Showing 18001 words to 21000 words out of 143522 words

Chapter 7 - DAHUWAR 'KAHO BOOK COMPLETE Hausa Novels By Ameera Adam.pdf

18 Jun 2025

5513

abada ni da 'ya'yana ne a gaba. Amma wallahi ba zan ɗauki kowanne irin cin kashi
da yarinyar nan za ta yi mini ba."

Kamar Alhaji zai yi magana sai kuma ya fice daga cikin ɗakin zuciyarsa tana suya. Can ɗakin
Shukura ya shiga, tana ganinsa ta tashi zaune ta ce.
"Ya ake ciki ne?"

Dafe kansa ya yi ya ce, "Wallahi ta ƙi amincewa, ni na rasa yaushe Hajiya ta fara musu da ni."
Shukura tana jin haka ta fashe da kuka, cikin tashin hankali ya riƙo ta ya ce.

"Don Allah kada ki ɗaga hankalinki, wannan ba abin damuwa ba ne. Wallahi na yi bakin ƙoƙari
don ta amince amma fir ta ƙi amincewa. Har tana ce mini za ta bar gidan nan idan aka fitar mata
da kaji." Da sauri Shukura ta ɗago ta ce.

"To sai me? Ba sai ka sake ta ba tun da ba za ta bi umarninka ba. Daɗin abin ai ba ita kaɗai ce
matarka ba." Da wani irin sauri Alhaji ya fisge jikinsa daga jikin na Shukura, har sai da ta tsora
ta. Rai a ɓace ya nuna ta ya ce.

"Ko a mafarki kada ki sake tunanin zan iya rabuwa da Hajiya Karima, wannan matar da kike
gani ita ce komai nawa. Kuma ban auro ki saboda na daina sonta ba, ina son matata domin ita
ce rufin asirina. Duk wani mataki da kika ga na kai, wallahi ta silarta ce." Alhaji ya gama faɗa ya
fita daga ɗakin a zuciye.
GIDAN HAFIZ

Bayan Hafiz ya watsa ruwa, zama ya yi daga shi sai kayan shan iska.A gefen Amina ya
zauna, ya fara bin ta da wani irin kallo. Murmushi ta sakar masa, ya shafo fuskarta ya ce.

"Na yi kewarki Meena."

Cikin zolaya ta ce, "Ba wani nan ni ban ga alama ba." Matse ta yi a jikinsa tsam, ta saki 'yar
ƙara kaɗan lokaci ɗaya suka saki dariya. Janye jikinta ta yi ta ce.

"Akwai tea akwai drink wanne za ka fara sha?"

Lumshe ido Hafiz ya yi ya ce. "Da ke zan fara mana." A ɗan shagwaɓe Amina ta ce.

"Habibi ka fiye wasa fa."

Sauka ya yi ƙasa, Amina ta zuba masa ruwan shayi a kofi, ta buɗe fulas za ta zuba masa
abinci, daga bakin ƙofa suka ji Bilkisu ta zuro kwano cike da abinci ta ce.

"Idan har kin yi haka don ki kashe ni ko ki kashe 'ya'yana, In Shaa Allahu sai dai ki gani a
kanki. Saboda kin ɗebi naki abincin da na Abban Sayyid shi ne mu za ki hala ka mu, ai shi
kenan Allah Yana kallo." Daga haka Bilkisu ta bar wurin.
Kallon juna Hafiz da Amina suka yi, a sanyaye ta miƙa hannu ta ɗauko kwanon tana kallonsa,
sai dai ko kaɗan ba ta ga komai ba. Abu ɗaya ta ji shi ne wari-warin fetir, Hafiz ya ɗauki abincin
ya shinshina ya ce.

"Me kuma ya kawo warin fetir a abinci?" A sanyaye Amina ta ce.

"Wallahi ban san yadda aka yi ba. Lafiya ƙalau na yi girki na gama." Ajiye kwanon ta yi, ta fara
zubawa Hafiz shi ma. Yana matso da plate ɗin gabansa ya ji warin fetir ya doki hancinsa, da
sauri ya ɗago ya ce.
"Amina wai me yake faruwa ne? Wannan wanne irin wulaƙanci ne za ki saka mana fetir a cikin
abinci? Ina ce galan ɗin fetir daban na mai ma daban?" Idanun Amina suka ciko da ƙwalla, ta
saka hannu ta share hawaye murya tana rawa ta ce.

