Showing 60001 words to 63000 words out of 141487 words

Chapter 21 - TURKEN GIDA BOOK 2 COMPLETET BY JANAFTY.txt

Janafty   

18 Dec 2025

869

saba. Wani iska na furzar daga bakina da ya sa sai da suka kalleni gabaɗayan su.

"Lafiya?

Ya faɗa ya na kallona, wani irin kallon sama da ƙasa na yi masa kawai na ɗauke kaina shima kuma ya ga yanayin kallon shi ya sa bai ƙara nema na da wata mgana ba ya kama kan shi.

"Na san kun san dalilin da ya sa na tara ku anan ko?

Daga ni har ita shuru muka yi masa, ni ko a raina na ce to kasan mun sani uban miye kuma za ka taramu? Amma dai ban yi magana ba sai ma na maida kaina ƙasa kawai ina wasa da gefen Hijabina.

"Duk da kun sani amna tunatarwa tana daɗi. A matsayina na wanda kuke zaune domin shi akwai wasu mganganu da ya kamata na sake tunatar daku game da su."

Uhm! A cikin raina na ja sheɗata na fesar ta baki, saboda yau wai ni ce zaune da wata matar a matsayin matar Yallaɓai bayan ni. Na kasa gasgatawa amma yanzu gasgatawa ya zama dole tunda ba mafarki ba ne a zahirin gaskiya ya ke faruwa.

"Sadiya ga abokiyar zama nan na kawo miki. Aurena da Daugther Allah ne ya kaddaro shi, ke ma Daugther ga Yayanan na yi miki. Abun fatana na farko shine haɗin kan ku, ku sani wata ba ta fi wata a wajena ba dukkan ku mata ne da aure ya samar min da ku, ina fatan za ku haɗe kan ku ku zauna da juna lafiya domin samun zaman lafiya ta nima."

"In sha Allahu."

Ta faɗa cikin sanyin murya, ni ko ban ce komai ba sai daga baya da na ga ya yi shuru kenan ni ya je jira na ce wani abu.

"Allah ya ba mu zaman lafiya."

Suka amsa a tare da shi da Amin.

"Sadiya ki sani ban aure Daughter domin kin taɓa gaza min ba. Ki kaddara zaɓin Allah ne sannan ikonsa ne. Ke ma ki sani ba ta rage ni da komai ba kar ki yi tunanin akwai ta bangaren da ta gaza min ne ko ɗaya. Ke ma ki ɗauka a kaddaran Allah ne aurena da ni da ke, ki yi mata biyayya domin wakiliyata ce, in ta yi miki gyara ki gyara in ta kwaɓa miki ki kwaɓu, in ta ba ki umarni ki bi wanda bai saɓa ma shari'a ba. Ba zan lamunci ki yi mata cin zarafi ko rashin kunya ba ba na so na ji wata baraka a tsakanin ku, Ku ba yara ba ne ballatana na ce komai sai na faɗa muku dukkanmu nan mun san komai saboda haka ina roƙon ku ku haɗe kan ku mu zauna da juna lafiya har mu zama abin kwantance a wajen su don Allah."

"In sha Allahu."

Ta sake faɗa ni kuma a yangance na ce" Allah ya sa."

Sai kawai ya juyo kaina.

"Sadiya."

Sai na kalleshi sannan na amsa masa.

"Na'am."

"Na ɗora miki wani girma. Ki sani ki ce ni i don ba na nan ko da ma ina nan ke ce wakilyata. Kin fi ta sanina sosai fiye da ita. Ki riƙe girman ki, ni ma kuma ki riƙe min nawa girman. Don Allah ki yi zama da ita da zuciya ɗaya in wani saɓani ya haɗa ku ku zauna ku warware a tsakanin ku kar ki biye ma masu an ce ka ce domin ya na ɓata alaqa ba na fatan ku samu saɓanin da har ni sai na shiga ciki. Na fi son ku  yi zaman lafiya da har ni ba zan ji kan ku ba don Allah."

