Showing 30001 words to 33000 words out of 143522 words

Chapter 11 - DAHUWAR 'KAHO BOOK COMPLETE Hausa Novels By Ameera Adam.pdf

18 Jun 2025

6725

sati sau biyu
ragowar kwanaki sai kunu. Hatta abincin dafawa ita ta saka su yin tazarce daga rana zuwa
dare, don haka Mommy ta same shi da maganar.

"Daddyn Mami shin ka san abin da yake faruwa a gidan nan? Yanzu saboda Allah a ce
kowanne irin abinci tazarce za mu yi masa." Fuska a haɗe Daddy ya ce.

"Ai wallahi ban taɓa sanin ba ki da hankali ba sai yanzu, yanzu ke Karima tsofai-tsofai ba ki
san ya kamata ba? Yanzu a ce yarinya ƙarama ita za ta fi ki tattali da sanin ya kamata? Wallahi

kin ba ni kunya." Duk yadda ta so shawo kan Daddy fir ya ƙi amincewa. Sai ya zamana idan
tana son su sauya abinci, sai dai ta fitar da kuɗi a jikinta ta bayar su sayo abin da suke so, a
haka suka cigaba da tafiya har bikin Ruƙayya ya rage saura kwana goma.
Da farko Mommy ido ta kawo masa, saboda ta ga ko zancan kujera bai yi mata ba. Duk wani
abu da uwa take yi wa 'ya na kicin babu abin da Mommy ba ta saya wa Ruƙayya ba, sai kayan
gado ne kawai ya rage take jira daga gare shi. Ana saura kwana bakwai biki ta je har ɗakinsa ta
same shi, fuska a sake ta fara yi masa maganar duk da lura da ɓata ran da yake yi. Sai da ya
gama sauraronta sannan ya ce.

"Kayan gado da duk wani abin buƙata kama daga kan abinci, garar amarya da komai da kika
sani na buƙata na damƙa wa Shukura, ba sai kin wahalar da kanki ba za ta aiwatar da komai
tun da ita kin ga ta zamani ce za ta fi ki sanin abin da ya dace." Hajiya Karima ji ta yi kamar ya
watsa mata ruwan zafi, rai a ɓace ta ce.
"Wallahi na gaji Alhaji, yanzu saboda wulaƙanci na haifi 'yar a cikina. Duk wata ragamar
ɗawainiyar raino da tarbiyya na yi mata, rana tsaka ka ba wa wata bare kuɗin hidimar bikinta,
wallahi ba zai yuwu ba. Ai kuwa wannan karon sai dai duk abin da zai faru ya faru."

"Rashin mutumci za ki yi mini Karima?"

"Wallahi duk abin da za ka faɗa sai dai ka faɗa, amma babu ƙatuwar da za ta yi mini wannan cin
kashin." Ita ma Mommy ta katse shi a zafafe, Daddy ya miƙe a fusace ya ce.

"Ba ni ne ubanta ba, wallahi idan kika saka tsiya auren ma sai na fasa shi." Cak Hajiya Karima
ta tsaya, ta dube shi rai a ɓace ta ce.
"Saboda mace za ka zubarwa da kanka mutumci, to wallahi bari ka ji idan har ka yi wannan
abin kunyar. Wallahi zamana da kai ya zo ƙarshe, sai dai ka zauna da Shukura ba ni ba." Daddy
ya matsa gabanta ya ce.
"A yanzu ma kina iya tafiya ai ban riƙe ki ba."

"Wallahi da zaman wulaƙancin da kake yi mini gara ka sawwaƙe mini, amma wallahi ka ji na
ratse ba zan yarda ace kayan ɗakina da kuɗin hidimar biki yana hannun matarka ba."
Hajiya Karima tana rufe baki Daddy ya ce.
"Karima ba ki san na jima ina haƙurin zama da ke ba ko? To tun da haka ne ki je na sake ki
saki ɗaya. Idan ya so sai ki yi rayuwar jin daɗi, 'ya dai ni na haife ta. Zan ga uban da zai ɗaura
mata aure." Yana gama faɗa ya fice a fusace.



Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko
ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma,
don haka a kiyaye.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka
arashi ne.

SHAFI NA GOMA

ALL NATURAL PRODUCT💃🏻
Tsumi
Tsumin tighten
Tsumin Sanyi
Tsumin basir
Tsumin 3in1

Kazar Amare yan mata.
Kazar Amare zawarawa.
Kazar Masu haihuwa.
Kazar 3in1
Kazar uwargida ko amarya da suke son burge oga.

Gumbar dabino.
Gumbar kwakwa.
Gumbar Madara.

Garin dahuwar kaza.
Garin dahuwar ciccibi.
Garin dahuwar hanta.
Garin dahuwar kwai.
Garin dahuwar kifi.

Garin hakin maye na sha da Madara ko nono.

Ingantaccen tsumin maganin sanyi, wanda aka samo daga masunta masu kamun kifi,bayan
maganin infection yana magance sanyin da aka sha a ruwa ko a tiles ko irin sanyin nan mai
kumbura jikin mutum.

Bugu da kari ana iya ba yara kanana masu fama da mura ko tari, haka akan dace idan yaro

yana fitsarin kwance aka bashi in sha Allah yana dainawa.
Ta tuntuɓe mu a wannan lambar. 09065730652

***

Wani irin sanyi ƙafafuwan Mommy suka yi, kanta ta ji ya sara kamar an buga mata guduma.
Da sauri ta tsugunna a ƙasa, saboda yadda ta ji juwa tana barazanar taɗe ƙafafuwanta zuwa
ƙasa. Cikin ɗacin zuciya ta fashe da wani irin kuka, jin kukanta ya sa Ruƙayya ta shiga da gudu
tana tambayarta. Yadda jikin mahaifiyarta yake rawa ne ya sa ta riƙe ta hankali a tashe ta ce.
"Mommy lafiya me yake faruwa?" Har lokacin ba ta daina kuka ba, don haka ita ma Ruƙayya
hawayen ya fara zubo mata. Sai da Mommy ta yi kuka mai isarta sannan ta ce.

"Daddynku ne ya sake ni Ruƙayya."

Da wani irin kallo Ruƙayya ta bi mahaifiyarsu, sai kuma ta zabura kamar zararriya ta miƙe tana
ja da baya.

"What are you trying to said Mommy? Don Allah kada ki maimaita mini wannan maganar, saki
like how? Kina nufin Daddy ya sake ki, babu aurensa a kanki or what?"

Cikin kuka Mommy ta ce, "Haka nake nufi Mami, tun farkon aurena da mahaifinku ko yaji ban
taɓa yi ba. Amma because of that yarinyar har yau ni mahaifinku ya saka, Mami har yanzu ina
ganin kamar mafarki nake yi."

Ruƙayya tana shirin yin magana suka ji ƙarar taunar cingam ƙas ƙas ƙas, da sauri suka ɗago
sai suka ci karo da Shukura a tsaye tana bin su da wulaƙantaccan kallo tana taunar cingma.

"Ke! Zo ki karɓi takardar sakin uwarki ki kai mata, sai ku yi hanzarin tattare kayanku ku bar
gidan nan. Don ba zan iya ganin wannan abar tana giftawa a gaban mijina ba, kin san zuciya ba
ta da ƙashi. Kada shaiɗan ya gifta su fara wani irin zama da ita." Shukura ta furta cikin isa da
izgilanci. Ran Mommy sake ɓaci ya yi, za ta yi magana Ruƙayya ta ƙarasa zuciyarta tana zafi.
Cike da tsanar Shukura ta karɓi takardar ta fara kantawa. Babu ko tantama rubutun mahaifinsu
ta gani, sai dai a wannan lokacin ta fi ganin laifin Daddy fiye da na Shukura, saboda da bai ba ta
ba; ba za ta samu ƙwarin gwiwar zuwa wurinsu tana rashin mutumci ba. Shukura ta sake
yamutsa fuska ta ce.

