Showing 6001 words to 9000 words out of 143522 words
Chapter 3 - DAHUWAR 'KAHO BOOK COMPLETE Hausa Novels By Ameera Adam.pdf
shiga ba tanan yake fita ba. Daga ƙarshe ya ɗora da cewa.
"Kuma ki buÉ—e kunnenki da kyau ki saurare ni, wallahi koda wasa na kuma jin kin aikata
makamancin wannan haukar ni da ke ne. Idan kuma kika kuskura kika ƙure yaron nan har ya
sake ki, wallahi sai kin fi jin daÉ—in zaman gidan yari a kan gidana. Allah Ya gafartawa
mahaifiyarki, ke dai albasa ba ta yi halin ruwa ba. Lokacin da zan ƙara aure mahafiyarku ce ta
tara mini kayan lefe, kuma har ta rasu ba ta taɓa aikata mini wani abin ɓacin rai saboda kishi
ba. Shashasha sakarai marar tunani." Baba yana gama faÉ—a Yaya Salis ya É—ora, haka Bilkisu ta
dinga share hawaye har suka gama suka tafi.
Tun daga wannan ranar Bilkisu ba ta sake yinƙurin cutar da Hafiz ba, sai dai kala-kalan ruwan
rashin mutumcin da take zabga masa. Don kusan a wannan lokacin ta daina girki da shi,
tsakaninsa da ita sai ɓacin rai da baƙar magana. Idan ya zo neman haƙƙinsa wurinta haka za ta
gasa masa maganganu ta juya masa baya. Ire-iren abubuwan da Bilkisu take yi bai tsaya iya
kansa ba, har sai da ya shafi danginsa. Domin duk wanda ya je gidanta, matuƙar daga
ɓangarensa ne ko karɓar kirki ba ta yi musu, ko ruwa ba ta ba su haka suke karkaɗe
ƙafafuwansu su tafi. Gabaɗaya Bilkisu kallon munafukai take yi wa dangin Hafiz, don haka su
ma suka janye jikinsu daga wurinta.
Duk wani shige da fice da Bilkisu za ta yi don ta san yarinyar da Hafiz ya aura ta yi, sai dai har
lokacin ba ta samu ba. Watarana da daddare, kimanin biyun dare. Ta jango wayar Hafiz, ganin
password a jiki ya sa jikinta ya yi sanyi, wani tunani ne ya faÉ—o mata. Da sauri ta shiga gwada
sunayen yaranta bai yi ba, sai ta gwada sunansa ta samu wayar ya buÉ—e. Whatsapp É—insa ta
shiga, a nan ta fara cin karo da lambar Amina da irin zafafan kalaman soyayyar da suke yi wa
junansu.
Da farko É—aukar lambar ta yi za ta kira ta zagi Amina, sai kuma wani tunani ya faÉ—o mata. Cikin
sauri hannunta yana rawa ta rubuta.
_Ni Hafiz Adam, na saki Amina saki É—aya, na sake ta saki biyu na sake ta har saki uku.
Sakamakon saɓanin da nake samu da matata saboda na aure ki, domin ba zan iya ɓata wa
matata rai ba._
Bayan saƙon ya tafi sai ta goge saƙon daga kan wayar, sannan ta ajiye masa wayar a gefensa
ta koma ta kwanta tana jin zuciyarta fes.
Ummou Aslam Bint Adamí ¼í¼š
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko
É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma,
don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka
arashi ne.
https://chat.whatsapp.com/IAZVt2Pz4LvIcklCxSTHwo
SHAFI NA UKU
Lokacin da Hafiz ya tashi zai yi sallar asuba misscall É—in Amina ya gani rubutu, yake ya ji
masallaci sun shiga da sauri ya zura wayar a aljihu ya nufi masallacin saboda tuni ya yi alwala.
Ana idar da sallah ya fito daga masallacin, ya ciro wayar a nan ya sake cin karo da wani kiran
nata. Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, hannu yana rawa ya ɗauki wayar yana faɗin.
