Showing 45001 words to 48000 words out of 143522 words

Chapter 16 - DAHUWAR 'KAHO BOOK COMPLETE Hausa Novels By Ameera Adam.pdf

18 Jun 2025

5564

wallahi da matsala." Daga can ɓangaren Inna ta ce.
"Tun tasowa ta ban taɓa cin karo da matsala ba, don haka a yanzu ma ba zan ganta ba. Tun
bayan sallar asuba na fito zuwa wurin malam, yanzu haka zan haÉ—a ki da shi a waya ki masa
cikakken bayani." Bakin Shukura har rawa yake ta ce.

"Ba shi Inna, maza ba shi don Allah."
Tana faɗar haka ta miƙe ta shige banɗaki, don kada Daddy ya jiyo wayar da suke yi.


Littafin kuÉ—i ne 500 idan ya kammala 800 ne. Za a turo a acc Aisha Adam 3090957579 First
bank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624.


Ummou Aslam Bint Adam🌚
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko
É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma,
don haka a kiyaye.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka
arashi ne.

SHAFI NA SHA HUÆŠU

Daga can ɓangaren Inna ce ta ba wa Malam waya, yana karɓa ya ce.
"Yarinya faɗi buƙatarki." Kamar Shukura tana jira ta ce.
"Malam duka aikin da ka yi mini a wancan karon ne ya lalace."

"Yarinya aikinmu ba ya buƙatar garaje, ki yi mana bayani dalla-dalla ta yadda za mu san yadda
aka haihu a ragaya."
Malam ya faÉ—a a É—an tsawace. Ta cikin wayar ta ji Inna tana faÉ—in.
"Ke Shukura ki shiga nutsuwarki mana, ki yi masa bayani dalla-dalla yadda zai fahimta." Tsawa
ta ji Malam ya buga wa Inna ya ce.

"Tun kafin ki zo, muka san abin da yake tafe da ke. Kada ki sake cewa za a fahimtar da mu,
domin mu masu sani ne. Kawai dai muna son ji daga gare ta ne, kin san waƙa a bakin mai ita ta
fi daÉ—i." Baki yana rawa ta ji Inna ta ce.

"Tuba nake malam, a yi mini aikin gafara."
Amsa mata ya yi, sannan ya sake yi wa Shukura magana. Tiryan-tiryan Shukura ta yi masa
bayanin abin da ya faru, tun daga tashin Daddy daga bacci har zuwa dawowarsa. Sai da ya
gama sauraronta sannan ya ce.

"Haƙiƙa kishiyarki ta tashi tsaye ba da wasa ba, kuma wannan birkicewar da kika ga mijinku ya
yi asiri ne ta yi masa." Shukura ta yi zaraf ta ce.
"Ai wallahi na zargi matsiyaciyar nan."

"To wannan ba damuwa ba ne, tun da kayanki suka tsinke a gindin kaba. Za a yi miki aiki iya
aiki, amma fa sai kin zubar da kuɗi. Saboda aikin za mu yi da baƙaƙen aljanu, kuma su kansu
za mu zubar musu da jini. Ragowar kayan aikin ma idan muka faÉ—a miki su, idan za ki shekara
É—ari ba za ki same su ba." Ta ji malamin ya yi mata bayani. Cikin sauri ta ce.
"A'a Malam, gara dai ka sayo da kanka. Ni kuÉ—i ba matsalata ba ne, nawa kake ganin za a
bayar?"

"Zan sanar da mahaifiyarki, domin ita ya kamata ta damƙa mini hannu da hannu." Amsa masa
ta yi sannan suka yi sallama, sai bayan ta gama sannan ta fito ta koma kan gado ta kwanata.

Tana jin damuwar da take ciki kusan kaso casa'in ta tafi, don haka ta samu bacci ya yi awon
gaba da ita.

