Showing 27001 words to 30000 words out of 141487 words
a lokacin cikin maimuna ƙarami ne a jikina. Maman farko da kike gani bashi ita a ka yi abokin mahaifinsa ne ya bashi ɗiyarsa. Da maganar da auren tsakani wattani huɗu ne, amma ya kasa faɗamin saboda ya na tsoron tashin hankalina gashi ina da ciki kar wani abu ya samu cikin jikina kar na ɗaga hankalina wani abu ya same ni ya sa bai iya faɗamin da kansa ba sai amininsa marigayi Tafidan Rano ne ya zo ya same ni ya sanar da ni a lokacin sai da ya kalleni kafin ya ce" Hauwa'u ki godema Allah kin yi dacen samun nagartatten mijin da ya ke gudun ɓacin ranki da tashin hankali. Yususa ya ƙi sanar da ke labarin matar da aka bashi ne saboda ba ya so ya tashi hankalinki wani abu ya same ki, ya na jin kunyar ki matuƙa duk da ba haramci zai yi ba, a lokacin ya ce min Hauwa ba duka maza ne irin Yunusa ba, ba duka maza ke iya jin kunyar matansu kamar yadda Yunusa ke jin kunyarki ba ya sake sanar da ni cewa ba duka maza ke tsoron tashin hankalin matansu ba, saboda haka ki daure ki kuma yi haƙuri ki ba ma mijikin goyon baya kar ki ɗaga masa hankali, ki yi masa alfarman guje ma tashin hankalinsa kwatanƙwacin yadda ya guje ma na ki."
Sadiya tun daga waɗanan kalaman da ya yi mini har ya bar duniya da gangan ban taɓa ɗaga masa hankali ba, in ma na ga hankalin shi ya ɗaga ni ce zan zama sillar kwantar masa da hankali, har ya yi duka aure aurensa ban taɓa ɗaga masa murya ba, na yi hakuri na danne saboda wannan nasabar da Ubangiji ya yi min a zuciyar mijina ba na so na bashi kunya. Na ci riban hakurina na zauna lafiya da shi da matansa tun yana rage ni ce giwarsa a cikin gida da waje har kuma ya koma ga Allah hakan bai sauya matsayina a wajensa ba sai ma ya ƙara hauhawa ninƙi ba ñinƙin, faruwan wannan lamarin ya sa kawai in na kalli Tafida sai na ga kamar na ga makwafin mahaifinsa ne a tare da shi, Sadiya ba wai ina faɗa miki wannan ne saboda tausan baki ba. A'a ina faɗa miki ke ma Allah ya yi miki wannan nasibin. Ba kowacce mace ba ce za ta samu miji na jin nauyinta ba, ba kuma kowace mace ba ce ke samun darajawa da mutumtawa a wajen mijin auranta ba. Ba kuma kowacce mace ke iya samun namijin da ke gudun tashin hankalinta da damuwarta ba. Ke Allah ya baki wannan nasibi na kawo miki wanman labarin ne saboda na ankar da ke wasu abubuwa guda biyu zuwa uku."
Ta ƙarishe faɗa ta na kallona. Na kuma natsu na ba da duka hankalina a kanta ina sauraranta.
"Sadiya."
Na amsa da "Na'am Nene."
Sai kawai ta yi mirmishi kafin ta ce" Kin ga duk sanyin halin Hauwa na sha yin shari'a tsakaninta da muttaƙa."
Ido na zaro ina kallon Nene sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce" Ba tonon asiri ba ne Sadiya Nasabar da Ubangiji ya yi miki na ke son ƙara tunasar da ke. Sadiya tun auran ku da Tafida bai taɓa kawo min ƙaran ki ko da rana ɗaya ba. Bai taɓa zama ya kushe ki ba sai dai ya yabeki, ke ma haka ba ki taɓa kawo min ƙaran Tafida ba,duk da na san kuna samun matsala domin babu auran da bashi da matsala sai dai ku binne shi ku kaɗai ba tare da sanin kowa ba. Sadiya wannan ma wata Nasaba ce da Ubangiji ya yi miki, kuma a cikin idanuwana ina karrama wannan ƙimar ta ki."
