musu kamar yadda suma na ga ƴaƴan gabaɗaya ba sa nuna bambamci a tsakaninsu. Gimbiya dai har da su Cake ta yi amma ina tunanin ba dawa ta yi aka yi mata an kawo min da yawa jiya har da dambun nama ga soyayye. Na gan shi na ma su Anty Bahijja suna ta ci da Naja'atu da ta zo daga baya.
Wannan salla Yallabai bai siya mana kaji ba wai ya manta lokacin da na tuna masa kuma duk an siye sai dai bayan sallah ya ce mu bi shi bashi, ni kuma ban ji daɗi ba saboda ni dai na fi son naman kaza fiye da naman rago shi ya sa ban ma wani ci naman sosai ba kuma wannan sallar ban yi dambu ba na gaji Marwa ta ce za ta yi na ce ta bar shi kawai.
Sai da Yallaɓai ya dawo sannan ya ɗauko mu gabaɗaya wannan karon ma a gidan gaban ya ce na zauna ita kuma a baya ita da yara. Sai dai muka fara kaita gida muka sauke su ita da Jidda sannan muka juya gida, muna hanyar komawa gida Yallaɓai ke faɗa min gobe zai kai Rano Gombiya ta kwana biyu.
"Gobe? Ita da ba ta da lafiya?
Na faɗa ina mai kallon shi, sai ya kalleni shima kafin ya mai da hankalin kan tuƙin shi ya na cewa" Nima haka na ce mata amma ta matsa ita sai ta je. Sai na ce ta je ta kwana biyu ko?
Kai na gyaɗa kafin na ce"Haka ne. Tunda kuma ai ba kwance take rigis ba."
Daga haka na yi shuru ina jin shi ya na faɗa min wai ta matsu ne ta ta ji an ce duka yan'uwanta sun je can sallah.
"Har da Tariq da Farida?
"E mana. "
Sai na jinjina kai kafin na ce" Ban ɗauka za su zo ba. Na ga ba su daɗe da komawa ba ne."
Ya na dariya ya kalleni kafin ya karkato ya na min raɗa.
"Maaganar Kawu da ɗiyarki ne musabbin zuwan shi."
Sai na kalleshi ina faɗin" Da gaske? Sai ya koma ya gyara zama hankalinshi na wajen tuki ya na mai faɗin" Da gaske na ke faɗa miki. Gobe in na kai Gimbiya za mu haɗu mu kara tattaunawa yadda muka tsaida za ki ji "
Sai na jinjina kai kafin na ce" Allah ya tabbatar mana da alheri."
"Amin. Ai in sha Allahu Alheri ne tun da na ga Kawu ya susuce shi fa ya matsa mana sai mun haɗu akan mganar nan"
Ina mirmishi na ce" Allah ya tabbatar Yallaɓai."
Ya amsa da Amin muna tafe muna hira har gida, Marwa suka shige ciki da Baby ni da Yallaɓai muka zauna a falo muna kallo muna ta hira sai a lokacin ya ke faɗa min ya kama min shagon su na ƙasa sai kuma ga maganar auran shi da Gimbiya wai ya yi tunanin ya yi min mganar zan ce dannen kirji ne. Shi ya sa kawai ya buɗe ma su Musbahu da wani ma'aikaci da ya ɗauka suna zama a ƙasa shi kuma office ɗin shi na sama.
"Bakomai. Allah ne bai yi lokacin ba. "
"Zai yi lokacin in sha Allah soon."
Na ce Allah ya sa amma ba wai domin na wani yarda da shi ba.
"Wai shi Musbahu wani matsayi ka ba shi a wannan kamfanin naka ne Yallaɓai?
"Manaja na ne shi. Wanda na ɗauka kuma mataimaki ne kafin dai mu ga abin da Allah zai yi kin san komai a sannu sannu ya ke tafiya."
"Haka ne. Kai kuma fa?
Ya na yar dariya ya ce" Ni? MD Managing derector."
Hannu na ɗaga masa ina faɗin" Allah ya ƙaro dubban Nasarori mai girma MD"
Ya amsa ya na shafa gashin kaina daman ina saman kirjinsa ne muna zaune a waje ɗaya muna hira muna kallon wani film a MBC action.
