Showing 24001 words to 27000 words out of 143522 words
Chapter 9 - DAHUWAR 'KAHO BOOK COMPLETE Hausa Novels By Ameera Adam.pdf
keɓe a wani wurin idan ina da buƙatarta? Wai yaushe kika sauya ne
Karima? Girmai-girmai da ke ki zauna kina kishi da 'yar cikinki? Me Shukura ta tsare miki ne a
gidan nan? Wallahi idan ma baƙinciki kike yi da cikin jikinta, to In Shaa Allahu za ta haife shi
lafiya."
Alhaji Ya furta kalamansa rai a ɓace, kasa daurewa Hajiya ta yi ta ce.
"Wai Alhaji me kake nufi ne? Saboda kawai na tambayi a inda ka kwana? To Allah Ya ba ka
haƙuri, amma ka sani wallahi ko kaɗan ba na baƙinciki da abin da Shukura za ta haifa."
"Idan ma kina yi sai dai mugun halinki ya faÉ—a kanki, sannan magana ta gaba da zan faÉ—a miki
a kan wancan kiwon kajin da kike yi ne. Na gaji da ganin ana ɓa ta mini gida, kuma ba zan juri
É—aukar matar aurena ina yawon hotel da ita ba. Na ba ki daga yau zuwa gobe ki kwashe mini
duk wani abu da ya danganci kiwon kaji, ko buhun dusa É—aya ba na son sake gani." A hargitse Mommy ta dube shi ta ce.
"Au ta nan kuma ka ɓullo, ai sai ya yanzu na gano inda maganarka ta dosa. Kaji ba yau na
fara kiwo ba, kuma wata ba ta isa a saka na fitar da su ba. Idan ba haka ba sai na bar maka
gidanka."
Kamar Alhaji yana jira ya ce, "To ki tafi mana, idan haka kika zaɓa ai ƙofa a buɗe take ban riƙe
ki ba." A razane Hajiya Karima ta zaro ido ta ce.
"Ni kake cewa na tafi Alhaji?"
"Ƙwarai kuwa, idan har haka kika zaɓa kina iya kwashe 'ya'yanki ku tafi."
Yana gama maganar ya fita daga É—akin. A sanyaye ta zauna a bakin gado, kawai sai ta fashe
da kuka. Tana cikin wannan yanayin su Ruƙayya suka yi sallama cikin ɗakin hankali a tashe.
Cikin damuwa Haidar ya ce.
"Mommy wai lafiyar Daddy kuwa? Muna yi masa magana kin ga yadda ya hankaÉ—e Mami har
ta faɗi ƙasa kuwa? Kuma bai tsaya ba ya fice daga gidan..." Maganarsa ce ta maƙale ganin
mahaifiyarsu tana zubar da hawaye, da sauri suka ƙarasa cikin damuwa suka ce.
"Mommy mai ya faru kike kuka? Ko Daddy ne?" Sai da Hajiya Karima ta share hawayenta
sannan ta ce.
"Daddynku yana buƙatar addu'arku Haidar, saboda jikina yana ba ni kamar ba ya cikin
hayyacinsa. Yanzu haka kaji can ya ce a fita da su, ba ya buƙatar abin kiwo ɗaya a gidan nan."
"A fita da su?"
Suka tambaya kusan lokaci ɗaya, gyaɗa musu kai ta yi. Ruƙayya ta yi murmushin takaici ta ce.
"Wallahi ba kowa ba ce sai annamimiyar yarinyar nan, hmmm amma a wannan karon ta yi
ƙarya don uwarta. Wallahi ba za a fita da su ba."
Waya Hajiya ta ɗauko ta ce, "Ku fita zan kira Alhaji Gambo." Damuwa lulluɓe a fuskarsu suka
tashi suka fita, suna jin tsananin tsanar Shukura a ransu. Saboda tun da suka yi wayo, ba su
taɓa ganin mahaifiyarsu tana kuka saboda ɓacin ran mahaifinsu ba.
