Showing 96001 words to 99000 words out of 143522 words
Chapter 33 - DAHUWAR 'KAHO BOOK COMPLETE Hausa Novels By Ameera Adam.pdf
Bab Ibrahim a fusace ya ce, "Wallahi gaskiya ka faɗa, yadda kake sakin jiki kai da matan da
kake aura kana saki da ina da iko sai na farke ka na ƙone maka su kowa ya huta. Tun da
haihuwar kawai ka sani ba ka san jidalinsu ba."
A ɗan tsorace Baba Inu ya dafe ƙirji, yana bin Baba Ibrahim da wani irin kallo ya ce.
"Kai dai Iro an yi mai mugun hali, mugun bakinka ya faɗa kanka. Sai ja je ka yi ta fama da
'ya'ya huɗu, ni kam haihuwa yanzu na fara tun da ban san mai jin ƙaina ba."
Ganin Baba Inu bai ɗauki zugar Baba Ibrahim ba ya sa Mai maganin ya zuro kai ya ce.
"Ai mai gida shi ya sa a kullum idan za mu fito, muke addu'ar neman tsari miyagu irinsu masu
hana a yiwa bayin Allah ciniki." Takaici ya sa Baba Ibrahim ya shige cikin gida ba tare da ya
tanka musu ba. Saboda halin yayan nasa ba ƙaramin ɓata masa rai yake ba.
Baba Iro yana shirin yin magana daga soron gidan ya ji, gijif! Kwacakwar! Alamar ana jan kaya
a buhu. Baba Saleh ne ya fito da ƙaton buhun magungunansa, ganin motar mai magani a ƙofar
gidan ya sa ya murtuke fuska yana harare-harare cikin habaici ya fara waƙa.
Komai baƙin cikin tsololon ƙato.
Wallahi sai dai ya yi ƙototo.
Na zama kainuwa a wannan loto.
Ƙaryar mai baƙinciki ya ga bayana, har masu ƙin sayan maganina.
Yana gama faɗar haka ya fizgo ƙaton buhunsa da yake ja da ƙyar, sai ga shi bisa tsautsayi ya
fiszo da ƙafar bencin da Baba Inu yake kai. Bencin ya yi gaba shi kuma Baba Inu ya hantsila ta
baya ji kake darr ya yi zaman 'yan bori a ƙasa.
Kamar bai san da shi a wurin ba Baba Saleh ya saki buhun hannunsa yana rafka salati sannan
ya ce.
"Wai Yaya dama kana nan ƙofar gida? Ikon Allah sannu!"
Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin riƙo hannun Baba Inu, da sauri ya bige hannunsa rai a ɓace
ya ce.
"Wallahi duk baƙincikin mutum bai isa ya ga bayana ni Inusa don uban mutum! Haka zan daɗe
na yi ƙarko shekaru irin na dabino, sai na ga bayan maƙiyana. Kai mai magani, ungo dubu biyar
ka yi mini haɗin komai da ruwanka."
Baba Inu bai yi niyyar sayen maganin dubu biyar ba, amma don ya ɓa ta wa Baba Saleh rai ya
yi haka. Baba Saleh ya buga tsaki yana wurgawa mai maganin harara, ya nufi wata tsohuwar
motarsa da yake tallan magungunansa, ya buɗe ya tura buhun maganin da ke cike da jarkokin
magani sannan ya rufe.
Inna ce ta fito daga gida a fusace hannunta riƙe da Laraba, ta dubi Baba Inu bayan sun yi
sallama da mai maganin ta ce.
"Inu na gaji da cin kashin da ake yi mini a cikin garin nan."
Da mamaki Baba Inu ya dube ta ya ce, "Me aka yi miki Inno?"
"Ba ni aka yi ba Laraba aka yi wa, kuma duk wanda ya yi wa Laraba ni ya yi wa. Mai gari ne
yake son ganina da ita, wai Laraba ta tare Ɗahe ɗan gidan Sa'a mai ragadada ta cinye masa.