"Salamu alaikum, Amina."
Kuka ya ji ta fashe da shi, hakan ya sake É—aga hankalinsa. Jikinsa yana rawa ya sake cewa,
"Amina me yake faruwa a gidan ne? Lafiya kike kuka?" Daga can ɓangaren Amina ta sauke
ajiyar zuciya murya a dashe saboda kukan da ta sha ta ce.
"Tambayata ma kake yi Hafiz? Tambaya kake yi me ya faru? Dama ka so cin mutumcina ne
shi ya sa ka zo gidanmu neman aurena?" Da mamaki ya É—ago wayar yana bin lambar da kallo
don sake tabbatar da wacce take magana, cikin rashin fahimtar zancanta ya ce.
"Amina wai me kike faÉ—a ne? Kin san wa kika kira kuwa?"
"Kana nufin na fara hauka ne Hafiz? Ko ka É—auka ina shaye-shaye ne?" Ita ma ta faÉ—a a É—an
fusace. Shiru ya yi yana nazari, don ya san Amina sarai mace ce mai haƙuri. Tun da suke tare
ba ta taɓa faɗa masa makamantan irin maganganun nan ba. Gwaron numfashi ya sauke cikin
tausasa murya ya ce, "Don Allah Amina ki yi mini bayani ban san me yake faruwa ba." Wani takaicin ne ya sake rufe Amina, cikin gatse ta ce.
"Kana nufin har ka manta sakin wulaƙancin da ka yi mini, saboda matarka ta fi ni a wurinka
don kuna samun saɓani shi ne za ka sake ni? AlhamduLillah tun da har na fahimci matarka ta fi
ƙarfinka, na gode ka aiko gidanmu a karɓar maka sadakinka." Daga haka Amina ta katse wayar.
Wani irin gumi ne ya lulluɓe Hafiz, da sauri ya jingina da bango sakamakon jin da ya yi juwa
tana yunƙurin taɗe ƙafafuwansa.
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un." Ya furta a fili, sannan ya zura wayarsa a aljihu. Da sauri ya
nufi gida, ya shiga kiciniyar fito da mashin É—insa waje. Yana rufe gidan ya hau mashin É—insa, kai
tsaye ya wuce unguwarsu Amina.
Yana zuwa ƙofar gidan ya ciro wayarsa ya yi mata kiran duniya ta ƙi ɗauka, ƙwanƙwasa ƙofar
gidan ya fara yi a rikice. Don kallo É—aya za ka yi masa ka fahimci yana cikin damuwa. Mahaifinta
ne ya buɗe ƙofar ya fito, cikin girmamawa Hafiz ya tsugunna ya gaida shi sai kuma ya yi shiru
ya ma rasa ta ina zai fara yin magana.
"Hafiz dama na so kiranka da kaina zuwa an jima. Amma na ji daÉ—i da Allah Ya kawo ka
yanzu."
Da sauri Hafiz ya É—ago ya ce. "Baba lafiya kuwa? Dama... dama na ji Amina tana ta wasu
maganganu." Mamaki ne ya kama Baba, sai ya ce.
"Shigo É—akina, wannan ba maganar tsaiwa ba ce."
Baba ya furta yana shiga ciki, kamar zakaran da ya bi ta mahauta haka Hafiz ya bi bayan Baba
jiki a sanyaye. Yana nan zaune a É—aki Amina da Baba suka yi sallama suka shiga, wayar Amina
ya karɓa ya nuna masa ya ce.
"Da asubar nan Amina ta nuna mini saƙon da ka turo mata cikin dare." Hafiz yana gama
karanta saƙon ya ce.
"Wallahi Baba ban san yadda aka yi ba, wallahi ba ni na rubuto mata wannan saƙon ba. Tun
da ko a daren jiya lafiya ƙalau muka gama waya da ita." Hafiz ya yi jim, ya ɗago da sauri ya ce.