"Wallahi ban san komai ba, lafiya ƙalau na gama girki."

"Ƙafa gare shi man ko hannu da zai zuba kansa? Shi kenan sai ki san yadda za ki yi da shi."
Hafiz ya furta cikin fushi sannan ya zura doguwar rigarsa ya fice. Bilkisu da ke ɗaki murmushin
ƙeta ta saki, ta ɗauko waya ta kira shi tana ji ya ɗauka ta ce.

"Abban Sayyid yanzu ya zan yi da yara? Ga shi suna kukan yunwa."

"Ki dafa musu taliya mana." Hafiz ya faɗa a ɗan faɗace. Kwantar da murya Bilkisu ta yi ta ce,
"Ai ina tsoron ko man ne yake da fetir kada na sake saka musu a koma 'yar gidan jiya." Shiru
Hafiz ya yi sannan ya ce.

"Ki fara dubawa kafin ki zuba, idan kin dafa kuma ki zuba mini ni ma a cooler ina dawowa."
Daɗi ne ya cika Bilkisu, ta amsa masa sannan ta kashe wayar.


Ummou Aslam Bint Adam
07062062624

[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko
ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma,
don haka a kiyaye.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka
arashi ne.

SHAFI NA BAKWAI

AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu
kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin
zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu
lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono
yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin
magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara
amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma
kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace
idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna
turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN
NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon
Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko
ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci_

_nfection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!
infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula
mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi
amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara
garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma
muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari
domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ *08089965176*
*07084653262*

***

Bilkisu drower kayanta ta buɗe, ta jima a tsaye tana nazarin waɗanda za ta ɗauka. Wata
doguwar riga shara-shara ta ɗauko ta zura, ta shiga ɗakin yaran ta same su har sun fara bacci
da yake an yi sallar Isha'i. Shimfiɗa ta yi musu ta ɗauko net ta saka musu, ta koma ɗaki sannan
ta ɗauki ragowar taliyar da suka ci ita da yaran wacce ta zuba a cooler ta ajiye. Motsin Amina ta
ji, don haka ta yi zaraf ta fito ta ɗauki buta ta yi kamar banɗaki za ta shiga. Amina ta gani ta fito
da abincin ta saka a kicin, murmushin ƙeta Bilkisu ta yi ta shiga banɗaki bayan wani lokaci ta
fito har za ta shiga ɗaki ta ja tsaki ta ce.
"Aikin banza, haka kawai a jaza wa mutum ɗora girkin dare. Ai shi ma Abban Sayyid ɗin
maganinsa kenan, kana tare da matarka cikin rufin asiri ka ci ba ka ci ba babu wanda ya sani.
Amma haka kawai rana tsaka a ɗauko maka baƙar ƙaddara ta addabe ka, tun da nake a gidan
nan 'ya'yana ba su taɓa kwanciya ba su ci abinci ba sai yanzu."Ta gama faɗar haka ta faɗa
ɗaki. Amina da ke durƙushe tana juye abinci a tukunya ta share hawayen idonta, saboda ta yi

tunanin duniya ba ta tuna a lokacin da ta zuba fetir a madadin mai a abinci ba. Kuma ko da ta
gama girki ba ta ji warin komai ba, a sanyaye cikin damuwa ta koma ɗaki ta zauna. Waya ta
ɗauka ta kira layin Hafiz ta ji bai ɗauka ba, abin duniya duk ya dame ta don bai taɓa yin fushi da
ita irin haka ba.
Bilkisu tana daga ɗaki wani tunani ne ya faɗo mata, da sauri ta ɗauki waya ta je bakin ƙofa
yadda Amina za ta ji ta ce.

"Hello Abban Sayyid, na ce ka haɗo mini da tsiren jiya da ka sayo mini. Amma dai yau kada a
cika albasa, sai kuma su Sayyada yogot ɗin nan za ka taho musu da shi." Sai Bilkisu ta yi shiru
kamar ana ba ta amsa sannan ta sake cewa.

"A'a ba sai ka sayo mini kifi ba, kai dai ka sayo wanda za ka ci taliyar da shi." Ta sake yin shiru
sai daga ƙarshe ta ce.
"A'a ai abin da Amina ta yi maka bai kai ka ce za ka ƙauracewa kwanan ɗakinta ba. Ba a yi
haka ba, gaskiya kada kasa ta ƙulla ce ni. Sai dai ka shigo kawai." Bilkisu ta lallaɓa ta koma kan
kujera tana ƙunshe dariyar ƙeta, saboda ta san babu tantama Hafiz ba zai shigo ba sai da kifi.
Ɗabi'arsa ce indai ta yi shinkafa ko taliya fara da mai to ba ya taɓa ci sai ya sayo kifi ya ci da
shi, ita da yara kuma sai ya sayo musu balangu ko tsire.

