Showing 117001 words to 120000 words out of 143522 words

Chapter 40 - DAHUWAR 'KAHO BOOK COMPLETE Hausa Novels By Ameera Adam.pdf

18 Jun 2025

6710

ba, yana nan cikin ɗakinsa ku ƙwanƙwasa masa."
Yaron ya furta yana niyyar wucewa, Mudassir ya ce masa.

"Don Allah zo ka shiga ka yi mana sallama da shi, ka ce baƙi ne suka zo akwai muhimmiyar
maganar da suke son tattaunawa da shi."
Gaban Mai gari ya sake faɗuwa, nan take jikinsa ya shiga karkarwa. Jin furucin saurayin da
kuma baƙin da suke ƙofar gidan, ya sa shi sake firgicewa musamman da ya kallo ƙauren
ɗakinsa ya karye ba shi da damar rufewa duk abin da zai faru sai dai ya faru da shi. Doguwar
rigar shaddar jikinsa ya cire, ya zame dogon wandonsa daga shi sai gajeren wando. Don haka
ya wala ƙafafuwa ya saita bakin ƙofa, cikin shirin ko-ta-kwama. Don ya ci alwashin sai dai ya
fice a guje amma ba zai zaune hukumar kare haƙƙin aljanun ta sake hukunta shi. Musamman
da ya san idan suka ritsa shi a ɗakin babu mai ƙwatarsa sai Allah.. Cikin murna yaron ya shiga
soron gidan Mai gari yana sallama, ya ƙarasa bakin ƙofar ɗakin zai yi magana sai ji ya yi Mai
gari ya fito a guje ya baje shi a ƙasa. Ya tattakura ya fita da gudu, a daidai lokacin, yaron ya
fasa ihu saboda zafin buguwar da ya yi. Su kuma su Mudassir ganin yanayin da Mai gari ya fita
a guje su ma sai suka rufa masa baya suna gudu, don a tsammaninsu wani abin ne ya koro shi
daga cikin gidan. Saboda yadda Mahmud ya fi tsorata shi ne yake biye da Mai gari, hularsa da
glass ɗinsa sai da suka yi kusa tsalle uku sannan suka faɗi a ƙasa. Abin da ya sake ɗaga
hankalin mai gari, yadda ya ga duk waigen da ya yi sai ya ga su Mahmud suna biyo shi a baya.
Don haka ya tattakura ya ce.

"Jama'a ku kawo mini ɗauki, hukumar kare haƙƙin wancan jinsin za su halake ni."

A madadin a samu wasu su fahimci maganar Mai gari, sai dai duk majalisar da suka wuce su
ma sai su rufa musu baya saboda tun da suke ba su taɓa ganin Mai gari da gajeren wando

yana gudu ba.

Sai da Inno ta bari jikin Malam ya sarara masa da zafi, sannan ta sake aikawa ɗaya bayan
ɗaya ta kira iyalanta. Tun da suka shiga ɗakin suka fahimci ran Inno ya gama ɓaci, Malam kallo
ɗaya ya yi wa Yaya Inu ya ji gabansa ya faɗi, don haka ya sauke kansa ƙasa.

"Gabaɗaya na tara ku ne domin na yi muku godiya a kan cin mutumcin da kuka yi mini. Ba
malam kuka wulaƙanta ba, ni kuka wulaƙanta. Idan har saboda na ce za mu yi aure da Malam
ne kuka yi haka mu zuba ni da ku, a yau ba sai gobe ba zan yi wa Malam Liman magana bayan
sallar Magriba a ɗaura mana aure." Gabaɗaya shiru suka yi Baba Ibrahim ya ya ce, "Har ga Allah Inno ni ban san abin da ya faru
ba, hasali ma ba na gidan a lokacin da abin ya faru."

"Dama ni ban ce kai ba ne Iro, jikina yana ba ni Inusa ne saboda na yanka zakarunsa na
dafawa malam."
Malam da ya tuna gargaɗin Yaya Inu ya yi sauri ya ce, "A'a Inno ba na jin Inu zai aikata mini
haka."

Inno ta sake ba wa Malam haƙuri, ta kuma ba su umarnin da su ba shi haƙuri tare da biyan
kuɗin sadaki dubu hamsin. Babu yadda suka iya haka suka ba shi haƙuri sannan suka fice.
Suna fita Inno ta aika aka kira mata Malam Liman, bayan sun gaisa ta kawo kuɗi ta damƙa
masa na sadaki. Ta yi masa bayanin duk abin da ya faru, Malam Liman ya yi mata Allah sanya
alheri sannan ya tafi.

Bayan sallar Magriba kuma aka ɗaura auren Inno da Mai Yasin a kan sadaki naira dubu
hamsin. Lokaci ɗaya gari ya ɗauka a kan maganar auren Inno, baƙinciki ya mamaye su Baba
Ibrahim.