"Sai dai idan matata ce, babu tantama wallahi sai dai idan ita ce Baba." Shiru Baba ya yi yana
nazari, ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"To a gaskiya idan har haka ne sai ka tashi tsaye Hafiz, don ba na son duk wani abu da zai sa
a dinga tashin hankali. Haka kuma wannan maganar ba za mu bar ta daga mu sai kai ba, dole
ne ka kirawo manyanka a yi magana. Ita ma ya zama wajibi ka tsawatar mata, ka kuma kiyaye
haƙoƙinta. Don za ka yi aure ba shi zai sa ka wulaƙanta matarka ba, ko ka dinga cin fuskarta
kana cin zarafinta. Ka ji tsoron Allah Hafiz, wallahi idan ka cuci 'yar mutane Allah ba zai bar ka
ba." Cikin girmamawa Hafiz ya russuna ya ce.
"In Shaa Allahu Baba."
Miƙewa Baba ya yi ya fita, har Amina za ta fita cikin sauri Hafiz ya ƙarasa ya riƙo ta. Rungumo
ta ya yi jikinsa ya haÉ—a ta da bango ya ce.
"Kina tunanin akwai ranar da zan iya rabuwa da ke ne?"
A ɗan shagwaɓe Amina ta ce, "Na sani tun da tsoron matarka kake ji." Sunkuyawa ya yi ya
sakarwa bakinta kiss ya ce, "Haka kike gani Meena, amma babu wani tsoro. Kin san duk macen
da za a ƙara wa abokiyar zama dole a lallaɓa ta, musamman Bilkisu da take da kishi." Janye
jikinta za ta yi ya sake matse ta ya ce. "Me ya sa kike guduna ne?"
"To ni kada wani ya ganmu a haka." Ta ba shi amsa a sanyaye, zuba mata ido ya yi yana jin
sonta na fisgarsa. Cikin wani irin yanayi ya ce, "Ai ba wamda zai shigo tun da kowa ya san ke
matata ce, ba ki ga ma Baba ya ba mu wuri ba."
Zaro ido ta yi tana rufe baki ta ce, "To wallahi ni tafiya zan yi, wato duk kallon haka suke yi
mini?"
Gyaɗa mata kai ya yi ya tallafo fuskarsa da hannu biyu ya ce, "Ina ƙaunarki Meena, na yi
mamaki da har kika yarda zan iya rabuwa da ke." Tura baki gaba ya ta yi cikin jin nauyinsa,
Hafiz lumshe ido ya ce.
"In Shaa Allah nan da sati biyu za a kawo kaya, sai a yi wunin biki a wuce wurin don haƙurina
ya fara ƙarewa." Sunkuyar da kai ƙasa ta yi cikin jin kunya, ya sunkuya saitin kunnenta ya yi
mata raÉ—a a kunne. Da sauri ta É—ago tana rufe ido cikin jin kunya ta ce.
"Allah Ya shirye ka, ni wallahi ba haka nake ba. Don Allah babu abin da ya dame ni."
"Ai shi ya sa na ga ba kya hana ni idan ina..."
Da sauri Amina ta saka hannu ta rufe masa baki, sai kuma ta ce.
"Ka zo ka tafi ka bar Madam tun da farar safiya." Cikin kwaikwayon muryarta ya ce.
"To duk ba ita ta ja komai ba."
Dariya Amina ta yi ta ce, "Allah Ya shirya ka Hubby."
Har ƙofar gida Amina ta raka shi tana jin soyayyar Hafiz a cikin ranta. Duk da ta ji zafin abin da
Bilkisu ta yi, ta wani ɓangaren tana yi mata uzuri, saboda ba kowacce mace ce take danne
zuciyarta ba idan za a yi mata kishiya.
Hafiz yana zuwa gida ya samu Bilkisu tana yi wa yara shirin makaranta, kallo É—aya ta yi masa ta
É—auke kanta. Haka shi ma bai kula ta ba ya zauna har yara suka gama cin abinci, ya É—auke su
ya kai su makaranta. Lokacin da ya koma tana kwance a kan gado, a gefenta ya zauna ya ce.