"Yawwa, a gaggauta fita tun da ba gidan..."

Marin da Ruƙayya ta zabga mata ne ya katse kalaman da take yi, cikin jin azaba ta dafe
kumatunta. Kafin ta ɗago Ruƙayya ta sake ɗauke fuskarta da mari har sai da kanta ya bugu da
bango. A razane Shukura ta ja da baya, ta saka hannuwa biyu ta dafe kumatunta cikin tsoro ta
ce.

"Ni kika mara Mami?"

Cikin zafin zuciya Ruƙayya ta sake yin kanta gadan-gadan ta ce, "Na mare ki, wallahi idan kika
sake furta kalma mara daɗi a kan mahaifiyata sai na yi ƙasa-ƙasa da ke. Annoba makira, In
Shaa Allahu da sannu za ki girbi abin da kika shuka."

Shukura ta sauke hannunta, ta nuna Ruƙayya da yatsa ta ce.
"Wallahi za ki san kin kai hannunki saman kumatuna, na rantse da Allah sai na rama a kan
wannan tsohuwar kilakin." Tana ganin Ruƙayya ta yo kanta, ta fita da gudu haɗe da fashewa da
kuka. Lokacin da Shukura ta fita harabar gidan, Alhaji Umar ya shiga mota kenan zai fita. Tana
zuwa jikin motar ta sake rushewa da kuka tana riƙe cikinta, da sauri Daddy ya fito jikinsa har
rawa yake yi ya ce.

"Me ya faru Shukura? Mene ne ya samu cikin naki?"

Durƙushewa Shukura ta yi cikin kuka ta ce. "Kawai daga kai wa Hajiya takarda, shi kenan ita da
Mami suka rufe ni da duka. Hajiya har tana dukan cikina, wai gara na rasa cikin kowa ya huta.
Ni gaskiya ba zan cigaba da zaman gidan nan ba, wallahi ko dai su fice su bar ni ko kuma ni na
fita bar su, don wallahi ba zan zauna su kashe ni ba."
Cikin kumfar baki Daddy ya ce.
"Ita Hajiyan saboda ba ta da hankali ta dake ki a ciki? Wato saboda na sake ta sai ita da Mami
su huce a kanki ko? Bari na shiga gidan." Yana gama faɗar haka ya shige da sauri, har babbar
rigarsa tana shirin kayar da shi. Shukura miƙewa ta yi tana sakin murmushin ƙeta, sannan ta rifa
masa baya. Maigadi shiru ya yi cike da jimami, don duk da 'yan gidan ba shiga huruminsa suke
yi ba amma ya fahimci zuwan Shukura bai kawo komai a gidan ba sai sharri.

Lokacin da Shukura ta fita da faɗa Mommy ta tari Ruƙayya tana faɗin, "Ruƙayya kanki ɗaya
kuwa? Kin san me kika aikata? So kike ki janyo wa kanki masifa kina zaune ƙalau?" Hawaye
yana zuba daga idonta ta ce.
"Mommy ba ki ji abin da take faɗa ba? Duk wannan maganganun sai na yi mata shiru, yanzu
saboda Allah ban da Daddy ya ba ta fuska ta isa ta faɗa miki haka?"

"Tun da mahaifiyarku ta ɗaure muku ai dole ku yi rashin mutumcin da kuka ga dama." Daddy
ya furta a zafafe, cikin sauri Ruƙayya ta waiga ta ce.
"Daddy ka ga..."

Tas! Daddy ya ɗauke fuskarta da mari, kafin Ruƙayya ta yi motsi ya sake sauke mata wani. Rai
a ɓace ya ce.
"Don ba ki da mutumci matar tawa uwarki za ta saka ki daka? Ni za ku wulaƙanta saboda
rashin tarbiyya."