ALHAJI UMAR
Abin duniya ne ya haÉ—e wa Daddy, gabaÉ—aya komai ya fita daga rayuwarsa. Har ji yake yi, a
kan Mommy matuƙar bai same ta ba zai iya rasa rayuwarsa. Babban abin da ya ɗaga masa
hankali, har kawo wani lokaci mai tsayi Baba malam bai sake bi ta kansa ba. Idan kuma ya kira
shi a waya ba ya ɗauka, haka ita ma layin Hajiya Karima ya kira babu adadi ta ƙi a ɗauka. Daga
ƙarshe ma sai ya ji wayar ta daina shiga, da Momny ta ga ya ƙara sauya layuka yana kiranta da
su, sai ta saka wayar a DND sannan ta samu lafiya da shi.

Da Daddy ya ga ya bi duk wata kafa da zai samu Mommy bai samu ba, sai ya koma kiran
ragowar 'yan'uwansa yana kai kukansa wurinsa. A ranar da ya kira yayansa Baba Yunusa ya
gama zayyane masa damuwarsa, ba ƙaramin tausayinsa ya yi ba. Saboda ya san duk abin da
ya yi a baya ba yin kansa ba ne. Cike da tausayin É—an uwansa ya ce.
"Umar wannan matsalar taka tana hannun Baba malam, saboda ni da 'yan'uwana ka san ba
mu da hurumi a kan wannan maganar. Yanzu dai ka yi haƙuri, In Shaa Allahu zan gwada sa'ata
na kira shi na ga ko zai saurare ni." Jiki a sanyaye Daddy ya taso daga gidan, bayan kwana
biyu a tsakani Baba Yunusa ya kira shi ya ce Baba malam bai saurare shi ba. Tun Daddy yana ganin abin kamar wasa har aka sake shafe watanni a haka, duk wanda ya
kira ya je wa da ƙorafin maganar Mommy sai dai ace masa ya bi ta wurin Baba malam. Wannan
yanayin ya sake birkita shi, har zamansa da Shukura ya koma irin zaman doya da manja.
Kwata-kwata ba ta ganinsa a gida idan ba dare ne ya yi ba, idan gari ya waye zai fice. Idan
kuma ta matsa sai ya zauna a gida, ba shi da magana sai ta Mommy da iyalanta. Ga kaÉ—aici da
ya dame ta, saboda gidan ya yi mata girma wani lokacin har tsorata kanta take yi. Musamman
idan zuciya ta fara yi mata ayyane-ayyane, ga shi duk kuÉ—aÉ—en da suke kashewa a wurin
malamai babu aikin da yake ci. A kan haka har faɗa suka taɓa yi da mahaifiyarta, saboda
Shukura gani take kamar cinye mata kuɗi Inna take yi. Ita kuma Inna ganin bakin ƙoƙarinta take
faɗi-tashi wurin bin malamai sai ya abin ya ɓata mata rai. Sai daga baya suka daidaita, ta
cigaba da bata miyagin shawarwari amma babu wacce take mata amfani.

Bayan kwana biyu da faruwar al'amuran, watarana da safe ciwon hawan jinin Daddy ya tashi.
Hankali a tashe Shukura ta fita wurin mai gadi cikin kururuwa ta sanar da shi, da sauri ya shiga
ɗakinta ya riƙo Daddy da ya fara fita daga hayyacinsa ya saka shi a mota. Da sauri Shukura ta
shiga mazaunin direba ta tuƙa shi ta nufi asibiti da shi, cikin kulawa likitoci suka karɓi Daddy
suka shiga ba shi agajin gaggawa. Sai da ta ga ya É—an dawo hayyacinsa, sannan ta zame jiki ta
fice daga É—akin, ta latsa lambar Inna ta kira ta sanar da ita. Sai da ta gama sauraronta ta ce.

"Wai Shukura me ya sa ba ki da wayo ne wani lokacin? Dama kin san haka jikinsa ya yi zafi
shi ne ba ki sanar da ni ba? So kike mu gama ƙarar da gishirinmu a dahuwar ƙaho, ba tare da
ya amfane mu da komai ba? Ko so kike mu yi wahalar hura wuta, zafin hayaƙi ya gama kashe
mana idanuwa ba tare da mun sharɓi romon ƙahon da muke dafawa ba?"