Sai na ji kaina ya yi girma cikin alfahari Nene ba ta bani damar mgana ba ta cigaba da faɗin" To ba na so saboda wata ta zo ki sauya Sadiya. Kin zama turken gidan Tafida duk matar da ta zo daga bayanki sai dai ta ɗora igiyanta a kan wannan turken da kika riga kika kafa shi Sadiya. Kar ki sake da wannan matsayin da Allah ya ba ki na uwargida kan gida, kar ki yi sake da shi ya tashi a banza. Akwai zafi amma ki daure ki gani ƙi ƙi gani, ki ji kuma ki ƙi ji, a zo a gaya miki ki toshe kunnen ki in kika yi haka za ki zauna lafiya, ki ba ma mijinki dama damar da ya ke so daga wajen ki, ki yi ta addu'an zaman lafiya da salama Sadiya wallahi tallahi ba Saudatu ba ko Tafida bai isa wata rana ko halin su na maza ya motsa masa ya tozartaki ba saboda kin tsare mutumcin kan ki, na san Saudatu ke ma na san ki Sadiya in kuka yi hakuri za ku ba da shaidar kyakyawan zurua anan gaba. Ina roƙon ki da ki riƙe wannan nasabobin da na sanar da ke Ubangiji ya yi miki, ko an yi miki wani abu in kika tuna su sai ki danne zuciyarki ki yi haƙuri in kika yi haka tabbas wata rana sai kin ci riba in sha Allahu."
Kamar hadda haka na haddace kalaman Nene a cikin kaina kuma cikin ikon Allah da kalamanta sai na ji zafin da ke cikin zuciyata ya na raguwa. Ina jin haushin ta da na fara ji ita da Yallaɓai ya na raguwa. Duk da an ce tsakanin miji da mata sai Allah gaskiya ne zan kalli Nasabar da na ke da shi a wajen Yallaɓai na lulluɓe duka sharrinsa a gareni kamar yadda shima ya ke kallon alherina ya lulluɓe sharrina ba kuma wai domin ba ni da shi ba, kowani ɗan adam ya na da na shi alherin kuma ya na da na shi sharrin.
Sai kawai na kalli Nene ina murmishi kuma tabbas murmishi daga ƙasan zuciyata ya fito ba a iya saman leɓena ba ne.
"Na gode Nene. Kuma na yi miki alkwarin ba za ki ji saɓanin tunanin da kike da shi a kaina ba in sha Allahu."
Sai ta jinjina kai kafin ta ce" Amin. In sha Allahu na gode nima da samu abin da nima na yi tsammani daga wajen ki. Na gode Allah ya yi muku albarka Allah kuma ya zaunar da ku lafiya ya kuma kaɗe fintintunu."
Na amsa mata da Amin Amin sai ta ce za ta wuce amma kafin nan na yi ma Yallaɓai mgana kafin ta wuce, ni na tashi na leƙa falon da suke zaune shi da Musbahu na kira shi muka dawo tare wannan karon kasan cafet muka zauna ni da shi gabaɗaya ta kallemu kafin ta ce.
" Na ƙara tunasar da Sadiya abin daman ta riga ta sani na auranka da Saudatu. Tafida sauran aikin na ka ne, ka zauna da matarka ku yi mgana ku fahimci juna ku tattauna rayuwarku tare. Dukkanku ina fatan tsamanin abin da na ke tsammani daga gare ku. Allah ya ƙara muku zaman lafiya da fahimtar juna. Dukkanku da ku da yayanku Allah ya yi muku albarka gabaɗaya."
Muka yi ta amsa mata da Amin sannan ta yunƙura ta miƙe ta na faɗin" In ina da rai wata rana ina fatan alheri ya sake dawo dani gidan ku."