"Ai ba ita ba ce har da Hajiyan, kuma wallahi sai ka rama mini ko ni na rama." Shukura ta faɗa

a shagwaɓe. Daga Mommy har Ruƙayya ɗagowa suka yi suna kallon Shukura, ta fakaici idon
Daddy ta sakar musu gwalo sai kuma ta sake fashewa da kuka.

"Ni ba zan rama miki ba, sai dai ki rama da kanki."
Daddy ya faɗa yana matsawa gefe. Babu ko kunya Shukura ta matso da niyyar yi wa Mommy
mari a fuska. Ruƙayya ce ta sha gaban Mommy, fuska a haɗe tana wurgawa Shukura mugun
kallo.

"Za ki matsa ta rama marin da uwarki ta yi mata ko sai ranki ya ɓaci?" Daddy ya buga wa
Mami tsawa. Zuciya a ƙeƙashe ta ce.
"Duk wani hukunci da za ta yi ta sauke shi a kaina, amma idan ta sake ta ɗora hannu a jikin
mahaifiyata wallahi za ta gane kurenta." Cikin zafin zuciya Daddy ya sake marin Ruayya ya ce.
"Haka Karima ta gurɓata tarbiyyarku ban sani ba? Ba za ki matsa ba sai na sumar da ke."

"Ko za ka kashe ni Daddy ba zan bari wannan matsiyarciyar ta mari mahaifiyata ba." Ruƙayya
ta faɗa zuciyarta a dake, don a yadda take ji a ranta komai za ta iya aikatawa a kan
mahaifiyarta. Tana nan tsaye Daddy ya rufe ta da duka, amma taurin kai irin na Ruƙayya ya sa
ta ƙi motsawa daga wurin. Kuka Mommy ta saka, ta janye Ruƙayya ta ce. "Ba sai ka illata mini yarinya ba, za mu tattara mu bar maka gidanka." Fisge Ruƙayya Daddy
ya yi, a zuciye ya dubi Mommy kamar zai kai mata duka ya ce.

"Kada ki sake shiga tsakanina da 'yata idan ina hukuntata. Idan ba haka ba wallahi ranki zai yi
mummunan ɓaci." A daidai lokacin Haidar ya shiga, jin abin da ake tattaunawa ya sa ransa ɓaci.
Shukura ta sake fasa wani sabon kukan ta ce.

"Yanzu shi kenan sun daki banza da wofi ko? Wallahi ba zan sake kwana a gidan nan ba,
kuma wallahi idan ban rama ba sai ka sake ni" Da sauri Daddy ya janyo Shukura jikinsa ya ce,
"Babu inda za ki je, kuma mari kamar kin rama kin gama." Shukura da ke gaban Mommy ta
ɗaga hannu ta zabga mata mari a fuska, ko sauke hannu ba ta yi ba Haidar ya ɗauke fuskarta
da mari. A zafafe Daddy shi ma ya sauke wa Haidar mari sannan ya ce.

"Ni za ka wulaƙanta ka tozarta Haidar? Ashe kai ma ba ka da mutumci?" Rai a ɓace Haidar ya
ce, "Daddy ba ka ga abin da ta yi ba ne? Ni fa dama na jima ina tara yarinyar nan. Wallahi
tuntuni darajarka take ci, da tuni na ɓarar da ita." A zafafe Daddy ya ce.
"Za ka gane ba ka da hankali kuwa, idan hauka ne a kanka zan sa a sauke maka shi." Yana
gama faɗa ya zaro waya ya nemo wata lamba, yana jin an ɗauka ya ce.

"Hello officer, ina son ganinka yanzu. Please ka taho da yaranka." Daga haka ya katse wayar,
da mamaki Mommy take kallonsa kamar za ta tanka masa sai kuma ta haƙura. Suna nan tsaye
suka ga ya ja hannun Shukura yana lallashi suka fita. Daga Haidar har Ruƙayya rungume
Mommy suka yi, Mommy da Mami sai kuka suke yi. Haidar ne ma yake iya lallashinsu, ba su
ɗauki lokaci ba suka haɗa kaya a cikin akwatunansu. Gabaɗaya kallo ɗaya za ka yi musu ka
fahimci suna cikin matsananciyar damuwa. Suna gab da fitowa suka ji ƙarar motar 'yan sanda,

babu jimawa suka ji muryar Daddy yana cewa.

