Showing 30001 words to 33000 words out of 141487 words

Chapter 11 - TURKEN GIDA BOOK 2 COMPLETET BY JANAFTY.txt

Janafty   

18 Dec 2025

898

aikin da zai yi, ya fita ya barni a falo yau har haraba na raka shi, ni kaina na yi mamakin ji na sakayau kamar ba ni ba. 
Bayan fitansa ba daɗewa aka kawo naman rago kilo biyu duk da ma muna da sauran naman salla a cikin kakide, sannan ga dambun nama bai ƙare ba Musbahu ne ya kawo min tare da kayan miya da kayan lambu. Daga Yallaɓai ne, kawai sai na samu kaina da tambayan shi ina Yallaɓan ya ke.?

"Ya na can office akwai mutanen da ya ke ganawa da su."

Har ya bar gidan ina zaune ina tunanin dalilina na tambaya. Me na ke tsoro? Kar ya je wajen Gimbiya? Wata zuciyar ta ce kar ki manta ya aure ta wata rana tare za su kwana a ɗaki ɗaya. Sai na ji hankalina ya tashi amma sai na fara kiran sunan Allah har na samu natsuwa. A raina na saka jarumta sannan zan ɗauki shawaran Nene zan riƙe Allah domim shi kaɗai ne za ba ni ƙwarin gwiwan fuskantar wannan yaƙin da ke gabana.

Wanka na fara yi sannan na shiga kitchen na soya naman nan gabaɗaya. Kayan miyan ma na yi blanding ɗin su, na tafasa na ɗiba na yi miya sauran na saka a fridge kafin wani lokaci na gama aikina na gyara kitchen ɗin wajen ƙarfe uku na rana ina falon yara lokacin mun gama waya da Balaraba kenan na ce Saude ta yi zamanta kawai sai gobe  sai ga kiran Hauwa a waya wai gobe ta na nan zuwa na ce Allah ya kawo ta a raina na kuduri niyyar sai na yi ma Hauwa tsinin baki domin ina jin haushin su ita da Munnira.

Ina gida har yamma yara sun dawo daga makaranta har sun ci abinci. Mun yi waya da Yallaɓai ya na tambaya akwai kayan marmari? Na ce sun ƙare sai ya ce gashi nan zuwa zai taho dashi. To bayan mun yi mangariba muna azkar da yara ya sake kirana.

"Sadiya ta."

"Yallaɓai."

Na amsa masa a sanyaye.

"Ina Gwammaja yanzu haka bayan na tashi aiki sai na biyo zan duba Daughter daman ba ta jin daɗi da safen ma sai da Nene ta ce in na fito na zo na duba ta. To ina sauri ban biyo ba sai yanzu na kuma zo na iske ta ta na ta amai zan kaita asibiti a duba ta yanzu."

Cikin danne abin da ke taso min na ce" Subhanallah. Ku je mana a duba ta ka yi mata sannu Allah ya ba ta lafiya."
"Amin Sadiyata. Take care sai na dawo "
Da haka muka yi sallama ban bari na saka tunanin komai ba muka cigaba da azkar din mu bayan mun gama ni na ɗora da karatun Qur'ani Allah ya cire min lamarin a cikin zuciyata. Kafin Yallaɓai ya dawo na sake wanka na yi masa kwalliya sai tara da rabi ya shigo gidan muna tare da su Jidda a falo muna kallon Cartoon ya shigo gidan suka tashi suna masa oyoyo ya tarbe su ni ma na miƙe ina masa sannu da zuwa ya amsa ya na kallona duk da bai furtamin ba amma na ga jin daɗi a fuakarsa da muryansa da ya ganni cikin kwalliyata kamar ko yaushe.

Ledan hannunshi na karɓa zuwa kitchen na cire kayan marmari a leda na saka a frezer sauram kuma na wanke na yayyaka mana a Filet na kawo falon ya na zaune tare da su ya na yi musu hira.

"Ya mai jikin?

Na faɗa ina zaman gefen jidda, min jera da shi ya na gefen Jidda Baby kuma na kan jikin shi.

"Ta ji sauƙi. Ulcer an saka mata drip da mganguna."

"Ash. An ba ta gado ne?

Na faɗa ina kallonshi sai ya kalleni kafin ya ce" No mun dawo gida. Sun ce dai ta riƙa cin abinci ta shan mganuna nan da sati ɗaya sai ta koma ta ga likita."

"Allah ya ba ta lafiya."
Ya amsa da Amin Baby sarkin mgana ta fara tambatyan waye ba lafiya?
Shi kuma sai ya ce musu Anty Gimbiya ce da ya ke yaran suna son ta daga Jidda har Baby suka fara ma sa magiyan gobe ya kai su suke su duba ta sai ya fara cewa akwai makaranta su bari weekend su sai suje.
Ina gefe na ce" Ya yi nisa. Ko da daddare gobe haka Yallaɓai?