Amina tana daga ɗaki wani irin takaici ya lulluɓe ta, musamman da ta ji wai Hafiz yana faɗa wa
Bilkis zai ƙauracewa kwanan ɗakinta. Kiransa ta gani, saboda haushi kawar da kai gefe ta yi ba
ta ɗauka ba. Miƙewa ta yi ta shiga uwar ɗaki ta cire kwalliyar atamfar da ta yi, ta ɗauki wasu riga
da wando marasa nauyi na bacci ta saka, sannan ta fita ta ɗauro alwalar Isha'i ta gabatar da
sallah.
Tana nan zaune ta ji sallamar Hafiz, mamaki bai gama kashe ta ba sai da ta ga Hafiz ya nufi
ɗakin Bilkisu. Bai wani jima ba, ta ga ya ɗawo ɗakinta ya zauna, sai dai har lokacin fuskarsa a
haɗe take. Kifin da ta ga ya fito da shi ya sake tabbatar mata da wayar da ta ji Bilkisu tana yi,
Hafiz bai kalli ɓangaren da take ba ya ce.
"Idan za ki ci ki sauko."

Haushi ya kama ta da jin abin da ya faɗa, zuciya ce ta ciwo ta ta ce.
"Na ƙoshi."
Sai a lokacin ya ɗago ya kalle ta, bai tanka mata ba ya cigaba da cin abincinsa. Sai da ya gama
ya tura mata ledar wani ƙunshin kifi gabanta ya ce.

"Ga shi nan ki tashi ki ci."

"Na ƙoshi ka cinye."
Amina ta faɗa a karo na biyu, ransa ne ya ɓaci don ya san ba ta ci abinci ba. Cikin faɗa ya ce.

"Wai saboda na yi miki faɗa shi ne za ki hau ɓata rai? Wani sabon hali za ki tsiro mini Amina?

Kin san asarar yawan abincin da kika yi mini?" A ɗan zafafe ita ma ta ce.

"To yanzu me nace maka? Kawai don na ce na ƙoshi sai ya zama abin faɗa? Idan ba da son
ranka ka dawo za ka kwana a nan ba, ba sai ka koma can."

"Me kike nufi Amina?"
Ya jefa mata tambaya rai a ɓace. Shiru Amina ta yi, cikin hawaye ta miƙe ta shiga ɗaki tana
kuka. Kukan da Amina ta yi shi ya sake harzuƙa Hafiz, don gani ya yi bai ga abin fushi da kuka
ba saboda kawai ya nuna mata kuskurenta. Hafiz yana gama cin abinci kallo ya kunna, don ba
ya son ya sabarwa kansa da zaman majalisa. Yana nan zaune har ya ji bacci don haka ya
kashe ya shiga ɗaki, a lokacin da ya shiga Amina ta yi bacci. Rage kayan jikinsa ya yi sannan
ya haye gado ya kwanta.

Duk abin da ya faru tsakanin Amina da Hafiz, Bilkisu tana laɓe tana jin su. Daɗi ne ya cika ta,
cikin farinciki ta koma ɗaki ta buɗe ledar kifin da Hafiz ya ajiya mata. Sai da ta cinye shi tas,
sannan ta ɗauki ruwa ta sha ta haye gado ta kwanta hankali kwance.

WASHEGARI

Washegari koda Amina ta tashi yanayinta babu yabo babi fallasa, haka shi ma daga wurin
Hafiz. Sai da ta zo yin wanke-wanke ta juye shinkafar a leda, saboda ko akuyoyi ba za su iya ci
ba. Bilkisu ce ta sharo ɗakinta a lokacin tuni Hafiz ya jima da fita, da gayya ta sharo wata
ƙatuwar takardar tsire wacce take sharkaf da mai, ƙuli da albasa. A yatsine ta sharo takardar da
ta yi fakaka a saman makwashin shara ta ce.

