Showing 1 words to 3000 words out of 143522 words
Chapter 1 - DAHUWAR 'KAHO BOOK COMPLETE Hausa Novels By Ameera Adam.pdf
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko
É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma,
don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka
arashi ne.
MABUÆŠI
Idan aka ambaci kalmar 'Fuska' abin da yake fara zuwa zuciyoyi da dama, ita ce fuskar
É—an'adam da Allah Subhanahu Wata'ala Ya hallita masa. Wacce a cikinta Ya samar da rassa
mabambamta, don a mafi yawancin lokuta ta hanyar ganin fuskar ne ake gane É—an yanki kaza
da kuma al'umma kaza. Idan muka dubi aure ta fuskar addinin Musulumci, za mu fahimci abu ne mai kyau. Domin koyi
ne, ga sunnar Annabinmu Annabi Muhammad (S.A.W). Wanda hawa doron sunnar yana iya kai
miliyoyin Al'umma zuwa ga turbar tudin tsira, wato Aljannar da kowanne cikakken É—an'adam
musulmi yake fatan rabauta da ita. Kuskurewa haka; ko wofantar da ƙa'idojin bin sunnar, suna
iya kwasar al'umma zuwa ga wutar Jahannama. Wacce duk musulumin ƙwarai yake bakin
ƙoƙari, wurin yin katangar ƙarfe/ tsari da ita.
Kamar yadda muka sani, zamani rikiÉ—a yake tamkar hawainiya/wahainiya. Haka kowanne
zamani da suffar da yake tafiya, tare da al'ummar da suke rayuwa a cikinsa. A wannan zamanin
da ake tafiyar biri a yashi, mata da dama suna kallon aure da ta fuskoki daban-daban. Haka
kuma wasu sukan kalli ƙarin aure, ko kawo abokiyar zama ta munanan fuskoki mabambamta.
Musamman yadda iyayen gida suke ganin wayo ko dabararsu ce, ta sa aka auro su a
matsayinsu na iyayen gida. Har wasu daga cikinsu suke cin duniyarsu da tsinken tsire, ta
hanyar gasa wa amare gyaÉ—a a hannu. Ko kuma É—anÉ—ana wa maza kuÉ—arsu, domin hana su
rawar gaban hantsi da amarensu. Saboda suna ganin sun zama tamkar ruwa a cikin gida ko
kuma kujerun zama, da ko an ƙi ko an so dole a zauna da su. Ba tare da sun hangi me gobensu
za ta haifar musu ba.
To amma duk da yadda ake ganin iyayen gida suna wasan juyin waina da amare, lamarin bai
sauya zani ba. Domin a ɓagaren amaren da suke ta cin alwashin mijin wata ne zaɓinsu, a
guntun tunanin wasu daga ciki. Sukan yi tsammanin gazawa, gajiyawa da rashin so ne yake sa
miji yake nemansu har ya aura a matsayin mata ta biyu, uku ko huÉ—u. Musamman da ya
kasance maza da dama, sukan kwayewa iyayen gida baya tun a neman auren. Silar haka ne
yake sa amare suke hangen kansu a bigiren cusguna uwargida, duk don su nuna musu miji ya
daina yayinsu. Ko kuma sun daina ganinsu, a matsayin mata masu ƙirar da Allah (S.W.A) Ya
hallata musu, domin su kasance sanyin idaniya a wurinsu. Ba tare da amaren suna tsalle ko yin
É—age ba, don su hangi yankan kunkurin Balan da suke yi wa rayuwarsu.
SHAFI NA ÆŠAYA
Gidan Yaya Salis cike yake da mata har da ƙananan yara, saboda yinin dannar ƙirjin da ake yi
wa Aunty Murja. Tun da yamma ta ƙarato gabanta yake ta faɗuwa, don haka ta koma cikin 'yan
uwanta da ke É—akin gadonta. Musamman da giftawa É—aya-biyu idan ta yi, daga tsakar gida
zuwa falonta sai ta ji maganar da za ta sosa mata rai. Bilkisu zaune take a falon gidan ita da ragowar 'yan'uwanta, don yawanci cikin falon cike yake
da su dangin miji. Kallon Hafsa ta yi ta ce.
