Showing 129001 words to 132000 words out of 143522 words
Chapter 44 - DAHUWAR 'KAHO BOOK COMPLETE Hausa Novels By Ameera Adam.pdf
gararanba a
titi. Sai na sake inganta su, don ina da burin har jami'an lafiya zan zuba tun da ni dai ka san
summun bukumin ne, zo na kashe ka da turanci ban sani ba ballantana na san harkar
gwaje-gwaje."
Fadil ya saki murmushi, ya yaba masa sosai da sabon tsarin inganta maganin da ya É—auko,
har zai tafi ya waigo ya ce.
"Na ji Daddy ya ce an yi wa yaron nan shayi ya jikinsa?"
Jin tambayar Fadil ta sa hawaye ya zubo masa, ya saka hannun rigarsa ya share. Mamaki ne
ya kama Fadil yana shirin magana Baba Sale ya ce.
"ÆŠan Bishir dai ga shi can rai a hannun Allah, daga kaciya jikin yaro sai fitar da ruwa yake
duk ya jagalgale abin ba kyan gani. Na saka masa magani a banza, haka wanzan da ya yi
masa kaciyar ya aiko masa da magani amma sai ta fara kamewa sai ta koma 'yar gidan jiya." Ya
ƙarasa maganar yana fashewa da kuka.
"Subhanalla, kuma ka kai shi asibiti?"
Kamar Baba Sale yana jira ya ce, "Kaciyar zan kai asibiti don lalacewa? Wai me ya sa a kullum,
sai ka nemi wulaƙanta mana sana'ar wanzanci ne?"
Fadil ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Ni fa ba da wata manufa na faÉ—a ba, yanzu mu je na ga
yanayin jikin na sa."
Babu musu Baba Sale ya yi gaba Uwale da Fadil suna biye da shi. Suna zuwa suka samu
Ɗan Bishir a yashe a ƙasa, kudaje sun yi yamama a kan jikinsa. Da sauri Fadil ya ƙarasa ya
fara karkaÉ—e masa, ya É—ago a É—an zafafe ya ce.
"Garin yaya kuka bari jikin yaron nan ya yi haka? Saboda Allah dubi yadda ƙudaje suka bin sa
ko su ba su isa su saka masa wata cuta a jiki ba."
Mai shirin kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, jin kalaman Fadil ya sa Baba Sale ya saki
wani wawan kuka har sa da ya tsorata Uwale da Fadil. Ya riƙo hannun Fadil jikinsa yana rawa
ya ce. "Boka wallahi ban san yadda aka yi ba, don Allah yanzu mene ne abin yi?"
Jim Fadil ya yi sannan ya ce, "Mafita kawai a É—auke shi zuwa asibiti shi ya fi fa'ida. Don haka
a yanzu muke bayar da shawara idan za a yi kaciya a san wuraren da ya dace a kai yara, ba
zan kushe ta wanzamai ba. Domin tun daga shekarun baya zuwa kusan É—an shekara ashirin da
yake a yanzu, kusan yawancin duka kaciyar gida aka yi musu. Amma a inda gizo yake saƙar,
rashin kula da tsaftace kayan aikin yin ta zuwa kula da ita bayan an yi wa yara, sune manyan
ƙalubalen."
"Wai boka da kake ta ƙafafa a kan shayin, asibiti shin tana da bambamci da ta gida ne? Duk
dai ba abu É—aya ake yi ba?"
Uwale ta tambaya, don ta fara jin haushin yadda Fadil yake fifita aikinsa a kan sana'ar mijinta.
Fadil ya cigaba da karkaɗe wa Ɗan Bishir ƙuda ya ce.