Ajiyar zuciya na sauke domin na ga ya ƙura min ido sannan na ce" Allah ya ba ni ikon ɗaukan girman."
Abin da kawai na ce kenan na yi shuru ita kuma sai ta ce" In sha Allahu ba za ka taɓa samun baraka daga bangarena ba"

"Ma sha Allah na ji daɗin haka. Allah ya yi muku albarka ya kuma zaunar damu lafiya gabaɗaya."

A cikina na amsa da Amin, ya ɗan sake yin shuru kafin ya ce" Sai maganar raba kwana. Wani tsari kuke ganin za ku yi?
Ya fada ya na kallon mu, ni ko sai na yi kamar ban ji ba.

"Duk yadda Maman Jidda ta tsara dai dai ne ni a wajena."

Ta faɗa ta na kallona sai nima na kalleta kafin na ce" Ah ke ma kina daman ki tsara ɗin."
Sai ta kalleshi kafin ta ce" To kai ka faɗa mana."
Kai tsaye ya ce" Ni ba ruwana wannan ai maganar ku ne."
Ya faɗa lokaci ɗaya ya na duba wayarsa.

"Ni dai sai na ga gwara ita ta faɗa "

Ta faɗa tana kallona, nima ko ina kallonta na ce" Ke ma kina damar ki faɗa duka ɗaya ne da ni da ke ɗin"
Ganin mun fatra ja in ja ya sa ya kalleni kafin ya ce" Sadiya ki faɗa mana ke ce Babba."
Zan yi magana ya dakatar da ni da cewa" Ke za ki tsara na ce ko?
Sai na ga ya wani haɗe rai ya na kallona a raina na ce daga baya kenan.

"To kamar kwana bibbiyu ya yi ko?

Na faɗa ina kallon su sai ya kalli Gimbiya kafin ya ce" Ya yi ko? Da sauri ta ce" Ya yi."
Sai ya juya ya na kallona kafin ya ce" Shikenan kwana biyu ya yi Madam."
Ko kallon shi ban yi ba domin ni yaudaran Yallabai wanne ne ban sani ba.

"In ba na gidan ɗaya to haƙƙi ne a kaina na je na duba yadda ta kwana. In kuma wani uzuri ya taso zan iya kiran waya. Kuma duk wacce ke son mgana da ni za ta iya kirana nima kuma a duk in da na ke zan iya kiran kowaccen ku, dukkaa ku mata na ne da Allah ya ba ni ku ta ƙarƙashin inuwar aure saboda haka ba bu shamaki a tsakaninku gabaɗaya ɗaya kuke a wajena."

"Allah ya zaunar da mu lafiya. Madam ɗina yi mana addu'a.".

Sai kawai na yi kamar ba da ni ya ke ba sai na kalli Gimbiya ganin ta na kallona shima sai na ga ya na kallona cikin basarwa na ce" Wai ni?
Mirmishi ya yi kafin ya ce" Wace ce na ke kira Madam in ba ke ba? Sai na jinjina kai a raina na ce ai ka ce Madam tun da ka gama da ni ka yo sabuwa na zama cus ba ni da amfani dole na koma Madam ko burgeni sunan bai yi ba domin tabbas na ke da shi wulakanci ne na ɗa Namiji shi ya na kiran ta da Daughrt ni kuma Madam kamar wata inyamura.

Ni na rufe zaman da addu'a sannan ya ce mu yi musabaha da juna, hakanan na mika mata hannu muka yi masabahan shi kuma ya duba lokaci ya ce goma har ta gota bari ya zo ya maida ta gida.
Shi da kanshi ya leƙa falo ya ce Baby ta yi barci sai Jidda kaɗai a gaba na ya ce ta je ta haɗo kayanta na kwana biyu ta zo su tafi kamar zan yi magana amma sai na ce ba yanzu ba ba tare da ya yi magana da ni ba ina ji ina gani ya ta sa Jidda tare da Amaryansa da ba zai bari ta kwana ita kaɗai ba ya je maida su gida. Mun yi sallama da Gimbiya kadahan kadahan Jidda kuma na ce ta tafi da azkar ɗin ta da Qur'ani kar ta manta da koyarwa da na yi mata ta ce min in sha Allahu.