Saboda Allah ina Laraba za ta kai ragadada cikin ɗan bokiti ban da son zuciya?"
Jin haka ya sa Laraba ta juya gefe a fakaice ta sake suɗe hannunta da ya yi shanana da
miyar ragadada.
Baba Inu ya zuba mata ido ya ce, "Wallahi duk abin da aka ce mini wannan hatsabibiyar
yarinyar ta yi ba zan musa ba, shi ya sa tun da satin nan ya kama nake jiran shigowar Uwar
marayi garin nan. Wallahi babu abin da zai hana Laraba zuwa birni, ta je can ta yi aikatau ko na
huta da takaicinta. Ni duk cikin 'ya'yana babu sai siffar 'ya'yan aljanu irinta." Wani irin haushin Baba Inu ya kama Inno, sai kawai ta ja hannunta suka wuce wurin mai gari.
Tun daga nesa da aka hango Inno tafe da Laraba ƙananan maganganu suka fara tashi a fadar
mai gari. Sanƙira ne ya yi magana sannan kowa ya yi shiru. Da sallama Inno ta zauna a kan
tabarmar fuska a haɗe ta ce.
"Allah Ya taimake ka, na ji wai kana nemanmu ni da Laraba!"
Mai gari da tun da Laraba ta zauna yake bin ta da mugun kallo ya ce, "Wai ne ma Inno?"
Ya mayar da kallonsa wurin Laraba ya ce.
"Ke Laraba waye wannan?"
Laraba ta yi kicin-kicin da fuska tana duban Ɗahe kamar ba ta gane shi ba ta ce, "Ban san shi
ba, amma na ga yana yi mini kama da 'ya'yan Baraka mai hancin salansa."
Haushi ya sake cika Mai gari ganin irin rainin hankalin da Laraba ta yi masa. Ya sake nuna
Huwaila wacce ta kai ƙarar Laraba, a kan ta jefa mata bokiti da guga a cikin rijiya. Laraba ta
sake ƙanƙance ido ta ce.
"Wannan kam Lado ƙeya ne!"
Sai kuma Laraba ta washe baki ta ce, "Lado ƙeya dama ka dawo daga Legas?"
Haushi ne ya lulluɓe mai gari, mutanen wurin wasu suka fara dariya yayin da wasu kuma
haushin Laraba ya cika su, don kusan duka mutanen garin babu wanda ba shi da tabon ɓacin
ranta.
Tsam mai gari ya taso ya zo gaban Laraba, a tunaninta tambayarta zai yi sai ji ta yi ya zabga
mata gigitaccan mari, har sai da ta ga waɗansu taurari sun gilma mata. A razane Laraba ta dafe
kunci saboda marin ba ƙaramin zafi ya yi mata, amma sai ta basar don ba ta san ta kunyata
kanta a gaban mutanen garin. Ta sake basarwa ta sake ba shi irin amsar da ta ba shi da farko.
A wannan karon ma haushi ya sa Mai gari ya sake ɗauke fuskarta da mari, abinka da farar fata
lokaci ɗaya fuskarta ta yi jajir. Ganin haka ya sa ran Inno ya ɓaci ta dube shi a fusace ta ce.
"Wallahi Sama'ila ka kiyaye ni, jikata fa ba jaka ba ce..."
"Ai dama duk wani iskanci da yarinyar nan take yi ke ce kike ɗaure mata, wallahi mai gari sisina
ba zai yi ciwon kai ba sai an biya ni ragadadata. Har kayan miya da mahaɗi kusan dubu biyar
na kashe."
Sa'a mai ragadada ta faɗa a ƙufule.
Cikin tsoratarwa da burgagi Mai magari ya miƙe tsaye yana buɗa kafaɗu ya ce, "Inno tun da
haka kika ce, bari na aika ku birni wurin hukuma ta yanke mata hukunci. Kin ga idan aiƙali ya ji
irin tuhume-tuhumen da ake yi mata ƙila ma ya aikata gidan yari."