"Bilkisu ki tashi za mu yi magana da ke."
Ɗagowa ta yi ta kalle shi a sheƙe ta ce.
"FaÉ—i maganarka ai kunne ne yake ji."
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Bilkisu kin san ina sonki ina ƙaunarki, kuma kin san babu macen
da zan kawo na bari ta raina ki, ko ta ci mutumcinki. Kin san ba zan É—auki haka ba, duk abin da
kike wa 'yan uwana ina sane, amma duk da haka ban bari ɗaya daga cikin ƙannena sun raina
ki..."
"Don Allah idan ba wata magana mai muhimmanci za ka faɗa mini ba ka ƙyale ni." Bilkisu ta
faɗa rai a ɓace. Girgiza kai ya yi yana danne ɓacin ransa ya ce.
"Muhimmancinta ne ya sa na same ki da maganar. Bilkisu yanzu ba ki ji kunyar saƙon da kika
turawa Amina a matsayin ni ba ne? Ko kin É—auka aure wasan yara ne da za ki yi wannan
shirmen? Don Allah ki kama girmanki Bilkisu, ina respecting É—inki a wurin Amina. Don haka ita
ma ko da wasa, ba ta taɓa kawo maganar wargi a kanki ba, ina girmamaki fiye da yadda kike
tsammani. Ki girmama kanki ta yadda ba za ki bada ƙofar da yarinyar nan za ta raina ki ba, ni
idan kin yi mini zan iya shanyewa. Amma kin san ba lalle ne ita idan kin yi mata wani abin ta
ɗaga miki ƙafa ba..."
"To duk abin da za ka saka ta yi mana, wallahi duk shegiyar da ta kawo mini raini sai na yi
mata dakan sakwara." Bilkisu ta faÉ—a tana tashi zaune. A É—an zafafe Hafiz ya ce, "Kada ki sake
zagar mini mata."
Bilkisu ji ta yi kamar ya watsa mata ruwan zafi, don haka a zafefe ta ce.
"Na zaga idan ka ga dama ka rama mata, 'yan iskan 'yan mata ba za su nemi mijinsu su aura
ba sai mace ta raini mijinta su zo su aure suna tunƙahon mijinsu ne." Jin ba zai iya ɗaukar
maganganun da Bilkisu take faÉ—a ba, ya sa shi ficewa daga É—akin ya nufi É—akin yaran ya kwanta
a can.
Kamar yadda Hafiz ya faɗa cikin ƙasa da sati biyu ya ƙarasa haɗa duk wani abu da ake buƙata
na lefe, juma'a tana zuwa aka kai kaya gidansu Amina. A nan su kuma iyayenta suka tsayar da
ranar juma'a mai zuwa, a matsayin ranar da za a yi wuni da kai amarya. Hafiz ya yi ƙoƙari sosai,
akwati biyar ya yi mata daidai rufin asirinsa. Ya ba ta kuÉ—in kamu da gyaran jiki don shi ba shi
da ra'ayin zuwa wurin kamu. Haka ita ma Bilkisu akwati guda ya cika mata da kaya, dangin
atamfofi da lesuna da kayan shafe-shafe har da kayan bacci. Yaran kuma ya saya musu
sababbin ƙananan kaya kala ɗaiɗai da shadda kala bibbiyu.
A cikin satin Hafiz ya sa aka fitar da kujerun Bilkisu aka kai wurin kafinta ya gyara mata su, aka
saka sababbin sosuna da sababbin yadi suka dawo kamar sababbi. Sai labulaye da ya saya
mata masu yanayi da kujerunta duk don ya faranta mata. Sannan ya ba ta dubu hamsim ya ce
ta yi duk wani gyara da za ta yi dangin kitso da ƙunshi. Ana saura kwana biyu Amina za ta tare
ya kira masu fenti suka yi wa gidan fenti, sai dai jere ne ya hana 'yan uwan Amina su yi a ranar
saboda yana tsoron kada Bilkisu ta aikata abin da za ta kunya shi a wurinsu.