"Shi ma Abban Sayyada na faɗa masa ya cewa mai tsiren nan ya rage zabga mana albasa,
amma kullum sai ya manta." Ta gefen ido Bilkisu ta kalli Amina da ke wanke-wanke, sai da ta je
wucewa ta gabanta sannan ta saki takardar ta faɗi ƙasa da gayya don ta gani. Tsugunnawa
Bilkisu ta yi ta share ta saka a shara, sannan ta wuce ɗaki tana murmushin mugunta. Wunin
ranar haka Amina ta yi shi cikin damuwa, zuciya ta raya mata munafurcin da Hafiz zai tsiro
mata. Har take ji a ranta da ya san ba zai yi musu adalci ba, da ba ta aure shi ba. A yammacin
ranar sai da ta yi wanka sannan ta ɗora girki, bayan ta gama ta ɗebi nata ita da Hafiz sannan ta
ba wa Bilkisu da yaranta. Kuma a wannan ranar lafiya ƙalau suka ci abinci, har Hafiz yana janta
da hira saboda girkin da ta yi ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba. Hakan ne ya sanyaya zuciyar
Amina har ta sauko daga fushin da take yi, ta so ta yi masa magana a kan rashin adalcin da ya
fara yi amma sai ta ƙyale shi don kada ya ga kamar ta cika ƙorafi.

Sannu a hankali rayuwar gidan Hafiz ta cigaba da tafiya, da daɗi babu daɗi haka suke rayuwa.
Saboda kusan kullum da abin da Bilkisu take tsiro da shi, musamman idan Hafiz yana ɗakin
Amina. Sautari idan yana ɗakin Amina sai dare ya yi za ta buga masa ƙofa ta ce ɗaya daga
cikin yaran babu lafiya, ko kuma ta ce ya fito ya duba mata ɗakinta ta ji motsin wani abin. Tun
Hafiz bai fahimta ba, yana biye mata. Har ya fahimci kamar da makirci a cikin lamarinta, saboda
idan yana ɗakinta lafiya ƙalau suke kwanciya su yi bacci.

Ana cikin haka sai Bilkisu ta tsiri idan Hafiz yana ɗakinta sai ta fice ta koma cikin yaran ta
kwanta, a ranar farko da ta yi da ya tambaye ta sai ta ce ita ta fi jin daɗin kwanciya a cikinsu. Da
ya nemi kasancewa da ita nan ma sai ta ce ba ta buƙata, daga haka sai ta koma idan ya dawo
ɗakinta sai dai ta zauna ta yi ta rusa kuka ko ta ce ya sake ta. Hakan ba ƙaramin ɗaga
hankalinsa ya yi ba, da ya tambaye ta sai ta ce masa idan yana ɗakinta ji take kamar ta kashe
shi. Kuma sai jikinta ya ɗauki zafi kamar ana dafa namanta ko ana tsira mata allura. Wannan
lamarin ne ya ɗaga hankalin Hafiz, ya shiga nema mata maganin aljanu a tsammaninsa ko su
suka fara shafarta. Watarana da safe Hafiz yana shan shayi, ta fara shara, da gayya Bilkisu ta
sharo ƙarƙashin kujera sai ga wata ƙatuwar laya ta fito. Da mamaki ta ɗauki layar ta ce.

"Abban Sayyid kai ne ka ajiye ta." Yamutsa fuska ya yi ya ce
"Ni kuwa me zai haɗa ni da laya Bilkisu? Miƙo mini na gani." Ƙin ɗauka ta yi ta janye gannu
gefe ta ce.
"Cab wallahi ba zan taɓa ba, haka kawai ban san ta mece ce ba zan taɓa ina zaune ƙalau."
Miƙewa ya yi ya ƙarasa wurin ya yi bismillah ya ɗauka. Ya shiga warwarewa yana buɗewa sai
ga wani busasshen ɗanyan nama, da ƙananan allurai a ciki. Wata takarda ya gani ya buɗe ta, a
ciki ya ga an rubuta sunansa da na Bilkisu na farraƙu. Daga ƙasa kuma an saka sunansa da na
Amina an yi rubutun mallaka." A firgice ya ɗago yana bin Bilkisu da kallon tausayi, sai a lokacin
ya fahimci irin abin da ta ce masa tana ji a cikin jikinta. Kamar Bilkisu ba ta san da komai ba, ta
matsa kusa da shi ta ce.

"Me aka rubuta a ciki, ba ni mu gani." Naɗe takardar ya yi, don ba ya son ta gani ya cusa a
aljihu ya ce.
"Ƙarasa shararki babu damuwa." Haɗe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login