Na faɗa ina kallon shi, sai na ga ya kalleni kafin ya ce" To shike nan sai mu je ɗin."
Suna jin haka suka fara murna. Nan muka bar su da shan su kankana ni da shi muka shiga ciki sai da ya yi wanka sannan na haɗa masa tea na kawo masa abinci tare muka ci tunda ni daman ban ci ba tuni su Jidda suna ɗaki sun kwanta muna ci muna ɗan taɓa hira ya ce min jibi Jumma'a zai shiga Kaduna domin ya duba aikin nan na ce Allah ya nuna mana.
Bayan mun gama ya ta ya ni muka kwashe komai zuwa kitchen, muka kakkashe hasken ɗakunan da falo sannan muka koma ɗaki muka yi shirin kwanciya yau dai ban hana shi kaina ba na saki jiki mun farantama juna, muna riƙe da juna cikin yanayi na ma'aurata sai wayarsa ta yi ƙara alamun shigar saƙo sai bayan mun natsa har ma mun yi wankan tsarki ya duba ashe cikon kuɗin aikin da ya yi na gina tiolets da wasu azuzuwaa makaranttun gwammatin kano na tuntuni n a ka turo masa.

Sai ya kamani ya rumgumeni ya na faɗa mini. Sai na riƙe shi nima ina mai ta ya sa farinciki. A zahirin gaskiya kuɗin nan ba su iya zuwa lokacin da ya dace ba. a can baya ne na yi zumuɗin zuwansu amma yanzu sai na ji ba na musu zumuɗi ko na so ko ban so wannan kuɗin da su za a yi shirye shiryen tariyan Gimbiya. Ana nufin kishiyar da za a kawo min wataƙila a nan wataƙila a wani gidan na dabam.



*Janafty*
*TKG*

06.

FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622

Yallaɓai fa miliyoyi sun dira a cikin account ɗin sa na banki ba zama. Tun safe ya fita ya ma riga yara fita saboda sauri, bayan kuma tun asuban fari ya fara waye waye da mutane bakinsa ya kasa shuru. Ni fa tun a farkon auran mu tun ina mamakin halin Yallaɓai har ya zame min jiki, in ya yi wani abin na daina ganin sa a sabo a wajena.
Tun da na san shi, shi ne mutun ƙwara ɗayan da zan ce na sani mai bayyana ya samu kuɗi a duniya. Kowa sai ya sani daman kuma tun kafin kuɗi su zo zai ta yi ma jama'a alƙwari da cewa in an biya shi kuɗin aikin sa na kaza zai baka kaza, a farkon auranmu na ga lamarin na shi wani bambaraƙwai wai namiji da suna Hajara, tu ina yi masa mgana har na gaji na kama kaina domin na tabbatar da halin shi ne, ba zai iya dainawa ba.

  Ni dai kafin ya fita sai da na yi masa maganar kar ya je ya yi ta facaka da kudaɗen nan ya rage sauran basukan mutane da suke kansa. Sai ya ce min zai rage daman na Kawu Abba ne mai yawa zai biya shi sai na Tariq da ya karɓa a wannan aikin na kaduna amma shi ba zai biya shi sai an biya shi na kadunan. Sai yaran shi da zai cika ma kuɗin aikin da suke yi rabi ya ba su, wasu ma bai ba su komai ba saboda ba kudaɗe a hannun shi. Ya fita da cewa office zai je amma tunda ya na da kuɗi sai in da mansa kuma ya ƙare ya bar ni ni kaɗai a gida tun da su Jidda sun tafi makaranta suma.

Bayan fitan shi ba daɗewa ya kira wayata ya na faɗa min na rubuta list ɗin duk abin da muke buƙata a gida na kayan abinci da sauran kayan amfanin mu ni da yara, sai na amsa masa da to, bayan mun gama wayar na tashi na shiga Kitchen ina duba abin da babu. Sai da na gama gani sannan na koma ɗaki na rubuta a cikin wayata kayan amfanin mu kuma ni da yara sabulun wanka ne na su, sai nawa wanda na siya wajen Lame ya kawo gangara. Sai su man wanke kai da maclean sai izel da klin muna da komai su kaɗai ne suka yi ƙasa, sannan a raina na ce zan tuna masa da kuɗin makarantar yara domin wannan term ɗin ne ƙarshe, in suka yi hutu suka koma akwai biyan kuɗin makaranta. Test ma Jidda ta ce min suke yi sun kusa hutun kirisimet na ƙarshen shekara.
Allah ya sa ma ya yi dubara lokacin da zai biya a second term ya biya gabaɗaya na season ɗin.

