Showing 39001 words to 42000 words out of 141487 words

Chapter 14 - TURKEN GIDA BOOK 2 COMPLETET BY JANAFTY.txt

Janafty   

18 Dec 2025

863

in wata za ta samu zuwa duka dai suka ce ba za su samu zuwa ba sai kawai a ka saka Zaitunan Yaya Abubakar a cikin masu tafiya.
A raina na ce sai dai mu haɗu a can domin can anjuma da na sake hawa na ga Ya Murja na min mgana ni ba zan je ba ne? Kafin na ba ta amsa ma Amina ta faɗa mata gobe za mu tafi ni da Rahila saboda mun yi waya da ita da safe na faɗa mata.

  Kawai sai Ya Murja ta yi tagging ɗina da cewa" Uwar gida yaushe ne tariyan Amaryan ta ki?
Kamar zan amsa ta, sai na fasa kowa ya kirani a waya amma ban da ita, shi ya sa na yi kamar ban gani ba, amma ga mamaƙina Ma'u ce da ta zo ta ba ta amsa da cewa" Ƙarshen watan ne fa Ya Murja."
Mamakinta ya ƙara kamani wato ita har ta sani kenan, ina gani Ya Murja na sake tambayan a ina amaryan za ta zauna? Ta ce ba ta sani ba tukunna amma dai haya a ka ce za a kama mata.

  Ni dai kawai sai kallo na kasa magana Amina ce ta shiga hiran ta su ta na faɗin"Ya Ma'u ki bari Uwargida ta amsa mana mana"
Sai ta tura emojin dariya kafin ta ce" Na wakilceta ne.'
Yaya Murja ke ce ma Amina wai ta san akwai wata yayar mijina da suke aure a gida ɗaya da Ma'u suna shiri sosai a wajenta ƙila ta ke samun labari. Amina ta ce ikon Allah! Daga nan ba ta ƙara magana ba. Ta bar su suna ta mganganun su kamar ma da gayya suke yi ban ce komai ba na kashe data kawai na ijiye wayar saboda in na ma zauna ina gani sai raina ya yi ɓaci a banza.

Kayana na shirya a cikin akwatina mai ɗan girma. Lame ta aiko min da mai da showel gel jiya. Kaya na diɓa sama da kala biyar domin sati zan yi a Yashe haka na yi niyya. Har wajen la'asar mai kitso ba ta zo ba sai da na ƙara kiranta sai ta ce min tana hanya. Ba na so na je da kaina a tsife domin na gaji da shi a haka gwara na kiteshi ga shi an fara sanyi ma kar ya karye min.
Zuwan mai kitso ya sa na ɗan saki da ya ke ƴar zamfara ce ta na da hira muna ta fira muna dariya har su Jidda suka dawo makaranta ban yi girki ba daman sai na ce in sun cire kaya Jidda ta sulala musu ko indomie su ci, mai kitso na ta mamakin girman Jidda ina dariya na ce.

"Kin dai daɗe ne ba ki ganta ba Maman Nana."

Ta na jinjina kai ta ce" Ko! Amma duk da haka Jidda ta ƙara tsawo masha Allah. Mun kusa kaiwa ga suruki ga Baby ma masha Allah itama ta na ta girma."
Ina ta dariya ban yi magana ba ina kallon Jiddan da ta cire unirform ta saka doguwar riga na atamfa sai nima na ga ta yi min girma, ba ta ma gama cika 14 ɗin ma sai watan gobe, sai dai nima na yarda ta ɗauko tsawon kafan babanta, Baby ce ke da jikin gaba gaɓan girma. Ni na ce Jidda ta dafa duka indomie ɗin tare da mu, Baby dai sai da tasha tea kafin a gama sai kuka ta ke yi wai ta na jin yunwa, sai da muka gama kitson sannan muka ci indomie Maman Nana ta ce ba za ta ci ba na ce sai dai na saka mata a cooler ta kai ma yara. Haka ko aka yi gabda mangariba ta tafi na ba ta kuɗin kitsonta da na adaidaita sai indomie ɗin da na saka mata a wata roba na ce ta kai ma su Nana daman haka na ke yi mata wani lokacin ko ma ta ci in za ta tafi in akwai na kan zuba mata na ce ta kai ma yara.

Da a niyyata yau ba zan yi girki ba, sai kuma daga baya na ga bai kamata ba. Ya fita bai karya ba yanzu kuma ya dawo ba abinci? Duk da wata zuciyar tawa mara kirkin ciki na faɗa mib sun je duba gida da amaryansa kika sani ko sun biya gidan cin abinci sun ci? Amma ban biye mata ba na yaƙe ta, na miƙe na faɗa kitchen bayan na yi sallar mangariba na bar su Jidda a falo suna duba littafan makaranta domin ta ga ya min next week monday za su fara jarabawa shi ne na ce maza su ɗauko littafan su mu yi karatu, mun fara kenan tunanin dafa wani abu ya shige ni sai na tashi na bar su, suna yi su kaɗai.