Bayan tafiyarsu na kai Baby ɗaki na gyara mata kwanciya tare da yi mata addu'an barci. Sannan na rage mata hasken ɗakin na fito. Heater na kunna ya yi zafi sannan na yi wanka na saka kayan barci na duba agogo Yallaɓai ya fi mintina talatin da fita bai dawo ba, har na je kitchen na sha ruwan zafi daman da rana shinkafa na da fa Jallop. Ban damu da Yallaɓai ba tun da sai dare ya zo min gida ai ya cika cikinsa a can shi ya sa ko tunanin dafa wani abu ban yi ba. Bedroom na koma na kwanta amma na kasa barci tun ina mamakin Yallaɓai har na daina mamakinsa domin lamarinsa ya wuce tunanina da hasashena.

Ba ni na ji karan buɗe get ɗin Yallaɓai ba sai sha ɗaya da mintina na dare, saboda akwai waya a gefe sai da na duba ajiyar zuciya kawai na saki a ƙasan raina ina tausan kaina kar Yallaɓai ya shigo na yi masa dibar albarka, saboda ma kar a samu matsala sai na yi lamo cikin bargo kamar mai barci ina jin sa ya shigowarsa cikin gida da zagayen da ya yi ya rarrage hasken ɗaku nan sannan ya shigo cikin bedroom ɗin ya zube key ɗin motarsa da laptop ɗin a saman madubi ta gefen ido na ke kallon shi shammata ta ya yi ya kamani ina kallon shi sai ya yi min mirmishi kafin ya ce.

"Sorry kin ga na daɗe ko?

"Akwai ruwan Zafi in za ka yi wanka ne."

Na katse shi daga maganar saboda ba na son na ji. Karya ce da renin wayau ne kawai a cikin zencen sa.

"Ok."

Ya faɗa, ya na mai tuɓe kayan jikinsa ya rage daga shi sai gajerun wando sannan ya kalle ni kafin ya ce" Zan samu tea mai zafi Madam?
Ya faɗa ya na min wani kallo, da kamar na ce a can ɗin da ka tsaya ba ta ba ka ka sha ba ne? Amma dai na danne zuciyata  na mike na zo zan fita ya ja min kumatuna lokaci ɗaya ya na faɗin" Na gode Matata ta kaina."
Kai na fara tunanin ƙila dai Yallaɓai ya zauce ni domin ya na ta surutai marasa ma'ana.

Kitchen na shiga na kunna gas na ɗora masa ruwan tea. Ina da shayin goriban da na siya wajen Aisha Lame saboda Yallaɓai shi na zazzaga masa na dafa masa bayan ya tafasa na tace masa a mug na kai masa ciki na iske har ya fito wanka ya na shafa mai, kan madubi na ijiye masa, kamar ina sauri na koma kan gado na kwanta sai ya juyo ya na kallona kafin ya ce.

"Ko taya ni ma shiryawa ba za a yi ba?

Ya faɗa ya na wani mini mirmishin da a baya ya san ya na kunna ni, amma a yanzu da zan fito na faɗa masa yadda na ke ganin baƙin sa in ya yi min wannan mirmishin da tuni ya kama kan shi.
Sai da na shige cikin bargo sannan na leƙo kaina ina faɗin" shirin barcin ne sai an ta ya ka?
Na faɗa ina masa wani kallo, shi wai ba shi da ganewa ne, ni fa da zai ƙyaleni da ya burgeni bai san bina ma da ya ke wani ƙara min takaicinsa ya ke yi ba.

"Da ko barcin ne ai kina shirya ni ko?

"Da ka ce yanzu kuma kiɗa ya sauya dole ma ruwa ya sauya."