Sai wajen sha biyun dare muka kwanta ni da Yallaɓai kafin mu kwanta sai da ya kira Gimbiya ta yi barci ba ta ɗauka ba sai da asuba ya same ta. Jikinta ya tambaya ta ce da sauƙi ina gefen shi ni ban ma ce ya ce mata ina gaisheta ba amma sai gashi ina jin sa ya na ce mata na ce ina mata sannu sai kawai na kalle shi ta gefen ido girgiza kawai na yi saboda Yallaɓai ya yi nisa ba ya jin kira lamarin na shi ya koma har da kage ni yaushe na ce ina mata sannu! Ai na yi mata sannun jiya da muka haɗu ba shiken nan ba.
Daga ni har shi da wuri muka shirya ni duk da na tsaya na dafa shinkafa da miya da salat wanda zan tafi dashi ɗorayi. Yallaɓai sai da ya ci sannan ya fita ya ce zai je ya ɗauko su Gimbiya mu shirya in ya ijemu a Gwammaja za su wuce. Ban yi masa mgana ba sai da ya ɗaukota suka dawo gidan ta shigo na yi mata ta yin abinci ta ce ba za ta ci ba ganin kamar ta na wani zumɓuran baki da ya ce tare za mu fita gabaɗaya sai kawai na ce masa su tafi mu in mun tashi za mu hau adaidaita.
"Kin tabbata ba matsala?
"Babu ku je kawai Allah ya kiyaye hanya."
Na faɗa kai tsaye, saboda na ga sai wani cin magani ta ke yi ni dai ban ko bi ta kanta ba can su ƙarata yara ne suka raka su haraba ni dai daga ƙofar falo ban ƙara gaba ko'ina ba. Sun tafi ba daɗewa nima na tattara Iyalaina muka ya da zangon mu a Ɗorayi duk sammakona sai da su Rahila suka rigani zuwa Ma'u ce kawai na riga ta zuwa Amina daman tun jiya ta iso gida ya cika maƙil kwanmu da ƙwarkwatan mu Alhajinmu baki ya ƙi rufuwa.
Ko su Ya Hamza ban da salla ba abin da ke fitar da su waje duk ana tare a falon Alhaji ana ta hiran yaushe gamo. Abinci daman kowwccen mu ta yo girkinta nan fa aka baje ana ta liyafa ana hira ana ta dariya cikin Annushuwa kowa kuma da ruƙunin da ya ke zaune ni dai ina zaune ne da Khaleesat da Amina sai Ya Hamza saboda daman tun muna yan mata Ya Hamza na cikin Fav ɗina shi ma haka domin yadda ya ke kula da ni ko Rahila da suke uwa ɗaya albarka haka itama Rahila Ya Auwal ne na ta ko da matarsa ma sun fi ɗasawa ita kuma daman Ma'u tana rukunin Ya Murja ne Ya Aina kuma ita da Yaya Abubakar da Ya Balki ne in dai ya na gidan to tare suke zama Datti kuma ɗan gatan Alhaji ne ya na gefen shi. Saboda yau ta ke salla kuma an daɗe ba a haɗu ba sai ba a yi faɗa ba ana ta hiran zumumci ana ta shewa sai salla ke ta da mu.
Mun haɗu gabaɗaya mun yi ta hotunan tarihi da mu da ƴaƴanmu gabaɗaya. Mu ne har dare sannan Alhajinmu ya ce kowacce ta yi shirin tafiya gidan ta. Ni ban jira Yallaɓai ba domin ban san ko yaushe zai dawo ba, Ya Aina ta ce gobe Marwa ta koma gida sai na marairaice ina faɗin" Haba Ya Aina sai jibi dai. Kin ga gobe zan dawo za mu je can Gandun albasa ne"
"To Allah ya kaimu."
"To ke Ya Aina ku bar ma Sadiya Marwa ɗin gabaɗaya mana tun da dai ta na son ta."
In ji Ya Hamza saboda shi ɗan ba ruwan shi ne, ba kuma shi da tsoron yin mgana in dai ita ce a zuciyarsa.
"Sai ta haɗa da Jidda duk su aurar da su ita da Injiniya."
Ya Auwal ya faɗa ya na dariya Gwaggo na wajen har ta saka baki da cewa" To ko a yanzu Sadiya ce uwar Marwa. Ita Aina Mama ce ita kuma Sadiya Umma ce ka ga ko Umma ce uwar amarya."