Ina shiga kitchen ɗin bayan tsayawa na tsawon mintina goma da nazari na ji kawai tuwo na ke son yi, to amma Yallaɓai bai cika son tuwo ba wani lokacin, na so na kira shi amma sai na fasa kar ya zo suna tare da Gimbiya sai na koma falon na ɗau wayata na tura mata saƙo.

"Na yi mana Tuwo yau?

Kamar ya na jira duka duka da turawan ko minti biyu ba a yi ba sai ga amarsa shi.

"Da kin faranta mini zuciyata Madam."

Sai da na yi mirmishi da na karanta sakon. Ni na san ya na can cikin damuwa bai yi tunanin buɗe masa mganar da na yi ba ɗazu ya fita cikin sanyin jiki ya na tunanin ina can ina fushi da shi, ni ko bai san abin da na faɗa ni tuni ya wuce daga wajena ba, na dai fitar da abin da ke raina ne saboda ba na so ya ƙara maimaita abin da ya yi yau, sannan kuma ya daina min kame kame ni da shi duk mu san gaskiya.

Nan take na kunna gas na dora ruwan tuwo na deɓo shinkafar tuwo ina ɗan gyarawa, wanketa na yi na zuba na rufe sannan na dauko sauran man suyan salla da na saka kasusuwan da suke rage daman tuni tuni na ce miya zan yi da shi na yauƙi na ci tuwo da shi, to na duba kubewata ta kare sai kawai na ce ba ri na yi miyar zolagale, saboda dare ya yi sai na kunna wani gas ɗin na ɗora miya saboda ina so na gama a kan lokaci kafin Yallaɓai ya dawo.

Allah ya taimake ni bayan isha'i na gama tuwon, har na ɗaure a leda, kuma daman bai da yawa saboda ma ɗumamen safe ne, miyan ne a kan wuta ba ta karisa ba sai tashin kamshi take yi sannan na saka mata man shanu tunda akwai sauran shi, Jidda na bar ma sallahu in miyan ta ƙarisa ta kashe gas ɗin duk da na ɗan rage ni kuma na je na yi wanka na ɗauro alwala na yi sallar isha'i sannan na sauya kaya na saka wasu riga da wando pakistan Mimisco ce ta taɓa kawo min tsaraba da ta je England. Kitson 2steps a ka yi min sai na zubo shi ta baya, saboda hulan da na saka tsakiyar kai ana gani shara shara ce ta na dai da tuntun love daga tsakiya, hulan mai adon pick irin adon jikin pakistan ɗin da ke jikina har da su jan baki na saka na sha gazal da mascara.

Har taran dare Yallaɓai bai dawo ba, Baby ta yi barci ni da jidda kawai muka ci tuwon muna ta santi faɗi ta ke yi" Umma tuwon nan ya yi daɗi."
Ina mirmishi na ce" Na gode ɗiyar Umma."
Kallonta na ke yi ina mirmishi ni kaɗai bayan mun gama ci ita ta kwashe komai ta kai kitchen, nima bin bayanta na yi na wanko hannuna sai da muka dawo falo ta na tattara littafanta na kira sunan ta.

"Jidda."

"Na'am Umma."

Ta amsa min ta na mai mayar da hankalinta a kaina.

"Gobe za mu tafi biki Yashe ni da Ummar ku Rahila."

Ina kallona sai na ga ta buɗe baki amma ba ta yi magana ba.

"Kuma sati ɗaya zan yi in sha Allahu."

Ido ta zaro kafin ta ce" Sati ɗaya Umma? Ina dariya na ce" E ko ya yi kaɗan ne?
Sai ta dawo gefena ta zauna ta na faɗin" Umma zan biki don Allah ban taɓa zuwa ba."
"A'a makaranta Jidda. Ki bari dai in an yi hutu in da mai zuwa sai na haɗa ku ku je tare."
Ta na wani kwabe fuska ta ce" Umma to da wa za mu zauna a gida?
"Da wa kuwa? Ga Abban ku.'
Sai ta yi shuru ba ta yi magana ba amma ta ɓata rai, a raina na ce tafiya fa ba fashi  ko ya riƙa dawowa gida da wuri ko ya kwashe ku zuwa Gwammaja wannan duk ya rage na shi.