Jin haka ya kaɗa hantar cikin Inno, hankali a tashe ta zungoro Laraba ta ce.
"Ke Laraba ki yi magana."
Laraba ta yi wa Mai gari ƙuri tana yi masa kallon ba ka daki banza ba, har sai da cikinsa ya
kaɗa amma sai ya basar ya ce.
"Laraba kin tare Ɗahe kin cinye masa ragadada kin tula masa ƙasa a ciki, ita kuma Huwaila kin
jefa mata guga da bokita a rijiya yanzu da kin jefa ta ciki me za ki ce?"
Laraba ta wurga wa Huwaila harara ta ce, "Kai Lado ƙeya tun da ka dawo garin nan yaushe
muka haɗu da kai!"
Huwaila ta fashe da kuka cike da takaici ta ce, "Mai gari kana ji tana mayar da ni Lado, yanzu
Laraba ta rasa da wa za ta haɗa ni sai Lado ƙeya?"
Mai gari ya kalli Sanƙira yace ya tsinko masa itacen dalbejiya ya zuge masa ganyenta. Jikin
Sanƙira har rawa yake ya haye bishiyar da ke gefensu, ya fisgo manyan reshe ya zuge ya miƙa
wa mai gari. Kafiya da taurin kan Laraba ya sa ko gezau ba ta yi ba, duk da gabanta sai faɗuwa
yake yi.
Rai a ɓace Mai gari ya shiga rafta mata ta ko ina, mutanen wurin suka marmatsa don kar a
same su. Tun Laraba tana daurewa har dauriyarta ta ƙare ta fashe da kuka tana mutsu-mutsu.
Inno ban da kuka da kururwar neman taimako babu abin da take yi.
Yaran da suke zagaye da su ne suka fara tafi suna tsalle da waƙa, saboda tun da suke ba su
taɓa ganin abin da ya saka Laraba kuka ba.
Laraba mai kuka ye ye.
Ga majina da yawu ahayye.
Gobe ma ta ƙara ye ye.
Ku zo mu yi mata ɓarɓaɗan tusa a tsakar ka.
Idan suka kai baitin waƙar sai su ƙarasa su dunguro kan Laraba da ke shasshekar kuka.
Mai gari sai da ya gaji don kansa sannan ya koma kujerarsa cike da son nuna birgewa ya ce.
"Duk wanda ya sake aikata makamancin abin da Laraba ta yi, hukuncin da za mu yi masa
kenan. Ina Inno take?"
Cike da jin haushi a daƙile Inno ta ce, "Ga ni."
"Za ki biya Huwaila da Sa'a kuɗin ɓarnar da Laraba ta yi musu." Inno ta yi tsagal ta ce.
"Ai kuwa ba za ta saɓu ba, ya za a yi a daki yarinya sannan kuma na biya."
Mai gari zai yi magana suka ga Laraba ta miƙe zumbur! Kamar wacce aka yi wa allurar doki.
Don irin zaburar da ta yi ba ƙaramin tsoro ta ba shi ba, ba shi kaɗai ba, hatta ragowar mutanen
wurin sai da suka ja da baya.
Idanunta sun yi jawur saboda kuka, ta dube su ɗaya bayan ɗaya abinka da mai manyan idanu
sai suka sake fito. Ta fara takawa a hankali wurin saitin fuskokinsu, ta cigaba da kallonsu ɗaya
bayan ɗaya kamar wacce take haddace kamanni da sunayensu. Da ta je kan mai gari sai ta
matsa dab da shi ta gwalalo masa ido waje har sai da ta ja baya, sannan ta cigaba da kallon
mutanen gefensa Tana zuwa ƙarshe, sai kawai suka ga ta ɗiba a guje ta fice daga cikin fili ta
nausa daji, hankali a tashe Inno ta rufa mata baya tana faɗin.