Muna ta dariya gabaɗayanmu Ya Aina dai ba ta ce komai ba sai mirmishi. Tare muka fita da Ya Ainan Ya Auwal ya ɗau motar shi ya kai mu gida ni ya fara ijewa ni da yara ita kuma ya tafi kaita gida.
Yallabai kuma sai wajen sha ɗayen dare ya dawo ni kuma na gaji domin har ma na fara barci sama sama na ji dawowar shi da mganar shi da safe kuma bai yi min wata mgana ba nima ina sauri za mu je gidan su Mama sai ban tambaye shi ba. Tare da yaran muka sake komawa can Gwammaja daga can muka haɗu gabaɗayanmu ban da dai Ma'u. Daman jiya ta ce za ta je kura wajen Baaba amma kaf ɗin mu ne muka je gandun albasa gidan su Mama. Inna Mariya daman ta na gida ne mijinta ya daɗe da rasuwa.
Mun daɗe domin sai la'asar muka koma Gwammaja Ya Auwal da Ya Hamza sun yi musu alheri nima na kai musu nama da cincin da cake wanda na diɓa cikin wanda Gimbiya ta kawo min, suna ta mana godiya sun daɗe daman ba su ganmu mun haɗu gabaɗaya a lokaci ɗaya ba sai dai wani lokacin leƙowa dabam dabam. To wannan karon salla duk ya game mu waje ɗaya. Bayan mun dawo Gwammaja ne Yallaɓai ya kirani a waya ya ce na tura masa lambar Mijin Ya Aina Allah ya sa ina da shi na tura masa kuma ni ya ƙi faɗa min komai ya dai ce in na dawo za mu yi mgana saboda zumuɗi ana mangariba na tarkata su muka hau adai daita muka koma gida shi ko Yallaɓai sai wajen goma ya dawo min gida ina ta jiran shi in ji labari. Na yi ta naniƙe masa ina tambayansa ya ƙi faɗa min sai ja min rai ya ke yi daga ya ce bari ya yi wanka sai ya ce bari ya yi kaza har na gaji na ƙyale shi da muka zo kwanciya ma sai da ya ja muka yi ɓarnan ruwa bayan mun gama kuma ya ce ya na jin barci sai da safe da dai na fahimci da gangan ya ke wasa da hankalima sai na ƙyale shi.
Da asuban fari wayar Ya Aina ta tashe ni daga barcin da na koma sai ga labarin da Yallaɓai ke min ƙwalele ta na faɗa min domin ina ɗaga wayar ta ko gaisawa ba mu yi ba ta ce.
"Ke Sadiya jiya da daddare ba sai ga Baban su Jidda tare da baƙi ba."
"Baƙi? Wasu baƙin?
Ba maganarta ne ya ba ni mamaki ba sai illa baƙin da ta ce ya zo da su.
"E mana ko ba ki sani ba ne?
"Ban san ko abin da na sani kike son ki sanar da ni ba Ya Aina."
"To ke wani labari kika sani?
Kai tsaye na ce" To ni dai na san Autan su Nene Kawu Abba ya zo gidana ya ga Marwa ya ce ya na so. Kuma Yallaɓai ya ce min sun haɗu jiya sun tattauna kuma shi Yallaɓai ya karɓi lambar Baban Marwa a wajena ban san kuma da mganar wasu baƙi ba."
Cikin sauri ta ce" To ai mganar ne. Sun zo su uku da Baban jidda da wani sai shi mai son Marwa ɗin."
"Ma sha Allah? Da me suka zo?
"Sadiya wai neman izini suka zo suna so a ba su dama ya fara mgana da Marwa in sun dai daita ba su son ya ɗau lokaci."
"Alhamdulillah. Ya Aina Allah ya sa an ba shi dama."
"Babanta ya bashi dama Sadiya tun da dai daga bangaren ki da mijinki ne. Ba ki ga yadda ya ke jin daɗi yadda suka mutumtata shi ba ya ce tabbas ya ƙara ganin darajansu na yadda kafin su fara magana da Marwa sai da suka zo neman izini."
Ina murmushi na ce" Ya Aina ai Kawu Abba mutum ne. Tare suka tashi da Yallaɓai fa tun suna ƙanana da wannan wanda suka zo tare Yayan Gimbiya ne Amaryan Yallaɓai. Kuma ina mai baki tabbacin ki bi lamarin da addu' a in dai Marwa ta auri kawu ta gama yin miji."
Ya Aina