"Miƙo kuɗin na ki ankon, dama ai kin ce idan muka haɗu yau za ki ba ni. Kin san yanzu an
daina kasuwanci da bashi, maza ki ba ni na É—ora lissafi." Murmushi Hafsa ta yi ta ce.
"Aunty Bilkisu duk cinikin da kika yi ina laifi ma ki bar mini a ribar da kika samu." Harararta
Bilkisu ta yi, za ta yi magana suka ga Aunty Murja ta fito ta shiga kicin. Salma ce ta É—an zunguro
Bilkisu, ta yi ƙasa-ƙasa da murya ta ce.
"Ni fa wallahi Aunty Murja tausayi take ba ni, duk da tana danne kishinta amma kin ga duk ta
rame, ji fuskarta duk ta sauya kamar kuka ma ta yi."
Taɓe baki Bilkisu ta yi ta ce, "Ni babu wani tausayi da ta ba ni, ai wallahi ba ƙaramin daɗi na ji
ba. Ki duba fa ki ga yadda ta samu wuri a gidan nan, duk girman É—akunan nan a ce daga ita sai
'yan 'ya'yanta uku. Duk ta bi ta kanainaye shi kullum sai uwar ƙiba yake yi, yanzu idan aka kawo
amarya ai dole ta lanƙwashe ƙafafuwanta." Lokaci ɗaya suka saki shewa haɗe da tafawa. Hadiza da ke gefe, abokiyar wasan su Bilkisu ce ta ce.
"Magana ta domin Allah fa babu macen da ba ta san sakewa a gidanta, sai dai idan ba ta
samu yadda take so ba. Kishiya kuwa ai babu daɗi, ni wallahi Aunty Murja ma ba ƙaramin birge
ni ta yi ba. Saboda ko babu koma ta kama kanta, babu abu É—aya da za a ce ta yi a lokacin bikin
nan."
"Allah ko sakaran neman wurin zaman? To ni dai ina shafin amarya. Don jiya da na je lalle na
biyo ta nan, danginta sun zo jere har taya su buga ƙusar labule na yi. Ke zanin gado ma ni na
shinfiɗa, yoo hauka ake zan bi bayan matar wa ga wurin da ɗan'uwana zai ɓarje amarci."
Bilkisu ta faɗa cikin isgilanci, sai kuma ta sake taɓe baki ta ce.
"Wai kun ga yadda jiya ya tasa ta a gaba yake aikin lallashi, kai na sake yarda wallahi an
shanye Yaya Salis har ƙafafuwansa. Wai duk yadda yake bautawa matar nan jiya har ji na yi
yana yi mata alƙawarin sayen mota. Wallahi wannan auren da ya yi na san har da addu'arsu
Baba, don yadda ta wanke hannu a kansa idan an ce zai kalli mace ma zan yi mamaki." Sadiya ta saki dariya ta ce, "Ni duk ba wannan ba, wallahi idonta kawai nake son gani idan an
kawo amaryar. Yen yen yen yen abu kaÉ—an Abban Sajida, Allah Ya sa ya yi mata halin mazan ta
gani ba dai ya yi auren..." Maganar Sadiya ce ta maƙale sakamakon ganin Aunty Murja ta fito
daha kicin za ta wuce, duk da ta ji wasu daga cikin kalaman da suke tattaunawa sai ta yi kamar
ba ta ji ba. Da za ta wuce ta sakar musu murmushi ta ce, "Sannunku da hutawa."