"Magana ta gaskiya hankalina bai kwanta da wannan mutumin ba, na ɗauka maganar auren
nan za ta kwana biyu har na yi musu gwajin jini saboda muhimmancinsa. Gaskiya duk kun
jagula al'amarin nan."
Baba Ibrahim ya furta cike da takaici.

"Uwar me gwajin zai yi ne da ka addabe mu da zan can nasara, da tun can da ake yin aure
babu gwajin me ya faru da mutanen baya? Ko shi Baffa lokacin da zai auri Inno an yi musu
gwajin ne? Kai ni ba wannan ne agabana ba, fargabata kada tsohon nan ya sake gangancin
taɓo garkena." Yaya Inu ya faɗa. Baba Ado ya tuntsire da dariyar ƙeta ya ce, "To garkenka kuma ai sai dai kar
a kuma, ba ka ji labarin Inno ta sa an fita da matashin ragonka ba? Ɗazu nan fa aka wuce musu
da shi wai Ali mai tsire ne ya gasa musu..."
Tun bai gama magana ba Yaya Inu ya shaƙo wuyansa jikinsa yana rawa ya ce.

"In ji uban wa?"

Baba Ado ya zame hannunsa yana ci gaba da ƙyaƙyata dariya, jikin Yaya Inu ne ya sake sanyi
don ya san Ado da miskilanci idan ka ga dariyarsa to wata ƙetar ya samu.
Bai iya tankawa 'yan'uwansa ba ya faɗa cikin gidan da sauri, kai tsaye ɗakin Malam ya nufa
don a can yake jin muryarsu sama-sama. Kamar wanda aka jefe haka ya faɗa ɗakin, Yaya Inu
ya yi turus ganin wani shimfiɗeɗen gasasshen nama a gaban su Inno suna reɗa da wuƙa. Ta ci
sabuwar atamfa sai murmushi take, Malam da bai san naman ragon Baba Inu suke ci ba, ya
sake yanko wata shimfiɗeɗiyar tsoka cikin gadara ya tura a baki.

Yaya Inu da ya rasa mafita sai kawai ya zauna a bakin ƙofar ya fashe da kuka, Sai a lokacin
Inno ta lura da shi. Ta washe baki ta ce, "Kai Ɗan Inuna, a duniya me za ka yi wa kuka tun da
kana faranta ran iyaye. Wai dama haka ragon nan ya kiwatu, ni fa lokacin da ka ce mini an taya
shi dubu hamsin na yi mamaki. Ashe-ashe rabon mu sharɓi ganimarsa a daren tariya ta da
babanku ne."


07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[17/12/2024, 19:46] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya
kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA

https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd

Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a

youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻

SHAFI NA TAKWAS

Duk maganar da Inno take yi babu ɗaya da Baba Inu yake ganewa, saboda wata irin juwa
da ya ji tana ɗibansa. Hankali a tashe Mai Yasin ya furzar da naman bakinsa, gabansa yana
bugawa ya dubi Inno ya ce.

"Inno kina nufin wannan ragon da aka gaso mana muke ci ragon Inusa ne?"

Cike da son birgewa Inno ta saki murmushi ta ce, "Ragon Inusa ne, ai sau biyar ana taya shi
yana ƙin sayar da shi, mutumin ƙarshe da ya zo ko sati uku ba a yi ba dubu saba'in ya taya shi."
Inno ta kalli wurin Yaya Inu da har lokacin kuka yake yi kamar wanda mahaifiyarsa ta mutu, ta
kalli Mai Yasin da ya gama firgicewa ta ce. "Na jima ban ci gashin nama da ya yi daɗi kamar wannan ba, ai wallahi Inusa Allah ne kaɗai
zai biya shi saboda ko lokacin da na sa aka fita da ragon ba ya gidan..."
Kukan da Mai Yasin ya saki ne ya katse furucin da Inno take yi, hankali a tashe ta dube shi
haɗe da faɗin.
"Malam lafiya kuwa?"
Mai Yasin ya girgiza mata kai cikin kuka ya ce, "Babu komai Inno, kawai ina taya Inusa jimamin
rashin ragon da ya yi. Gaskiya Inno ba ki kyauta masa ba, me ya sa ba ki nemi jin ta bakinsa ba
kafin a yanka."
Mai Yasin yana gama faɗar haka ya sake ɓarkewa da kuka. Sororo Inno ta yi jin abin da ya
faɗa, saboda yadda ta san shi da son nama ba ta taɓa tsammanin zai faɗi haka ba.
"Malam ai saboda wancan karon na ga ya ji haushin zakarun da aka yanka masa shi ya sa na
ɗauki rago, yanzu da a zo duk bayan kwana biyu muna yanka zakaru ba gara mu yi mai
gabaɗaya ba."