"Laraba! Ke Laraba ina za ki je?"
Tun ba a je ko ina ba Laraba ta yi wa Inno nisa, ganin Inno za ta tafi ya sa Mai gari ya ce.
"Inno wai ni za ku yi wa dirama? Ke da Laraba wa ya ba ku ikon tashi daga wurin nan. Wallahi
ba don ina duba darajar marigayi Baffa babba ba, da ke da jikarki tuni na kore ku daga garin
nan."
Mai gari yana rufe baki, suka hango Laraba ta tunkaro wurinsu a guje, hannuwanta ɗauke da
wasu tafka-tafkan reshen bishiya. Ba ta yi wata-wata ba ta shiga tafka musu kan mai uwa da
wabi a haukace tana wani irin ƙaraji. Lokaci ɗaya wurin ya hautsine, Mai gari saboda tashin
hankali da rarrafe ya dinga tafiya, domin da farko da ya saka gudu sai da ya yi adungure sau
uku babbar rigarsa tana taɗe shi.
07062062624
Ummou Aslam Bint Adamí ¼í¼š
[04/12/2024, 15:03] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya
kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
SHAFI NA BIYU
Kamar wata fusatacciyar zakanya, haka Laraba ta cigaba da yin kan mutane tana fatka
musu itacen da yake hannunta. Ban da wani irin gurnani babu abin da take yi, Inno da ke raɓe a
can gefe jikinta ya shiga karkarwa saboda tsoro da tashin hankali. Don tun da take da Laraba
ba ta taɓa ganin ta yi irin haka ba, Sanƙira ta hango maƙale a gefen bishiya. Ta yi wani irin zullo
haɗe da ƙaraji ta tunkari wurinsa, kamar sabon marayan da ba shi da mafita. Haka Sanƙiran ya
saki wani marayan kuka zai fita da gudu, Laraba ta tuna yadda Sanƙira ya dinga zuge ganyen
bishiyar yana wurga mata harara sai kawai ya ɗaga hannu ta tafka masa itace a baya. Sanƙira
ya gantsare cikin azaba ya ce, "Wayyo Mai gari bayana wash! Wallahi wannan ba dukan
bil'adama ba ne."
Mai gari da babbar riga ta sarkafe shi yana rarrafe yana dungurawa ya ce, "Wallahi na ajiya
sarautar na damƙa maka yanzu kai ne mai garin."
Laraba ta saki murmushin ƙeta ta riƙo babbar rigar Sanƙira ta baya, suna gudu tana tafka
masa ice a baya. Ganin Larabar tana neman kai shi ƙasa, ya sa Sanƙira ya yi wani ƙaraji ya
dara gaban rigarsa gida biyu, da yake dama rigar ta kwana biyu nan take ta rabe biyu. Sanƙira
ya zuba a guje ya bar Laraba da babbar riga a hannu, filin wurin ya sake cakamewa da ƙurar
ƙasar da take tashi. Mai gari ya hango Laraba tana tunkaro shi, cikin tashin hankali ya zuba
kabbara kamar wanda yake filin jihadi. A wannan karon Allah Ya ba shi sa'a ya samu da ya
miƙe bai sake faɗuwa ba, gudun kada babbar za ta sake ba shi matsala ya sa ya tuɓe ta ya
wurgar. Ya taƙarƙare ya fita da gudu, takalmansa da hularsa sai tsalle suke yi suna tashi sama.
Laraba ta so ƙyale shi amma da ta tuna irin marin da ya zazzabga mata sai ita ma ta rufa masa
baya da gudu.
A lokacin da Mai gari ya ƙarasa gida, Salame matarsa ta rako Inna mahaifiyarta da ta zo duba
ta sakamakon rashin lafiyar da ta yi. Suna nan a soro ya shiga a guje, cikin neman maɓoya ya
fisgi hijabin jikin Inna ya yi gaba da ita. Cikin tashin hankali Inna ta fara ihu tana kiciniyar ƙwace
kanta, don Mai gari janta yake da gudu ga kanta ya cukwikwiye mata a cikin hijabi.