"Ku shigo ga yaron nan, ku zo ku tafi da shi. Ba shi tarbiyya ko kaɗan yaron nan, duk wanda
ya zo belinsa kada a bada shi sai saka hannuna. Ku hora shi yadda ya kamata." Mommy da su
Haidar suna tsaye, suka ga 'yansanda biyu sun shiga falon Mommy. Nan take suka saka masa
hangoff a hannu, Daddy ya ba su umarnin su tafi da shi. Mommy tana kuka tana riƙe shi haka
suka tasa ƙeyarsa suka tafi da shi, da ƙyar Ruƙayya ta lallashi Mami ta tsagaita da hawaye.
Sannan suka ɗauki jakunkunansu suka fito harabar gidan.

GIDAN HAFIZ

Wani dogon tsaki Bilkisu ta saki cikin jin haushi ta ce.
"Da ka san ba kai kaɗai ba ne ai da sai ka sanar da ni." Ajiye akwatin Amina ya yi ya rungumo
ta jikinsa ya ce.

"Kafin a fara faɗan ya kamata a yi mini oyoyo ɗin tukunna." Ajiyar zuciya Bilkisu take saukewa
akai-akai, saboda yadda ta ji zuciyarta tana harbawa kamar ta faɗo daga ƙirjinta. Amina ta taɓe
baki ta ce.

"Sannu da gida Aunty."

A sheke Bilkisu ta dube ta, ta ce. "Ke zan yi wa sannu, ni da nake gidan mijna sannun me za ki
yi mini." Amina ta fahimci maganarta, don haka ta ce.
"Ai da yake tare muke da Habibi, na san kuma kin sha aikin gida shi ya sa na miki sannu. Ga
shi sai da na ce ya kira ki kafin mu ƙaraso amma ya ƙi."
Bilkisu ji ta yi kamar an zuba mata borkon, Hafiz da ke tsaye mamaki ya kama shi, don shi dai
ya san bai yi haka da Amina ba. Yana shirin yin magana Amina ta yi gaba tana faɗin.

"Baby ka shigo mini da akwatin, kuma ni yau kwana za ka yi kana matsa mini ƙafa don ciwo
take yi mini."
Bilkisu jin haka ya sake hargitsa ta, rai a ɓace ta saki hannun Hafiz ta wuce ɗaki fuuuu kamar
za ta tashi sama. Amina tana ganin haka ta saki murmushi, a ranta ta ayyana.
'Ashe dama matar nan sakarya ta mayar da ni, shi ne take kunna ni ban sani ba. Ai kuwa da ni
take zancen.'

Tana shiga ɗaki Hafiz ya shigar mata da akwatin, sannan ya fito ya nufi ɗakin Bilkisu. A kan
kujera ya same ta, ya faɗaɗa fara'arsa ya ce.
"Baby kin yi kyau sosai." A madadin ta ba shi amsa sai ta ce.

"Wato Hafiz ni ka so tozartawa ko? Saboda za ka dawo da matarka shi ne ba za ka sanar da ni
ba. Na gode, ai yanzu amfanina ya ƙare tun da ta dawo." Zama Hafiz ya yi a gefenta ya ce.
"Haba Bilkisu, me ya sa za ki ce haka? Ina kasuwa mahaifinta ya kira ni, amma don Allah ki yi
haƙurin rashin kiranki." Yana rufe baki sai kawai Bilkisu ta fashe da kuka, janyo ta jikinsa ya yi

ya shiga lallashinta. Sai da ta tsagaita da hawayen sannan ya ce.

"Ina abincina?"

"Yana kicin." Ta ba shi amsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login