Bilkisu ta yi zaraf ta ce, "Aunty Murja ai ke ce da sannu, kishiya ai ba sauƙi ba ce. Ni wallahi
idan aka ce akwai ranar da Yaya zai yi miki kishiya ƙaryatawa zan yi, hmmm namiji rumbun
ƙaya mai abin mamaki." Kafin Aunty Murja ta yi magana suka ji tsaiwar motocin 'yan kawo
amarya a ƙofar gida. Guɗa aka fara saki ta ko'ina hakan ya tsananta bugawar zuciyar Aunty
Murja. Idanunta suka ciko da ƙwalla, ba ta yi aune ba sai ji ta yi hawaye yana zuba. Bilkisu ce ta
yi saurin sunne kai ƙasa tana dariyar ƙeta, da sauri Aunty Murja ta wuce ɗakinta jin kukan da
take dannewa zai ƙwace mata. Su Sadiya ne suka miƙe da sauri suka nufi hanyar waje don
tarbar amarya. Yadda Bilkisu ta zaƙe a lokacin za ka ɗauka ciki ɗaya suka fito da amaryar, don
har wasu daga cikin dangin amaryar sun gane ta musamman waÉ—anda suka je jere.
Yadda su Bilkisu suke haba-haba da amarya da danginta ya sa daÉ—i ya mamaye su, har suke
ganin kamar sun fi sonta a kan Aunty Murja. Wasu daga ciki har suke tsegumin ko Aunty Murja
ba ta da hali mai kyau, shi ya sa suke yin nan-nan da ita.
Kusan duka 'yan uwan Yaya Salis sun watse tun bayan da aka kawo amarya, haka daga
ɓangaren 'yan uwan uwargida Aunty Murja. Sai Bilkisu ce kawai ta rage, da yake ta ce mijinta
Hafiz ne zai biyo ya É—auke ta su tafi.
Aunty Murja ba ƙaramin mamakin Bilkisu ta yi ba, a tsammaninta koda ya kasance yayanta ne
zai yi auren, amma za ta iya yi mata kara ko don kada ta ji haushi. Amma abin da ya tsaye mata
a rai Bilkisu ce har da fitar da atamfar anko, domin har wunin bikin Aunty Murja ta ce ba za ta yi
ba, Bilki ta ce su za su yi idan ita ba za ta iya ba. Ganin irin rawar jikin da suke yi a kan amaryar
ya sa ta sake janye jikinta da su.
A lokacin da Hafiz ya zo É—aukar Bilkisu a daidai lokacin Yaya Salisu ya shiga gidan, da gayya
Bilksu ta raka shi sashen Murja don ta ga abin da zai faru. Tana tsaye a bakin ƙofa ta ga ya
rungume Aunty Murja, daga shi har ita aka rasa wanda ya riga wani fara zubar da hawaye.
"Ki yi hauri Ummu Sajida, kin san wane ne mijinki. Na san duk abin da zan faÉ—a a yanzu ba za
ki yarda da ni ba, but trust me wallahi ban yi auren nan don na wulaƙanta ki ba. Har abada ke ta
dabance a cikin raina, ke ta musamman ce 'yar Aljannata." Yaya Salis ya furta yana sakar mata
fake a goshi, saboda Aunty Murja mace ce mai haƙurin gaske. Kuma har cikin zuciyarsa yake
faÉ—ar kalaman bakinsa, guntun tsaki Bilkisu ta saki ta nufi sashen amarya. Tana shiga ta ga
ƙawayenta sun yi carko-carko, ta ji ɗaya daga ciki tana cewa.
"Na'ima mu kam za mu wuce tun da angon har yanzu bai shigo ba, wai ba kin ce ya ce miki ya
kusa ƙarasowa gidan ba?"
Bilkisu ta taɓe baki ta ce.
"Ina za ku gan shi yanzu? Yana can waccan uwar kusasun ta saka shi a É—aki sai lailaye ta
yake yana lallashinta. To Aunty Na'ima ni zan wuce, don na ga abin na yaya ba me ƙarewa ba
ne, sai ya kawo ki gidana bayan kwana biyu." A É—an kunyace Na'ima ta amsa, Bilkisu ta fita ta
haye mashin É—in Hafiz suka wuce gida.