Sanin Saude na makaranta sai in ta dawo ne in ta na da lokaci ma ta ke zuwa. A ranakun makaranta zuwanta ya koma sau huɗu ne kawai a sati. Alhamis da jumma'a sai weekend na san yau za ta zo amma sai wajen biyu na rana, kuma ga shi Hauwa ta ce min za ta zo sai ban kwanta ba na miƙe na yi aikin gidana da kaina ban bari wani tunani ya ziyarce ni ba, karatun Qur'ani na saka a wayata ina ta ji, kuma ina bi da bakina ko kafin goma na safe na gama komai gidana sai kamshin turaren wuta ya ke yi, haraban gidan ne na ga ya yi datti sai na bar shi da cewa in Saude ta zo sai ta share ta gyara wajen.  Wanka na yi na shirya cikin wani leshi na mai sauƙakƙan nauyi, ina falon yara ina hutawa wayata na hannuna ina danne danne, yanzu sai na yini na kwana ban buɗe data ba, ba na so na ga ma abin da zai ɓata min rai ko ya ɗaga min hankali shi ya sa na kama kaina.

Ina nan zaune, ba kallo na ke yi ba saboda sun ɗauke wuta yau tun safe ba su dawo da shi ba. Ina ta mamakin ma rashin dawo da shin da ba su yi ba, saboda in suka ɗauke in ta daɗe ba su dawo dashi ba awa ɗaya amma yau sama da awanni uku ba wutar. Karatun Qur'anin na cigaba ji a wayata ina kuma zaune na kishigiɗa a saman kujera a sannu sannu ina bin karatun, idanuwana a lumshe suke sai na ji karatun ya tsaya wayar ta fara vibration alamun ana kirana, a kasalance na ɗan tashi daga saman kujeran da na ke zaune, ina mai buɗe idanuwana da suka yi min nauyi, domin sai na ji kamar barci barci ma na ke ji, hannu na saka na jawo wayar ina duba mai kiran nawa saboda kafin na ɗauki wayar kiran ya katse.

"Yaya Aina ce."

Da sauri na bi bayan kiran. Bayan ta ɗauka mun gaisa ta na min tsiya da cewa"Uwargida ran gida. Ko kina barci ne?
Ina ɗan mirmishi kamar ta na ganina kafin na ce"Barci kuma Ya Aina? Na tashi tun safe."
Yara ta tambaya na ce suna makaranta, Yallaɓai kuma da za ta tambaye shi sai da ta yi dariya kafin ta ce" Ina Yallaɓai Ango? Dariya na saka mai sauti kafin na ce" Ya na nan lafiya. Sai dai ya ɗan fita tun safe."
Fatan dawowa lafiya ta yi masa sannan ta yi min mganar kan dalilin kiran na ta.

"Kan maganar bikin Yashe ne. Yau fa saura kwana takwas. Na fara haɗa gudummuwar ne ina kira ina ƙara tunasar da ku, kema ina jiran na ki, gwara mu haɗa da wuri mu aika musu dashi kafin tafiyar tamu."

Kai na gyaɗa mata kamar ta na kallona kafin na ce" Gaskiya ne. To kamar nawa nawa za mu ba da?
Ya Aina ta ce" Ban yanke ma mu mata ba. Mazan dai na yanke ma nasu, mu kawai kowacce ta kimanta abin da ta ga za ta iya ba da wa sai kawai kowa ta ba da nata."
Nan ma na ce hakan ya yi, mun rabu da cewa za ta ji saƙo tun da ina da acct lambarta sai ta ce min kar na tura a nata Atm ya yi expire sai dai na tura a na Marwa anan ta ke tara kuɗin, in ma sun gama haɗuwa ta na tunanin anan za mu yi siyayya wasu kaya duk da yadda suka ce a yi daga can haka ɗin za a yi.
Mun gama waya kuma sai ta bar ni da tunanin nawa ya kamata na ba da, acct balance ɗina na duba kuɗin da ke ciki duka duka 35k ne, shima sun taru ne da kuɗin asibitin da Yallaɓai ke ba ni, wannan zuwan da na yi ma ko na adaidaita bai ba ni ba, ni kuma ban yi masa magana ba, tun da na san ya na yi sai na saka tsarin haka a raina na cewa a ranar ƙila bashi da kuɗin ne.