"Gaskiya akwai bambamce-bambamce da dama. Kamar yadda muka sani shayi wacce a
kimiyance ake kira (Circumcision) wata ƙaramar tiyata ce da ake cire fatar loba (Foreskin)
wacce take zazzagowa ta rufe kan al'aurar namiji(Glans). Kaciya tana da dalilin da ya sa ake yin
ta, daga ɓangaren addini zuwa al'ada. Mafi yawancin ƙasashen da suka ci gaba, suna yin shayi ne a rana ta farko da aka haifi jariri.
Wasu ƙabilun kuma suna yi bayan suna ko idan an yaye yaro. To amma kin ga a irin yankin
ƙabilunmu, yawanci ana yi wa yara daga shekara uku zuwa bakwai. Sannan rashin yin ta
babbar barazana ga lafiya ne. Kamar yadda shayi ke da dalili akwai amafanin da take da shi,
musamman a ɓangaren lafiya. Domin yin ta yana bayar da kariya daga saurin ɗaukar cutar
infection, saboda cututtuka suna iya ɓoyewa a ciki idan ba a cire fatar ba. Tana bayar da kariya
daga kamuwa da penile cancer, a ɓangaren mata kuma zai rage musu kamuwa da cervical
cencer, har ma da matsalar saurin kamuwa da ciwon (Balanitis) kumburin saman al'aurar namiji.
Da ma sauran cututtukan da ban lissafa ba."
Jikin Uwale ba ƙaramin sanyi ya yi ba, Baba Sale ya zube a ƙasa kamar wanda aka zare wa
laka ya ce. "Yanzu boka duk wannan bayanan a kimiyance ka karance shi? Shi ÆŠan Bishir
wannan ruwan da take yi na me ne ne?"
Ganin yadda Baba Sale ya É—aga hankalinsa, ya sa Fadil ya tsugunna a gabansa ya ce.
"Ka kwantar da hankalinka Baba Sale, wannan ba komai ba ne In Shaa Allah za a kamo
bakin zaren matuƙar aka je asibiti. Rashin kula da tsaftar wurin ya sa infection ya shiga, har ya
haifar da zubar wannan ruwan da kake gani. Idan har aka je asibiti za su duba shi, su yi abin da
ya dace su ba shi magunguna. Ni ma don dai ina da uzuri, da zan iya yi masa treatment. Amma
ba zai yuwu, a bar yaro haka har tsawon lokacin da zan dawo ba. Sannan yana da kyau a kula
da tsaftar raunin, kada a bari ƙudaje da wasu ƙwarin su dinga hawa jikinsa; saboda za su iya
fesa masa ƙwayoyin cutar da ido ba zai iya gani ba. Rashin kulawa da tsafta, haɗe da
takatsantsan zai iya haifar da kamuwar cutuka, har ya haifar da fiye da wannan da muke gani
wanda ba ma fatan hakan."
"Uwale maza É—auki ÆŠan Bishir mu tafi asibiti, wallahi ni babban tashin hankalina kada ma abin
ya guntule ya faɗo ƙasa."
Baba Sale ya faɗa cikin hawaye. Fadil ya jima yana ba su shawarwari da ƙwarin gwiwa sosai,
sannan suka fito suka shiga mota ya sauke su a asibiti shi kuma ya tafi uzurinsa.
Motar Fadil ta fita babu jimawa Mai adaidaita sahu ya sauke Baba ÆŠanladi, hannunsa É—aya
riƙe da matarsa ɗayan hannun kuma riƙe da akwati. Sai da ta sauka sannan ya ɗauko musu
akwatinan su ya ajiye a gefe. KuÉ—i ya zaro ya biya mai adaidaita sahun, ya kamo hannunta
yana shirin shiga gida Uzee gaye ya ƙarasa wurin bakinsa a washe kamar gonar auduga ya ce.
"Oyoyo jirgin ceto, Oga murfi namu na gargajiya, uban gidan kowanne mai cin mushe. Duk
wanda kwaɓarsa ta yi ruwa ya zo a ɗaure masa, ka suturta kuma ka rufa asirin gayu. Ina wanda
ya samu 'yar shila ya bige aka samu matsala? In wanda bargon suturarsa yake son yayewa? Ya
zo ga mai lulluɓe masa har ya yi bacci. Oga murfi wannan 'yar shilar ita ma zuwa ta yi a kifar da
madafun ikonta ne?"