"To Inna ya kike so na yi? Ba fa ni na É—ora masa ciwon nan ba, duk ta sanadin tsohuwar matar
nan yake neman kassara rayuwarsa. Wallahi ba na son na rasa Alhaji, saboda ba ƙaramin so
nake yi masa ba." Shukura ta furta muryarta tana rawa.
Dogon tsaki Inna ta ja sannan ta ce.
"Wallahi kin ba ni mamaki Shukura, au ke da soyayyar gaskiya ce ta kai ki gidan? To ki buÉ—e
kunnenki da kyau ki saurare ni."

Murya a sanyaye Shukura ta ce, "Ina jin ki Inna."
"Har yanzu ba ki ci adadin kwanakin da na É—ebar miki a gidan Alhaji ba, duka-duka yaushe
aka yi abin da mutuwa take ƙoƙarin hana mu rawar gaban hantsi? Ko fa haihuwar fari ba ki yi
ba, idan ya mutu yanzu ribar me muka ci?" Inna ta furta cike da damuwa, kamar Shukura za ta
yi kuka ta ce. "A'a Inna don Allah ki daina zancan mutuwa, ni dai tsakani da Allah nake son shi wallahi. Ina
laifin abin da muke samu yanzu ma."

"Shashasha! Ana nuna miki gabas kina cewa kudu ce. Yanzu dai abin da nake so da ke, ki
shirya ki tafi gidan yayansa Baba malam É—in, ki sanar da su rashin lafiyarsa. Sannan ki fashe da
kuka ki nemi yafiyar Hajiyan da 'yan'uwansa, ni kuma duk abin da na zo asibitin na aikata a
kanki kada ki tuhume ni. Duk a cikin plan ne, ke ko dawo da itan ne ki tsaya tsayin daka a dawo
ita ai ribarmu ce."

"Haba Inna, me kike faÉ—a haka? Gidan Baba malam fa? Kin san yadda suka tsane ni kuwa?"
Murmushin manya Inna ta yi ta ce, "Yaro man kaza, kin san dai ba na ƙwaina ai sai da zakara.
Kuma banza ba ta kai romo kasuwa. Tun da kika ji na faÉ—i haka ki bar ni mu tafi a haka, idan
hagu ta ƙi ai sai mu koma dama. Tun da asirin ya ƙi ci, sai mu gwada kissa mu gani."
Cikin damuwa Shukura ta ce, "Gaskiya Inna hankalina bai kwanta da wannan shirin ba, yanzu
sai mu bari ya dawo da Hajiya ana zaune..."

"Shukura kin san dai ba zan saka ki a hanyar da ba za ta ɓille mana ba. So nake mu dafa ta
da ruwan jikinta, ta yadda za ta gwammace zamanta a waje saɓanin cikin gidan." Inna ta furta
cike da kwantar da hankali. Murmushi mai sauti Shukura ta yi, sannan ta ce.
"Allah Ya bar mini ke Innata." Inna ta amsa sannan suka yi sallama.

Shukura tana shiga ta tarar har lokacin Daddy bacci yake, da yake allurar da suka yi masa mai
ƙarfi ce. Kuma a wannan asibitin Daddy yake ganin likita, nurses ɗin ta samu ta ce musu za ta
je gida ta dawo. Amsa mata suka yi, sai da suka kira wasu daga cikin ma'aikatansu suka zauna
a wurin Daddy sannan ta wuce gidan Baba Malam.
Shukura tana zuwa gidan Baba malam ta yi horn a bakin gate, mai gadi ne ya tambaye ta
wurin wanda ta zo. Bayan ta sanar da shi, sai da ya É—aga waya ya kira Baba malam ya sanar
da shi sannan ya buÉ—e mata ta shiga.
Duk da Baba malam ya ji É—acin zuwan Shukura, amma ya bar ta ta shigo ne albarkacin tana