Alhaji Gambo aminin Daddy ne, garinsu É—aya da shi. Kuma duk gwagwarmayar rayuwa kusan
tare suka yi, kowa ya san sirrin kowa. Kuma duka su biyun suna ba wa junansu shawarwari,
haka idan wata matsala ta iyali ce. Matar wannan tana iya kiran wannan ta yi masa ƙorafi domin
a gyara. Hajiya Karima kiransa ta yi, bayan sun gaisa take sanar da shi duk abin da ya faru. Ko
kaÉ—an bai ji daÉ—i ba, don dama tun da Alhaji ya É—auko maganar auren Shukura, da ya bincika ya
ji yanayin tarbiyyar gidansu Shukura sam auren bai kwanta masa ba. Don kafin a yi ya sha ba
shi shawara, a kan ya haƙura da ita ya nemi wata. Haƙuri ya ba ta sosai, sannan ya ce ta bari
zuwa dare zai zo gidan domin su tattauna gabaÉ—aya.
Tun da suka gama Alhaji Gambo ya kira Daddy, ya ce masa zai shigo bayan sallar magriba. A
yanayin muryar Daddy da ya ji sam kamar bai yi murna da zuwansa ba, ya yi mamaki matuƙa.
Saboda koda a fushi yake bai cika nuna masa fushinsa ba.
Bayan sallar Isha'i, Alhaji Gambo ne ya yi fakin a ƙofar gidan Daddy. Waya ya ciro ya kira shi
ya sanar da shi, babu jimawa Daddy ya fita suka suka gaisa babu yabo babu fallasa sannan
suka shiga. A falonsa na saukar baƙi suka zauna, Alhaji Gambo ya dube shi ya ce.
"Wata magana ce fa tafe da ni, É—azu Hajiya Karima ta kira ni. Amma kafin nan ka kira ta
tukunna sai mu tatattauma gabaÉ—aya."
Nan take Daddy ya haÉ—e fuska ya ce.
"Dole sai ta zo? Duk abin da za mu faÉ—a mu yi mana." Shiru Alhaji Gambo ya yi, ya É—an haÉ—e
fuska ya ce.
"Ka ga malam ka kira ta mu yi magana, ka san ni dai ba baƙon gidan nan ba ne. Idan ba za ka
kira ta ba, zan leƙa na ce su Haidar su yi mata magana." Guntun tsaki Daddy ya yi ya fice,
bayan wani lokaci sai ga shi sun dawo yana gaba Hajiya Karima tana biye da shi.
Gaisawa suka fara yi, sannan Alhaji Gambo ya wassafa duk maganar da suka yi da ita,
sannan ya É—ora da cewa.
"A gaskiya ka ba ni mamaki Alhaji Umaru, yanzu kai ko wani ne ka ji zai yi wa iyalinsa haka ba
za ka tsawatar masa ba?"
"Dakata Gambo don Allah, wannan sabgar iyalina ce. Ban ce ka tsoma bakinka a ciki ba,
wallahi sai ta fitar da kajin nan tun da Shukura ba ta son warinsu. Idan kuma rabuwarmu ta
zaɓa, a yanzu sai na rubuta mata takardarta ta kama gabanta." Yana gama maganar ya wuce
fuu har zai fita, sai ya sake waigowa ya ce. "Kuma daga yau babu kai babu sake shiga duk wata magana ta iyalina, kai ma idan har ka ce
za ka bi wani ra'ayin ba na Shukura ba, a shirye nake da na datse duk wata alaƙa da ke
tsakanina da kai." Daga haka ya saka kai ya fice.
Daga Mommy har Alhaji Gambo jikinsu ba ƙaramin sanyi ya yi ba, saboda ɓacin rai sai kawai
ta fashe da kuka.
GIDAN HAFIZ
"Za ki buɗe baki ki yi mini magana, ko sai ranki ya ɓaci?"
Hafiz ya buga wa Amina tsawa a zafafe, hawaye ta shiga yi baki yana rawa ta ce.