Tun da Uzee guye ya fara maganar kan Baba Ɗanladi ya ƙara girma, ya faɗaɗa fara'arsa ya
ce. "A dai dinga iya baki Uzee saboda tsaro ba don tsoro ba. Wannan da kake gani ba costomer
ba ce, matar da na auro ce." Murmushi ta yi tana jifan Uzee da wani karuwan kallo, wanda kallo
ɗaya kawai ya yi mata ya fahimci ita ma 'yar hannu ce. Uzee ya yi ƙasa da murya ya ce. "Wallahi Oga murfi ka zo a daidai, domin yanzu haka akwai
wata yarinya da rana ta ƙwace mini. A taƙaice dai cikinta wata biyu kenan, don Allah ka rufa
mini asiri kamar yadda ka saba ka ɓarar da shi."
Baba ÆŠanladi da irin su Uzee suke kira da Oga murfi ya ce. "Ka ga zuwana kenan, ko cikin
gida ban shiga ba. Koda zan dawo bakin aiki sai zuwa nan da sati guda, domin shi kansa
chemist ɗin yana buƙatar gyara."
Uzee gaye ya yi masa godiya, sannan Baba Ɗanladi ya shige cikin gida hannunsa maƙale da
na matarsa da yake jin ta kamar tsoka É—aya a miya.
Tun daga harbar gidan mutanen cikin gidan suka shiga yi masa barka da zuwa, sai dai kusan
kowa bakinsa ƙunshe yake da magana kasancewar ganin Baba Ɗanladi rungume da wata
mace mai zubin 'yan duniya. Amma da yake ba su ga fuska ba, sai kowa ya tsuke bakinsa.
"Lale marhabun wa nake gani haka da hantsin nan?"
Inno ta faɗa tana washe fuska, turus ta yi ganin Ɗanladi sarƙafe da mace a gefe. Inno ta
ƙanƙance ido tana ƙare mata kallo ganin gashin doki ya yi mata yaro-yaro a fuska.
"ÆŠanladi daga ina ka samo wannan abin?"
Inno ta tambaya tana miƙe wa tsaye rai a ɓace.
ÆŠanladi ya saki murmushin soyayya, ya shafo fuskar matarsa cikin so ya ce. "Inno wannan ita
ce matar da na auro ai, so nake sai mun zauna na gabatar miki da ita."
Inno ta fara bin ta da kallo, tun daga ƙafa har zuwa tsakiyar kanta.
"Baby ina buƙatar hutu ka san na gaji. Mu je ɗaki ka yi mini tausa."
Ta furta tana shafa jikin ÆŠanladi. Inno salati ta saki tana tafa hannu ta ce. "Yanzu ÆŠanladi,
ƙaddarar da ka kwaso mana kenan wannan mai zubin alakwankwan ɗin?"
ÆŠanladi ya sunkuya ya sumbaci matarsa ya É—ago ya cewa Inno, "Wallahi Inno kamar kin sani
wannan ita ce ƙaddarata. Jin ta nake har birnin zuciyata. Beb wannan ita ce Mom ɗina, you
know i told you Dad É—ina ya jima da mutuwa."
Ta É—ago tana taunar cingam ta ce, "Am so sorry Mom, ya kike?" Inno ta saki baki da hanci
tana kallon ikon Allah.
Jin maganganu a tsakar gida ya sa Mai yasin ya leƙo yana faɗin.
"Inno ke da waye ha..."
Maganarsa ce ta maƙale, sakamakon haɗa ido da suka yi, lokaci ɗaya wani irin tari ya turnuƙe
shi. Daga can ɓangarenta ita ma ido ta zaro, amma sai ta daidaita nutsuwarta ta basar kamar
ba ta san Mai yasin don kada su gano su.