WASHEGARI
Tun da gari ya waye Bilkisu ta lura da sauyin Hafiz, sai wani nannan yake yana haba-haba da
ita. Sai da yaran suka tafi makaranta gabaÉ—aya sannan ya cewa Bilkisu.
"Ummu Sayyid, don Allah magana nake so mu yi da ke ta fahimta. Kuma ki kwantar da
hankalinki wannan ba wani abu ba ne, ni dai kin san ina sonki kuma ina matuƙar ƙaunarki
Bilkisu." Gabanta ne ya faÉ—i, da sauri ta haÉ—e fuska ta ce.
"Ka ga ni ba na son wannan kewaye-kewayen, duk me ya kawo waÉ—annan maganganun?"
Murmushi ya yi ya ce.
"Haka ne, to kin san komai da kika sani a rayuwa muƙaddari ne daga Ubangiji. Kuma kin san
akwai abin da yake ƙaddara a cikin rayuwar mutum, ko ba ya so babu yadda zai yi da shi."
Hafiz ya É—an yi jim sai ya cigaba da cewa.
"Dama tun kwanaki nake son sanar da ke, akwai wata yarinya da na yaba da hankalinta. Ko
kaÉ—an ba ta da hayaniya, shi ya sa nake son aurenta. Don ba zan kawo wacce za ta tarwatsa
mini gida ba..."
"Dakata don Allah Hafiz, wannan wacce irin maganar banza kake faÉ—a mini? Yanzu dama
akwai ranar da za ka munafurce ni? Ni za ka ƙara wa kishiya Hafiz?"
Bilkisu ta furta cikin fusata. Hafiz ya sake kwantar da murya ya ce.
"Wallahi na so sanar da ke tun rannan, sai kuma na ga za ku shiga bikin Yaya Salis don haka
na bari sai an gama. To jiya bayan kin fita su Baba Ƙarami suka je kai kuɗin aurena wurin
iyayen Amina."
A wannan karon ma É—agowa Hafiz ya yi yana satar kallonta sannan ya ce.
"Wallahi ana zuwa, mahaifinta ya ce a É—aura aure idan har da gaske nake yi. Idan ya so ko
daga ba ya a yi duk bidi'o'in da ake yi na al'ada, wai saboda wasu samarin suna amfani da kai
kuɗin aure don su ɓata ya..."
"Kutumar..."
Uban ashar É—in da Bilkisu ta lailayo ta maka ya katse maganar Hafiza, nan take jikinta ya É—auki
karkarwa cikin tsananin zafin kishi ta cikumo wuyansa ta ce.
"Wallahi duk shegiyar da ka aura sai ka sake ta, ni za ka wulaƙanta ka tozarta? Wallahi ko ka
sake ta ko na kashe ka, kuma na kashe kaina yanzun nan." Bilkisu ta ƙarasa maganar tana
fisgo sharɓeɓiyar wuƙa a kwandon wanke-wanke.
GIDAN ALHAJI UMAR
Hajiya Karima wayarta ta É—auko ta latsa layin lambar mai gidanta, ba a É—auki lokaci ba ta ji ya
ɗauka. Don haka cike da ƙosawa ta ce, "Alhaji ko na wuce ɗaki ne? Tsawon minti goma sha
biyar fa kenan da ka ce na fito kuma na ji ku shiru."
"A'a ga mu nan zuwa." Daga can ɓangaren Alhaji Umar ya ba ta amsa. Tana nan zaune babu
jimawa ta ji ya shigo falon baki É—auke da sallama. ÆŠago da kai ta yi ta amsa masa, ta hangi
hannunsa a maƙale da na Shukura da take biye da shi. Zama ya yi a kujerar da ke kallonta,
Shukura ta matsa jikinsa tana lafe kanta a gefen kafaÉ—arsa. A É—an duburburce Alhaji Umar ya
ce.