Mai Yasin yana haɗa ido da Yaya Inu ya ga ya yi masa wani mugun kallo, mai ɗauke da
manufar za mu haɗu da kai, sai kawai ya cusa kansa cikin cinyoyi kamar ƙaramin yaro ya sake
ɓarkewa da kuka. Shiru Inno ta yi ta rasa bakin magana, kukan Yaya Inu da na Mai Yasin ya
cika ɗakin. Jiki a sanyaye Yaya Inu ya miƙe yana dafa bango, don ji ya yi wata hajijiya tana
yunƙurin taɗe masa ƙafarsa. A daddafe ya fice daga sashen su Inno ya wuce sashensa, su
Baba Ibrahim suna wurin da ya bar su amma saboda halin da ya shiga ya sa har ya wuce bai
tanka musu ba. Zazzafan zazzaɓi ne ya rufe shi don haka ya shige ɗakinsa ya ja bargo ya rufa,
domin kusan a ƙasa da shekara goma sha biyar wannan ce asara mafi muni da ya tafka.

Bayan Yaya Inu ya wuce sashensa, Baba Ibrahim ne ya shiga sashen Inno ya yi sallama daga
tsakar gida, Inno ce kawai ta amsa masa ya yi gyaran murya sannan ya ce.
"Inno dama wata 'yar magana gare ni idan babu damuwa."
Daga can ɓangaren Inno ta ce, "Na taso ko za ka shigo ciki?"
Baba Ibrahim ya ji daɗi yadda ya ji muryar Inno wasai, don haka yake fatan Allah Ya sa ta ba
shi haɗin kai a game da buƙatar da zai je musu da ita. Ya matsa bakin ƙofar sannan ya ce.

"A'a zan shigo ma, da yake maganar da ku duka za mu tattauna."
Sai da Inno ta amsa masa sannan ya shiga cikin ɗakin ya zauna daga gefe, ganin har lokacin
Mai Yasin bai daina kuka ba ya sa mamaki ya kama Baba Ibrahim don haka ya ce.
"Inno lafiya? Me ya samu Malam?"
Inno ta ɗan canza fuska ta ce. "Wai fa don ya ji na ce ragon Inusa na saka aka gasa mana, shi
ne yake taya shi kukan jimami!" Baba Ibrahim ya yi ƙuri yana kallon Malam, saboda haka kawai
ya ji bai yarda da hujjar yin kukansa ba.

"Inno magana ta gaskiya ba a kyauta wa Yaya Inu ba, ina laifin ma ki sa a ɗebi kaji amma a ce
rago guda ai kuma ya yi muku yawa."
Baba Ibrahim ya furta, don ya san fiye da jinya ma ɗan'uwan nasa yana iya yi saboda
soyayyarsa da abin duniya.
"Mu ajiye wannan zancen a gefe Iro, yanzu me yake tafe da kai."
Baba Ibrahim ya yi jim sannan ya ce.

"AlhamduLillah! Haƙiƙa ina godiya ga Allah (S W.A) da Ya sa haɗuwarmu da kai Malam da
zamo mana alheri. Tun da aka ce harka ta auratayya ta shiga tsakani, to kuwa ta wuce komai.
Amma wani hanzari gare ni ba gudu ba Inno da kuma Malam!"
Baba Ibrahim ya ɗago ya ɗan dube su sannan ya cigaba da cewa.

"Dama maganar gwajin jinin da na yi rannan ita ce na zo zan sake maimaitawa. Don Allah ina
son ka fahimce ni Malam, ba ina son a yi wannan gwajin don wata manufa ta ko saboda ba mu
yarda da kai ba ne. A'a ina son a yi muku wannan gwajin ne saboda a tantance lafiyarka da ita
Inno, saboda kada a cutar da ɗaya daga cikinku ko kuma gudun samun wata matsalar da ba
ma fata a nan gaba."

Tun da Baba Ibrahim ya fara magana Mai Yasin ya haɗe rai, Inno ta dube shi sheƙeƙe ta ce.

"Kai Iro fita daga idona na rufe, yadda yahudanci ya ratsa ka so kake ni ma ka ribace ni ko?
Wallahi tun ranar da na ji kana yi wa Inusa faɗa, a kan yawan haihuwa na fara zargin ka karɓo
kwangilar yahudawa. Kai Iro ka ji tsoron Allah, yanzu lokacin da na auri ubanka akwai wani
tsirfar gwajin jini kafin aure ne? Ni za ka haramtawa sunnar Annabi ina zaune ƙalau?" Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya cikin damuwa, don dama ya san za a rina an saci zanin
mahaukaciya. Shi kuwa Malam zuciyarsa fes, duk da ya san lafiyarsa ƙalau amma shi kansa bai
yarda da sabuwar al'adar da ta shigo ta gwajin jini kafin aure ba.