Na faɗa ina hararan shi ta gefen ido, tsabar ma Yallaɓai ya maida ni shashashan madina sai kawai ya kwashe da wata dariya kafin ya ce.

"Me ya sauya? Uhm My Sady Baby?

Bakina ne na yi masa limzani amma na kusa na yi masa wani gimgimeman tsaki, ganin in ma tsaya ina biye masa mahaukaciya zai maida ni nishaɗi ya ke yi shi fa amarcin ya karɓe sa matuƙa sai faman washe baki ya ke yi, baya na juya masa kawai ina ƙokarin ya ƙi da abin da ke taso min daga ƙasan zuciyata ina jin sa har ya gama shirin barcin sa ya kashe mana fitila ya zo ya kwanta na ɗauka zai yi gefen sa ne sai kawai na ga ya matso kusa da ni ya kwanto saman jikina ya na kiran sunana.

"Saddy.."

Wato saboda ya yi mini kishiya na zama abin dariyan shi kaɗan ya rage ban ture shi ba amma na yi masa bakam sai ya fara min cakulkuli tun ina kannewa har na kasa ina dariya na mirgina ina faɗin" Ka bari mana Yallaɓai."
Amma bai ƙyale ni, sai da ya ga na kusa fita hayyacina har ina hawaye duk mun birkita gadon sannan ya ƙyaleni shi ma ɗin bi na ya yi ya danne ya na min wasu abubuwan, tun ina ture shi har dai ya fi ƙarfina dole na ba da kai bori ya hau, sai da muka samu natsuwa sannan muka yi wanka muka kwanta da asuba ma bayan ya dawo masallci sai da ya ƙara nema mana wani ɓarnan ruwan

"Yallaɓai da sanyin nan kasan ɓarnan ruwa akwai wahala."
Ya na shafa fuskata kafin ya ce" Ya fi daɗi ne. Kuma kin san cewa kin ƙara daɗi Madam?
Ya faɗa ya na sumbatar goshina lokacin muna kwance a tare ne, saboda kalamansa sun yi kama da na yaudara yasa na yi masa banza. Wai kin ƙara daɗi! Duk da bai san na ƙara daɗi ba ne sai yanzu da ya je ya ɗanɗano wata? Ɗan renin wayau kawai.

"So na ke yi na sake ajiyar mai sunan Alhajinmu ko Baban Gwammaja"

Ya faɗa ya na shafa cikina zuwa saman marata, nima sai na ɗora hannuna saman hannun shi har na ji tahowar ƙwallah.
"Allah ya sa haka Yallaɓai na."
Ina so na sake haihuwa ni ko da guda ɗaya ne."
Na faɗa ina jin sukan abin daga ƙasan raina.

"In sha Allahu za ki ƙara haihuwa ba ma ɗaya ba dozin."

Mirmishi kawai na yi amma ban yi mgana ba.

"Ya ku ka yi da Likita zuwan ki na ƙarshe asibiti?

Bayani na fara yi masa da cewa gwajin na ƙarshe ma ya na lap on 12 january zan koma in na karɓa sai na je na kai mata na ji me za ta ce tukunna.
" In sha Allahu ba matsala."
Na amsa da Allah ya sa.

Bai kuma ƙyale nin ba sai da ya saka mu muka sake ɓarnan ruwa da safen nan. Ranar dai a gida ya yini bai fita ba saboda shi ma na ƙi dukan Baby domin tunda ta tashi barci ta ga ba Jidda ta fara rigima da Yallaɓai baya nan da tuni jikinta ya faɗa mata, shi ya zauna ya na lallashinta ni ko kallo ba su ishe ni ba. Sai washegari ya fita ya ce min zai biya ya duba Gimbiya daga nan zai shiga Office. Baby ta nace masa da ita ya tafi da cewa wai zai dawo da ita in zai dawo gida ni dai ban yi magana ba ina jiran na ga iya gudun ruwan shi.