Ragowar mutanen gidan suna jin ihu daga waje, da suka ga a yadda mai gidansu ya shiga
yara da manya sai kowa ya nemi maɓoya. Laraba ce ta yi tsaye tana wani gurnani, ta ga tsakar
gidan kowa ya fashe sai wani ɗan ƙaramin yaro da bai fi shekara biyu da rabi zaune a kan fo.
Irin kallon da Laraba take yi masa tana gwalo ido, ga zungureren itacen da ya gani ya sa yaron
ya miƙe a zabure yana ihu ya shige ɗakin mahaifiyarta.
Tun da Mai gari ya fisgi hijabin Inna, ba shi ya tsaya a ko ina ba sai a uwar ɗakin Salame a
can ƙarƙashim gadon ƙarfenta. Ya shiga sauke numfashi da ƙyar yana muzurai, hannunsa ya
kai wurin wandonsa ya ji ya yi sharkaf. Jiki yana karkarwa ya zura kansa cikin hijabin Inna ya
ce.
"Salame ina jin fa gudawa na yi, wallahi har yanzu ji nake abu yana tsiyaya a jikina kamar an
kunna fanfo."
Inna da kunya, haushi da baƙincikin Mai gari suka cika ta murya a dakushe ta ce.
"Ai kana da hannu ko?Sai ka yi ƙoƙari ka kashe fanfon."
A razane Mai gari ya ɗago, sai a lokacin idanunsa suka sauka a kan fuskar sirikarsa. Ya fito
daga ƙarƙashin gadon a guje, yana zuro kai ya ga Laraba ta ƙwalla wata irin ƙara ta yanke jiki ta
faɗi. Daga Mai gari har ragowar mutanen garin da suke leƙowa tsaye suka yi suna kallonta, aka
rasa wanda zai tunkare ta ballantana ya yi yunƙurin tashinta. Laraba ta ɗan jima a haka sai
kuma ta fara buɗe idonta a hankali tana salati, tashi ta yi zaune tana kalle-kalle kamar mai
neman wani abu ta ce, "Kai, waye ya kawo ni nan?"
Shiru gabaɗaya suka yi mata, ta tunkari wurin mai gari a ɗan razane ta ce.
"Mai gari me nake yi a nan?"
Baki yana rawa Mai gari ya ce, "Ni ma tambayar da nake son yi miki kenan, amma yanzu ki
fara zuwa gida tukunna."
Laraba ta saki murmushi a fakaici ganin yadda duk ya birkice, sannan ta fito ta nufi hanyar
gida. Kamar sun ga sabuwar hallita haka mutane suka dinga bin Laraba da kallo, ita kuwa ta
maze tana tafe tana hura hanci tana buɗa kafaɗa har ta je gida.
Baba Inu yana shiga gida kai tsaye ɓangarensa ya nufa, tun daga bakin ƙofa ya tsaya ya yi
gyaran murya yana haɗe fuska, lokaci ɗaya yaran suka fara shiga taitayinsu. Iyayensu kuma
suka shiga tsawatarwa 'yan ƙananun da ba su yi wayo ba.
Larai ce da girki ranar, a tsakiyar gida ta ajiye tukunyar abincin rana sai ƙanana da manyan
kwanuka birjik a gabanta. Waɗansu ƙananan yara ne kusan su huɗu waɗanda ba su wuce
shekara ɗaya zuwa da rabi ba, biyunsu riƙe suke da kwanuka suna kukan yunwa suna kama
zanin Larai.
"Gaskiya Indo ba kwa kyauta mini, da wanne zan ji? Da aikin abinci ko da waɗannan yaran. Ke
Kulu zo ki janye mini su don