"Wallahi Inno ba ni da wata alaƙa da Yahudawa kamar yadda kuke zargi, shi wannan gwajin
jinin yana bayyana rukunin jinin da kika ɗauke da shi. Gwari-gwari bari na yi miki bayani, nau'in
rukunin lafiyar jini na gado shi ake kira da Genotype. To kamar yadda muka sani Inno kowanne
ɗan'adanm da Allah Ya hallita, yana tare da wasu ƙwayoyin halitta da suke gudana a jikinsa,
kuma waɗannan ƙwayoyin halittar gadonsu ake yi. Misali idan iyaye suna da nau'in jini mai kyau
sai su haifi yara lafiyayyu, idan kuma aka samu akasin haka sai a haifi yara masu ɗauke da

matsalar amosanin jini wacce aka fi sani da sikila. Bayan wannan gwajin akwai kuma wanda
yake bayyana cututtuka da dama kamar: Ciwon hanta, hawan jini, cutar damuwa (Depression)
sai uwa-uba cutar ƙanjamau (HIV/AIDS) da ragowar cututtukan da ban lissafa ba. A
gwaje-gwajen da ake yi kafin aure akwai cutukan da idan aka same su, ake haƙura da auren.
Akwai kuma wanda ake yin auren sai a bayar da shawarwari."
Baba Ibrahim ya faɗa cikin tattausan lafazi.

"Innalillahi wa 'inna'ilahi raji'un! Yanzu Iro ni ko Malam a cikinmu wa kake yi wa fatan ƙanjamu?
Mu za ka mayar 'yan iska, masu yawon kwararo? Idan na ce kana ƙoƙarin raba sunnar Annabi
ka ce ba haka ba. Yanzu tun da ubanku ya rasu akwai ƙaton da ya sake taɓa mini hannu? Ta
shi ka fice mini tun raina bai ɓaci ba." Inno ta faɗa a zafafe tana nuna masa hanyar fita.

"Don Allah Inno ki fahimce ni, ba ina nufin zarginku nake yi ba. Ita cuta mai karya garkuwar jiki,
ai ba sai an sadu tsakanin mace da namiji ake samunta ba, ana iya ɗaukarta ta hanyoyi da
dama kamar amfani da reza ɗaya, burushin wanke baki, kibiya wacce mata suke kitso, kilifa ta
masu aski, askar wanzamai, wuƙa, abin yankan farce, allura ta asibiti da allurar ɗinki. Duk ana
iya ɗauka da su matuƙar dai jinin mai ɗauke ita zai taɓa abubuwan da na lissafa, wanda ba shi
da ita idan ya yi amfani da su to tabbas zai iya kamuwa shi ma. Inno hanyoyin suna da dama fa,
kuma gwajin jini na genotype yana bayyana rukunin jinin da ya dace su haɗu wurin aure da
waɗanda ba su dace ba. Kin ga mai rukunin jinin AS ba zai yiwu ya auri mai irin nasa na AS ba,
haka zalika mai jinin SS ba zai auri mai SS ko mai AS ba saboda gudun kada su haifi yaran da
za su zo da lalurar sikila, su yaran su wahala haka su ma iyayen su wahala wurin ɗawainiya."
Kallon da Inna take jifansa da shi ya sa ya tsahirta sannan ya ce, "Inno na ga kamar ba ki
gama fahimtar bayanina ba. Ana sanin genotype idan anyi gwajin jini, kuma daga gwajin ake
samun genotypes a jikin mutane cikin nau'i guda uku kamar haka: AA, AS da SS.
AA sune masu cikakkiyar ƙwayar halitta, AS kuma su ake cewa carrier, akwai ɗan rauni a
cikin ƙwayar halittarsu, sai kuma na ukun sune SS masu ɗauke da amosanin jini wato sikila.
Saboda raunin ita wannan ƙwayar halittar ya kai maƙura.
Shi ya sa muke yawan jan hankulan mutane, da su tabbatar da sun yi gwaji jini tun kafin
soyayya ta yi ƙarfi. Muke kuma hankaltar da muhimman abubauwan da ya kamata a lura kafin
aure, idan an duba genotype din sune kamar haka:

Rukunin farko yana nufin mijin, ba biyun kuma yana nufin matar, sakamakon kuwa irin yayan
da za a samu ne.

1. AA +AA = AA, AA, AA, AA (Za a samar da 'ya'ya masu cikakkiyar lafiya.)

2. AA + AS = AA, AS, AA, AS, (Shi ma aure ne mai kyau, kuma babu matsala a lafiyar 'ya'yan
da za a haifa, amma bai kai na saman ba.)

3. AA + SS = AS, AS, AS, AS, (Shi ma wannan auren ana iya yin sa, duk da akwai 'yar matsala
kaɗan a kan 'ya'yan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login