auren É—an'uwansa. Uwa-uba kuma ya sa an buÉ—e mata ne, don ya ji abin da yake tafe da ita.
Shukura ta yi mamakin yadda mutanen gidan suke ta karrama ta, duk sai ta ji ta tsargu. Tana
nan zaune Haidar ya shiga falon, wani mugun kallo ya wurga mata. Da sauri ta kawar da kanta
gabanta yana faÉ—uwa, buÉ—e firji ya yi ya É—auki ruwa ya yi gaba. Fitarsa babu jimawa Mommy ta
shiga da niyyar cire wayarta a caji, kallon-kallo suka shiga yi wa junansu. Mama ba ta taɓa
tsammanin Mommy za ta kula Shukura ba, amma sai ta ga ta saki murmushi ta ce.

"Aunty yau baƙi ne a gidan namu?"

Mama ta ce, "Eh wallahi, Shukura ce ta zo wurin Daddyn yara. Wai Daddyn Mami ne a asibitu
ba shi da lafiya." Ɗan taɓe baki Mommy ta yi ta ce.

"Oh dama fa haka ake ta fama, Allah Ya sawaƙe." Daga haka ta ɗauki waya ta nufi ɗakinta.
Baba malam ne ya shiga cikin falon, Shukura tana ganinsa ta cigaba da share hawaye cikin
shasshekar kuka.

HAFIZ
Su Hafiz suna zuwa asibiti likitoci suka shiga yi wa Amina tambayoyi tana ba su amsa,
gwaje-gwaje suka yi mata suka tabbatar da cikinta lafiya ƙalau yake ba su ga wani abu da yake
damunta ba. Sai kuma jininta da ya ɗan yi ƙasa kaɗan, abin da suka ce sun gani a jikin Amina
kenan. Gudun kada Hafiz ya gano Amina, sai ta ce musu tana É—an yawan ciwon kai. A nan suka
sake ba su shawarwari a kan ta dinga samun bacci wadatacce, ta kuma dage da cin abubuwa
da ke gina jiki. Suna fitowa daga asibitin ya ga kiran mahaifinsa, sai da suka shiga adaidaita
sahu sannan ya É—auka cikin girmamawa. Bayan sun gaisa Baba ya ce.

"Hafiz kana ina ne?"

Hafiz ya ce. "Baba yanzu na fito daga asibiti."

"To idan ka gama ina son ganinka kai da Amina."
Baba ya furta a gajarce, sannan ya katse wayar.

Gaban Hafiz ne ya faÉ—i, don tun da ya ji haka ya san ba ya wuce Bilkisu ce ta kira ta faÉ—a masa
wani abin. Ita kanta Amina sai da ta ji gabanta ya faÉ—i, da yake ba ta saba irin waÉ—annan
ƙarairayin ba har gani take kamar idan suka je za a iya gano ciwon ƙarya take yi.
Lokacin da suka ƙarasa gidansu Hafiz, su Sayyid suna tsakar gida suna wasa. Oyoyo suka yi
masa, bayan da suka gaisa da mutanen gidan sannan suka wuce É—akin Mahaifinsa. Tun da ya
ga su Sayyada jikinsa ya ba shi Bilkisu tana gidan, sai da suka gaisa sannan Baba ya sa aka
kira Bilkisu. Fuska a haÉ—e ta shiga ta nemi wuri ta zauna, Baba ya dubi Bilkisu ya ce.
"Bilkisu maimaita mini abin da kika ce ya haÉ—a ku."
Kamar tana jira, Bilkisu ta shiga wassafa jawabin abin da ya faru. Baba ya dubi Hafiz ya ce.

"Shin abin da matarka ta faÉ—a haka ne?" GyaÉ—a kai ya yi sannan ya cigaba da cewa.