Ina zaune Jidda ta kwashe duka littafab makarantar su ta kai ɗakin su, sannan ta zo ta ta da Baby suka shige ɗaki na bi su da cewa su yi fitsari kafin su kwanta kar kuma su manta addu'an barci shigan su ba daɗewa sai ga Yallaɓai ya shigo gidan, ya siyo min kwaakwa mai yawa saboda ya san ina so, akwai halin Yallaɓai da na ke matuƙar so shi ne ba ya shigowa gida hannu rabbana ko ba shi da kuɗi sai ya san abin da ya tsaya a siya a hanya ko saboda yara in ba su yi barci ba su ta so suna masa oyoyo sai ya ji nauyin in bai taho musu da wani abu ba, ni kaina in dai ya san abu ina so to ko a ina ya gan shi sai ya siyomin ya taho min dashi.

Bai ma tsaya wanka ba ya  ce na zuba masa tuwon yana gaya min tun safe kankana ce kawai a cikinsa muna kan dining zaune lokacin ina zuba masa tuwon na ce"Kai. To me ya sa ba ka tsaya a gida ka karya ba.?
Na faɗa ina tura masa filet ɗin gabansa, sai da ya saka cokali ya fara kai lomar farko ya haɗiye sannan ya kalleni ya na faɗin" Saboda kina jin haushina."

Waro ido na yi kafin na ce" Ni? Sai ya gyaɗa min kai lokacin akwai tuwo a bakinsa sai da ya haɗiye sannan ya ce" E. Haka kika ce min da safe ko kin manta ne?
Ya faɗa ya na mai kallona sai kawai na ce Uhm! Daga nan ban ƙara mgana ba shima sai da ya ci ya koshi ya haɗa da ruwa sannan ya yi hamdala, ni daman tun farko na ce masa na ƙoshi mun ci tare da Jidda.

"Girki ya yi daɗi. Allah ya yi miki albarka amma a bi ni bashi zan biya tuƙwaici."

CMirmishi kawai na yi ban yi mgana ba, hannun shi kawai na ji a wajen wuyana ya na jan jelan gashina lokaci ɗaya ya na faɗin" Kitso a ka yi ba a gaya min ba? Kai tsaye na ce" Kitson tafiya ne"
"Tafiya kuma?
"E. Ka manta za mu je can Yashe biki."

Sai ya kaɗa kai kafin ya ce" Na sha'afa. Tafiyar ba sai jumma'a ba ne?
Ina kallon shi na ce" Gobe ne."
"Gobe fa?
Ya maimaita cikin mamaki ni kuma sai na ƙara gyaɗa masa kai, bai ce komai ba kamar dai ya na mamaki ne ni kuma sai na shanye masa mamakin na miƙe ina tattara kwanukan da ya ɓata na ɗauka zuwa kitchen, lokacin da na dawo ba shi a falon ya shige ciki, ni kuma bayan na gama abin da na ke yi sai na kashe hasken falon na rufe ɗakin su Jidda na leƙa na duba su, bargo na gyara ma Jidda a kafafunta da ya janye Baby kuma kai ba ɗankwali sai da na binciko mata hula mai igiya na saka mata tana ta ture min hannu a cikin barci bayan na gama na rage musu hasken ɗakin na jawo musu kofa bayan na tofa musu addu'an barci.

Har falon yara da kitchen sai da na rage hasken wuta na kashe komai sannan na wuce bedroom na iske Yallaɓai har ya yi wanka ya na saka kayan barci sai da na shigo na tuna da akwatina da na bari a kan gado sai na saka hannu na dago shi na sauke shi a gefe.

"Kwana nawa za ki yi ne?

Na ji Yallaɓai na tambaya, ban juyo na kalle shi ba na ce" Sati ɗaya in sha Allahu."
Na kalle shi, ya na goge kansa da ƙaramin towel ne a lokacin amma sai da ya tsaya kawai ya na kallona ni ko na sha kuni na ƙarisa gaban wardrop na buɗe ina neman kayan barcin da zan saka.

"To yara fa?

"Su zauna anan ko Gwammaja."

  Na faɗa ina mai tube rigar jikina bai ce komai ba, nima ban neme wata mgana ba har muka gama shirin barci mu ka kwanta gabaɗaya. Ina jin sa ya na ta juye juye ya na so ya yi magana amma ya kasa, ni ko da gangan na mulmula na haye jikinsa na sagalo hannayena ta wuyansa na yi lamo har na yi barci ina jin bugawar zuciyarsa sannan hannayensa da ya riƙe da su duk a sanyaye, ni dai ban san lokacin da barci ya kwashe shi ba, ni dai sai asuba na tashi saboda zan yi tafiya kuma har ga Allah ya ba ni tausayi shi ya sa ya na dawowa salla asuba na rumgumeshi ina faɗin" Mu yi ɓarnan ruwa ne Yallaɓai na? Ko na bankwana ba za ka nema ba?