Ranar juma'a tun da sassafe 'yan uwan Amina suka je gidan Hafiz yin jere, kallo É—aya suka yi
wa Bilkisu suka fahimci zai yi wuya a yi zaman lafiya da ita a cikin gida. Don haka suka dinga
kaffa-kaffa, gudun kada ta ce sun yi mata wani abin. Saboda sun ji sai faÉ—a take yi wa yara da
habaici, kuma abu kaÉ—an yaro zai yi mata sai su ji ta rufe shi da duka. Kusan azahar suna ta
aiki sai ga Fadila ƙanwar Hafiz, ta yi sallama cikin gidan hannunta ɗauke da ƙatuwar cooler. A
ƙofar ɗakin Amina ta tsaya suka gaisa da masu jere, ta miƙa musu abincin ta yi musu bayanin
kanta. Ta sake fita ta shigo da ruwa da manyan lemuka ta ajiye musu, sannan ta nufi É—akin
Bilkisu.
Tun da Fadila ta shigo Bilkisu ta hango ta, ta cikin labule. Ta dubi ƙanwarta Hafsa ta ce.
"Hmmm dangin miji ko baƙaƙen munafukai, dubi Fadila can ki ga. Wai ita aka aiko ta kawo
musu abinci, saboda neman wurin zama. Wai yanzu duk yadda nake da su Fadila, haka za su yi
mini su koma ɓangaren amarya." Bilkisu ta ƙarasa maganar cikin ƙwafa.
Ajiyar zuciya Hafsa ta sauke ta ce, "To ya za ki yi ai sai haƙuri, kin san mijinki ne fa ɗan'uwansu.
Kuma duk abin da yake so shi za su so, tun da ke dai bare ce a cikinsu." Shiru Bilkisu ta yi ta
cigaba da girgiza ƙafa, suna nan zaune Fadila ta shiga ɗakin da murmushi bakinta ɗauke ta
sallama.
"Ina wuni Aunty Bilkisu." Fadila ta faɗa cikin girmamawa, tun daga ƙasa Bilkisu ta ɗebo Fadila
da harara ta watsar a gwasale ta ce.
"Lafiya."
Shiru Fadila ta yi tana tsaye, don ba ta ga fuskar da za ta zauna ba. Bilkisu ta ce, "To ai sai ki
koma can tun da wurinsu kika zo."
"A'a abinci ne kawai na kawo musu." Fadila ta faÉ—a a sanyaye. Kamar Bilkisu tana jira ta ce.
"Ai shi ne na ce ki koma can, tun da ni matar yayanki ce waccan É—inma da za ki wurin matarsa
ce." Fadila ba ta tanka wa Bilkisu ba ta fice daga É—aki ta yi wa 'yan'uwan Amina sallama ta tafi.
"Haba Aunty Bilkisu, ki dinga rage wani abin mana. Wai ba ki ga yadda Aunty Murja ta yi ba
ne, kowacce mace fa tana jin kishi kawai iya taku ne." Hafsa ta furta, don ta lura idon yayarta ba
ƙaramin rufewa ya yi ba. Cikin masifa ta ce .
"Ita daban ni daban, malama kema idan ɓata mini rai za ki yi ki fice ki ba ni wuri." Hafsa ta yi
shiru tana mamakin zafin ran 'yar uwarta.
Koda 'yan uwan Amina suka gama jere ba duka suka tafi ba, sai aka bar mutum biyu a É—akin
da yayarta da kuma ƙanwar babanta. Suna gani Bilkisu shiga ɗaya-biyu idan ta yi sai ta yi musu
habaici, ko ta saki tsaki tana harararsu. Sai da aka idar da sallar Magriba, sannan Hafiz ya aika
aka É—auko Amina zuwa gidansa.
GIDAN ALHAJI UMAR
Tun ranar da Shukura ta cika kwana shida a gidan Hajiya