Muka ƙara amsa mata da Amin. Yallaɓai ya shiga ƙwalama Musbahu kira ni kuma na je na kwaso mata takalmanta na jera mata ta zo ta saka ta na faɗin" Allah ya shi albarka. Allah ya ba ku zaman lafiya."
Ni na buɗe mata kofa muka fita har haraba sannan sai ga Yallaɓai da Musbahu, sun fito na buɗe mata gaban mota ta shiga sannan na rufe ina ɗaga mata hannu Yallaɓai kuma ya tafi buɗe musu get har Musbahu ya fita da mota na ga ya tsaya Nene na mgana da Yallaɓai ta window na ga ya na gyaɗa mata kai sannan suka wuce shi kuma ya rufe get ɗin ina tsaye na harɗe hannu a kirji ina kallonsa sai yanzu da na ƙare masa kallo na fahimci ba ni kaɗai na yi raman tsaye ba Yallaɓai ma duk ya rame sai karan hanci kamar bashi ba.
Ban san ya ƙariso gabana ba sai da na ji yana shafa kumatuna sannan na fahimci ya ƙariso kusa da ni.
"Ya dai?
Ya faɗa ya na kallona sai kawai na sauke ajiyar zuciya.
"Bakomai."
Na sauke hannayena na juya zan tafi sai ya riƙo hannuna na dama, na juyo ina kallon shi.
Sai kawai ya wuce gaba ya na riƙe da hannun nawa, nima ban kwace ba sai na bi bayan shi. Bai direni ko'ina ba sai a kan kujeran mai zaman mutum ɗaya shi kuma sai ya durkusa a gabana ya na mai riƙe duka hannayena biyu a hannayensa ina kallon shi ya na kallona sai na ji rauni ya na kama ni. Zan iya fashe masa da kuka sai na yi saurin kauda kai, shi kuma sai ya kai yatasun hannuna ɗaya bayan ɗaya a bakinsa ya na sumbata. Kallon sa na ke yi da duka zuciyata ina jin ta na sake buɗewa a karo na biyu na yarda da kaddara wataƙila zantu kan Nene ne suka farkar da ni, wataƙila ba za ta ga laifina ba domin itama ai ta san kishi ta kuma ce ya na da zafi sai an daure.
"Sadiya ta."
Ya kira sunana cikin raunin murya sai na ɗaga ido na kalle shi kwarmin idanuwana suna mai cika kwallah.
"Sadiya wallahi ban ɓoye miki wannan auran da wata manufa ba, sai domin na kasa. Na Kasa jarumtar sanar da ke na ƙara aure. Ban san da wata kalma zan yi amfani da shi ba,ban kuma san ta yadda za ki karɓi mganar ba. Ba na so na faɗa miki wani abu da zai ɓata farincikin ki na wannan ranar. Ban san dalili ba sai na ji ina jin kunyarki. Ina jin kamar ban kyauta miki ba, har ma a cikin kwanakin nan Sadiya sai na riƙa ji a ƙasan zuciyata kamar na ci Amanarki ne, don Allah ki yi haƙuri ki yi haƙuri ki ya fe min don Allah SADIYA TA."
Ya ƙarishe faɗa ya na mai ɗora fuskarsa a saman tafukan hannayena ba kuka ya ke yi ba amma ina jin hucin numfashinsa lokaci ɗaya da bugawar zuciyarsa. Yau fa ban san me ya faru dani ba, kamar ruwa ruwa da an fara mgana sai na ji kamar na fi kowa rauni a duniya sai na fara kuka yanzu ma ɗin ma hawaye na ke yi, ina danne abin da ke taso min a cikin zuciya ta. Kai na ƙara yarda da cewa kishi cuta ne kishi masifa ne da bala'i domin a lokacin ji na ke yi ko na ce gani na ke yi yadda ya kwanta a jikina yana lallashina wata rana fa zai kwanta a jikin Gimbiya itama ya na lallashinta ko? Kawai sai na ji zuciyata na rufewa da kanta, ƙuncin da ya fara barina na ƙara ziyarta ta.