"Wallahi... ban... san yadda aka yi ba, wallahi ban san komai game da wannan layar ba."
Furzar da iska mai zafi Hafiz ya yi, zuciyarsa tana tafasa ya matsa kusa da ita kamar zai tsinka
mata mari. Da sauri Amina ta ja da baya cikin matsanaacin tsoro, don ta gama saddaƙar da
Hafiz hannu zai kai jikinta. Rai a ɓace ya nuna ta da yatsa ya ce.
"Uwargidana, kuma uwar 'ya'ya ko hanyar gidan malamai ba ta sani ba, haka kawai ina
zamana lafiya da matata za ki haukata mini ita. Shi ya sa kullum take yin abu kamar na mai
shafar aljanu, ki buÉ—e kunnenki da kyau ki saurare ni. Wallahi idan na sake ganin makamancin
wannan shirmen sai ranki ya yi mugun ɓaci. Saboda mugun hali ki zo ki samu mace a ɗakinta
kina ƙoƙarin illatata, ba zan juri ki zo ki hargitsa mini gida ba."
Hafiz ya juya ya fita, kai tsaye kicin ya shiga ya ɗauko ashana ya fita da layar ya ƙona a waje.
Duk abin da yake faruwa Bikisu tana daga É—aki tana ji, zuciyarta fes don haka ta cigaba da
harkokinta hankali kwance.
Tun daga wannan ranar Bilkisu ta warware tas, ta daina duk wani makircin nesanta kanta da
Hafiz. Wannan ya sake tabbatar wa da Hafiz zarginsa na Amina ce ta yi wa Bilkisu asiri, dalilin
haka ya ƙara tsaurara tsattsamar alaƙa tsakaninsa da Amina. Suka koma irin zaman cin
kunamar ƙadangare, don Amina wani haushin Hafiz take ji a kan abin da ya yi mata. Shi ma
kuma haushinta yake ji, don haka ya koma kwanan falo. A kullum idan a É—akinta yake zai É—auko
filo ya fito falo ya kwanta, saboda idan ya kwanta a kan gadon ma sai dai Amina ta juya masa
baya.
A wannan kwanakin Bilkisu sai nannan take da Hafiz kamar ta haÉ—iye shi, haka shi ma yake
ba ta kulawa; saboda yadda ya ga ta saki jiki da shi saɓanin tun lokacin da ya auri Amina.
Watarana Hafiz yana É—akin Amina, har ya yi shirin zuwa kasuwa sai ya shiga É—akin Bilkisu don
ya yi mata sallama. Yana shiga bisa tsautsayi hannunta da manja ya kife masa a gaban riga, a
kan dole ya shiga uwar É—akinta ya cire kayan jikinsa ya É—aura towel. Da yake Bilkisu ta É—ora
ruwan wanka, sai ta ce bari ta juye masa ya sake yin wanka tun da duk jikinsa ya ɓaci. Sai da
Bilkisu ta shiga uwar É—aki ta É—auro zani, sannan ta je ta juye masa ruwan a banÉ—aki. Hafiz ne ya
shiga banÉ—aki cikin sauri, saboda ya yi rana bai fita da wuri ba. Bilkisu tana ganin haka ta yi
zaraf ta fito tsakar gida, sai da ta je bakin ƙofar ɗakin Amina ta yi ƙasa da murya yadda Hafiz ba
zai ji ba ta ce.
"Ban da abin Abban Sayyid ka ce ba ka gajiya da ni saboda Allah, tun da dai ba kwanana ba
ne ai sai ka bari sai ka dawo nan É—in tun da ba guduwa zan yi ba. Ga shi haka kawai za ka saka
ni jiƙa kaina ban shirya ba." Da ta tabbatar da Amina ta ji abin da ta faɗa, sai ta ce.
"Koda yake bari na zo na taya ka, tun da shi ma sunna ne."