Ga shi nima ina son zuwa bikin nan in na tura 30k gabaɗaya ni ba ni da kuɗin da zan riƙe a hannuna. Kuma a yanzu ba zan iya tambayan Yallaɓai kuɗi ba. Sai na ke ganin kamar komai ya tashi daga yadda na san shi zuwa wani abu na dabam. Na yi ta tunanin mafita ban samu ba sai kawai na ce zan tura 25k, ni sai na riƙe 10k a hannuna na tafiya in Yallaɓai ya ba ni kuɗin mai da sauran su na san zan samu wani abu a ciki ko da in mun je can zan iya ƙara ma mai bikin.
Amina na kira muka yi mganar sai ta ce Ya Aina ta kira ta itama jiya da daddare. Ta ce min 20k mijinta ya ba ta ita kuma ta na da 10k za ta ƙara zama 30k kenan ni kuma sai na ce hakan ya yi ta yi ƙoƙari.

"Yaya Sadiya ke hamsim za ki ba da ko? Matar Yallaɓai ce da kanta."

Ta faɗa cikin zolaya, nima sai na biye mata har kuma muka gama waya ban iya faɗa mata ga abin da zan ba da ba. Yanzu fa ba da ba ne, gani na ke yi kamar an shata mana wani dogon layi tsakanina da Yallaɓai a raina na ji ba zan iya tambayar shi kuɗi ba, ba kuma domin in ya na dashi ba zai ba ni ba. Zan iya  karesa a gaban ko waye, in dai Yallaɓai na da kuɗi nima ina da shi, zai ɗauka ya bani kuɗi kawai na hidimata bayan na hidiman gida zai ba ni sama da adadin da na ce, in kuma na ce masa ina da buƙata jikinsa na rawa zai ba ni sai dai in dan bai  da shi ne gabaɗaya. Na kuma san in na faɗa masa muna da biki a Yashe an yanke mana kuɗi wallahi zai ba ni kawai ni ɗin ce ba zan iya yi masa mganar ba.
Tun da yanzu ya zama ba nawa ni kaɗai ba. Na saka ma raina ya zama dole na miƙe na nemi sana'ar yi ko domin wata rana. Tunda in a baya ina tunanin daga ni sai shi sai ƴaƴanmu yanzu kiɗa ya sauya dole ma rawa ya sauya. Ya auro wata kuma in suka fara zama akwai yuyuwar su tara wasu zur'an to abubuwa da dama za su tashi daga yadda suke a baya su sauya wani muhalli yanzu.

Nan take ban tsaya ma wani cewa ko zuwa anjuma ba na tura kuɗin, nan ta ke na tura ta acct ɗin Marwa na kira Yaya Aina na faɗa mata na tura 25k ta yi ta godiya da saka albarka sai ta ke faɗa min Ma'u 100k ta turo yanzu itama ita 50k mijinta 50k, na san wacece Ya Aina ba da munafunci ta faɗa ba da dai Ya Murja ce sai na ce da gayya ne, addu'an Allah ya saka musu da alheri na yi, mun rabu da ita cewa zuwa gobe in kuɗin sun haɗu za ta je gida ta gaya ma Alhajimu sai a san yadda za a yi. A bakin ta ma na ke ji Rahila tun ranar talata za ta wuce in ji Ya Muntari a raina na ji kamar nima na shirya na bi tun daga ranar ban taɓa jin ina yin nesa da Yallaɓai ba irin yanzu, kawai ina son na je can wani wajen da zan manta da ƙarin auran sa ma'ana dai zuciyata ta samu kyakyawan natsuwa. Duk da ban tambayi izininsa ba na yanke shawaran zan shirya ina tunanin tare za mu tafi da Rahila.

Saboda ma jin haka ni da kaina na kira Rahilan a waya muka yi mgana. Ta ji daɗi da na ce mata ina ganin tare za mu wuce ranar talata ɗin. Bayan mun gama wayar da ita ina zaune ina tunanin wai ba mu da wasu ƴan'uwane daga nesa? Ko a wasu garuruwan? Ko dangin Mama ni dai na san duk suna kano ne, Alhajinmu kuma daga yan tumaki sai Yashe, ina zaune ina tunanin da a ce muna da dangi a can Lagos in na tafi sai an ganni. Sai Gimbiya ta tare Yallaɓai ya gama amarcinsa sannan zan dawo saboda ina jin kamar ba zan iya zama a gidan nan ina ji ina gani Yallaɓai na tafiya gidan wata ya na kwana ba. A cikin daren nan kishi zai iya saka ni na haɗiyi zuciya na mutu, ina zaunen nan ina faman tunane tunane Hauwa ta zo ta na ta buka get ban ji ba sai da ta kira wayana sannan na tashi na je na buɗe mata.

Ita kaɗai ta zo yara duk suna makaranta.  A falon yara muka zauna na kawo mata ruwa da lemu sai soyayyen nama da dambun naman da ya yi mini saura. Sauran cincin da cake su Jidda duk sun cinye tare da Yallaɓai ni gabaɗaya ma komai ya fita kaina a bakina ma ina jin kamar na rasa ɗanɗano.
Hira kawai muke yi da Hauwa yadda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login