Bai san ina kuka ba sai da ya ji ɗigan hawayena a saman hannunshi na dama da ya sauke shi a saman cinyata. Da sauri ya ɗago ya na kallona ai sai ya ga ina hawaye wasu na koran wasu da rawan jiki ya miƙe zaune ya samu hannun kujeran ya zauna ya mai sanya yatsun hannunsa ya na share min hawaye amma kamar sun sani ya na share min wasu suna ƙara ɓulɓulowa.
"In kina kuka Sadiya ta. Ni me kike so na yi?
Haka ya faɗa ya na share min hawaye, kawai sai na fashe da kuka har da buɗe murya saboda ji na yi kamar in ban fittar da kukan ba zan iya mutuwa, tashi ya yi a ruɗe ya cicciɓeni shi ya koma ya zauna ya ɗora ni bisa jikinsa ya rumgume ya na ta share min hawaye, ya na kuma lallashina ni bai ma san ma lallashin na shi ke ƙara sakani kuka ba, ina shessheƙan kuka na ƙwaɓe hannun shi daga saman fuskata ya ƙara kawowa na ƙara kwaɓewa sai ya tsaya ya na leƙen fuskata da na ke boyeta a saman ƙirjinsa.
Sai kawai ya daga hannayensa sama ya na faɗin" To na bari tunda ba ki son lallashin."
Saki na ya yi sai gashi na zamiye kamar zan faɗi kasa kuma shi bai riƙe ni ba, gani zan sha ƙasa ya sa na ƙamƙame shi ina kallon shi ya na murmishi ya ce" Na kawo hannu ki ture ni?
Ya faɗa ya na kallona wani abi ya soki zuciyata a raina na ce ai in Gimbiya ce ba zai bari ta kai ƙasa ba. Kawai sai sai na ƙara saka masa kuka lokaci ɗaya na saka duka hannayena ina dukkansa a ƙirji bai hanani ba sai da na yi har na gaji sannan na koma na lafe a saman kirjinsa ina maida numfashi hannayena suna zagaye a wuyansa.
Sai da ya ga na yi laushi sannan ya saka hannuwansa ya tare ni sosai a saman jikinsa bai sake yi min mgana ba amma hannunsa guda ɗaya da ke bayana da shi ya ke ɗan bubbugamin bayan alamun lallashi, ina ta jan majina da jan numfashi cikin lokaci kuma sai kukan nawa ya ɗauke na koma ina ajiyar zuciya, har kuma na koma na yi lamo idanuwana suna lumshe amma ba barci na ke yi ba. Mun zauna a haka sama da awa ɗaya na san hannayensa da kafafunsa sun gama sandarewa da gangan na ƙi sauka a raina na ce gwara duk na gama more jikin ko ta zo sai dai ta samu saurana.
Kuma na samu natsuwa sosai fiye da tsammani na. Ba tare da ya nuna ya gaji ba na sake shi ya saka hannu zai riƙe ni na ce" Zan ta shi.'
Sai ya taimaka min na miƙe hijabin jikina duk ya bushe da ruwan hawaye shima miƙewa ya yi ina gani yana juya wuya da hannayena. Sai da na yi dariyan mugunta a raina, ban ce masa komai ba ya ga na fara ta ku zan bar falon sai ya biyo bayana ya na faɗin"
"Sadiya ba mu karya ba fa yau"
Sai a lokacin sai kuma ya na mganar na ji cikina na juyawa sai na juyo muna fuskantar juna kafin na ce" In soya ƙwai mu sha tea."?
Na tambaya cikin sarƙewa muryan. Ya ƙariso gabana ya kuma saka hannunshi ya riƙo hannayena lokaci ɗaya ya na faɗin" Za ki iya?
Ko na kama miki?