Ta nufi ƙofar banɗakin tana gimtse dariyar mugunta, tana zuwa cikin sanɗa ta tsaya a ƙofar
banÉ—akin. Saboda ta san ko kaÉ—an Hafiz ba zai bari ta shiga su yi wanka tare ba, tun da ba
ranar girkinta ba ne. Tana jin motsin zai fito ta ce.
"Idan ka gama Abban Sayyid ba ni bokitin ni ma zan yi wanka."Ajiye mata ya yi, sai ya wuce ya
shiga É—akin Amina ya sauya kaya ba tare da ya tanka mata ba. Tana ganin ya saka wasu kayan
ya fita, ta shiga uwar É—aki ta fashe da kuka. Sai da ta yi mai isarta sannan ta share hawayenta,
ta kwanta tana jin gabaÉ—aya zaman gidan ya ishe ta. Uwa-uba ga laulayin da take fama da shi,
don a wannan lokacin ko abincin kirki ba ta ci.
Bilkisu tana fitowa daga wanka ta shige É—aki, sai da ta shirya tsaf sannan ta É—auko wayarta ta
kira Lami mai wanki. Tana ji an ɗauka ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Yawwa Lami na haÉ—a kayan wankin namu, ki aiko yaro ya zo ya É—auka. Da nawa da na yara
gabaÉ—aya set goma sha biyar ne, yawwa akwai kuma na Abban Sayyid za ki gansu daban. Su
kuma sai ki ba wa Babansu Bala (Mijin Lami) ya wanke ya goge. Idan an gama sai a yi mini
lissafi zan bayar da kuÉ—in." Amsa mata Lami ta yi sannan ta katse wayar, da sauri ta matsa
bakin ƙofa. Sai ta latsa ainahin ringing ɗin wayarta ta ware volum, sai da ya yi na ɗan sakanni
sannan ta kashe. Sai ta kai shi kunne a zuwan kiranta aka yi ta ce.
"Hello Abban Sayyid, ka yi mantuwa ne?"
Sai ta yi shiru kamar wacce ake yi wa magana ta sake cewa.
"Kai Abban Sayyid yanzu bayan kuɗin makarantar yara da aka ƙara ga hidimar gida har da
wanki? To shi kenan, bari na karɓo na wajen nata, Allah Ya ƙara buɗi Habibi." Sai ta yi ƙasa da
murya kamar mai kukan gaske ta ce.
"Haƙiƙa samun miji kamarka sai an tona Zauji, Allah Ya kula mini da kai." Daga haka sai
Bilkisu ta ƙarasa ƙofar ɗakin Amina ta yi sallama, jin ta amsa sai ta ce.
"Abban Sayyid ya ce ki haÉ—o kayansa na É—akinki za a kai wanki."
A sanyaye Amina ta amsa mata, sannan ta shiga É—aki ta haÉ—o kayan wankin Hafiz ta kawo
mata. Sai da ta karɓa ta ɗan yamutsa fuska ta ce.
"Ni kam ko ba kya jin daɗi ne Auntyn yara? Na ga tun safe kina ɗaki." Murmushin yaƙe Amina
ta yi ta ce.
"Ba na jin daÉ—i ne shi ya sa."
Bilkisu ta rausayar da kai alamun tausayi ta ce.
"Ayya sannu, dama kin san fa sai an rabu ake jin daÉ—in jiki. Ni na yi mamaki ma, da Abban
Sayyid yake fita ba tare da ya yi miki share-sharen É—aki ba, don lokacin cikin Sayyid hatta
moping sai ya yi mini yake fita." Wani zafi Amina ta ji a ranta, tana ayyana wato ita da yake ya
daina sonta ko gyaran gado bai taɓa yi mata ba. Bilkisu ta saci kallon Amina a fakaice sannan
ta ce.
"Kodayake bari na dinga rage miki wasu ayyukan, ai ban san ba ki da lafiya ba." Tana faÉ—ar
haka ta fice, sannan ta É—ebo kayan wankinta ta fito da su tsakar gida ta É—auki waya ta kara a
kunne bayan wani lokaci ta ce.