Sai ga shi tare da Gimbiyar suka kawo Jidda da Baby tun da yau ɗin ya na wajen ta ne. Ba su dade ba ni ma kuma ko fuska ban ba su ba muna gama gaisawa na bar su a falo na yi shigewata ciki sai da ya biyo ni muka yi sallama, hug ɗin ma na ƙi yarda na shige tiolet na bar shi nan dole ya wuce sai da na ji sun bar gidan na fito. Baby sun dawo da chaculte sai cincin da su alhaki suna ta budirinsu kallo ba su isheni ba suma ɗin haushin Ubansu ne duk ya shafe su.

Tun ina ganin lamarin Yallaɓai in ya yi kwana biyu a gidana ya je can ya yi kwana biyu a wasa har na tabbatar da cewa gaskiya ne. Ba ni kaɗai ba ce matar Yallaɓai yanzu ba. Yana da wata matar shi ya sa ko cefane yanzu biyu ne Musbahu ya kawo min itama ya kai mata. Ya na kawo ta gidana su zo tare amma ni ban taɓa marmarin zuwa gidanta ba. Kuma in dai ya na gidana sai ya dauki Jidda ya kai mata in kuma ya ma can sai ya dawo da ita yadda bai taɓa min magana kan Jidda ba nima ban taɓa yi masa ba. Kwanaki can ya yi min maganar kan me ya haɗamu da Anty Bahijja.?
a lokacin sai na tambaye sa.

"Me ta ce maka hala?

"Kawai ta na ta faɗa ne wai kin yi mata rashin kunya."

Sai na jinjina kai kafin na ce" Ita ya ɗauke shi a rashin kunya amma ni ba haka na ke nufi ba"
Sai ya tambaye ni mai ya haɗamu na ɗan faɗa masa da cewa" Na faɗa mata ko kai da na ke zaman ka, in ka matsa min da zuwa haƙuri zan ba ka. Ina ga shi ne ta ji haushi."
A lokacin bai ce komai ba amma dai ya ce na kira ta na bata haƙuri ni ko dai na ce masa toh amma ban kira ba domin ban ga abin da na yi mata da zan kira ta na bata hakuri ba in ta so kar Allah ya sa ta haƙura in mun haɗu in na gaisheta kar ta amsa ita ta sani.

Shi daman Yallaɓai ba mai damuwa da bin diddigi ba ne bai ma ƙara ta da mganar ba, ba ni ƙila ma tuni ya manta da batun in dai ba ita Anty Bahijjan ta sake masa mgana ba. Ga shi muna cikin sati na biyilu da tariyan Gimbiya tun ina tunanin zan iya sabawa da sallaman Yallaɓai in zai bar gidana har na fara tunanin har abada ba a sabawa kullum ne lamarin ni sabo na ke kallon shi a idanuwana. Ga shi tun bayan bikin ba wanda ya dawo gidana sai dai mu yi magana da su Hauwa ta waya Suwaiba ma sai da na kirata sannan ta turamin hotunan da ta ɗauke mu ni da Yallaɓai sun yi kyau amma ko status ban yi da su ba amma dai na ga Anty Maimuna ta sassaka hotunan su na bikin tariyan ƙila a lokacin ba ta samu sukunin sakawa ba, duk na kalla daga baya ne na yi ta daman kalla domin har da hoton Yallaɓai da Gimbiya su biyu, ta kwantar da kanta saman kafaɗansa ta na dariya shi kuma ya juya ya na kallonta kamar dai magana ya ke yi mata aka ɗau hoto.
A ƙasan hoton ta saka caption.

"Tafida da Gimbiyarsa. Alƙawarin Allah ya tabbata."

Lalle fa Gimbiyarsa. Hoton nan da na gani ya daɗe yana gilmamin a cikin mafarkina da zahirina. Duk in da na zauna ko na kwanta da na runtse ido su na ke gani sai da na yi ta kiran sunan Allah sannan na samu sukuni da salama. Sai a yanzu na ke ganin cewa daman tun can Yallaɓai na son Gimbiya dama ne bai samu ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login