Kamar na yi masa sosa a in da ya ke masa ƙwaiƙayi tun da ya dafe ni sai da na gaya ma aya zaƙin ta kwanakinsa ya fanshe, sai bakwai fa muka yi wanka sannan na fita wajen yara, na sha dai sambatun Sadiyata ki yi hakuri ki yafe min wallahi ina son ki, da dai sauran su, har su Jidda suka tafi makaranta ban faɗa ma Baby zan yi tafiya ba saboda ba na son ta yi min rigima mun yi yar daɗi da Yallaɓai bayan tafiyan su Jidda ma ruwa muka koma shi dai kawai ya na faɗa min ya yi matuƙar kewata, ni kaina na yi kewarsa kuma na yi masa rawan jiki kamar yadda ya yi min.
  Shi da kanshi ya ce yara Gwammaja za su koma har na dawo saboda gobe ma Kaduna zai tafi bai san kuma lokacin da zai dawo ba shi ya sa na shirya musu kayansu a cikin ƙaramar akwatin su, ni ban nuna masa komai a fuska ba amma a raina na san Gimbiya za ta yi rawan jiki da su tun a baya ma ta yi balle yanzu mai dalili.

Ƙarfe goma muka fito daga gida na rufe gidan da key, Yallaɓai daman na da makullin shi, muna hanya zai kai ni Ɗorayi Rahila na can na jirana daga nan zai je Gwammaja ya kai kayan su Jidda daga nan na ya wuce Office, sai da muka je ƙofar gidanmu sannan ya turamin 20k na mota ya ce in na dawo za mu yi mgana. Tare muka shiga gidan dashi ya na riƙe da akwatina suka gaisa da Gwaggo da Alhajinmu.
Gwaggo dai sai ta yi masa fatan alheri. Alhajinmu kuma ya ce shi dai bai ji daɗi ba da ba a gayyace shi wajen ɗaurin auran ba duk kunya ta kama Yallaɓai ina gani duk ya kasa natsuwa. Ni ko a raina na ce Alhajinmu da kalan dangi.
Bai wani daɗe ba muka yi sallama ya wuce daman mun samu Rahila a gidan Ya Aina muke jira ta zo ta kawo mana kaya sai Ya Muntari da ya je karɓo ɗinkuna.

Mu ne ba mu tafi ba sai azahar motar mu ta tashi, ta yantumaki muka hau daga can ne in mun sauka za mu hau na Yashe, Rahila ce ke da goyo ni dai daga ni sai kayana ina zan iya, ba mu muka isa Yashe ba sai biyar na yamma ko a yan tumaki mun daɗe ba mu samu mota ba sannan wacce muka hau daga kano ta samu matsala a hanya. Ni fa sai yau na ƙara yarda da cewa tafiya yankin azaba ce mun gaji ga kishi ga yunwa, yarinyar Rahila na ta rigima na ce kya yi yarinya mu kan mu iyayenki mun jiggata.

Mun ga tarba a Yashe daman ahalin Alhajinmu Ahali ne masu karamci da son zumumci a ɗakin uwar Amarya muka sauka wato Marliya abokiyar zaman Mahaifiyarsu Muntari Jummai, gida ya sha fenti an gyara shi tsab yadda ƴan'uwa suka zagayemu ana ta hira ne ya sa na ji na manta da damuwata kamar na zo wata sabuwar duniya. Wayata na jaka sai da bayan isha'i na duba na ga Yallaɓai ya kikkirani ban gani ba sai daga baya na kira shi, ya ce min lokacin ya na Gwammaja ne zan yi mgana da Baby ta na ta rigima kuma shi yanzu ya dawo gida amma zai saka Gimbiya ta kirani sai na yi magana da ita. Kai tsaye na ce.

  "Ƙyaleta kawai za ta ba ri ne."

Domin ba na son magana da Gimbiyar ne gabaɗaya. Mun ɗan taba hira tunda daman da muka sauka na tura masa saƙo, tun da muna hanya ya na ta kirana, Yallaɓai fa ya na da kulawa matsalan kishiyan da ya yi min ne ya sa duk na daina ganin kirkin shi, a daran nan ba abin da ba'a kawo mana ba tuwo ni dai na ci miyar kuɓewa, na kuma sha fura har wajen sha ɗayan dare muna ta hira da su Baba Aminu haƙika ko ba su nuna ba sun yi farinciki da zuwan mu tun ballatana ma da muka ce musu har Gwaggo za ta taho su Alhajinmu kuma sai ranar ɗaurin aure.

"Ma sha Allah. Gidan Yaya Sule gabaɗaya za su yi mana baƙunta kenan."

In ji Baba Sani cikin murna da fara'a. Ni dai ina kwance a kan kafitar da aka sauke mu, Rahila ita na kan gado domin ta ce ba za ta kwana da ni ba kar na shure mata da ƴa da kafafuwata.
Sai na buɗe baki ina kallonta ita kuma ta na dariya kai na jinjina kafin na ce" Rahila ki sani zan rama ne."
Ta na dariya ta ce sai dai na rame, na daɗe ban yi barci ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login