"Hello, Abban Sayyid." Shiru ta yi sai ta sake cewa.
"Ashe Amina ba ta jin daɗi tun safe, na ce ko na karɓi kayanta a haɗa da namu a kai wankin?
Tun da ka ga kayana da na su Sayyada ba su da yawa." A wannan karon ma shiru ta sake yi,
sai bayan wani lokaci tace.
"A'a don girman Allah ka yi haƙuri, ya za a yi ka ce ka rantse ba za a haɗa da nata ba. Don
Allah kada ka yi haka ba za ta ji daÉ—i..."
"Don Allah ki daina yi masa magiya Aunty, tun da bai yi niyya ba ai shi kenan. Wanki ai ba zai
kashe ni ba."
Amina ta furta cikin zafin zuciya, don a wannan karon ta gagara riƙe ɓacin ranta.
Girgiza kai Bilkisu ta yi ta ce.
"Haba ta ina za a yi haka, to ai kuwa nawa ma sai dai a bar shi gaskiya." Jim ta yi kamar mai
sauraren abin da yake faÉ—a, sai ta ce.
"To shi kenan, ka yi haƙuri zan bayar da su. Wai dama don kada ta ji babu daɗi ne ya sa na yi
maganar, amma tun da maganar kayan na ta ya ɓata maka rai ka yi haƙuri." Bilkisu tana sauke
wayar sai ga Habibu ɗan gidan Lami ya yi sallama, kayanta da na Hafiz ta haɗa ta ƙulle ta
ɗaura masa a kansa. Amina tana shiga ɗaki, ta ɗauko hijabinta ta zura sannan ta rufe ƙofarta ta
fice ko sallama ba ta yi wa Bilkisu ba. Tana jin zuciyarta na zafi, don yadda ta fita daga gidan ta
ci alwashin ba za ta koma ba sai dai Hafiz ya kai mata takardar sakinta.
Ummou Aslam Bint Adamí ¼í¼š
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko
É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma,
don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka
arashi ne.
SHAFI NA TARA
ALL NATURAL PRODUCTí ½í²ƒí ¼í¿»
Tsumi
Tsumin tighten
Tsumin Sanyi
Tsumin basir
Tsumin 3in1
Kazar Amare yan mata.
Kazar Amare zawarawa.
Kazar Masu haihuwa.
Kazar 3in1
Kazar uwargida ko amarya da suke son burge oga.
Gumbar dabino.
Gumbar kwakwa.
Gumbar Madara.
Garin dahuwar kaza.
Garin dahuwar ciccibi.
Garin dahuwar hanta.
Garin dahuwar kwai.
Garin dahuwar kifi.
Garin hakin maye na sha da Madara ko nono.
Ingantaccen tsumin maganin sanyi, wanda aka samo daga masunta masu kamun kifi,bayan
maganin infection yana magance sanyin da aka sha a ruwa ko a tiles ko irin sanyin nan mai
kumbura jikin mutum.
Bugu da kari ana iya ba yara kanana masu fama da mura ko tari, haka akan dace idan yaro
yana fitsarin kwance aka bashi in sha Allah yana dainawa.
09065730652 A tuntuɓi lambarmu.
***
Bilkisu tana kwance a É—aki ta ji fitar Amina, da sauri ta fito tsakar gida don ta sake tabbatar da
zarginta. Ƙofarta ta gani a garƙame da kwaɗo, kuma ta san duk rashin daɗin zaman da suke yi
da ita idan za ta fita sai ta yi mata sallama. Wannan ya sa ta sake tabbatar da zanginta na
Amina yaji ta yi. Cikin tsananin farin ciki ta koma É—aki ta haye kan gado, wayar Hafiz ta kira don
ta bigi cikinsa tana jin ya É—auka ta ce.
"Yawwa na manta ban tamabaye ka ba, me za a dafa ne. Saboda na ga Auntyn yara