'Me ne ne alaƙar wannan yaron da 'yar gwal? Ko dai aurensa ta yi ban sani ba, lallai kuwa
dara ta ci gida idan har haka ne.'
Mai Yasin ya raya a ransa.
ÆŠanladi ya zaro mukulli a aljihu, ya buÉ—e É—akinsa ya fara jan akwatinansu ya shigar musu da
su ciki. 'Yar gwal a wurin ta fara rage kayan jikinta, ta zame mayafinta ta wurga a kan igiya. Ta
zamo hular gashin dokin kanta za ta wurga igiya a daidai lokacin Yaya Inu ya shigo cikin gidan,
a bisa tsautsayi ta jefa masa a fuska. Warin gashin ya daki hancinsa, a tsantsance ya wurgar da
shi gefe rai a ɓace yake kallonta, cikin tsawa ya ce.
"Ke! Wace ce ke?"
Daga cikin É—aki ÆŠanladi ya ce, "A'a Yaya Inu, kada ka sake ka sake yi wa 'yar gwal tsawa don
ba zan lamunta ba."
Da mamaki Yaya Inu yake ƙare mata kallo ya furta.
"Za ki fice daga gidan nan ko sai na sumar da ke? Kai ÆŠanladi, a gidan uwar wa ka samo
wannan abar mai zubin surar Fir'auna?"
'Yar gwal ta bi Yaya Inu da kallo a ranta ta raya. 'Ni za ka yi wa barazana? Ai kuwa za ka ga
aikin 'yan bariki. Sai na nuna maka sheÉ—an ne uban gidana ba Fir'auna ba.'' Yaya Inu yana
shirin sake magana, 'Yar gwal ta yi wata wawar sufa ya É—ane shi.
Na kusa kammala free page In Shaa Allah, ma su son cigaba za su fara payment daga yanzu.
500 Aisha Adam 3090957579 Firstbank evidance ta wannan no ba 07062062624
Ummou Aslam Bint Adamí ¼í¼š
[04/01, 13:36] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya
kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd
Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page É—in, ya taimaka ya yi mana Subscribe a
youtube channel É—inmu.í ½í±†í ¼í¿»í ½í±†í ¼í¿»í ½í±†í ¼í¿»
SHAFI NA SHA ÆŠAYA
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Ke! Wane irin iskanci kike yi haka? Ba za ki cika ni ba, sai
na saɓa miki."
Yaya Inu ya yi kalamansa yana kokawa da 'Yar gwal amma fir ta ƙi sakinsa, ta ƙadandane shi
sosai kamar mayen ƙarfe.
"Ke yarinya, ba ki da mutumci ashe ban sani ba, ba za ki sakar mini yaro ba."
Inno ma ta yi maganar tana ƙarasawa wurinsu. Mai Yasin ya gimtse dariyar ƙetarsa, saboda
dama a ciki yake da Yaya Inu. Kuma ya san fiye da haka ma 'Yar gwal za ta iya aikatawa.
Ganin da gaske 'Yar gwal ba za ta sake shi ba, ya sa ya tattare iya ƙarfinsa da niyyar ya
warɓo ta ƙasa, sai ta maƙale shi ƙam a madadin 'Yar gwal ta faɗo sai wata wawiyar tusa ce ta
ƙwacewa Yaya Inu.
"Subhanallahi! Inusa mene ne haka da sakin tusa?"
Mai Yasin ya furta, sannan ya ce. "Ke yarinya kanki ɗaya kuwa? Kamar muna ƙasar kafirai za ki
ƙadandane mutumin da ba muharraminki ba." 'Yar gwal ta ɗago tana bin sa da wani irin kallo,
sai kawai suka ji ta saki jiki ta faɗi yaraf a ƙasa. Sai a lokacin Yaya Inu ya ja gefe yana kaɗe
riga, ya cigaba da wurga mata kallon tsana kamar zai mata duka.