Kai kawai na gyaɗa masa alamin zan iya. Amma bai bar ni ba duk in da na bi yana bi na, hijabin jikina ma shi ya cire min tare muka soya ƙwanan ko na ce shi ya ma soya a falon yara muka karya dka da shima bai ja ni da hira ba amma zai kalleni da kulawa in ya ga na yi shuru na kasa kurɓan tea ɗin
"Are you ok?
Da kulawa ya ke tambayata amma ga ni na yi ni da ya yi ma kishiya sai na ga kamar tambayar ta renin wayau ne shi ya sa na bi na haɗe rai, duk da haka bai ƙyaleni ba bayan mun gama shi ya kwashe komai ya kai kitchen ya dawo ya iske ni dafe da kai ya na tambayata na ce kaina ne ya fara ciwo jikinsa na rawa ya je ya kawomin panadol ya ɓallo ya ba ni tare da ruwa na sha ya kuma riƙe ni har bedroom ɗin mu na kwanta na ya rufa ma ƙafafuna blanket.
"Ki kwanta ki ɗan huta ina ga kukan da kika yi ne ya sa ka miki ciwon kai."
Ya faɗa lokaci ɗaya ya duƙa ya sumbaci goshina. Ya juya zai fita sai na riƙe masa hannu sai ya juyo ya na faɗin" Me kike so uhm?
Sai na ce"Ba za ka fita ba ne?
"Ko zan fita sai zuwa anjuma."
Sai na gyaɗa kai sannan na sakar masa hannu
"Menene ko kina son wani abu ne?
Sai na girgiza masa kai alamun babu, sai ya ƙara dawowa ya duƙa ya sumbaci bakina, har zai tashi na riƙe masa wuyan rigarsa da hannuna guda ɗaya na ɗago kaina nima na sumbaci bakinsa sannan na sake shi sai kuma da sauri na juya masa baya har ina runtse ido kamar na yi abin kunya na san ya na ta kallona sannan na ji sautin mirmishinsa kafin na ji takunsa da fitarsa lokaci ɗaya ya na faɗin.
"Ina son ki Sadiya ta."
"Ina sonka Yallaɓai na."
Na faɗa a hankali tare da jin wasu tasowar wasu hawayen amma na danne. Ni fa sai yanzu da kishiya ta faɗo kaina na fahimci halin da waɗanda kishi ke saka su kashe miji ko su illata kishiya, a da in na ji labari in ta mamaki ina zaginsu a raina har ina ji ma a tunanina kawai saboda namiji sai mace ta haukace har da kisa. Wato daga ranar da na san Yallaɓai ya zama namu ba nawa ba na fara yi musu uzuri da gaske ba sa cikin hayyacinsu. Sheɗan na ƙawata zafin kishi, ka ji kamar ka yi hauka, ka koma kana ganin hotuna kala kala waɗanda in ba ka da imani tsab za su iya saka ka aikata abin da za ka dawo kana nadama. Ka koma kana ganin mutane dishi dishi tsabar kishi, zuciyata ta riƙa suya ta na kai ka in da in ka hasaso za ka ji kamar kowa ma na duniya ya mutu duk a huta. Ni kaina ba domin Allaah da addu'ar da na riƙa yi da dauriya da tuni an ji kanmu ni da Yallaɓai tsabar yadda na ke jin haushinsa sai sheɗan ya sarrafa tunanina na yi masa illa.
"Astagafurillah."
Na furta a fili saboda tunanin da ya giftamin a fili na furta" Ya Allah ka sassautamin wannan zafin kishi. Sannan ka tsare ni da aikata abin da zai jawo min nadama a rayuwata."
Na duba wayata ban gani ba sai na tuna na baro ta can falo sai na koma na kwanta na runtse ido ina karanto suratul Jumma'a tirya tiryan ina cikin yin karatun barci mai cike da natsuwa ya kwashe ni ban farka ba sai sha biyu da wani abu na rana.
****
Ko da na tashi Yallaɓai ya gama komai na aikin gida. Girki ne kawai bai yi ba shima domin zai je office ne ya ce akwai