"Wallahi... kin san akwai gajiyar biki. Duk ta gaji ne."
Murmushi Hajiya Karima ta yi, duk da tana jin zafi a ranta amma sai ta danne ta ce, "Ai dama
gajiya sai a hankali za ta warware."
A hankali Shukra ta gyara mayafinta cikin dabara ta fara ƙarewa Hajiya Karima kallo.
Hajiya Karima babbar mace ce da za ta kai shekara talatin da bakwai zuwa arba'in, ita da Alhaji
Umar aure suka yi tun na saurayi da budurwa. Alhaji Umar zai yi shekara arba'in da bakwai
zuwa hamsin, tun da suke tare da Hajiya Karima bai taɓa ƙara aure ba, sai a wannan lokacin da
ya auro Shukura mai shekara goma sha takwas a duniya.
Ta cikin mayafi Shukura ta yamutsa fuska a cikin ranta ta ce.
'Gaskiya baby ya yi haƙurin zama da wannan abar, don Allah dubi yadda duk naman fuskarta
ya saki. Aba ta yi shirim da uwar ƙiɓa babu fasali.'
Gyran muryar da Alhaji Umar ya yi ne ya katse gajeren tunanin da Shukura ta faÉ—a.
"AlhamduLillah! Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangiji (S.W.A), Hajiya ke da
Shukura na haÉ—a ku a nan ne domin na yi muku 'yar nasiha. GabaÉ—ayanku matana ne, ke
Hajiya ke ce babba. Idan kika kama girmanki za ku zauna lafiya babu rashin kunya ko tashin
hankali, haka kema Shukura. Wannan uwargidana ce, ba ta da matsala da kowa tun zamana da
ita. Ban auro ki don ki raina ta ba, haka ita ma daga ɓangarenta."
Alhaji Umar ya furta cikin tausasan lafuza. Ya jima yana yi musu nasiha sannan kowa ya wuce
É—akinsa.
Tun da Hajiya Karima ta shiga É—aki ta ji zuciyarta duk babu daÉ—i, duk yadda ta kai ga danne
kishinta sai da ta ji ƙwalla ta zubo mata. Saboda rana ta farko kenan, da suka raba makwamci
da Alhaji tun tsawon shekara ashirin da biyar da aurensu. Alwala ta É—auro ya fara gabatar da
sallolin nafila, ta shiga kwararo addu'o'i sannan ta ji zuciyarta ta yi mata sanyi.
WASHEGARI
Asubar fari ta ji ana buga mata ƙofa, a hankali ta yunƙura ta zage sakatar ɗakin. Alhaji ta gani
sanye ta doguwar rigar, ta É—an murza idanunta ta ce.
"An kira sallar Asuba ko?"
Murmushi Alhaji ya yi yana É—an sosa kai ya ce, "A'a tukunna dai."
Shiru ta yi tana jiran abin da ya kawo shi a lokacin, Alhaji ya sunne kai ƙasa ya ce.
"Wallahi dama ashe gas É—inta ne ba a haÉ—a mata ba. Shi ne na ce za ki É—an É—ora mana ruwa."
Ƙirjinta ne ya yi wani irin bugu da ƙarfi, nan take ta ji zuciyarta ta ɗauki tururi. Da wani irin kallon
mamaki ta kalle shi, don ta yi tsammanin ko babu komai zai ji nauyin yi mata wannan maganar.
Tun da kawaici mai sunan kawaici ta yi a lokacin shirye-shiryen aurensa.
"Amm... dama... saboda ta ce ba za ta iya amfani da ruwan sanyi ba ne..."
Alhaji Umar ya furta a rarrabe cikin jin nauyi, musamman da ya lura da irin kallon da take jefa
masa.
Ummou Aslam Bint Adamí ¼í¼š
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko
É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma,
don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka
arashi