"Sannu babyna, ko jikin ne ya dawo?"
Furucin Baba ÆŠanladi kenan. 'Yar gwal ta fara jera atishawa, ÆŠanladi ya É—ago ya dubi Yaya Inu
ya ce.
"Shi ya sa tun farko na ce babu ruwanka da ita, saboda ni na san aljanun jikinta ba sa nisa da
ita. Ina zaman zamana za ka rikita mini mata babu gaira babu dalili." Ɗanladi ya ƙarasa
maganar yana É—aukar 'Yar gwal ya shige É—aki da ita. Inno ta shiga share hawaye ta ce.
"Inusa yaushe É—an'uwanka ya yi lalacewar haka? Wai Inusa saboda ya mayar da mu ba komai
ba a wurinsa, har shi zai je wani wuri ya aurar da kan shi. Inusa ba za ku yi wani abu a kai ba?"
Yaya Inu da ya gama cika da mamaki ganin ƙiri-ƙiri 'Yar gwal ta raina musu hankali ya ce.
"Inno kin fi kowa sanin wane ne ÆŠanladi, tun da rayuwar da ya ga ta fiye masa ba sai ya yi ba."
Daga cikin É—akin ÆŠanladi ya ce.
"Inno yanzu auren da na yi ne ba za ki saka mini albarka ba? A da kuna yi mini ƙage, kuna
cewa ina lalubar yaran mutane a chemist É—ina. Amma yanzu kuma na yi auren ma ba za ku
sarara mini ba? Sunnar Annabin ce kuke ƙyashi na raya?"
'Haƙiƙa na lura duk balaja'un Inusa ashe shi shafar mai ne a kan wannan. Tirƙashi, wannan
ÆŠanladin ai ya gama tashin kaina.'
Mai Yasin ya raya a ransa.
Yaya Inu ya kamo hannun Inno ya furta.
"Mu je Inno, idan kika biye ta wannan yaron ranki ne zai yi ta ɓaci a banza. Yanzu mu je ciki ni
ba wannan ce damuwata ba, wani tashin hankali ne yake tafe da ni da na garara samun
nutsuwa."
Inno ba ta musa ba, ta bi bayan Yaya Inu suka shiga É—aki.
"Inno É—azu Abu ta zo, ta kawo mini jaririyar da ta haifa..."
"Amma dai wannan yarinya an yi marar mutumci, yanzu ita saboda rashin hankali daga
haihuwar yarinyar za ta É—auko ta kawo maka? A kanta aka fara mutuwar aure?"
Inno ta katse shi tun bai ƙarasa magana ba.
"Don Allah Inno ki bari na dire maganata."
Inno ta yi fakare tana jiran ya gama magana ta É—ora daga inda ta tsaya.
"An samu matsala domin yarinyar zabiya ce. Ni kuma gaskiya ina zargin ba 'yata ba ce,
saboda kowa shaida ne ban taɓa haihuwar zabiya ba."
A razane Inno ta ja da ba ya tun bai gama magana ba, ta fara dubansa da wani kallo sannan
ta ce.
"Kada ka raina mana hankali Inusa, batun ka ce 'ya ba ta ka bace ai bai taso ba. Saboda kowa
ya san ta yadda ake samun zabiya, sai da ka je ka gama saɓon Allah sannan za ka same ni
kana yi mini 'yar murya? Me zan iya yi maka a yanzu? Bayan Allah ya yi ikonsa, ai sai dai ka
É—auki na Annabawa. Ka je can kai da Zainabun ku yi ta istigifari kuna tuba ga Allah." Inno ta yi
maganar tana miƙewa, har za ta shige uwar ɗakinta ta waigo ta ce.
"Yawwa dama daga yanzu kada ka sake ka shigo mini. Saboda kada zunubin