"Baba ni ban hankaɗe Bilkisu, saboda wata manufa ko don na wulaƙantata ba. Yanzu Baba
saboda kwananta ne, sai ta ce ba zan kai Amina asibiti ba don ba ta da lafiya? Ita Bilkisun sau
nawa idan kwanan Amina ne, za ta kira ni ta ce yaro ko ita ba lafiya amma haka nake fita na ba
su kulawa." Ajiyar zuciya Baba ya yi ya ce.
"A gaskiya Bilkisu ba ki kyauta ba, ko Hafiz ba ya nan ai ke mai kai 'yar'uwarki asibiti ne." Baba
ya nuna Amina, sannan da sake kallon Bilkisu ya ce.

"Ke Amina da Bilkisu na dawo gare ku, ku ji tsoron Allah a zamantakewarku. Ku sani duk
wacce kuka cutar Allah ba zai bar ku ba, zan yabi Hafiz ba don yana É—ana ba. Amma ku sani
yana ba kin ƙoƙarinsa a kanku, ku haɗa kanku ku rungumi mijinku ku zauna lafiya." Baba ya
jima yana yi musu nasiha, har jikin Amina ya yi sanyi ta ji za ta watsar da duk wani zaman ƙarya
da makirci da ta tsira. Ta saka wa ranta duk rintsi za ta cigaba da zaman haƙuri, da kyautatawa
mijinta. Musamman da Baba ya nuna musu muhimmanci haƙuri da ladan da mace take samu
ya yin ibadar aure.

A kwanaki biyun da suka biyo baya, gidan Hafiz suna zaune lafiya ƙalau. Saboda Amina
gabaÉ—aya ta zubar da makamanta, ta cigaba da zama da Bilkisu da zuciyarta É—aya tsakaninta
da Allah kamar yadda ta zo tun farko. Ita ma Bilkisu a haka nunawa ta yi kamar komai ya wuce,
don haka ta dinga kwantar da kai har Hafiz ya gama sakin jiki gidansa ya zauna lafiya.
Ana cikin haka kuma sai Bilkisu ta tsiro da wani sabon makircin, don har lokacin da cikin Amina
ya tsufa ba ta cire rai da fitar da ita daga cikin gidan ba. Sabon layi Bilkisu ta saya ta saka a
wayarta, idan Amina da Hafiz suna zaune sai ta tura mata saƙon soyayya. Idan ka ga irin saƙon
za ka yi tsammanin saurayi ne ya turawa budurwrsa da yake tsananin so. Tun abin bai fara
damun Amina ba, har watarana ta taɓa yin replay da cewar wrong number ne. Tun ana tura
mata text har ta kai wani lokacin ana kiranta a waya, amma idan ta É—auka sai ta ji an yi shiru.
Tafi-tafi sai ya zamana idan ta É—auka sai dai ta ji an ce ana sonta, ko an yi kewarta. Wani zubin
har cewa ake yi an yi kewar ni'imarta. Tun da ta ji ire-iren miyagun kalaman, ba ta sake É—auka
ba. Kuma ba ta taɓa tunanin faɗa wa Hafiz ba. Ita kaɗai ta bar abin a cikin ranta, don ba ta
É—auka lamarin zai yi tsamari ba.

Watarana da daddare Hafiz yana ɗakin Bilkisu yana cin abinci, sai ji ya yi ana ƙwanƙwasa ƙofa.
Miƙewa ya yi ya fita ya buɗe ƙofar, wani almajiri ya yi gani da wata leda a hannu. Almajirin
bayan ya gaishe shi ya ce.

"Ai ko ni aka yi."

"Kawo saƙon, waye ya turo ka?" Hafiz ya furta yana kai hannu zai karɓa, da sauri almajirin ya
janye ya ce.
"Mutumin ya ce kada na ba wa kowa sai Amina."

Da mamaki Hafiz ya ce.
"Wani ne ya turo ka? Wane ne shi?"

Almajirin ya ce, "Eh wani ne a mota, ya ce na kawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login